Rashin Jini A Jiki (ANEMIA)

0
33

Kusan kullum ka shiga asibiti sai ka samu ana sa jini wa marasa lafiya dayawa. Hakan ƙalu bale ne babba ga al’ummar mu. Rashin jini yafi takurawa mata da yara yan kasa da shekara 5 da kuma tsofi masu fama da dadadden rashin lafiya. WHO ta wallafa cewa, a kalla yara kashi 42 cikin dari  da mata kashi 40 cikin dari ne suke fama da rashin jini a duniya.

Akwai abubuwa dayawa da suke kawo rashin jini. Rashin jinin ma kala kala ne. Mafi yawa a wannan kasata Nigeria bazai wuce mai alaka da abun da muke ci. Rashin cin ingantaccen abincin da ya kunshi isashshen sinadarin iron da sauran vitamins da mineral wanda suke taimakawa wurin habaka yawan jini a jiki.. 

Mutane dayawa za suyi noma sosai amman sai su sayar gaba daya su karbi kudin su biya buƙatun su na wani lokaci,  su bar iyalan su cikin yunwa da wahala. Sai mutum ya noma wake ya sayar gaba daya,  yanzu kuma a gidan shi ana shan bakar kuka babu nama,  babu waken. Haka gyada,waken suya,ridi,alkama,shinkafa,acca,wani har zogale yake dashi amma na sayarwa ne bana ci a gida ba. 

Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan

Rashin jini na haifar da matsaloli masu hatsari sosai,  daga cikin alamoninta da illarta

Akwai:

  • Ciwon Zuciya
  • Karya gakuwan jiki
  • Numfashi sama sama
  • Yawan kasala
  • Jiri
  • Ciwon kai
  • Sanyin jiki ( ido,jiki,bayan farce suyi fari fat) 

In ana jin wasu daga cikin alamomin nan aje asibiti don bincike mai kyau da inganci.

Abincin da suke taimakawa wurin karin jini suna daya amman wanda suka fi sun hada da:

  •      Nama 
  •      Fruits  
  •      Ganyayyaki musanman zogale,ugu. 
  •      Wake;  farin wake da waken suya.

Zogale ana sarrafashi ta hanya daban daban, ana miya,  gwate/fate,  kwado ana iya shan ruwa.

Kusan cewa Haihuwa A Gida Ba Jarumta Bane Kuskure Ne Danna nan domin sanin dalili

Ugu ma haka,  ana iya miyarshi, ba dole matsewa a hada da maltina ne kadai hanyar amfani da shi ba.

Maltina da madara ba maganin karin jini bane, kasha kaji dadi dai malam. In kasha tabbas daka ji dan garau na wani lokaci saboda sugar content na maltina. Duk jirin da su dan sauka amman fa zasu dawo. Yana da amfanin shi amman banda karin jini,  sai dai zai iya taimakawa in ya hadu da sau ran sinadiran.

A kula da mata musanman masu ciki da shayarwa da kuma yan mata( rashin jini na iya kawo daukewar jinin alada) da yara harda tsufin mu,  wurin samun in gantaccen abinci.  Allah ya kara mana lafiya.

Domin karanta cikekken bayani akan Ƙaiƙayin Matsematsi (Jock itch) Danna nan 

labarin da ya wuceƘaiƙayin Matsematsi (Jock itch)
Labarin na GabaYan Mata Masu Shirin Yin Aure Da Amare Da Kuma Masu Sabon Ciki Karkuga Kamar Na Takura Muku Da Maganar Folic Acid