Kishi wani al’amari ne babba. Kuma ɗabi’ace da Allah Ya halicci mutane da ita.
Maza da mata, kuma kowacce mace na da kishi. Matan Annabi (SAW) sun yi kishi.
A’isha (R.A) tana cewa :
Ban taɓa yi wa wata mace kishi ba, kamar Khadija (RA) sai dai su kishinsu akwai ilmi, hikima, da tsoron Allah.
A yanzu kuwa, akwai matsalolin da muke fuskanta da yawa. Saboda zafin kishi dake sanya ayyukan da-na-sani. Da kawo rabuwar aure. Da gurɓacewar tarbiyyar yaranmu.
Domin maganin matsalar zafin kishi. Sai maza sun fahimci ɗabi’un mata. Tabbas mace ba ta son abokiyar zama. Amma fa akwai yadda za a bi da ita.A yi amaryar nan cikin lumana. Haka ma dai mata su fahimci irin ɗabi’un maza. Ba shakka maza suna son mata. A wajensu fa zama da mace ɗaya larura ce. Kuma maza suna da kishi mai zafi har ya fi na mata ma. Duk da yadda wasu mata ke da kunya, daraja. Da kamun kai, har ma da kiyaye abin da zai motsa kishin mazajensu. Amma fa sai kin ji wasu mazan na zafafa kishi, yadda matansu kan rasa inda za su ji sanyi a ransu.
Saboda haka dole ne mata mu yi kaffa-kaffa da mu’amalarmu da ‘yan uwanmu Waɗanda su ka balaga. Abokan aiki da na karatu. Domin ta irin wadannan hanyoyin muke rura zafin kishin mazajenmu.
Maza masu tsananin kishi har iyayenka sai sun nuna ma ba sa jin daɗi. Dole kawai a fifita ra’ayin miji sama da na kowa. An ce zama lafiya ya fi zama ɗan Sarki. In ba haka ba kuwa, kullum babu kwanciyar hankali.
Shi Namiji mai kishi na da daɗi, muddin babu zargi a ciki. Domin irinsu na ƙoƙarin killace matansu sosai. Kamar kai su unguwa. Da damuwa sosai, su dinga kula da al’amarin matansu. Ba irin wanda za ki bar gida. Bai damu da tuntuɓar ki ba. Ko mai daɗewar ki, ko kwanaki ma. A addinance ma ba a son namijin da ba ya kishin matarsa.
Wasu mazan su ne ke haukata mata da gangan. Su ke jefa su cikin matsalar zafin kishi. Za ki ga ƙarfe 1:am wani na waya ko chatting da wata a kan shimfiɗarki. To ko zuciyar katako ce da mace, dole ne fa ranta ya ɓaci.
Ba shakka hakan da ciwo ainun. Amma wai masu juriya irin wannan ba sa kishin mazajensu ne? Tsoron Allah, Natsuwa, da Iya taku kawai . Duk fa haukan da za ki yi, ba zai magani ba. Sai dai ma ya ƙara yin nesa dake. Ya cigaba da harkokinsa. Kawai ki nemo hanyoyin da Za a raba shi da chatting ɗin da ba na aiki ba ne cikin siyasa. Yawanci wasu matan ba raba shimfiɗa muke da mazan ba. Mu bar kaɗaici ya da mu mazajenmu . Ni ko kai ka ce mu raba ɗaki, ba zan iya ba. Zan ce ba na iya barci, dole sai na manne da kafaɗa, hannu ko kan ƙirjinka.
Wasu matan ma su ke manne wa wayoyinsu, su yi ta chatting da ƙawaye, ba sa ma kallon mai gida. Ba sa ɗan tura masa komai. Hotunan Zuciya, furanni, waƙoƙin soyayya, hira. (Chatt, Love pictures, Cards, video shows,… etc).
Wannan dabarun ma za su yi amfani. Sai mace ta zama tana da tasiri wajen mijinta. Ko ta hanyoyin sadarwa na zamani, Ba a bar ta a baya ba.
Wasu matan na zuba kishi har ya ƙetare Shari’a. Wata ta nakasa mijin, ko tai ta bala’i ya gaji Ya sake ta. Ko a kulle ta ma a kurkuku. Shi kuma da aka yi, domin shi ya sake sabuwar amaryarsa. Ko ta hallaka miji ta yiwa kanta asarar duniya da lahira. A garƙame ta a kurkuku tun daga nan duniya. Ta jefa iyayenta, danginta baƙin ciki da gori. Allah Ya raba mu da aikin da-na-sani.
Bai kamata muna ɗaukar hukunci a hannunmu ba.
- Hanyoyin da za mu bi, domin rage zafin kishi
1 – Mata mu dinga duba ƙarin aure nassin Alkur’ani ne da ya fara daga mata biyu. Ubangiji ne ya halatta musu.”Ku auri abin da ya muku daɗi daga mata biyu, uku, hudu….. “.(Nisa’i :3)
2 – Maza ku dinga duba muhimmaci yin adalci.
: “.. Idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, ku auri guda …. “.(Nisa’i:3) Tabbas kwatanta adalci na kawo zaman Lafiya.
3 – Idan miji ya shigo da zalunci, sai ki yi ta masa addu’ar Allah ya shirye shi. Ko ki kai ƙarar sa wajen Allah. Allah Yana karɓar addu’ar wanda aka zalinta.
4 – Nasiha, rarrashi, da amfani da hikima na sa maza su yi nasarar maganin zafin kishi matayensu. Haka kuma mata masu yi wa maza nasiha, ‘yan hikimomi. Har ma wasu na da jarumta. Na ta ya mijinsu neman aure. Haka na janyo musu samun alkharai masu yawa.
5 – Idan abubuwa sun cakuɗe, sun girmama. Sai ki shigo da manya a ciki. Domin a yi maganin matsalolin.
6 – Yawan ambaton Allah, karatun Qur’ani, da ƙiyamul laili na kashe zafin kishi. Yayin da mijinki ke neman aure, amarya, hulɗa da wasu mata da bai dace ba.
5- .Kowacce mace ta san kanta, yadda ko mijinta ya yi mata abokiyar zama, za ta fita biyayya, tattalinsa, kwalliya da iya girki. Haka zai sa ya gane ashe dai shayi ruwa ne. Sai uwargida ta fi amarya matsayi.
7 – Maza su dinga koyon irin kulawa da kyautatawa da mata ke buƙata. A irin lokacin da kake ƙarin aure. Irin su sanar da mace, da gyara mata ɗakinta, da turaruka, da zannuwanta muddin akwai halin haka. Ya kamata mu dinga sara muna duban bakin gatari. Zafin kishi na ƙarewa ne a mutuwar aure, ko aikin da-na-sani.
Na ji wani hadisi Annabi (SAW) ya ce “Ina kashedin ku da kishi, domin shi mabuɗi ne na saki.. “Zai fi kyau mazanmu da mata kowa ya nuna wa abokin zamansa ya ji tsoron Allah.
Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya ce, “Ka so wa ɗan uwanka abin da kake so wa kanka”.
Mace ta kula da haƙƙoƙin mijinta. Su ma Maza su kula da haƙƙoƙin matayensu. Kuma da sanin yadda ake gyara soyayya zai tamaka mana gyara a matsalar zafin kishi.
Danna koren rubutun nan domin samun bayanin Yadda Ake Gyara Soyayya.