Tag: ilimi

  • Yadda Ake Zikiri Yayin Fita Daga Gida

    Yadda Ake Zikiri Yayin Fita Daga Gida

    “Bismillaahi Tawakkaltu alallaahi walaa haula walaa ƙuwwata illaa bil-laahi”.

    {Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu ƙarfi sai da Allah}.

    “Allahumma inni A’uzu bika an adhilla au udhilla, au azhilla au uzhalla, au azlima au uzlama au ajhala au yujhala alayya”.

    {Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na ɓata ko a ɓatar da ni, ko na zame ko a zamar da ni, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Zikiri Yayin Shiga Gida danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Falalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana Ya Ke

    Yadda Falalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana Ya Ke

    An karɓo daga Anas ɗan Malik (Radiyallahu Anhu) yace; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) yace; “Wanda ya yi sallar asuba a cikin jam’i, sannan ya zauna yana ambaton Allah har rana ta ɓullo; sannan ya yi salla raka’a biyu za a ba shi lada hajji da umra cikakku, cikakku, cikakku (Tirmizi 586).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar La Ilaha Ilallahu Ta Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Ilimin Ma’ana (Semantics)

    Ilimin Ma’ana (Semantics)

    JADDADA MA’ANA (ENTAILMENT)

    GABATARWA
    Masana da dama sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da nazarin ma’ana. Kasancewar ma’ana wani ɓangare ne na kimiyyar harshe wanda ya ta’allaƙa a kan ma’ana.

    MA’ANAR HARSHE

    Sapir (1956) ya bayyana harshe da cewa “wata hanya ce ta bayyana kai da kuma hulɗa a tsakanin mutane waɗanda dabbobi ba su da irin ta.” Semantics kalma ce ta Ingilishi wacce ta samo asali daga “Semantikos” ta harshen Girkanci, wadda take nufin yin fiɗa ko ƙirƙira ko furta kalmomi (making of signs).

    Shi dai ilimin ma’ana (semantics) fanni ne ko reshe ne na kimiyyar harshe da ya raja’a wajen yin nazarin ƙwaƙƙwafi tare da samar da gaskatattun bayanai game da ma’ana, walau ta kalmomi ko ta jimloli ko kuma zantuka.

    Ilimin harsuna bai taƙaita kaɗai a ɓangaren ƙwarewa wajen sanin ma’anar ɗaiɗaikun kalmomi ba. Tabbas kalmomi na haɗuwa ta hanyoyi mabambanta don samar da ma’anoni ta hanyoyi daban-daban. Saboda haka, kalmomi na bayyanuwa wajen nuna dangantakar ma’ana a cikin jimla. Waɗannan dangantakar ma’ana ana samun su ne a wasu fagen nazari kamar haka;

    Paraphrase
    Ambiguity
    Tautology
    Presupposition
    Entailment
    Redundancy
    Anomaly
    Da dai sauransu.

    Amman mu a nan, za mu yi magana ne a kan abin da ya shafi “Entailment”.
    Entailment na nufin dangata tsakanin wata jimla da wata jimla wajen fayyace ko jaddada ma’anar jimlar farko daga jimla ta biyu wajen jaddada ma’ana. Misali;

    Lee kissed Kim passionately.
    Lee kissed Kim.
    Kim was kissed by Lee.
    Kim was kissed.
    Lee touched Kim with her lips.

    Judas murdered Sinbad
    Judas killed Sinbad.
    Sinbad was killed by Judas.
    Sinbad was killed.

    Aliyu ya tafi kasuwa`
    Kasuwa Aliyu ya tafi.
    Ya tafi kasuwa Aliyu.
    Aliyu kasuwa ya tafi.

    Audu ya zauna
    Zama audu ya yi.
    Audu zama ya yi.

    Halima ta siya takalmi
    Takalmi Halima ta siya.
    Ta siya takalmi Halima.

    Sahal ya sha ruwa
    Ruwa Sahal ya sha.
    Ya sha ruwa Sahal.

