Na Kan Wuni Cikin Kasala A Duk Sanda Nai Jima’i Ko Inzali

0
65

Wannan na daga cikin alamomin larurar da muke wa laqabi da Fost Ogasmik IliNes Sindurom,wato rukunin alamomin matsala dake biyo bayan inzali.

Wata matsala ce da wasu rukunin mutane cikin maza ke fuskanta,yadda zarar sukai inzali wato releasing takai ga maniyyi ya fita a jikinsu walau yayin saduwa da iyali, lko yayin istimna’i,ko kuwa dalilin mafarkin jima’i a sanda suke bacci,da dai duk wata hanya da maniyyi ka iya fitowa a jikin su toh zasu sami kansu cikin yanayi na rashin jindadin jikinsu a wannan rana har zuwa kwana biyu,ko kwana biyar kai wasu ma har tsawon sati ɗaya cikin rashin daɗi.

Domin a wasu in sukai inzalin nan abin kan biyo musu da alamu irin na me yin mura inda nan take zasu fara jin zazzaɓi-zazzaɓi,tsananin kasala,da ƙaiƙayi ko raɗaɗin idanu,wasu harda ciwon kai.

Domin karanta Alamomin Cancer Danna nan

Wanda kuma abin kan cigaba har su kasa samun nutsuwa suyi aikin dake gabansu a wannan lokaci,sam suke rasa concentration,har suma riƙa jin ɓacin rai ko hayaniya basa so kusa dasu,saidai duk wannan alamomin zaka samesu ka rasa bayan kwana 3 zuwa 7,shikenan mutum zai dawo normal,bazai ƙara jinsu ba har sai inya kuma samun fitar maniyyi.

Wannan al’amarin kansa da yawa cikin irin wadannan mazajen ƙauracewa jima’i, bawai don basu da sha’awa ba,saidon sukan sami kansu a halin rashin daɗin jiki,amma haka inka kallesu lfy ƙalau surarsu da suffar su take dama.

Wannan na daga cikin larurorin da masana a fannin lafiya suka tasa gaba domin zurfafa binkice akan dalilin dake jawo hakan,wannan tasa har yanzu bawani sanannen abu da za’a iya dangantawa dashi ke jawo hakan, hakazalik rashin sanin abinda ke jawo ta yasa ba’a san maganin matsalar ba,ko a asibiti bamu da maganin larurar.

Saidai sabbin binkice da suka fara fitowa suna alakanta cutar da matsalar allergies ne dake faruwa sakamakon garkuwar jikin mutum da ya dace ace yana basa kariya daga cuttuka itace ke kuskuren fahimtar inzali a matsayin matsala inda take kai farmaki ga ƙwayoyin sassan halittar maniyyi na jikin mutum bayan sun aikinsu,inda mutum ke karewa da wannan alamomin wato dai Autoimmune Disorder, saidai har yau binkicen bai kammala ba,kuma duk abinda aka ce autoimmune ne to gaskiya galibi bashi da magani,saidai aba mutum abinda zai rage masa kaifin matsalar, wanda kuma zuwa yanzu galibi saidai karfafa guiwa,da kuma bin alamun matsalar daya bayan daya bayan sun afku.

Domin karanta bayani akan Idan Kaji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ] Danna nan

Wato in mutum na jin zazzaɓi a bashi maganin zazzaɓi,ciwon kai a bashi maganin ciwon kai,kasala a bashi maganin sanya kuzari,zafin idanu abashi maganin hakan,wato dai symptomatic treatment.

Sai Kuma in abin yai tsamari akan baiwa mutum maganin da suke aiki a ƙwaƙwalwa wajen sarrafa yanayin mutum,suke gusar masa da tunanin wannan damuwar inda hakan kan taimaka wasu su riƙa samun jima’i da iyalinsu,wasu kuma akan basu shawarar tsara irin lokacin jima’in yadda alamomin zasu ke zuwa musu da sauki.

Amma dai matsalar bata da magani zuwa yanzu,amma in anje ga babban likita mutum na iya amfanuwa daga wani tsarin.

Domin karanta Illar Wayar Salula Guda Goma (10) Ga Lafiyar Jiki Danna nan

labarin da ya wuceIllar Wayar Salula Guda Goma (10) Ga Lafiyar Jiki
Labarin na GabaMe Ke Jawo Karancin Numfashi Ga Jarirai Bayan An Haifesu