Irin wannan matsala su akan kira da [Birth injuries] wato raunukan haihuwa.
Sukan samo asali ne kodai a dalilin:
- Cystic fibrosis inda gland din dake Samar da majinar dake taimakawa da saisaita numfashi ke samun matsala
- Ko fuskantar matsalar rashin jini ayayin goyon ciki zuwa lokacin haihuwa
- Ko karancin iska yayin da jaririn ya fado musamman in ya taho da sauri
- ko sanadiyyar shigar ƙwayoyin cuta cikin laka (spinal cord) zuwa ga mayanin da ya rufe ƙwaƙwalwa wato (meninges) da akan kira da meningitis (sankarau).
- [Neonatal disorder]
- Hakan na faruwa ne ta sanadiyyar rashin samun cikakken kulawa da mai dauke juna biyu,saboda akwai irin abincin da ya kamata mace ta yawaita amfani dasu a lokacin da take dauke da juna biyu
- Haka kuma akwai wanda bai kama ta yawaita amfani dasu ba
- Rashin zuwa Awo akai-akai
- Saboda yana dakyau macen dake dauke da juna biyu ta ringa zuwa ANC domin duba lafiyarta dana jinjirin da take dauke dashi a cikinta.
- Rashin samun cikakkiyar kulawa takan haifar da matsala babba a lokacin haihuwa,kuma yana da kyau musan cewa duk lokacin da mace take da juna biyu garkuwar jikinta yana raguwa saboda {Hormonal inbalance}, wato duk wani hormones nata zai farayin (hypersecretion) ruɓanya aikinsa.
- Ko kuma haihuwa agurin da yake ba cikakkiyar tsafta inda saboda raunin garkuwar jikin jariri kwayoyin cuta kanyi wuf su shiga huhunsa suyita hayayyafa cikin sekonni su galabaitar da jaririn inda hakan shi kan kaishi ga mutuwa.
- Jinkiri: Wani lokacin ma da sakacin matan sai an rasa yarda za ai ake nufomu inda tun agida wani yaron ya riga ya galabaita yagama cin karo da a lot of birth injuries,ko ya jirkice aciki ko yayin yunkurin nakuda.
Shawara
A gaskiya munso duk mai juna biyu ta shirya asibitin da zataje ta haihu musamman mata masu haihuwar fari.
Domin karanta dalilin dayasa kakejin Kasala A Duk Sanda Nai Jima’i Ko Inzali Danna nan