Tag: ilimi

  • Zikiri Kafin (Gabanin) Da Bayan An Gama Alwala

    Zikiri Kafin (Gabanin) Da Bayan An Gama Alwala

    Zikiri Kafin (Gabanin) Alwala

    “Bismillaahi”.

    {Da sunan Allah}.

    Zikiri Bayan An Gama Alwala

    “Ashhadu an laa ilaha illallahu wah dahu laa sharika lahu wa Ashhadu anna Muhammadu abduhu wa rasuluhu”.

    {Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaɗai, babu abokin tarayya a gare shi, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) bawansa ne kuma manzonsa ne}.

    “Allahumma ja’alnii minat-tauwaabina waj’alnii minal mutaɗahhiriina”.

    {Ya Allah! Ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkaka}.

    “Subhanakal-laahumma wabi hamdika Ashhadu an laa ilaaha illaa anta wa astagfiruka wa atubu ilaika”.

    {Tsarki ya tabbata gare ka ya Allah tare da yabo gare ka. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai, ina neman gafararka kuma ina tuba gareka}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Zikiri Yayin Fita Daga Gida danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Ayyukan Gida Domin Taimako Juna danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Rasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo)

    Rasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo)

    Rasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo) Usman Ɗankwanagga a 1991.

    Sarkin Kiɗan Maradun, Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun, bayan wata gajeruwar rashin lafiya; Allahu cikin ikonsa ya karɓi rayinsa a ranar Juma’a 13 ga watan Satumba, 1991. Ya rasu a gidansa a Gidan Kano, Ƙaramar Hukumar Maradun, Jihar Zamfara.

    Allahu, karimun rahimun, ya daɗa haskaka makwancinsa, ya hore masa ni’imomi na Raudhatun min Riyadhil Jannah.

    Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo bawanka ne, ya sami shekaru talatin (30) izuwa ga jinƙanka; Allahu ka daɗa yafe kurakuransa, ka yi masa afuwa, ka kwantar da shi cikin Rahamarka, madauwamiya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Takaiceccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatar Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo

    Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo

    Abin Da Bincike Ya Gano Game Da Gudumawar Adabin Baka Wajen Haɓaka Tattalin Arziki: Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo

    Dukkanin wani bincike da za a gudanar ko aka gudanar; za a iske akwai irin nasarar da aka ci a sakamakon yin sa; wanda hakan ya sanya aka gano wasu muhimman abubuwa.

    A wannan nazari kan waƙar baka, an gano wasu muhimman abubuwa da suke da amfani ga rayuwar al’ummar Hausa da ma ƙasa baki ɗaya.

    Cikin abubuwan da binciken ya gano akwai:

    i. Yadda aka sami bibiyar sawu ta fuskar sana’a a tsarin waƙa, daga waƙar baka ta gargajiya zuwa waƙoƙin baka na Situdiyo. Wato sai ya zama kamar abin da Bahaushe ke cewa, “Sawun da na gaba ya taka, na baya ma kan takawa” amma fa ta fuskar sana’a.

    ii. Yadda aka fahimci mamayar mutane a cikin sana’ar waƙoƙin Situdiyo.

    iii. Yadda aka ga tattalin arziki na bunƙasa a dalilin waƙoƙin Situdiyo.

    iv. An fahimce yadda gungun jama’a ke cin abinci a dalilin waƙoƙin Situdiyo na Hausa.

    v. An gano yadda waƙa ta zama wata babbar sana’a a Ƙasar Hausa tun daga jiya har zuwa yau.

    vi. Binciken ya binciko irin nau’o’in mutanen da suke jinginuwa da wannan sana’a ta waƙa a matsayin hanyar samun abin masarufin rayuwa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudumawar Adabin Baka Wajen Haɓaka Tattalin Arziki: Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan

  • Zikiri In An Zauna A Wani Majalisi

    Zikiri In An Zauna A Wani Majalisi

    Ibn Umar ya ce: an kasance an ƙirgawa ga Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) a majalisi kafin ya tashi, yana cewa sau ɗari:

    “Rabbigfir lii watub alayya innaka antat tauwaabul gafuuru”.

    {Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, ka yi tuba a gare ni. Lallai kai ne Mai yawan karɓar tuba, Mai yawan gafara}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Tashi Daga Majalisi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Walaha danna nan.

  • Yadda Falalar Suratul Falaƙi Da Nasi Take

    Yadda Falalar Suratul Falaƙi Da Nasi Take

    An karɓo daga Uƙubatu ɗan Amir (Radiyallahu Anhu) yace; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) yace; “Ba ka ga waɗansu ayoyin da aka saukar da su jiya da daddare ba, ba a taɓa ganin irinsu ba”. Su ne ƙul’a’ uzu bi rabbi falaƙi” da ƙul’a’uzu birabbinnasi” (Muslim 814).

