Ciwon Mara (Pelvic Pain)

0
50

Mara ita ake kira “pelvis” a kimiyyance. An yi aron ta ne daga harshen “Latin” wanda mutanen tsohuwar daular Rumawa (Rome) suke magana da shi. Kalmar pelvis tana nufin mazubi mai siffar kwanon cin abinci (basin). Abinda yake da alaƙa da mara kuma shi ake kira “pelvic”.

HALITTAR MARA TA MUTUM (HUMAN PELVIC ANATOMY)

Mara mazubi ce ko kuma rami ne (cavity) wanda yake a tsakanin ƙasan cikin mutum da ƙashin ƙugunsa. Mara tana ɗauke ne da halittun da suke da alhakin haihuwa (reproductive organs), halittun da suke da alhakin yin fitsari (urinary organs), da halittun da suke da alhakin yin kashi (excretory organs).

A kwai bambance-bambance a tsakanin marar namiji da marar mace ta fuskar halitta da kuma abubuwan da suke ciki. Misali, ƙashin da ya kewaye ramin marar namiji ba shi da girma kuma ba shi da faɗi sosai, amma yana da ƙarfi sosai. Allah ya tsara shi a haka ne saboda bai ɗora ma namiji larurar ɗaukar juna biyu ba, domin haka babu buƙatar ƙashin ya zama mai faɗi. Sa’annan ƙarfin ƙashin ne yake taimakawa namiji wajen juriyar ɗaukan kaya masu nauyi fiye da yadda mace za ta iya ɗauka.

Shi kuma ƙashin da ya kewaye ramin marar mace, yana da faɗi kuma ba shi da ƙarfi sosai. Faɗinsa ne yake taimakawa mace wajen iya ɗaukar juna biyu cikin sauƙi, kuma rashin ƙarfinsa ne yake sanya ƙugunta ya buɗe a lokacin da take naƙuda domin samun sauƙin haihuwa.

Halittun da suke cikin marar namiji sun haɗa da jakar fitsari (bladder), mafitsara (urethra), jakar ruwan maniyyi (scrotum), jakar ruwan maziyyi (prostate gland) marufin da suke sarrafa zubar fitsari ko kashi (sphincters) da sauransu.

Marar mace ta ƙunshi dukkan halittun da namiji yake da su. Bugu da ƙari tana da jaka guda biyu da suke ɗauke da ƙwaya-ƙwayan haihuwa (ovaries), mahaifa (uterus), bututun da yake haɗa jakar ƙwan haihuwa da mahaifa (fallopian tubes), mahaɗar mahaifa da farji (cervix).

ABUBUWAN DA SUKE HADDASA CIWON MARA (CAUSES OF PELVIC PAIN)

Ciwon mara shi ne mutum ya riƙa jin rashin daɗi a mararsa (pelvic discomfort),  kuma ya rabu kamar haka:

✍. Jin raɗaɗi mai tsanani wanda yake zuwa farat ɗaya (sudden sharp pain).

✍. Ciwon mara kaɗan-kaɗan kuma yana yi yana dainawa (mild intermittent pain).

✍. Ciwon mara kaɗan-kaɗan amma ba ya dainawa (mild persistent pain).

✍. Jin nauyi a mara (feeling of pressure in the pelvis).

✍. Jin murdewar mara (twisted or knotted feeling).

✍. Ciwon mara haɗe da ciwon ciki (cramping).

✍. Ciwon mara wanda yake zuwa lokacin da mutum yake yin wani aiki, motsa jiki, jima’i, ko fitsari.

Abubuwa da yawa suna haifar da ciwon mara. Wani lokaci ciwon mara yana faruwa idan ƙwayoyin cuta suka kama halittun da suke cikin mara (infection). Wani lokaci kuma ciwon mara yana faruwa sakamakon sauye-sauyen da suke faruwa a cikin jiki tare da sauyin zubar sinadarai (physiological and hormonal changes). A nan za mu fahimci cewa ciwon mara ya rabu gida biyu. Ma’ana akwai ciwon mara na cuta, akwai kuma ciwon mara wanda ba na cuta ba.