    Umar ya tsinka takalmi
    Takalmi umar ya tsinka.
    Tsinka takalmi umar ya yi.
    Umar takalmi ya tsinka.

    Amina ta haihu
    Jego amina ke yi.
    Amina na jego.
    Amina jego take yi.

    Ya’u ya sayi mota
    Mota Ya’u ya siya.
    Ya’u mota ya siya.

    Musa ya ɗinka riga
    Riga musa ya ɗinka.
    Musa riga ya ɗinka.
    Ɗinka riga musa ya yi.

    Adamu ya shiga gida
    Adamu gida ya shiga.
    Gida Adamu ya shiga.

    Halima ta soya ƙwai
    Soya ƙwai Halima ta yi.
    Ƙwai Halima ta soya.
    Halima ƙwai ta soya.

    Idan muka dubi waɗannan misalan na jimlolin, za mu ga cewa duk ana magana ne a kan abu ɗaya ba tare da canzawar ma’ana ba, kuma za mu ga cewa duk sauran jimlolin suna ƙara yi mana bayani ne a jimlar farko. Amman idan muka dubi wannan misalin ;

    Lee married Kim
    Kim kissed Lee.
    Lee kissed Kim many times.
    Lee did not kiss Kim.

    A waɗannan misalan za mu ga cewa ba a sami entailment ba, domin kuwa waɗannan jimlolin guda uku babu wacce take yi mana bayani ko take ƙara fayyace mana haƙiƙanin bayanin jimlar farko.

    KAMMALAWA

    Duba da yadda bayanai suka gabata game da ilimin harsuna da bayani game da ilimin ma’ana tare da yin tsokaci a kan “entailment” da kuma misalai, an gamsu kuma an fahimci abin da ake kira da “entailment”.

    MANAZARTA

    Gennaro Chierchia and Sally Mcconnell-Ginet, Meaning and Grammar (2000) : An Introduction to Semantics, MIT Press.
    Gramley, S. (2001) The vocabulary of world English. London:Arnold.

    Kearns, Katherine 2000. Semantics. London: Macmillan.
    Raymond Hickey, English Linguistics Language Meaning and Use.

    Danna nan don karanta Adana Harshe (LANGUAGE PRESERVATION)

    MUHAMMAD SAHAL ALIYU
    07065994177

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Tarihin Gwani Daudu (1920-2000)

    Tarihin Gwani Daudu (1920-2000)

    An haifi Alaramma Malam Abubakar Yunusa a shekarar 1920 a garin Tsakuwawa a ƙaramar Hukumar Miga da ke cikin Jihar Jigawa. Ana yi masa laƙabi da Gwani Daudu saboda sarautar kakanninsa ta Galadiman garinsu.

    Alaramma Malam Abubakar ya shahara da baiwar karatu na yankan shakku. Saboda irin kaifin ƙwaƙwalwar da Ubangiji Maɗaukaki Ya ba shi, an ce Gwani Daudu ba ya manta duk abin da ya yi ido biyu da shi tun daga ƙuruciyarsa. Zarton malami, ma’abocin karamci da son almajirai. Gwani Daudu ya yi fice cikin dattijawan alarammomi da wayewa a zamanance da kuma kutsuwa fannonin ilmi Fiƙhu da Tafsir da Lugga da Nahwu.

    Gwani ya fita neman karatu bayan ya zama matashi mai kimanin shekaru goma sha biyar kuma bai koma gida ba sai da ya samu Alƙur’ani kuma ya rubuta shi. Ya yi tafiye-tafiyen neman karatu cikin Birniwa da Kirikasamma da Gayan. Gwani Daudu ya kafa tsangayun AIƙur’ani a birane daban-daban kamar garuruwan Mai Tafari da Kirikasamma da Kuka Uku.

    Don haka ne ma a halin yanzu ake kiran wata kasaitacciyar makaranta a garin Damaturu da tsangayar Gwani Daudu.

    Bayan Gwani Daudu ya dawo birnin Kano kuwa ya zauna a wurare daban-daban da suka haɗa da Durumin Zungura da Kankarofi cikin ƙaramar Hukumar Birni. Daga bisani kuma ya koma Unguwar Gwale.

