Cutar Mafitsara (UTI)

0
61

Urinary Tract Infection, cutar mafitsara a hausance, cuta ce dake addabar al’umma ƙwarai da gaske tunda ga kan maza har mata, cutar bai bar ƙananan yara ba bai bar manya ba. Sai dai cutar tafi shafar mata sosai da sosai, saboda yanayin halittar al’aurar su yadda take.

Ƙwayoyin cutar na hana sakuni ta hanyan sabbaba jin zafi lokacin da ake fitsari, yawan jin fitsari, fitar jini lokacin da ake fitsari da sauransu, kamar yadda zan bayyana nan gaba.

Cutar Urinary Tract Infection (UTI) cuta ce da ake samun ta daga ƙwayoyin cutuka (Microorganisms). Wasu ƙananan halittu ne da ido bai iya ganin su, sai dai da taimakon na’urar binciken ƙwaƙwaf (Microscope).

Mafi yawanci, ƙwayoyin cuta na bacteria sune ke haifar da su, amma wasu suna samuwa ne daga ƙwayoyin cuta na fungus (fungi). 

Cutar mafitsara (UTI) na cikin cututtukan da suka addabi mutane da dama a Duniya.

Domin karanta dalilin Rashin Jini A Jiki (ANEMIA) Danna nan

UTI na iya addabar a ko wane sassa na mafitsara, wanda ya haɗa da ƙoda (kidney), hanyar fitsari daya sauko daga ƙoda (ureter), matattarar fitsari (bladder) da kuma hanyar da fitsari ke fita daga jiki (urethra) waɗannan sune ake ƙira Urinary Tract, ma’ana Sassan mafitsara

Abubuwan Dake Kawo Cutar Mafitsara

Mafi girman abun dake kawo cutar mafitsara shine ƙwayoyin cuta na bacteria, musamman ƙwayar cuta wanda ake ƙira Esherisha Kolai (Escherichia coli ko kuma E. coli). Duk da wasu ƙwayoyin cutuka na iya kawo cutar amma E. Coli shine dalilin kaso casa’in (99%) na wannan matsalar. Shi kwayar cutar E. coli na zuwa ne daga uwar hanji ta hanyar abubuwan da muke ci ko kuma daga dubura.

Ko da yake a fitsarin da muke yi yana bamu kariya ta hanyar kashewa da kuma wanke waɗannan ƙwayoyin cutuka dake shirin shiga mafitsararmu, amma idan har ƙwayoyin cutar sun yi yawa, fitsarin bai iya wanke su ko kashe su gaba ɗaya, ai daman bahaushe yace idan dambu yayi yawa baya jin mai 

Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan

Mafi yawan UTI na haifar da cystitis wato kumburin matattarar fitsari (bladder), wasu lokutan kuma ƙwayar cutar na iya haurawa zuwa ƙoda inda yake haifar da matsalar kumburin ƙoda wato phyelonephritis

Rabe-Raben Cutar Mafitsara:

Cutar mafitsara ta (UTI) ta rabu gida biyu akwai mafi sauƙi da ƙarancin haɗarin kamuwa da ita wacce ake kira da lower tract infection, shine infection wanda yake cikin guri biyu, na farko urethra (hanyar da fitsari ke fita daga ciki,da kuma matattarar fitsari (bladder,) wannan shi ake ƙira Cystitis.

Sannan akwai wanda ake ƙira da Upper tract infection, shi wannan yafi haɗari domin yana faruwa ne a cikin ƙoda (kidney), misali kumburar ƙoda (phyelonephritis) da kuma Ureters (hanyar daya sauko da fitsari daga koda) wannan shine infection mafi haɗari a ciki. 

Kuma waɗanda suka fi shiga haɗarin kamuwa da wannan nau’i na biyun sune mata, saboda mafitsarar mace yana da kusanci sosai da al’aurar ta saɓanin na maza wanda yake da nisa, saboda haka ƙwayoyin cuta zasu iya haurawa cikin sauƙi.

Kusan da cewa Haihuwa A Gida Ba Jarumta Bane Kuskure Ne Danna nan domin karanta dalilai

Alamomin Cutar Mafitsara:

Kamar yadda nace akwai lower tract da kuma upper tract, haka suma alamomin cutar sun kasu kashi biyu, akwai wanda alamomin na lower tract ne akwai kuma alamomin upper tract.

