Yadda Ake Noman Wake

0
439

Wake muhimmin abinci ne wanda yake da matuƙar amfani a jikin mutane da dabbobi. Akwai manyan kasuwanni da ake sayar da wake, kuma manoma suna sarrafa harawar wake don sayarwa a lokacin rani don samun kuɗin shiga da kimanin kashi ashirin da biyar cikin ɗari (25%).  

Wake na taka muhimmiyar rawa wajen samar da sinadarin takin Nitrogen ga amfanin gona (kamar masara, gero da dawa); idan ana sauya abin da aka shuka bayan damina uku zuwa huɗu da wake ko waken soya, musamman a sauran wurare. Wake baya buƙatar a yawaita masa takin zamani, sabo da sauyi na inganta ƙasar gona. Wannan ƙasida na bayyana mana dabarun noman fari da jan wake da nufin taimakawa masu noman waken don riba.

Hoto na farko: Gonar wake

Gyaran Gona

 • Ka yi sassabe da sharar gona kafin damina, sannan in damina ta faɗi, ka yi feshin maganin ciyawa glyphosate (round-up) wanda aka fi sani da Randon adadin lita huɗu (4) a faɗin hecta ɗaya.
 • Bayan sati biyu, sai a yi kaftu, ko kuma haro ko a yi huɗa, daga bisani sai a yi shuka.

Gonar da ta dace a Noma Wake

 • Lokacin damina, ana iya noman wake a nau’o’in ƙasa masu yawa, amma zai fi kyau a gonakin tudu, wuri mai yashi-yashi kuma mai tsanewa da wuri.
 • In kuma da rani ne, za a noma waken, sai a sami gona a kusa da wurin da za a sami isasshen ruwa. (Wato korama ko dam ko rijiya mai ruwa).

Yanayin da Wake yake Buƙata

 • Ana iya noman wake a lokacin damina da lokacin rani, muddin akwai yanayin zafi kimanin awa 28-30 a dare da rana a lokacin noman wake.
 • Wake yana yabannya mai kyau a wuraren da ake samun ruwan sama da ya kai kamar kimanin ma’aunin 500-1200mm a shekara.
 • Amma saboda sabbin irin wake da aka samu, yanzu ana noma wake a wurare masu samun ƙarancin ruwan sama kamar ƙasa da ma’auni 500mm a shekara.      
 • Wake yana jure fari, kuma ana iya noma shi a gona mai yashi ko kuma saimon gona

Zaɓen Irin Wake don Shuka                                                                  

 • Ka zaɓi irin waken da ya fi dacewa da yanayin gonarka, ana zaɓen irin waken ne bisa la’akari da yawan kwanakin da yake ɗauka a gona kafin ya nuna da kuma yawan buhunan da yake bayarwa a hecta ɗaya, da jure ƙarancin ruwa, da jure wa ƙwari da cututtuka.
 • Kuma a yi lakari wajen zaɓen irin wake ta lura da launinsa da kuma girman ƙwayarsa.

Adadin Irin da Ake Buƙata

 • Ka yi amfani da kilo (12-25) sha biyu zuwa ashirin da biyar na irin wake a hecta ɗaya.
 • Wannan ya danganta ga kalar irin waken, girman ƙwayar waken da tsarin noman shi
 • Ana buƙatar irin wake mai yawa idan waken mai yaɗo ne?
 • Ba a buƙatar iri da yawa indai waken mai yaɗo ne.

Wanki da Gyaran Iri don Shuka

 • A wanke irin wake kafin shuka, gyara irinka, kafin shuka kuma a yi amfani da maganin wanke iri mai inganci saboda cututtukan dake cikin irin ko cikin ƙasa. Cututtuka da tsuntsaye suna kai hari ga wake kafin ya tsira da bayan ya tsiro.
 • Maganin wanke irin ya haɗa da MASHAL 2 percent APRON STAR, ALL STAR, DRESS FORCE SEED PLUS e.t.c. yi amfani da gram 10 domin wanke kilo 2-5 na iri.
 • Ka wanke hannunka da kyau da sabulu da ruwa bayan wankin iri da shuka.

Shukar Wake:

 • A lokacin damina, kada ka yi gaggawar shuka wake don kada ya nuna a tsakiyar damina, kuma kada ka yi jinkiri sosai don gujema matsalar ɗaukewar ruwan sama da wuri.
 • Abu mai muhimmanci wadda za ka yi la’akari da shi, shi ne, ka gane lokacin da ruwan saman ya fara da kuma tsawon lokacin da yake ɗaukewa da kuma tsawon lokacin da waken yake ɗauka kafin ya nuna.
 • Mafi yawan waken da yake yaɗo da mai girma a tsugune suna lura da faɗuwar rana kafin su fara fure.

