Yadda Ake Shafa Jiki Na Musamman Ga Ma’aurata.

0
2619

Shafa jiki yana inganta rayuwar ma’aurata. Domin abu ne dake isar da soyayya. Rashin sa kuma na kawo ƙiyayya da nesanta ma’aurata.

Kowanne mutum yana da abin da ya fi so. Ka so mafi yawa na mutane suna son a shafi jikinsu. Haɗa jiki na nuna ƙauna sosai.

Duba abin da Nana A’isha ( R.A) ke faɗa mana a ƙarshen hadisin nan.

A’isha (R.A) ta kasance tana cewa: “Ya mutu yana tsakanin saman kirjina da haɓata”.
(Bukhari da Muslim).
Masana sun gano cewa: Jarirai da ake yawan ɗaukar su, da rungume su, da sumbatarsu. Sun fi koshin lafiya da walwala a rayuwarsu.

Shafa jiki ko ince haɗa jiki na sanya soyayya ta dinga tasiri. Ma’aurata mu saki jikinmu mu dinga hutawa tare. Ko za ka iya tuna sau nawa kake haɗa jikinka da na matarka? To in ba ka yi , sai ka fara. Ga wani kyakkyawan misali.

A’isha ta ce:” Annabi (SAW) ya na kishingiɗa a kan cinyata, Alhali ina haila, sai ya karanta Qur’ani“.
(Bukhari ).

Ma’aurata da yawa kan ji sun shiga damuwa. Ba sa jin karsashi na soyayya. Ko auren ma ya zama kawai lallabawa ake yi. To yawan shafa hannu, runguma , sumba , kwanciya a jiki. Na farfado da soyayya ya rage damuwa.

Mata da yawa kan yi girke-girke, da kwalliyya, da gyara gida . Domin sanya farin ciki da jin daɗi ga miji. Amma sai ka ga duk ba ta burge mijinta ba. Wasu kaso na Mazaje sun fi ƙaunar a dinga tarairaya jikinsu sama da komai.

In kika haɗa waɗancan ayyuka da shafa jikinsu. To sai su ji ƙaunarki ta cika musu zuciya.

Haka ma wasu mata suke. Shafa jikinsu shi ne ya fi tabbatar musu da soyayya.

Ka tabbata matarka ta zama matashinka. Ka zama mai koyi da Annabi SAW.

HANYOYIN SHAFA JIKI

1 – Kwanciya a jikin Miji/ Mata. A kan ƙirjinsa, da cinyarsa , da kafadarsa.
Hadisi ne a babin taimama: … Wata rana A’isha (R.A) ta ɗora kan Annabi SAW a kan cinyarta, har ma Annabi ya yi barci. Sayyadina Abubakar ya zo yana zungurin ta. Amma sai ta ƙi motsi , Don gudun ka da ta katsewa Annabi ( SAW) barcinsa.

2 – Zama a tare waje ɗaya. A tabarma ko a kujera. Jikinka na manne da jikin matarka.

3 -Riƙe hannuwa tare ana tafiya. Ko yayin da ake rakiya.

4 – Rungumar juna akai-akai ya zama ɗabi’ar Miji da Mata. Daga A’isha (R.A) ta ce:” AbdurRahman dan Abi bakarin Sidiq (R.A) ya shigo, a lokacin ina rungume da Annabi a ƙirjina, ….

5 – Sumbatar juna da yawa.

6 – Tausa nasa warwarewa ta gajiya. Kuma tana sanya jin daɗi .

7- Ana hira ana wasa da yatsun hannu.

8 – Wajen gyara wa mutum kayan da yasa. Ko goge masa datti.

9 – Shafa fuskar matarka tare da faɗin: Allah Ya miki kyau Matata.

1O – Shafa kitson matarka , ko shafa mata mai a kitso : Masha Allah kitso ya miki kyau.
Mace kuma ta dinga tajewa mijinta Gashinsa.

Hadisi ne: Annabi SAW yana itikafi yana zuro kanshi. A’isha (R.A) tana wanke masa, ta taje masa shi.

11- Yi wa miji aski, da shafa Mai, da wankin kafa da dai sauransu.

A karshe dai Ma’aurata su karanci ɓangarorin jiki. Su gano wanda ya fi jin sako. Kuma ba lalle in da miji ya fi so. Ya zama shi ne matarsa ke jin sako ba. Sai ka tambayi matarka ɓangaren jikinta da ta fi so.

Shafa jiki na da muhimmanci sosai. Ya kamata ya zama mun saba da shi sosai. Domin tabbatar da ƙauna a tsakani Ma’aurata.

Dannan koren rubutu domin karanta yadda ake wankan soyayya ko yadda ake shagwaɓa maigida lokacin hutu

Litattafai da aka duba

Kitabu Tayammumi
Kitabul haidha
Babus swak
Mukhtasar Sahihul Bukhari.

Physical touch
The 5 love languages
Gary Chapman

Tasirin Soyayya
Amina Yusuf Gwamna

labarin da ya wuceYadda Ake Ayyukan Gida Domin Taimakon Juna
Labarin na GabaYadda Ake Bread-egg Toast A Sauƙake
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.