    Faɗakarwa

    Ina nasiha da ba da shawara ga ‘yan uwa musulmi da mu kula sosai da Alƙur’ani ta wajen haddace shi; da yawan karanta shi, da koƙarin fahimtar ma’anonisa da kuma yin aiki da shi; domin samun tsira da arziki da wadata a duniya da lahira.

    Allah ka sa mu dace, Allah ka sanya mu zama ahalinka a halin Alƙur’ani. Amin.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zikiri Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Zikiri danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Tarihin Alaramma Malam Salihu Ɗangalinja

    Tarihin Alaramma Malam Salihu Ɗangalinja

    An haifi Malam Salihu ɗan Dawuda a girin Galinja da ke Kanon Dabo a shekarar 1920 zamanin Sarkin Kano Usman. Mashahurin mahaddaci mai baiwar tilawa da kaifin basira.

    Malam Salihu Ɗangalinja ya yi tafiye-tafiyen neman karatu cikin ƙasar Gumel da Haɗeja; da garuruwa irin su Mainabindi da Kalali da Unguwar Jibrin.

    Bayan Malam Ɗan Galinja ya samu AIƙur’ani, sai kuma ya tsunduma cikin fannonin ilmin Fiƙhu da tajwidi. Ya karanta littafai irinsu Hidayatul Rahman wajen malaminsa Shehu Rabi’u Ɗantinki da Malam Husaini Gwauron Dutse. Saboda irin baiwarsa ta karatu an ce a lokacin ƙuruciyarsa zai yi wuya a lissafa manyan tsangayun da ya je ya sha fari ya tashi; Wannan ya sa sa’o’insa su ka sallama masa.

    Malam Salihu mutum ne mai yawan haƙuri da kawaici da kyautatawa ga almajiransa. Bayan girma ya kama shi sai ya kafa tsangayarsa da ke garin Ƙarfi a inda makaranta ke turuwa don sanin Alƙur’ani daga gare shi. Wadda hakan ya canza yanayin rayuwar mutanen Ƙarfi saboda maƙwabtakar da suka yi da ma’abota Alƙur’ani.

    Malam Salihu Ɗan Galinja ya kasance yana yi wa ‘ya’yansa da almajiransa wasiya da riƙo da Alƙur’ani da kaucewa kwaɗayin duniya.

    Malam Salihu ya rasu a shekarar 1997 ya bar ‘ya’ya da dama, kaɗan daga cikin mazan su ne:-

    • Halifansa Malam Kabir Ɗan Galinja
    • Malam Nafiu Ɗan Galinja
    • Malam Ɗahiru Ɗan Galinja, da ‘ya’ya mata guda tara.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Mahiru Sharif Bala danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Alaramma Malam Salisu Ɗanruwantsa

    Tarihin Alaramma Malam Salisu Ɗanruwantsa

    An haifi Alaramma Malam Salisu ɗan Malam Ahmad ɗan Usmanu ɗan Ahmad a garin Ruwantsa. An ce asalin zuriyarsu sun fito daga ƙasar Mali, Alaramma Malam Salisu ya taso a garin Ruwantsa a inda ya fara karatu a wurin Malam Abdul’Aziz ɗan Malam Ibrahim.

    Lokacin da ya ƙara datawa kuma idonsa ya yi ƙwari, sai tsananin kwaɗayinsa ga Alƙur’ani ya ƙaru, ya ƙara duƙufa. Malam Salisu ya kasance tun ƙuruciyarsa ba ya zama wuri guda face yana tsakanin wancan gari da waccan tsangaya izuwa waccan cibiya ta makaranta. Wannan ya ba shi damar huɗuwa da gwarazan malaman zamaninsa irin su Malam Haruna Ningi wanda a wurinsa ne ya haddace AIƙur’ani Mai Girma.

    Koda Alaramma Malam Salisu ya sami labarin bayyanar Gwani Hamad a garin Taura kuwa; sai ya zabura ya haɗa kayansa ya nufe shi kuma ya kamfata daga marmaron ilmin Gwani Hamad. Daga nan kuma ya wuce garin Malamawa wurin Bajimin malami Malam Abdullahi. Malam Sal ısu bai gushe ba yana kutsawa cikin kowane loko da saƙo na ƙasar Kano da kewayenta; har sai da ya dangana da garin Insharuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

    Bayan Dawowar Malam Salisu daga ƙasar Nijar ne ya yi aure a mahaifarsa. Daga nan ne ya taso tare da Wani adadi na almajiransa ya dawo Kano ya sauka Unguwar ƙofar Wambai; wurin Malam AbdulKarim inda ya karanta ilimin Tajwidi da Fiƙihu. Manyan malaman Malam Ɗanruwantsa sun haɗa da Shehin Malami Rabi’u Ɗantinki da Shehu Mai Hula. Bayan nan ne kuma ya sake zabura izuwa garin Ɗabbatta wurin babban malami Malam Adam; don sanin ilimi littafin Shaɗibiyya da ilmin Rasmu.