Tazarar Shukar Wake

 • Ana shuka wake mai yi a tsugune a tazarar kimanin 50cm a tsakanin kunya da kunya da kuma tazarar kimanin 20cm a tsakanin shuka da shuka. Wake mai yaɗo ana shuka shi a tazarar 75cm tsakanin kunya da kunya, 50cm tsakanin tushen wake zuwa wani tushen.

Zurfin Shukar Wake

 • Ana shuka wake a adadin zurfi na 2.5cm zuwa 5cm. Shukar farin wake fiye da zurfi na 5cm zai haifar da jinkiri wajen tsirar sa.
 • Idan ya yi zurfi sosai yana iya ruɓewa ko ya tsiro ɗaiɗai.

Adadin Takin da Wake Yake Buƙata

 • Noman wake ba ya buƙatar taki mai yawa.
 • Ya kamata a yi amfani da takin NPK 15;15;15, kowace hecta ɗaya a sa mata buhun taki biyu a lokacin huɗan gonan ko takin SUPA SSP 30kg bayan shuka.

Magance Ciyawa da Wuta-Wuta

 • A nome ciyawa aƙalla sau biyu. Noma na farko makonni biyu bayan shuka, sannan noma na biyu makonni huɗu zuwa biyar bayan shuka.
 • A iya amfani da maganin ciyawa wajen magance ciyawa a gonar farin wake
 • Wuta-wuta tana kawo illa sosai a gonar wake, takan fita a tushen waken ta dankwafe shi, ta hana shi fitowa ko girma, ganyensa ya rinƙa bushewa, kuma ya daina ‘ya’ya.
 • Saboda haka, ya kamata a cire wuta-wuta tun tana ’yar ƙaramar yabanya, kafin ta yi fure kuma yana da kyau a shuka wake mai jure wa wuta-wuta.
Hoto na biyar: Wuta-wuta a gonar wake

Kwarin Wake da Maganinsu

 • Matsalar ƙwarin wake su ne babban ƙalubale a kan harkar noman wake a Nijeriya. Ƙwarin sun kasu kashi uku:
Hoton na shida: Tsutsar wake

1. Ƙwari masu lalata ganyen wake kafin fure/huda.

2. Ƙwari masu lalata wake a lokacin fure/huɗa.

3. Ƙwari masu lalata wake bayan ya saki ‘ya’ya.

Dabarun Magance Kwari a Gonar Wake

 • Wake yana buƙatar feshi sau biyu ko sau uku ya danganta ga yanayin ɓarnar ƙwari a gonar.

Feshin farko: Ka yi feshin farko a tsakanin kwana talatin (30); ko talatin da biyar (35) bayan shuka lokacin da wake zai fara fure.

Feshi na biyu: Ka yi feshi na biyu kwana goma bayan feshin farko a lokacin da waken yake fure.

Feshi na uku: Ka yi feshi na uku idan ya zama dole, kwana goma da yin feshi; na biyu idan akwai mummunan farmaki daga ƙwarin wake MAIKOT (MARUCA) da kuma ƙwaro mai tsotse kalaben wake.

Roron Wake

 • Ka yi roron waken a lokacin da ‘ya’yan waken suka bushe.
 • Wake mai zuwa da wuri da kuma wanda baya yaɗo, ana roro sau ɗaya.
 • Wake mai yaɗo kamar kanannaɗo a kan yi roro sau biyu ko sau uku.
Hoto na bakwai: Roron Wake

Ajiyar Wake

 • Ka ajiye wake a mazubin da iska bata shiga kamar duro ko buhun leda ko jarka
 • Ka ajiye tsabar waken ta hanyar jera su a buhu mai leda a ciki ko kuma ta hanyan ninka buhuna uku.

Ajiyar Wake Na Lokaci Mai Tsawo

 • Ka yi amfani da maganin ƙwari mai suna samanda gari (Phostoxine). Ka lulluɓe maganin da tsumma ko takarda mai laushi wato (Toilet paper) ƙwaya ɗaya ko biyu sannan ka saka a cikin buhun wake mai nauyin kilo ɗari (100kg).
 • Kada ka yi amfani da, ko ka sayar da tsabar waken da aka cuɗanya shi da maganin ajiya har sai bayan wata shida.
 • Ka tabbata da tsaftar ma’ajiya, kuma duk sati biyu ka duba ko za a sami wani canji a yanayin ajiyar waken.

Domin karanta cikakken bayani a kan Jagoran Noman Shinkafa A Najeriya danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Noma A Najeriya danna nan.

labarin da ya wuceLokuta Da Yanayi Da Kuma Wuraren Da Ake Karɓar Addu’a
Labarin na GabaJagoran Noman Waken Soya
NAERLS
NAERLS na daya daga cikin cibiyoyi 18 na binciken noma na kasa (NARIs) da ke karkashin ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya. Cibiyar tana da alhakin haɓakawa, tattarawa, kimantawa da yada ingantattun sabbin hanyoyin noma da bincike kan hanyoyin haɓakawa da manufofin.