CIWON MARA NA CUTA (INFECTIOUS PELVIC PAIN)

Cututtukan da suke haifar da ciwon mara sun haɗa da:

  1. Kumburin ciki (constipation), wanda yake faruwa saboda rashin narkewar abinci a ciki.
  2. Cututtukan mafitsara (urinary tract infections – UTIs).
  1. Cututtukan da ake ɗauka a wajen jima’i (sexually transmitted infections – STIs.
  1. Ciwon ƙaba na ciki (appendicitis).
  1. Ciwon suhe ko sufe (peritonitis), wato naman da yake shinfiɗe a bangon ciki.
  1. Ciwon jakar da take sarrafa fitar fitsari, maniyyi da maziyyi (prostatitis)
  1. Ciwon kumburin jakar ƙwan haihuwa (ovarian cyst)
  1. Ciwon ƙaba na mahaifa (uterine fibroids).
  1. Ciwon kumburin mahaifa (endometriosis).

10.Cututtukan da suke kama halittun haihuwa na mata (pelvic inflammatory diseases – PIDs). PID ya ƙunshi duk cututtukan da suka shafi halittun mace masu alhakin haihuwa. Yakan mamaye su.

Idan mutum ya kamu da ciwon mara sakamakon abubuwan da na lissafa, to, a gaskiya a je hospital don a yi bincike a gano me ya haddasa ciwon mara.

CIWON MARA WANDA BA NA CUTA BA (NON-INFECTIOUS PELVIC PAIN)

Abubuwan da suke sanya ciwon mara ba tare da ƙwayoyin cuta ba sun haɗa da:

  1. Jinin al’ada (menstruation). Lokacin da mace za ta fara jinin al’ada ko lokacin da take yi, takan yi fama da ciwon mara. Wasu kuma da zarar sun gama jinin al’adar za su yi ciwon marar na wani ɗan lokaci.
  1. Juna biyu (pregnancy). Idan mace tana da juna biyu, takan yi fama da ciwon mara a kai-a kai.
  1. Saka ƙwai na haihuwa (ovulation). Lokacin da mace take saka ƙwan haihuwa bayan ta gama jinin al’ada takan yi fama da ciwon mara.
  1. Motsawar sha’awa (sexual arousal). Akwai mutanen da suke da tsananin sha’awa wacce idan ta motsa takan haifar musu da ciwon mara
  1. Fitar maniyyi (ejaculation). Akwai maza waɗanda idan suka yi inzali, to, sai mararsu ta riƙa ciwo har zuwa wani ɗan lokaci kafin ta bari. Haka kuma akwai matan da idan namiji ya yi inzali a cikin al’aurarsu, to, sukan yi fama da ciwon mara na wani ɗan lokaci kafin ya daina. Abinda yake kawo haka ga mata shi ne akwai wasu sukunin sinadarai a cikin maniyyin namiji wanda ake kira prostaglandins wanda farjin wasu matan yana samun damuwa (reacting) saboda su. Domin haka da zarar an zubawa mace maniyyi sai ta fara jin ciwon mara. Wannan halitta ne, ba wata cuta ba ce.
  1. Istimna’i (masturbation). Idan mutum yana yin istimna’i, to, zai iya fuskantar ciwon mara, saboda yana motsa sha’awarsa, amma ba ya samun isasshiyar gamsuwa irin ta saduwar aure.
  1. Amfani da magungunan tazarar haihuwa (family planning methods). Ciwon mara yana daga cikin laulayin da magungunan family planning suke haifarwa.
  1. Haihuwa, ko ɓari, ko aikin tiyatar cire da (child birth, miscarriage, or caesarean section). Duka waɗannan suna sanya ciwon mara.
  1. Tsananin damuwa (depression). Idan mutum yana fama da damuwa ta al’amuran yau-da-kullum, to, zai iya fuskantar matsalar ciwon mara. Hakan ba ya nufin akwai wata ƙwayar cuta da ta shiga jikinsa. A a, tsabar damuwa ce kawai.

10.Taruwar fitsari a marar mutum, yana jinsa amma ya ƙi yinsa yana sanya ciwon mara.

Idan mutum ya kamu da ciwon mara a dalilin abubuwan da na lissafa, to, ciwon zai iya warkewa da kansa ba sai an yi amfani da magani ba. Idan kuma ya tsananta, to, ana iya amfani da magungunan kashe raɗaɗi kamar paracetamol ko ibuprofen.

