Yan Mata Masu Shirin Yin Aure Da Amare Da Kuma Masu Sabon Ciki Karkuga Kamar Na Takura Muku Da Maganar Folic Acid

0
31

Kafin ki kai ga ɗaukar ciki (juna biyu) da wata guda ko bayan ta tabbata ciki ya shiga lallai a watanni ukun farkon nan na cikin ki tabbatar kin samo sinadarin (FOLIC ACID 5MG) kin riƙa sha tun wata ɗaya ma kafin ki ɗauki cikin, domin kaucewa zance da karkata-kai ko kuwa arba da abinda zai sanya damuwa tare fantsamar labarai tsakanin mutane na abin haihuwarki.

Domin yana daga cikin illolin ƙarancin folik asid haihuwar yara masu nakasa ko kuwa wasu irin munanan suffofin halitta da babu wanda zai so a sha wahalar goyon ciki karshe a haifo yaro ko yarinya wanda wani ma bazai iya ƙara kallonsa ba inya kalle sa sau ɗaya.

  • Akan haifo yara suzo da ƙaton ƙari ko tabo a gadon baya. ko yankakken leɓe ko datsatstsen dasashi (Encephalocele, spina bifida, cleft lips or cleft palates)
  • Wani ka gansa da ƙaramin ƙoƙon kai, ko mitsi-mitsin kunnuwa. (microcephalic with low set ears)
  • Wani a haifosa da ƙaton kai, wani da fuska kamar aljani (hydrocephalus abd dysmorphic facie)
  • Ko jaririn da baida dubura ko wajen fitsari. ko me yatsu shida zuwa bakwai da naniƙaƙƙen hanci.
  • Wani a haifosa da ƙatoton ƙari a ƙeyarsa, cikinsa, goshinsa, kirjinsa ko gadon bayansa. (teratoma, myelomeningocele)
  • Wani yazo kayan cikinsa a fili a bude, kamar yadda yan kwanakin nan gasu nan muna ta gani, wanda galibi ko anzo asibiti karshe macewa suke. (Gastroschisis, Omphalocele).
  •  Ko ƴan gujil-gujil ɗin gaɓoɓi da dogon ƙoƙon kai.
  • Ko yaran da kan zama wasu gaulaye, ko masu karkataccen wuya, rashin daukar karatu, kurumta, da sauransu.

Da de sauran tarin matsaloli, wanda galibi ƙarancin ko rashin shan sinadarin folic acid ne ya zamo sila

Domin karanta dalilin Rashin Jini A Jiki (ANEMIA) Danna nan

Wasu lokutan a asibiti akan ba mata su kyauta, amma rashin sanin amfaninsu yasa sai suje sui watsi dasu.

Shi wannan sinadarin yana da amfani ne a watanni uku na farkon ciki kacal domin a lokacin ake haɗa halittar jariri, sannan lokacin ne duk waɗancan illolin kan faru wanda da zarar ciki ya wuce watanni uku to shansu baida wani amfani domin lokacin halitta ta kammala in yaro ya sami matsala ya riga ya samu kurum, inbai samu ba nan ma bai samu ba.

Sanin hakan yasa musamman masu shiga gidan aure a karon farko wato yan matan da aka tsaida ranar biki, da ma bazawarar da zatai kome ko wani auren…indai akwai haihuwa a plan dinsu toh tun wata ɗaya kafin ɗaurin auren ya dace mace ta fara shan; FOLIC ACID Me 5MG kullum ƙwaya ɗaya. Insha Allahu da wuya kaga ankai ga haifo jariri me nakasa. baki daya ina jin banda abu da yai tsada na Naira ɗari biyu “N200” ada in mace ta sayo saita shekara tana sha bai ƙare ba, ko yanzu na tabbata Folic Acid na “Naira 300” ya ishi mace tai fiye da wata uku ma tana sha, bawani magani bane me tsada. 

Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan

Shansa zai taimaka tare da kaucewa zuwa aita camfe-camfen banza, ana bin yan tsubbu da bokaye neman lafiya, ko a riƙa mayu ne  suka jefi cikinki, ko a haɗaki gaba da wata ace ita tayi miki asiri, ko ariƙa kin haifo ɗan ruwa saboda kin rika debo ruwa da daddare a borehole ko rijiya dadai sauransu…. alhalin munanan suffofi ne da ko mayu basu isa su iya kirkirarsu a mutum ba.

Sannan haka yaro tun yana jariri iyaye suita faman zaryar asibiti ana cacar kudi, kuma su kansu ƙunshe yaron zaka ga suna yi saboda damuwa…bama sa so agansa, ballantana kuma gaba inya tasa haka yara babu me son yagansa cikin abokan wasan sa, ko a maida yaro matoni.

Shiyasa ako da yaushe ilimi abu ne me daɗi musamman kuma ace inka yaɗasa cikin al’ummar da kake da ƙwarin guiwar zasuyi aiki dashi.

Kusan da cewa Haihuwa A Gida Ba Jarumta Bane Kuskure Ne Danna nan domin karanta dalilai

Ku nemi wannan magani ga masu shirin amarcewa kusa, ko wacce take da sabon cikin da bai wata uku ba, wacce ko tasan ta taɓa haifo yaro me nakasa toh shekara guda ma ya dace tayi tana sha har zuwa ta sami wani cikin tai watanni ukun farko.

Idan ciki ya wuce wata 3 shansa baida wani amfani, already halittar sassan jiki ta kammala ba abinda zai canza

labarin da ya wuceRashin Jini A Jiki (ANEMIA)
Labarin na GabaCiwon Suga.(Diabetes)