Warin Baki (Mouth Odour)

0
29

Warin baki,abu ne me wuyar faɗi ga aboki ko wani da ake jin nauyinsa,to sai dai dole akwana atashi mutum zaisan yana dashi.akwai lokutan da dole akan ɗanji baki ya canza wanda canjin ka iya zama normal musamman in ana axumi ko anjima ba’a sa komi a baki ba

Toh sai dai in warin ya zamto koda yaushe akai-akai da har yakai yana hana mutum sakewa toh mahimmin abu shine ai ƙokarin gano abinda ke haddasa hakan sai a magance shi domin ta haka ne za’a iya rabuwa da matsalar.

Wasu lokutan ba rashin brush bane ko rashin tsafta bane kurum kamar yadda mutane kan ɗauka

Abubuwan Da Suke Kawo Warin Baki

(1) Da daɗɗiyar cutar ulcer, in mutum ya jima dauke da ulcer batare da maganceta ba, hakan nasa warin baki ko numfashi wanda ke tasowa daga can cikin uwar hanji tunda gyambo ne dama,shiyasa akan kirata da gyambon ciki tunda ko gyambon dake waje yakanyi wari ballantana na can ciki,  wurin da iska bata ratsawa.

Domin sanin menene Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo Danna nan

(2) Haka nan toshewar kofofin salivary gland wato bututun sashin dake samar da miyau abaki sakamakon tsakuwa data toshe (salivary stones) hakan yana sa warin baki sosai

(3) Haka ma samuwar tsakuwoyin tonsils wato tonsils stones dake faruwa sanadiyyar abincin dakan makale abaki da hakoran mu bayan gama cin abinci, inda a hankali yakan haɗu da kwayoyin cutar bacteria a bakin ya haddasa wannan tsakuwar dake haddasa warin bakin mara daɗi wanda har numfashi haka za’a ji yana ɗoyi.

(4) Haka ma matsalar shigar ƙwayoyin cuta ramuka ko kogunan ƙashin fuska (sinuses) dake ƙasan hanci suna haddasa (sinusitis) wato rauni agun, kaji harta hanci mutum wari yake gami da ciwon kai ko ciwon fuska. 

(5) Haka yanayin abincin da mutum ke ci akai akai irinsu albasa ko tafarnuwa batare da tsaftar baki me kyau ba. 

(6) Ɗabi’ar shan ababen zaƙi kamar tea empty ko yaushe, chocolates, candy, coke da lemukan gwangwani dana roba. In ba’a tsaftace baki da kyau tare da amfani da “tongue scraper” ana karce saman harshen wanke shi bayan anyi brush to ana iya wayar gari da warin baki akwana a tashi.

Domin karanta matsala da maganin Saurin Inzali (Premature Ejaculation) Danna nan

(7) Ko kuma idan mutum nada kogon haƙori sakamakon abincin dake shiga ciki ya maƙale nan ma yana iya haddasa warin baki

(8) Haka zalika rashin iya wanke baki koda ana yi kullum, shima brush din iyawa ne, don haka in ba a sakuce ko ina da kyau ana iya wayar gari da matsalar.

(9) Haka ma idan mutum na kwanciya bacci batare da wanke baki ba bayan yaci wani abu komi kankantarsa koda kuwa biscuits ne kada araina, wannan bama warin baki ba hatta miyawun bacci na daga abinda ke kawosa wato kwanciya batare da cikakken tsaftar baki ba.

Matakan  Ɗauka

(1) Idan tsakuwoyin stones ne dole sai anhuda anciresu, sai dai wannan aikin likita ne domin ba ganinsu ake ido da ido ba likita ne yasan mazauninsu a bakin, warin bakinsu yafi hamami in sune kamar anbude irin tukunyar gas dinnan haka zakaji bakin mutum.

(2) Idan rashin yin brush da kyau ne toh ya dace agyara.

(3) Idan hakori me kogo mutum garesa yaje a wanke acike kogon ko acire hakorin in bazai ciku ba, shikenan anrabu.

(4) In wani abu mutum yake ci toh sai ya kaurace masa musamman lokacin kwanciya bacci, karka ci komi awa 2 kafin yin bacci inba ruwa ba. 

(5) Wanke baki da ruwan sinadarin hydrogen peroxide irin wanda ake sayarwa don wankin ciwo, bayan antsiyaya anɗan qara masa ruwa kaɗan ankashe zafinsa sai ai amfani dashi ya zamto ana kurkure baki dashi sau 2 ko 3 ayini… yakan taimaka wajen rage matsalar idan har dalilin kwayoyin cuta ne.

(6) Tauna kanumfari kamar kwaya 3 yana sa aji saukin abin musamman wanda hakan ke hanasu sukuni.

(7)  Ko kuma tafasa kanumfarin kwaya 7 zusa sama a wadace da ruwa daidai misali arika kurkure baki da ruwan ana zubarwa ahankali, ake yi safe da yamma zuwa wani dan lokaci, musamman ace ana ƙarawa da gishiri acikin ruwan, ya danganta da tsananin warin da ake ji. 

(8) In ulcer ce ai maganinta itama, sannan ake brush kullum kafin a kwanta.

(9) Haka in “SINUSITIS” ne da hatta mutum shi kansa yana jin inya buso iskar hancinsa ya shaka tana warin ga ciwon kai toh shima yaje ga likita abashi magani a warkar da abin.

(10) Ko amfani da apple cider vinegar wajen kurkure baki safe da yamma inba kanumfari duk yakan taimaka.

(11) Hakama amfani man olive azuba arika kurkurawa tsawon minti 20 a baki kafin a zubar, hakan ajere akai-akai zai tallafa .

(12) Hakama amfani da baking soda wajen wanke baki safe da yamma ko duk bayan sanda aka gama cin abinci a madadin amfani da man goge baki.

(13) Sai canza brush akai akai kada ya ke wuce wata 3 ana amfani da brush guda.

(14) Koyon halayyar zuwa arika wankin hakora a clinics na dentist duk bayan wata 6 kimanin sau 2 a shekara zai taimaka, har lafiyar idanu da kunne saita ƙaru, basai me ciwon hakori ba wannan zuwa flossing abu ne da akeso ga kowa

Domin karanta Menene Amfanin Motsa Jiki Danna nan 

labarin da ya wuceMenene Amfanin Motsa Jiki?
Labarin na GabaYadda Zaka Bada Agajin Gaggawa Ga Wanda Ya Sha Kananzir (Kerosene)