Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo

0
29

Cutar dundumi ɗaya ce daga cikin larurorin dakan shafi idanu,wannan larura ce ta dakushewar kaifi/ƙarfin gani, yanda mutum shi akaran kansa ke tabbatarwa da kansa yana da larurar domin baya bukatar zuwa wajen likita yin gwaji kafin ganota.

Masu wannan larurar galibi in sun zo wajen likita sukan ce likita gani na baida kyau,idona ina jin kamar an zubamin mai acikin sa,dususu nake ganin abubuwa ba irin tar-tar ba kamar da bawai duhu mutum yake gani ba a’a yana ganin komi fes saidai ba tar ba, abubuwa musamman manya kamar motoci,gini,ko wani symbol duk yana ganinsu normal,amma kuma bai iya ganin rubutun jikin symbol ɗin fes-fes musamman in ƙanana ne bazasu karantu da kyau ba,zai iya ganin sun harhaɗe musamman in kwai yar tazara.

Wani lokacin sukan gani da kyau idan rana ta take,toh amma in yamma tayi musamman gefin magriba duhun nan nasa ganin nasu yai dususu sosai har sai daren ya taho anyi sallar magariba sai kyawun ganin nasu ya qaru,wanda ke da wannan larurar nasan zaifi fahimtar me nake bayani da kyau.

Domin karanta Amfanin Ruwa Da Lafiya Danna nan 

Jiya nasa wasu hotuna inda nake tambayar tsakanin “A” da “B” wanne yafi fita fes? Inda dukkan masu gaskiya batare da son raurawar zuciya ba suka tabbar da hoton “A” yafi “B” fita, wanda tabbas hakan ne, ai baka buƙatar ma yin wani tunani abu ne a fili, kai da gani kasani.

Don haka wanda suka zaɓi “B” bamu san meke damun idonsu ba, ƙila ko don ni nace “B” shiyasa suka zaɓi su bar gaskiya su ma su rufta rami

Nayi wannan tambayar ajiya ne kafin kawo wannan karatun don kowa ya fahimta. sashin ‘A’ ɗin shine yadda mutane masu “Normal vision” wato kaifin gani ke kallon abubuwa, yayin da shi kuma “B” ɗin tamkar hakane masu larurar dundumi ko gani hazo-hazo (blurry vision) ke ganin abubuwa, wato ga abin a haskake saidai ba fes ba kamar dai hotunan jiya da kuma na ƙasa jikin hoton ƙasan post dinnan.

Ita Wannan Larura Ta Rarrabu Zuwa Muhimman Gidaje Guda Biyu:

(1) Mai ganin hazo-hazo,dundumi-dundumi ko garara-garara daga nesa, wato “short ko near sighted” a turance,ko ince MAYOFIYA a yaren likitanci (myopia)

(2) Mai ganin hazo-hazo,dundumi-dundumi ko garara-garara daga kusa,wato “long ko far sighted” a turance,ko ace HAIFAROFIYA a yaren likitanci (Hyperopia).

Domin karanta matsala da maganin Saurin Inzali (Premature Ejaculation) Danna nan

Dukkan biyu dinnan abu iri guda idanunsu ke nuna musu. saidai

MAYOFIYA: Masu wannan su suna iya ganin duk abinda yake kusa dasu fes wanda nisan sa dashi bai wuce taku goma ba “10 feet” yana iya karatu da rubutu normal,inda matsalarsu take kurum in suka kallo abinda ke nesa sai suga baya fita sosai,ko fuskar mutum ce basa iya ganinsa fes sai ya matso kusa,haka ko tv suke kallo saidai su zauna agaba kamar dai yadda hotunan nan suka nuna. Yayin da shi kuma me.

HAIFAROFIYA: Suna iya ganin duk abinda ke nesa fes-fes kamar wata daren 14, amma kuma in abun kusa kusa dasu yake dab basa iya gani da kyau,wato me wannan matsalar shi abinda ke nesa kurum yake iya gani da kyau,wadannan sunfi shan wuya wajen karatu a littafi ko sarrafa wayoyin hannu domin baƙaƙen har haɗe musu suke, kaga mutum nata takure ido, har idanu suke zafi.

Shiyasa galibi za kuga malamai da medicated glass, ko manyan yan boko har ariƙa farar paper ta cinye musu ido, ba’a gani sai ansa glass.

Wasu zasu iya ma komi batare da glass ba toh amma zarar sun dau littafi to sai sun nemosa sun saka, shiyasa wasu sai zasui karatu suke sakawa.

