Tarihin Alaramma Gambon Takai

0
46

An haifi Malam Zakariya ɗan Adamu a garin Takai a shekarar 1928. Ɗan baiwa kuma ma’abocin himma da ƙanƙan-da-kai.

Malam Gambon Takai ya sha banban da sauran makaranta ta fuskar shuhura wajen buɗewa almajirai sirrin Alƙur’ani. Wannan ya sa dattijan malamai zuwa gari ya gari don su yi kwalli da shi. Wannan har yasa wasu na cewa Malam Gambon Takai ya yi gamo da aljannu ne a inda suka buɗe idonsa da sirrukan Alƙur’ani.

Abokan ƙuruciya lokacin neman karatun Malam Gambo kuwa ba su gushe ba suna bibiyarsa, har sai da wata rana bayan ya yi tafiya suka bincike lakkarsa ko za su ga wani nau’i na Alƙur’ani ko wani kundi na sirrukan Alƙur’ani da ya ke anfani da shi. Ubangiji Maɗaukaki Ya yi masa baiwar murya, koda yana karatu a hankali to kuwa wanda ke nesa zai jiyo muryarsa.

Da yawa yakan naƙaltawa makaranta sirrukan rubuta Alƙur’ani da haddace shi. Ya isheka misali ga tumbatsarsa wajen warware luggogin Alƙur’ani abin da muka gutsurowa mai karatu mai suna Logar Gambon takai a Babi na Uku, Sashe na Biyu cikin wannan littafin da ke maganan kan dabarun rubutun AIƙur’ani wurin ma’abota tsangaya.

Hatta malamai masu karatu kan zo tsangayarsa don kallon darasu; wanda ake farawa tun Asuba har sai an yi Azhar sannan a karya a koma.

Wani abu mai ban sha’awa game da rayuwar Malam Gambon Takai shi ne; himmarsa wajen dogaro da kai da yin kasuwanci. An ce a lokacin da ya ke fita rani da almajirai kamar 50 zuwa 70 zuwa garuruwan Gaya da Kibiya; ba a rasa raguna da tumaki a daure saboda kiwo.

A duk lokacin da matsuwa ta kama wani almajiri, to kuwa Alaramma ne zai ba shi rance. Bayan girma ya kama shi kuwa, ya kasance yana aikawa da gyaɗa da ƙuli-ƙuli Ikko don a yi masa kasuwanci.

Mafi yawan tafiye-tafiyen neman karatunsa sun kasance ne a tsakanin Kano da Haɗeja. An ce bai taɓa zuwa Maiduguri ba in ba da niyyar ziyara ba.

Ya kasance yana naƙalta wa almajiransa sirrin karatu ta hanyar:-

– Yin tilawar izu ashirin kullum
– Yin taƙarar izu ashirin kullum
– Biya allo sau ɗari kafin a yi sabon rubutu
– Yin rubutu kaɗan, kada ya wuce rubu’i
– Kada Almajiri ya tashi in ana darasu har sai an gama gaba ɗaya

Malam Gambon Takai ya rasu a shekarar 1998 ya bar ‘ya’ya shida:-

– Malam Musa Gambon Takai
– Malam Lawal Gambon Takai
– Malam Sani Gambon Takai
– Malam Saminu Gambon Takai
– Malam Salisu Gambo Takai

Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Malam Salihu Ɗangalinja danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Fa’idojin Wadatar Zuci danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceTarihi Da Falalar Husaini (Radiyallahu Anhu) A Taƙaice
Labarin na GabaNafilolin Aikin Hajji