Alamomin Cutar Mafitsara Na Lower Tract:
  •  Jin zafi ko raɗaɗi yayin da ake fitsari
  •  Yawan jin fitsari amma idan kin je ɗan kaɗan ke zuba 
  •  Rashin iya rike fitsari
  •  Ganin jini a fitsari
  •  Fitsarin ki zai sauya kala kamar na cola ko kuma kalar shayi 
  •  Fitsari mai zarni sosai
  •  Ciwon ƙugu ga mata.
  •  Ciwon dubura ga maza

Waɗannan sune alamomin cutar mafitsara na Lower Tract.

Alamomin Cutar Mafitsara Na Upper Tract:

 Ƙari a kan alamomin   lower tract 

  •  Zazzaɓi
  •  Tashin zuciya
  •  Amai
  •  Jin sanyi a jiki
  •  Jin zafi a ɓangare biyu na baya.

Sannan Upper Tract Infection wanda yake a ƙoda (kidney) ko ureters yafi haɗari da barazana ga rayuwa domin idan bacteria yayi yawa a ƙoda zai shiga jinin jiki ya haifar da matsala ta ƙarancin jini harma da ƙodar ta daina aiki yadda ya kamata (kidney failure). wanda haka yake kai mutum har lahira.

Tsanantar Cutar Mafitsara

Idan aka ƙyale cutar mafitsara ba a yi magani ba, ƙwayoyin cutar zasu cigaba da hayayyafa cutar na ƙara girma har ya kai matakin tsanani wato cutar ya tsananta zuwa waɗannan matakan:

(1) Jirkita siffar mafitsara wanda ya haɗa da dunƙulewar sinadarai a bladder ko a koda (calculi), jirkita aikin ƙoda ko wani sashi na mafitsara (tract anomalies), zama na dindindin da robar fitsari (indwelling catheter), rashin iya yin fitsari (obstructive uropathy).

(2) Matsalar rashin gudanuwa ko jujjuyawar sinadarai a jiki (metabolic diseases) wanda ke iya sabbaba matsalar ciwon sukari, matsalolin ƙoda da sauransu.

(3) Karya garkuwar jiki da sauransu.

Hanyoyin Kare Kai Daga Cutar Mafitsara

Idan mutum ya taɓa haɗuwa da matsalar mafitsara a rayuwa zai fahimci yadda yake matuƙar addabar rayuwar kwarai da gaske, ga wasu hanyoyin da mai karatu ya dace ya bi don kare kai daga kamuwa da shi nan gaba,kwantar da hankali, ku bi waɗannan matakan

(1) Ki kasance mai shan ruwa sosai akai-akai, an so mace take shan ruwa kofi 11.5  wato misalin lita uku kenan a rana. Namiji  kuma kofi 15.5 misalin lita huɗu kenan.

(2) Ki guji riƙe fitsari, a yi marmaza a je a yi fitsari da zaran an ji shi.

(3) Bayan gama bahaya ko fitsari ake fara wankewa daga gaba zuwa baya don gujewa shigar da ƙwayoyin cuta na bahaya a mafitsara, kamar yadda mukayi bayani a baya.

(4) Ake yin fitsari bayan saduwa hakan na taimakawa gun rage haɗarin zaman ƙwayoyin cuta a mafitsara kamar dai yadda muka bayyana ɗazun.

(5) A ƙauracewa cushe-cushe don ƙarin ni’ma ko matsin gaba.

(6) A kula da tsaftar muhalli musamman tsaftar bayan gida (toilet).

(7) A guji sanya matsastsun kayan ciki (undies), a samu masu taushi wanda iska ke iya ratsawa.

Saboda haka yan’uwa ku daina bin ruɗun masu magani barkatai suyi ta ce muku sanyin mara, sanyin mara, akwai abinda ya wuce nan a riƙa zuwa ganin likita idan an samu matsala domin gujewa halaka.

Domin karanta bayani akan Ciwon Suga.(Diabetes) Danna nan

labarin da ya wuceCiwon Suga.(Diabetes)
Labarin na GabaFitsarin Jini (BLOOD IN UTRINE)