    Gwani Daudu ya shahara da kyakkyawar maƙwabtaka da saraki da sauran al’umma. Saboda haka ne ma Sarkin Kano Ado Bayero ya ba shi filin da ya faɗaɗa tsangayarsa da ke Unguwar Gwale.

    Malaman Gwani Daudu sun haɗa da:-

    • Malam Mai Ɗanbahar Mai Tafari
    • Malam Iliya Gayan
    • Gwani Ɗankwandarai

    Gwani Daudu ya rasu a ranar 22 Sha’aban 1421, dai-dai da 17 ga Nuwambu 2000. Ya rasu ya bar ‘ya’ya da almajirai masu yawa:-

    ‘Ya’ya:

    • Malam Muhammad Abubakar
    • Malam Ahmad Abubakar
    • Malam Susi Abubakar
    • Malam Tamimuddari
    • Malam Adisaru
    • Malam Arisu

    Manyan Almajiransa sun haɗa da:-

    • Malam Ali Basukkwace
    • Malam Umar Panshekara
    • Malam Ahmad Ɗantsadawa
    • Alh. Hamza Yusuf
    • Malam Garba Na’ibi
    • Malam Muhammad Ɗan Meram

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Malam Isa ƊanƘauranmata Bin Umar danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Misalan Waƙafi Ababen Koyi A Tarihin Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

     

  • Misalan Malaman Yarabawa A Ƙarni Na Goma Sha Tara

    Misalan Malaman Yarabawa A Ƙarni Na Goma Sha Tara

    Malaman ƙarni na goma Sha Tara a ƙasashen Yarabawa sun haɗa da:

    • Sheikh Saleh bin Abdulƙadir
    • Sheikh Muhammad al-Busiri
    • Sheikh Harun
    •  Sheikh Abubakar bin Al-Qasim
    • -Malam Ahmad Qifu
    • Malam Usman bin Abubakar

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wasu Daga Fitattun Malamai A Ƙasar Sakkwato Da Kewayen Ta danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Farko Na Nijeriya (1500 BC- 500 AD) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Alaramma Malam Isa Ɗan Ƙauranmata Bin Umar

    Tarihin Alaramma Malam Isa Ɗan Ƙauranmata Bin Umar

    An haifi Malam Isa Umaru a garin Ƙauranmata zamanin Sarkin Kano Usman. Mahaifinsa Malam Umar ya aika da shi garin Bunkure wajen Malam Adamu Gangaran a farko-farkon zamanin Sarki Abdullahi Bayero. Bayan Malam Isa ya data ne ya nemi a kai shi garin Rimi cikin yankin Sumaila wajen Malam Isuhu.

    Gwanin Alƙur’ani, ma’abocin tawaru’u da yawan karamci, Malam Isa ya yi tafiye-tafiyen neman AIƙur’ani cikin ƙasar Gumel; wajen Malam AbdulHamid da garin Ciromawa a ƙasar Haɗeja.

    Saboda irin baiwar da Ubangiji ya ba wa Malam Isa abokansa ne suka gabatar da shi a matsayin mai darasu bayan rasuwar Alaramma Malam AbdulHamid a katafariyar tsangayarsa da ke garin Ciromawa.

    Dawowar Sa Kano Da Zama Bayan gwagwarmayar neman karatu daga wannan gari zuwa wancan; Malan Isa ya koma mahaifarsa a garin Ƙauranmata a inda ya cigaba da hidima ga mahaifinsa Malan Umar. Don haka kullum yana tsankanin cikin birni da ƙauyensu, sai dai ya yi ‘yan kwanaki ya koma gida.

    Daga ƙarshe wasu daga cikin attajirai irin su Alhaji Hamidu Namudi da ke Unguwar Dala; suka nemi mahaifinsa da ya yi masa izinin dawowa Kano don koyar da Alƙur’ani.

