Illar Wayar Salula Guda Goma (10) Ga Lafiyar Jiki

0
34

Wayar salula dai  wata aba ce da ake kiran ta da suna handset ko wayar hannu,ta kasance fasahar da aka samu a karni na 20,wayar salula ta zamanto wata fasaha ce wadda ta mamaye ko ina a cikin duniya,birane da  kuma kauyuka.

Masana kiwon lafiya sunyi bincike sosai su kace duk da amfanin da wayar salula ke da shi ga al’umma,har ila yau tana kuma dauke da wani abu wanda mai cutarwa ne ga rayuwarsu,da take iya yiwa lafiyar bil’adam.

Domin karanta Alamomin Cancer Danna nan

Ga Kadan Daga Cikin Illolin Wayar Salula Ha Jikin Dan Adam:

  1. Cancer: Masana kiwon lafiya sun bayyana cewar duk lokacin da mutun ke magana kimanin hyper-microwabes 9000khz na garzayawa ƙwaƙwalwar shi, wanda kuma shine ya kan haddasa illolin masu yawa da suka hada da kara yanayin da ita ƙwaƙwalwar da 1°C wanda kan iya haifar da cutar kansar ƙwaƙwalwa.
  2. Sleep Disorders: Wannan sanin kowa dadewa amfani da ita wayar salula da mukeyi ta hanyar chating ko kira yakan sa mu dade bamuyi bacci ba cikin dare yawaitar yin haka har ta sabawa ƙwaƙwalwar mu abin yazama jikin mu. wani bincike ya nuna awa 2 kafin baccin na kallon fiskar waya yana shafar bacci mai lafiya sannan yahana hutu mai dadi sakamon hasken wayar da kagama daukar lokaci kana kallo.
  3. Increased Accident-risk: Yana ƙara yawaitar hatsari,binciken hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta nuna cewa daga zuwan waya zuwa yanzu hatsari ya karu fiye da kashi 3 zuwa 4 kafin wayar salula tazo,yayin da mutum yake danne dannen wayar salula tana dauke masa hankali akan hanya,har yakai ga accident.
  4. Obesity: Bincike ya nuna cewa Yana kawo matsanancin ƙiba mara amfani saboda karancin motsa jiki sakamakon yawan ƙwanciya ko zama ana  amfani da ita wayar kamar chatin.
  5. Hearing Impairment: kira a wayar salula samada awa daya (60 minutes) a kunne yana rage lafiyar ji,yin waya yayinda take yin chaji yana kashe kunne gabadaya in an dauki tsawon lokaci anayi.
  6. Eye Problems: Yana kawo matsalar ido, bincike ya nuna yawan dadewa ana amfani da ita wayar salula yana iya haddasa cutar ciwon ido,saboda haske da “screen” na wayar ke samarwa,ba wai ga ido kawai hasken na screen ya tsaya ba, yakan kai ga jijiyoyin ido daganan kuma sai ya rasa zuwa  cikin ƙawƙwa.
  7. Infertility: Rashin Haihuwa,bincike ya nuna sinadarin radiation frequency dake fita daga wayar hannu ko komfuta musamman yawan saka wayar aljihun wando ko dora komfuta a kan cinyoyin kafa biyu yana kashe ko rage ƙarfin sinadaran haihuwa (sperm).
  8. Infection: Wani bincike ya nuna wayar salula na dauke da Kwayoyin baktriya fiye da ban daki (toilet) sabida yawan gaisuwa da mutane sannan ka tana shi da hannun ka kafin ka wanke,wassu ma suna tabawa sannan kazo kaci abinci da hannun hakan nasa ƙwayoyin cuta su samu hanyar shiga jiki.
  9. Skin Allergies: Wassu daga cikin wayar salula musamman bakckberry suna dauke da sinadaran nickel,chromium and cobalt wanda yakan kawo kaikayi da kurajen fata ga wassu mutanen.
  10. Stress : Yawan damuwa,bincike ya nuna daukan lokoci ana amfani da wayar salula tana kawo chanza taswizar ƙwaƙwalwa wanda hakan zai iya kawo stress.

Domin karanta Dalilin Shanyewar ƙafa Bayan Allura A Ɗuwawo Da Yadda Za A Magance Danna nan

labarin da ya wuceKa San Dalilin Shanyewar ƙafa Bayan Allura A Ɗuwawo Da Yadda Za A Magance
Labarin na GabaNa Kan Wuni Cikin Kasala A Duk Sanda Nai Jima’i Ko Inzali