    Sannan ya sake dawowa birnin Kano karo na biyu a inda ya sauka a wurin Malam Garba Tudun Nufawa.

    Ya zauna shekaru biyu a wurinsa yan karantar Alfiyyar ɗan Malik. A lokaci guda kuma, shi Malam Garba Tudun Nufawa (Malam Abubakar Ramadan) yana koyon ilmin Tajwidi da Kira’o’i a wurinsa; Daga nan ne ya koma Unguwar Yakasai ya kafa makarantarsa a shekarar 1945.

    Bayan ya tumbatsa da ilmi da Alƙur’ani; daga bisani kuma ya koma Gwauron Dutse kusa da Masallacin Juma’a na Sheikh Is’haka Rabiu a matsayin Na’ibin Limamin Masallacin.

    A takaice dai zamu iya cewa Malam Salisu Ɗanruwantsa shi ne magajin kambin Shehi Rabiu Ɗantinki a fagen ilmin Alƙur’ani; da ƙira’o’i a faɗin Kanon Dabo. Tsangayarsa ta shahara da tsare-tsare masu ban sha’awa tare da sanya cigaban zamani a Wasu ɓangarori daban-daban. Alal misali, akwai tsarin azuzuwa inda ake sanya yara goma sha bakwai; a Kowane aji ana biya musu rabin sumuni da safe har sai sun haddace. Da yamma kuma a ƙara musu rabi don a samu kyakkyawar haddar AIƙur’ani.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Gambon Takai danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tattali da Kulawar Ɗanƙwairo da Majiɓintansa

    Tattali da Kulawar Ɗanƙwairo da Majiɓintansa

    Kamar yadda tarihin rayuwar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya tabbatar; shi mutum ne mai kula da ciyarwa da shayarwa da tufasarwa da samar da muhallai na zaman iyalinsa da makusantansu; da sauran waɗanda suke majiɓinta a gare shi.

    Sannan yakan yi wa iyalinsa tarbiyya gwargwadon yadda addinin Musulunci da al’adu kyawawa na Hausawa suka tanada.

    Mutum ne kuma wanda yake fafutukar haɗa kan dukkan zuriyyarsa da yi musu addu’a su zauna salim alim; ba ƙyama ko faɗa ba wata hauragiya ko ƙiyayyar juna. Haƙiƙa, wannan wata hanya ce ta wanzar da zuriyya bisa haƙuri don ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

    Musa Ɗanƙwairo kamar yadda ya tashi, ya gani a gidansu, ya himmatu ta fuskar yin noma da duka ayyuka na gona; don samar da abinci da abubuwan masarufi waɗanda suka zamanto abokan zama.

    Sau da yawa; Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ba ya buƙatar duk wani abu da zai hana shi yin noma a kowace faɗuwar damina. Ta haka Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya nuna ba ya son jama’arsa ta tagayyara. Saurari wata damuwa ta makaɗa Musa

    Ɗanƙwairo a sa’ilin da Damina Bakolori ya tauye shi a yin noma a wata damina:

    Jagora(Daudu): Allah shi ka kawo komi,
    : Yaƙin Dam Bakolori ya ci mu,
    ‘Y/Amshi: Sai in faɗa ma Mamman,

    : Ban da gida yanzu ban da gona, Jagora(Daudu): Yanzu cikin damina ni kai ta shirin,
    ‘Y/Amshi: Gyaran wurin da za ni bacci, Jagora(Daudu): Yanzu gidan Makaɗa ya zamo gurbi na ƙwarai,

    : Wanda ad da zurhi,
    ‘Y/Amshi: Sarkawa su sukai da taru,

    Jagora(Daudu): Sarkin Daura ko da damina,
    : Sai kai ta shirin tariyab baƙi,
    ‘Y/Amshi: In wasu sun kore mu mu taso,

    : Muhammadu in wasu sun kore mu mu taso,
    Jagora(Daudu): Ba ni zama inda babu gona,
    ‘Y/Amshi: Ba ni zama inda ba abinci,

    : Babban jigo na Yari,
    : Uban Shamaki tura haushi.
    (Ɗanƙwairo, Waƙar Babban Jigo, ta Sarkin Daura, Alhaji Muhammad Bashar (1966-2007)

    Bayan harkokin noma, makaɗa Musa Ɗanƙwairo kuma ya yi kiwon shanu da tumaki; da awaki da Kaji da sauran dabbobi da tsuntsaye. Ya ƙaura ya bar wa iyalinsa yin waɗannan sana’o’i.