    Bayan samun izini mahaifinsa ne ya dawo Kano ya zauna a Unguwar Dala; daga bisani ya koma Gwale a farkon mulkin Sarki Ado Bayero Manyan abokan karatunsa su ne:-

    • Malam Saleh Ɗangalinja Ƙarfi
    • Malam Umar Magasawa

    Malam Isa Ɗan Ƙauranmata bai gushe ba har zuwa yanzu yana karantarwa a tsangayarsa da ke gidansa a Gwale.

    Yana da ‘ya’ya kamar haka:-

    • Malam Umar Isa
    • Malam Usman Isa
    • Malam Abubakar
    • Malam Abdulhamid
    • Malam Garba
    • Malam Sabi’u
    • Malam Aminu
    • Malam Jamilu
    • Malam Kabiru

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Malam Salisu Ɗanruwantsa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Magabata da Haihuwar Ɗanƙwairo danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Gwani Ɗanbirni

    Tarihin Gwani Ɗanbirni

    An haifi Malam Muhammad ɗan Malam Ali a unguwar Zage da ke Birnin Kano a zamanin Sarkin Kano Usman. Gwani Ɗan birni ya sha bam-ban da ragowar takwarorinsa makaranta.

    Domin kuwa ya fara neman ilmi ne a fagen Fiƙhu da Hadisi cikin tsarin ilmin zaure; musamman ma wurin Malam Baƙo da Malam Habu da ke Unguwar Ciromawa.

    Tsananin sha’awarsa ga zurfafa neman karatun Alƙur’ani ya sa ya nemi izinin mahaifinsa don ya fita zuwa wasu wurare da ke wajen Kano. Koda Gwani Ɗanbirni ya samu izinin mahaifinsa sai ya yi niyya ya fita. A lokacin ba wanda ya san inda ya nufa, ballantana inda za a same shi. Bayan wani lokaci ne aka samu labarin yana wurin Gwani Abdullahi da Gwani Ahmadu.

    Koda Gwani Ɗanbirni ya samu labarin wani mashahurin masanin Alƙur’ani a garin Ubba sai ya tafi izuwa gare shi. Daga nan ya dawo gida Kano bayan ya tumbatsa kuma ya shahara wajen ƙarfin tilawa da baiwa a fagen karatun Alƙur’ani. Wannan ya zaburar da irin abokansa na ƙuruciya da ke Unguwar Zage, saboda ganin irin ɗimbin ilmin da Ubangiji Maɗaukaki Ya yi masa a wani lokaci taƙaitacce. Manyan abokan karatun Gwani Ɗanbirni sun haɗa da Gwani Saleh Ɗanzarga da Malam Abdu Ɗankankare da Malam Kafi-ɓari da Malam Musa jikan Shehu da Malam Sani Adam.

    Manyan malaman Gwani Ɗanbirni sun haɗa da mashahurin masanin Alƙur’anin nan Gwani Hamad da Gwani Abdullahi Ɗan Gwani Ahmadu da Gwani na Ubba da Malam Awaisu na Madabo da Malam Inuwa almajirin Malam Salga da Gwani Dubu da Gwani Hamidu.

    Game da yawan almajiran Gwani Ɗanbirni kuwa za mu iya cewa ɗaruruwan almajirai sun sami Alƙur’ani a hannunsa Fitattu; daga cikin Su sun haɗa da Malam Tijjani Rabi’u da Malam Idi da Malam Ahmadu Ɗanjajaye da Malam Isa ƙofar Mata da Sharu Bala da Sharu Ahmadu da Malam Ahmadu Mai Makarantar Dare Gabari da Alhaji Gagara da Na’ibin Masallacin Juma’a na Shehu Ahmadu Tijjani da Malam Inuwa Mai Gemu da Alhaji Ali Indabawa.