Meke Haddasa Matsalar

(1) Wannan matsala takan bi cikin family wato ya zamto gado ce akai daga iyaye da kakanni,shiyasa sau tari koda a finafinan turawa zaku ke ganin yara ƙanana sanye da tubaran ƙara ƙarfin gani wato medicated glass, haka muma anan bazaku rasa ganin yara masu sanya glass ba kullum, cikin manya kuwa wannan kusan kowa ya gani, kwai yan mata da Maza yan kwalisa ma kuwa amma duk suna sanya glass ko yaushe saboda ganin su, prescription glasses ne ballantana iyayen mu dattawa ko manyan malamai.

(2) Canzawar girman ƙwayar ido wato eyeball, ta yadda tai girma ta kuma tsuke takai ga ko ido ya kallo abu wannan abin bai tsirgawa har cikin retina saidai ya yanke dab da tsayin da ya saba tunda kwayar idon ce ta matsa baya, shi kuma karfin yadda ido ya dauko abin bazai iya ƙetare yadda ya saba ya isa can ba,shine abin ke yankewa kaga dususu.

(3) Kwai yawan zama cikin daki musamman inda duhu kwana da kwanaki babu fita aga rana saidai kallon screen ko yaushe, wannan ma na taɓa ido,lokacin covid da akai lock down da yawa sunyi progressing zuwa myopia saboda zaman cikin daki 24/7,kuma shyasa galibi a wanda suka je prison ake cewa ansasu a ɗakin duhu zaku ga wasu in sun fito suna samun matsala da ganin su.

Karanta cikekken bayani game da Saurin Inzali (Premature Ejaculation) Danna nan

(4) Shekaru, eh mana daga sanda aka ba 40yrs baya karfin gani galibi kan canza, saidai wani canjin yafi bayyana sosai bayan an cimma 50yrs.

(5) Cuttukan dake bin sassan jiki wanda akai wasarairai dasu,wato hawan jini da ciwon sugar infact a yanzu galibi in patient suka zo da korafin idanu basa gani sosai sai dususu musamman in sun shiga rana yin gwajin sugar wajibi ne, da yawa diabetic ce har ta fara lalata musu idanu sun makaro basu sani ba. Haka ma daɗaɗɗen hawan jini da ba’a shan magani da kiyaye su gishiri da magi a abinci.

(6) Sai kuma hawan jinin ido wato glaukoma, da kuma cin ruwan idanu wato fafiladema.

Wannan sune muhimman dalilai a wasu kuma baka iya gano dalilin kai tsaye.

Maganin Matsalar Shine

Abu ne mai sauƙi, ana zuwa aka auna idon mutum da karfin ganin nasa shikenan sai a yanka masa glass dai dashi,an warware matsalar angama,domin karka dauka duk masu sanya medicated glass iri guda ne, a’a ba haka bane,kowa karfin ganinsa daban, wani ma baya bukatar glass sai zai karatu ko tuƙi.

Haka karka dauka me sanya glass makaho ne kurum refractive error ne inya sanya wannan glass din ya fika gani da kyau kai wanda bakasa glass din,ko tsoho karka kuskura ka raina sa ganin yana sa glass kace zakai masa wayo kar yake kallonka, saidai kai nasara ba akan baya gani ba, a’a sai akan ƙwaƙwalwarsa baya iya tuna abubuwa saboda tsufa.

Wanda kuma basason sanya glass akwai contact lenses shima kamar glass sai an auna idon, wanda da yawa har celebrities sun fi ga contact lenses tunda shi acikin idon za’a manna shikenan, har me kala da zai canza kalar idon zuwa blue ko gray duk akwai.

Domin karanta Dalilan Da Yake Kawo Rashin Zuwan Jinin Al’ada Ga ‘Ya Mace Shiga nan 

Haka nan akwai LASER SURGERY in bakason sanya komi, saidai shi yana da tsada, duk ido ɗaya yakan kai dubu ɗari shida zuwa milyan da ɗaya, shikenan sai a gyara, saidai kowa da yadda yake iya ganin results din, galibi anfi yiwa wanda basu kai shekara 35 ba.

Glass dai shine mafi sauki da arha, ku dubi hoton ƙasa yadda ta cikin glass komi yake ƙar-ƙar amma ta gefe inda ba tubaran ba dususu bama ka iya gane wasu abubuwan.

