Cikakken bayani akan kansa wanda ya haɗa da hatsarin ta, alamomin kamuwa da ita
Mecece Cancer?
Cancer tana iya kama ko wane ɓangare na jikin ɗan Adam hakan yana faruwa idan jinin wurin ya gaza aikin sa, hakan yakan janyowa jiki ya kasa aikin da ya kamata, ita cancer akan iya maganin ta, domin kuwa an yi wa mutane da yawa sannan sun cigaba da rayuwar su kamar sauran jama’a.
Za mu ba ku cikakken bayani akan cancer da kuma yanda ake maganin ta. za ku samu cikakken bayani akan cancer da kuma ma’anar ta a ƙarshen wannan rahoto.
Yana da kyau ku san Ba Kowane Ciwon Ƙirji Ba ne Ulcer
Asalin Cancer
Cancer bawai cuta ce guda ɗaya ba ta rabu kala kala, cancer takan iya farawa daga huhu, nono, ciwo ko kuma ta jini, cancer takan iya kamuwa ta gurare da dama amma kuma hanyoyin yaɗuwarta sun bambanta.
Ta Yaya Cancer Ke Farawa?
Kowace ƙwayar halitta ta jikin mu akwai aikin da take yi ita asalin ƙwayar halittar takan kasu kashi kashi suna mutuwa idan aka fitar da su ko kuma suka lalace sai wata ƙwayar ta maye gurbinsu a irin wannan lokaci ne cancer ke samun gurin zama ta zuba tata ƙwayar halittar ta kori asalin ƙwayar halitta, hakan yana janyo matsaloli a sassan jikin da cancer ta kama, ƙwayar cutar kansa takan watsu a sauran sassan jiki.
Misali
Kansar hunhu takan tafi cikin ƙasusuwa ta girma, a yayin da ƙwayar cancer ta yaɗu ana kiranta (meh-tas-tuh-sis) ita kuma cancer huhu idan ta tafi cikin kasusuwa ana kiranta (Lung Cancer) a turance, a ɓangaren likitoci ƙwayar cancer da ta shiga cikin ƙashi daidai take da ta huhu sai dai idan ta yaɗu a cikin ƙashin.
Domin karanta bayani akan Samiha-Borin Jini {Hives,Urticaria,Neetle Rash} Danna nan
[…] Domin karanta Alamomin Cancer Danna nan […]