    Gwani Ɗanbirni ya shahara da kyawawan halaye da sabo da jama’a. A lokaci guda kuma yana da ƙima wurin Sarki da attajirai na Kano irin su marigayiya Mai Babban ɗaki; mahaifiyar mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Khalifa Sarki Sunusi (Murabus) da Alhaji Aminu Ɗantata. Gwani Ɗanbirni ya rasu a watan 10 na shekarar 2004. Ya bar ‘ya’ya maza da mata goma sha biyar (15).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Mahmud Manzo Arzai danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Za Ku Gyara Zamantakewarku Ta Aure

    Yadda Za Ku Gyara Zamantakewarku Ta Aure

    Bincike ya nuna ma’auratan da suke sabunta yanayin rayuwarsu ta yau da gobe sun fi samun zaman lafiya a zamantakewar aure.

    Ga yadda za ku gyara zamantakewar aure naku:

    1. Kyakkyawan Yanayi (Zamantakewar Aure)

    • Misali zuwa sabbin gurare.
    • Cin abinci na musamman ko fita kallon wani abun tsoro ne ko na nishaɗi tare.
    • Motsa jiki ko wasanni tare.
    • Ziyartar wani guri da ba su taɓa zuwa ba.

    2. Shafar Juna

    • Ku kasance Kuna iya kusantar junanku a kodayaushe ba wai sai lokacin kwanciya ba.  
    • Kina iya shafar wuyan mijinki idan yana miki girki.
    • Ko shafar gashin kansa a lokacin da kuke zaune kuna kallo.
    • Riƙe hannun juna idan kuna tafiya tare.
    • Sumbantar kuncinsa a ba-zata.
    • Ko shafar bayansa a lokacin da yake wani yanayi mara daɗi.

    3. Tattaunawa Game Da Kwanciyar Aure

    Yana da kyau kuna canza yanayin salon kwanciyarku, ko tattaunawa game da abunda yake sa ku jin daɗin kwanciyar, ko wani abu da yake so kina masa da zai sa ya ji daɗi misali:

    • Canza salon kwanciya ko ku je ɗakin hotel.
    • Idan kuna da yara ku ba da su inda za a kula da su don ku samu isasshen lokaci.
    • Yiwa juna tausa.
    • Sabunta kayan bacci.
    • Samun ingantacciyar kwanciya da gamsuwa ba wai yawan kwanciyar ba.
    • Sumbantar mijinki tana da tasiri ƙwarai wajen ƙara danƙon ƙauna tsakaninku; kuma yana sawa ki janyo hankalinsa gareki. Ki yi ƙoƙari kina sumbantar mijinki ko da na tsawon sakan 10 ne a Rana.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za Ki Nuna Wa Mijinki Tsantsar Kula danna nan

  • Matakan Farfaɗo Da Tsangayun Alƙur’ani Da Raya Su

    Matakan Farfaɗo Da Tsangayun Alƙur’ani Da Raya Su

    Zai yi kyau kowace jiha ta bi hanyoyi don cimma wannan buri bisa shawartar masana da kuma jami’anta. Kaɗan daga waɗannan matakai sun haɗa da:-

    • Kafa ma’aikata ko hukumar ilmin Tsangayun Alƙur’ani.
    • Ƙididdigar yawan tsangayu da yawan malamansu da almajiransu don sanin girma ko faɗin nauyin da ke wuyan kowacce jiha, kamar dai yadda kowace gwamnati ta san yawan malamanta da ɗalibanta a kowace makaranta ta boko
    • Wayar da kan ma’abota tsangayu da kula da kyakkyawar dangantaka da su don samun jituwa da fahimtar juna mai ɗorewa ta hanyar tarukan ƙarawa juna sani da shirye-shirye a gidajen rediyo da talabijin.
    • Nusar da al’uma muhimmancin tsangayu da makaranta Alƙur’ani don ƙara samun gata daga Al’uma ta kafafen watsa labarai.
    • Gina tsangayu da gyara waɗanda suka lalace da samar da rumfunan darasu.