Masu ciwon sugar da hawan jini, bayan anyi control dinsu wasu ganin su na dawowa ya gyaru.

Illar Ƙin Daukar Mataki Ga Masu Larurar

Idan ka sami kanka da larurar karka bar idanunka haka kaita wahala kana takure su har su riƙa zafi da ƙaiƙai, lallai kai ƙokari kaje kaga likita kuma kabi duk abinda ya baka zaɓi,ƙin sanya glass da cigaba da zama haka shike haddasa wasu hatsarurrukan a titi saboda direba bai gani sosai.

Hakanan akwana a tashi zaka haɗu da strabismus wato jijiyoyin idonka zasu saki saboda halin matsin daka riƙa sasu,don za aga ƙwayar idon mutum ta waskace abinda ake kira harar garke, kaga ga inda mutum ke nuna ma amma inkana kallon ƙwayar indonsa inda take kallo daban, wanda matsala ce hakan, ai bazaka so a rashin sanya glass ko contact ka zamo haka ba.

Ko kuma illa mafi muni hawan jinin ido wato Glaucoma wace zata faru akwana atashi saboda matsin da ka riƙa da idon, wannan matsalar ita ke maida mutum makaho na dindindin har abada,kuma sai an riƙa turama allura a cikin ido jefi jefi tare da bincikar idon, kullum sai kasa magani, kuma kazo kasa glass ko baka so,don haka ba wanda muke mas fatan haka, shiyasa gara ai abinda ya dace tun farko.

Ina mai tabbatar muku kafin ma a yanka glass sai anyi gwajin glaucoma dole ne don kar azo ko ta fara samun mutum kila bai zo neman glass da wuri ba,saida yaga ba dama, ganinsa ya ɓaci da yawa.

Domin karanta bayani akan Hyperstimulated Nervous System Danna nan 

Shiyasa wasu wanda a kaiwa glass batare da screening me kyau ba na glaucoma daga baya kan dawo su koka cewa ganinsu ya ƙara raguwa,bisa tunanin ko glass ne amma a zahiri glaucoma garesu.

Shin Glass Na Ƙara Lalata Idanu:

Magana ta gaskiya karya ne,ba inda don kana sanya glass za’a ce ganinka na kara lalacewa, na gaya muku hawan jinin ido ake tsoratar wa ma wanda suka zauna haka. Kuma babu wasu shekaru da sai ankai za’a sa matukar kwai buƙata, wasu tun suna yan shekaru biyu haka suka taso suka ga kansu, kuma har mutuwar su wasu ahaka suke rayuwa da glass, wanka da bacci ne kurum basa yi dashi.

Kunga glaucoma ɗinnan inkai wasa yadda kaga ana ɗauke wutar nepa duhu ya wanzu kai tsaye haka wataran mutum zai iya naimar ganinsa ya rasa,ya makance, kuma ba wata alama kafin faruwar hakan, kana iya kasancewa da ita baka sani ba,musamman inkasan kwai tarihin matsalolin idanu a family ɗinku ko makanta ai hattara.

Medicated glass muddin kaje ga kwararren likitan idanu (Ophthalmologist) sai yai ma screening ma zai yanka ma daidai da ganinka. Illa iyaka tunda dai kullum ƙara girma muke, shima prescription din glass din zaike canzawa tunda ba natural kwayar idon bace, shine zaku ga ahankali ahankali wani yana canza glasses gwargwadon saurin canzawar idon. Kila wannan ake ganin kamar ko ganin ke canzawa.

Kusani ba a glass ɗaya permanent galibi, duk da wasu in akai musu guda shikenan har karshen rayuwa,wani sai zai karatu ma yake buƙata don normal vision garesa, kurum refractive yake fuskanta,wani na iya shekara 5 zuwa sama da glass ɗaya.

Idan kuma mutum nada halin biyan surgery kamar su PRK bayan angwada anga candidates ne ya cancanci aikin shikenan.

Shin Duk Me Sanya Glass Wannan Matsalar Ce Kenan?

A’a kwai saurin larurori masu jawo a sanya glass amma de kaso 95% cikin ɗari wannan matsalar ce dana tattauna

Fatan bayanin ya ankarar, ya kuma fa’idantar duk da yai tsayi da yawa.

Karanta cikekken bayani akan HIV/AIDS 

labarin da ya wuceAmfanin Ruwa Da Lafiya
Labarin na GabaGyanbon Ciki Wato Ulcer Disease