Haihuwa A Gida Ba Jarumta Bane Kuskure Ne

0
16

Jiya akwai wata baiwar Allah da ta rasa ranta lokacin aka kai ta cikin asibiti domin haihuwa bayan an sauko da ita daga abin hawa kafin akai ga shigar da ita dakin haihuwa,wannan mata kamar yadda bayana suka zo

  • Haihuwar fari ce
  • Ta dauki tsahon lokaci tana nakuda a gida 
  • Ta zubar da jini sosai a gida

Munyi imani rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah, amma kamar yadda bindiga keda hatsari ga rayuwar mutum haka wannan abubuwa 3 keda hatsari ga rayuwar mace mai ciki idan ta zauna haihuwa a gida, kuma ko tantama babu sune suka yi sanadiyar rasa wannan baiwar Allah.

Da yawan mutane na da tunanin cewa sai idan da matsalar za aje asibiti a haihu wanda ba haka bane, duk lafiyar ciki zai iya zuwa da matsalar da ba’ayi tsammani ba daga mahaaifiyar ko daga abinda za a haifa wanda idan matsalar a gida ta faru kafin a kai ga asibiti tayi illar da ake gudu cikin gajeren lokaci  ba kamar idan a asibiti ta faru ba akwai ma’aikatan a kusa da za suyi kokarin kawar da wannan matsalar.

Domin sanin menene Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo Danna nan

Misali.
  •  Idan aka haifi jariri ya kasa yin numfashi har ya kai tsahon mintina 4 a haka ba tare da anyi wani abu ba, ba dole ba, amma zai iya samun nakasar ƙwaƙwal ta har abada.
  • Idan mace ta zubar da jini fiye da kima a gida,  kafin  ayi shawarar  kawo ta asibiti, sannan nemo abin hawa da tsahon tafiya zuwa asibitin, sai kuma nemon wanda zasu bada jini, sannan a dauka,wannan bata lokacin ya isa mace tsa rasa ran ta kafin akai ga kara mata jinin.

Wannan misalai sun isa mu fahimci amfanin zuwa asibiti don haihuwa da tasirin lokaci wajen kaucewa matsala.

A karshe ku sani, kusan 90% na matsalolin dake haddasa mutuwar mata masu ciki, abubuwa ne da za a iya kare faruwar su cikin sauki.

Bai kamata mace ta rasa ran ta ba a kokarin ta na kawo wata rayuwar duniya

Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan

labarin da ya wuceAllurar Tsarin Iyali Ta Maza (Male Family Planning)
Labarin na GabaƊabi’ar Gyaran Jiki A Yau, Shin Ina Hakan Zai Kai Mu