YADDA AKE GANE CIWON MARA WANDA ƘWAYOYIN CUTA SUKA HADDASA (DIAGNOSIS OF INFECTIOUS PELVIC PAIN)

Ciwon mara na ƙwayoyin cuta yana da alamomi kamar haka:

  1. Naci, matsanancin raɗaɗi, da ɗaukan dogon lokaci kimanin makonni ko watanni, ko shekaru bai warke ba (very sharp and persistent pain).
  1. Zubar jini (bleeding) ga mace kaɗ an ko da yawa, wanda bata saba gani ba.
  1. Zubar ruwa mai wari ko ƙarni (discharge with offensive smell) ga mace, wanda ba ta saba gani ba.
  1. Jin zafi lokacin saduwar aure (painful sex).
  1. Jin zazzaɓi, wani lokaci haɗe da sanyi.
  1. Yin fitsari da jini (bloody urine).
  1. Jin zafin fitsari ko kasa yin fitsari (painful or difficult urination).
  1. Zubar jini a lokacin da ake yin jima’i, ko bayan an gama jima’i.

ABIN LURA

Ciwon mara yana iya kama maza, duk da kasancewar ya fi kama mata. Abubuwan da aka fi sani wadanda suke kawo ciwon mara ga maza su ne cututtukan mafitsara (urinary tract infections), cututtukan da ake ɗauka lokacin jima’i (sexually transmitted infections), cututtukan jakar da take sarrafa fitar fitsari, maniyyi da maziyyi (prostatitis), ciwon gwaiwa (hernia), matsanancin ciwon ciki (irritable bowel syndrome), ciwon ƙaba (appendicitis).

Ita kuwa mace tana kamuwa da ciwon mara ne bisa dalilan da suke sanya namiji yake kamuwa da shi. Bugu da ƙari, mace na kamuwa da ciwon mara sakamakon juna biyu (pregnancy), al’ada (menstruation), saka ƙwai (ovulation), ɓari (miscarriage), tiyatar cire jariri (cesarean section), ƙarin mahaifa (fibroids) da sauransu.

MAGANCE CIWON MARA (TREATMENT OF PELVIC PAIN)

Mata da yawa din sukan yi ƙorafin cewa suna fama da ciwon mara, domin haka suna buƙatar likitoci su faɗa musu maganin da za su yi amfani da shi domin samun sauƙi ko waraka. To, a gaskiya mawuyaci ne likita ya bai wa mace maganin ciwon mara ba tare da ya ganta ba. Dalili kuwa shi ne maganin ciwon mara ya danganta ne da abinda ya haifar da shi.

Idan ciwon mara ba na cuta ba ne, to, zai iya warkewa da kansa ba sai an sha magani ba. Idan kuma mutum ya damu sosai da irin wannan ciwon, to, yana iya yin amfani da maganin kashe raɗaɗi (pain reliever) saboda yin amfani da su ba ya da hatsari sosai.

Amma ciwon mara na cuta yana buƙatar a yi aune-aune (tests) ko hoto (scanning) kafin a tabbatar da shi. Sa’annan sai an yi amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics) waɗanda likita ne ya dace ya ɗora maras lafiya a kai kafin a magance shi. Wani lokaci ma sai an yi aikin tiyata (surgery) sa’annan za a iya magance shi.

Hanyoyin da za a iya magance ciwon mara wanda ba na cuta ba a gida sun ƙunshi:

  1. Gasa mara da ruwan dumi ko tsumman da aka jiƙa da ruwan ɗumi (warm compression).
  1. Yin wanka da ruwan ɗumi (hot bath).
  1. Yin atisaye ko motsa jiki (physical exercise).
  1. Kwanciya rigingine akan baya kuma a ɗaga ƙafafu sama domin jini ya zagaya jiki sosai (elevation of legs).
  1. Mammatsa mara (pelvic massage).
  1. Ƙauracewa ci ko shan maiƙo (oily foods).
  1. Ƙauracewa ci ko shan kayan zaƙi (sugary substances)
  1. Ƙauracewa ci ko shan abincin gwangwani (processed foods).
  1. Ƙauracewa ci ko shan abinci mai caffein.

10.Shan ruwan ɗumi.

11.Shan shayi mai citta.

Daga ƙarshe, dukkan wadannan bayanai da na gabatar ba za su iya gamsar da mu ba ɗari-bisa-ɗari akan matsalar ciwon mara. Sai dai kawai za su ɗan wayar mana da kai ne.

Danna nan don karanta Yadda Ciwon Sanyi Yake

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceAuren Annabi SAW Da Nana Saudat
Labarin na GabaWayewar Kan Ɗan Adam 2