    Shiri na musamman kan:-

    • Bunƙasa noman tsangayu ta hanyar raba taki da iri da kuma shawarwari daga ƙwararru.
    •  Bunƙasa sana’o’i don dogaro da kai musamman ga matasan alarammomi da ke yankan farce ko dako da sauransu.
    • Samar da ƙananan masana’antu mallakin tsangayu da jari kamar injinan niƙa da yin sabulu da na haɗa abincin kaji da makamantansu.
    • Yankawa makaranta ko mahaddata albashi ko alawus a matsayin su na malamai a tsangayunsu. Wasu a sanya su a rajistar jihohi, wasu kuma su kasance daga aljihun ƙananan hukumominsu.
    • Sauƙaƙawa makaranta masu sha’awar zurfafa iliminsu damar cigaba da ilmi a cibiyoyin ilmin da suka dace cikin jihohinsu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Samar Da Tsangayun Gwaji Na Gwamnati danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Jerin Gwamnonin Kano Daga (1967 zuwa yau) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Alaramma Gambon Takai

    Tarihin Alaramma Gambon Takai

    An haifi Malam Zakariya ɗan Adamu a garin Takai a shekarar 1928. Ɗan baiwa kuma ma’abocin himma da ƙanƙan-da-kai.

    Malam Gambon Takai ya sha banban da sauran makaranta ta fuskar shuhura wajen buɗewa almajirai sirrin Alƙur’ani. Wannan ya sa dattijan malamai zuwa gari ya gari don su yi kwalli da shi. Wannan har yasa wasu na cewa Malam Gambon Takai ya yi gamo da aljannu ne a inda suka buɗe idonsa da sirrukan Alƙur’ani.

    Abokan ƙuruciya lokacin neman karatun Malam Gambo kuwa ba su gushe ba suna bibiyarsa, har sai da wata rana bayan ya yi tafiya suka bincike lakkarsa ko za su ga wani nau’i na Alƙur’ani ko wani kundi na sirrukan Alƙur’ani da ya ke anfani da shi. Ubangiji Maɗaukaki Ya yi masa baiwar murya, koda yana karatu a hankali to kuwa wanda ke nesa zai jiyo muryarsa.

    Da yawa yakan naƙaltawa makaranta sirrukan rubuta Alƙur’ani da haddace shi. Ya isheka misali ga tumbatsarsa wajen warware luggogin Alƙur’ani abin da muka gutsurowa mai karatu mai suna Logar Gambon takai a Babi na Uku, Sashe na Biyu cikin wannan littafin da ke maganan kan dabarun rubutun AIƙur’ani wurin ma’abota tsangaya.

    Hatta malamai masu karatu kan zo tsangayarsa don kallon darasu; wanda ake farawa tun Asuba har sai an yi Azhar sannan a karya a koma.

    Wani abu mai ban sha’awa game da rayuwar Malam Gambon Takai shi ne; himmarsa wajen dogaro da kai da yin kasuwanci. An ce a lokacin da ya ke fita rani da almajirai kamar 50 zuwa 70 zuwa garuruwan Gaya da Kibiya; ba a rasa raguna da tumaki a daure saboda kiwo.

    A duk lokacin da matsuwa ta kama wani almajiri, to kuwa Alaramma ne zai ba shi rance. Bayan girma ya kama shi kuwa, ya kasance yana aikawa da gyaɗa da ƙuli-ƙuli Ikko don a yi masa kasuwanci.

    Mafi yawan tafiye-tafiyen neman karatunsa sun kasance ne a tsakanin Kano da Haɗeja. An ce bai taɓa zuwa Maiduguri ba in ba da niyyar ziyara ba.

    Ya kasance yana naƙalta wa almajiransa sirrin karatu ta hanyar:-

    – Yin tilawar izu ashirin kullum
    – Yin taƙarar izu ashirin kullum
    – Biya allo sau ɗari kafin a yi sabon rubutu
    – Yin rubutu kaɗan, kada ya wuce rubu’i
    – Kada Almajiri ya tashi in ana darasu har sai an gama gaba ɗaya

    Malam Gambon Takai ya rasu a shekarar 1998 ya bar ‘ya’ya shida:-

    – Malam Musa Gambon Takai
    – Malam Lawal Gambon Takai
    – Malam Sani Gambon Takai
    – Malam Saminu Gambon Takai
    – Malam Salisu Gambo Takai

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Malam Salihu Ɗangalinja danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Fa’idojin Wadatar Zuci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.