    Domin karanta cikakken bayani akan Rasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo) Usman Ɗankwanagga a 1991 danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun; A Aiwatar Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Falalar Sadaƙar Mai Ƙaramin Ƙarfi

    Falalar Sadaƙar Mai Ƙaramin Ƙarfi

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu anhu) ya ce: “Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) yace: “Sadaƙar dirhami ɗaya ta rigayi sadaƙar dirhami dubu ɗari” Sai wani mutum ya ce; Kamar yaya Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam)?

    Sai ya ce: “Mutum ne yana da dukiya mai yawan gaske, sai ya tsakuro dubu ɗari ya bayar sadaƙa; kuma wani dirhami biyu ne kaɗai da shi. Sannan ya yi sadaƙa da dirhami ɗaya” (Nasa’I Ibn Khuzaimah), (Sahihul Targib 875).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ciyarwa Da Shayarwa Da Tufatarwa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ratiban Nafiloli danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tarihin Gwani Saleh Ɗanzargu

    Tarihin Gwani Saleh Ɗanzargu

    An haifi Gwani Saleh ɗan Abdullahi jikan Abdullahi a Ƙasar Jahun. Mahaifin sa ya rasu yana ƙaramin yaro, don haka sai mahaifiyar sa ta koma da shi garin Zarga ta kuma kyautata tarbiyar sa.

    Gwani Saleh ya taso da kaifin basira da son Alƙur’ani. Don haka ya lazimci makarantan garin Zarga irinsu Malam Abdullahi har Ubangiji Ya hore masa Alƙur’ani ya haddace shi yana ɗan shekara tara (9). Gwanin Alƙur’ani ma’abocin ƙan-ƙan da kai da gaskiya da riƙon amana. An ce tun yana ɗan shekara sha biyu ya sha fari.

    Gwani Saleh ya yi tafiye-tafiye na neman karatu a inda yazo Kano ya sauka a tsangayar Gwani Nadudu. Daga bisani kuma ya lazimci mashahurin malami Malam Aliyu Basakkwace ya karanci Fiƙhu da Hadisi da tafsiri Shaharar da tsangayarsa ta yi ya sanya makaranta daga nisan duniya yin takakkiya don ɗosana daga haskenta. Manyan abokanen karatun Gwani Saleh sun haɗa da:-

    • Gwani ɗan Kwandarai
    • Gwani Ɗan birni
    • Gwani Daudu

    Game da yawan almajiran da suka samu Alƙur’ani a hannun sa kuwa, wannan ɗan littafi ba zai ɗauke ambaton su ba, sai dai mu yi ishara ga waɗansun su:

    • Malam Muktari Abdullahi
    • Yayan sa Gwani Yahuza da Gwani Lawi
    • Malam Husaini Rijiyar Lemo
    • Malam Sham’unu
    • Malam Ibrahim Maidarasu

    Gwani ya rayu cikin karamci da girmamawa daga maƙwabtan sa, musamman ma Alhaji Sunusi Ɗantata da al’umar Unguwar ƙoƙi da kewayenta. A halin yanzu wannan tsangaya tana ƙarƙashin kulawar ɗan sa Gwani Yahuza inda ta ƙara bunƙasa ta hanyar shigo da tsarin ilmin zamani, ɓangaren firamare da sakandare. A lokaci guda kuma, ga tsohon tsarin tsangaya na gudana da makaranta da mahaddata.

    Gwani Yahuza ya samu gogayya da wayewa ta zamani a inda ya dangana da ƙasar Masar don karatun sa na digirin farko. A halin yanzu Gwani Yahuza ɗaya ne daga manyan alƙalai na musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa. Gwani Yahuza shi ne ɗan Najeriya na farko da ya karɓi kyautar girmama mahaddata Alƙur’ani daga ƙasar Saudi Arebiya. Baya ga wannan rassa na makarantar akwai majalisai a unguwannin Gwammaja da Kurnar Asabe da Ƙoƙi.

    Ita wannan makaranta ta Gwammaja, Gwani Lawi ne ya kafa ta mai suna Ma’ahad Gwani Lawi Litahfizil Ƙur’anil Karim.

    Gwani Lawi ya yi babbar Diflomarsa a Jami’atul Ƙur’anil Karim da ke Sudan, kuma shi ne wan da ya kafa ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani ta farko a Najeriya, mai suna Rabiɗatul Huffazil Ƙur’ani, Nigeriya. Gwani Sale Ɗanzarga ya bar ‘ya’ya goma sha biyu, maza da mata.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Ɗankwandarai danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Farko Na Nijeriya (1500 BC- 500 AD) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.