Motsa jiki na taimakawa wajen ƙara kuzari da inganta yanayi (mood),motsa jiki nada matukar muhimmanci ga lafiya,sannan yana rage hadarin kamuwa da matsanantan cutuka.
Menene Motsa Jiki?
Motsa jiki na nufin duk wani kai-komo da zaisa duk wasu jijiyoyin mutum suyi aiki, sannan yasa jiki ya kone calories.
Akwai nau’ikan motsa jiki kala-kala
- Gudu
- Sassarfa
- Tafiya kasa
- Rawa ko wanka (iyo).
Ga Wasu Hanyoyi Biyar Da Motsa Jiki Zai Amfani Ƙwalwa Da Gangar Jiki
Motsa Jiki Na Taikawa Wajan Rage Ƙiba
Motsa jiki na matukar tallafawa jiki wajen sarrafa abinci da kara kone calories,bugu da kari yana taimakawa wajen gina tsoka da rage ƙiba.
Domin karanta bayani akan Gyanbon Ciki Wato Ulcer Disease Danna nan
Motsa Jiki Na Ƙara Farinciki
Motsa jiki na inganta yanayi da rage yanayin damuwa kamarsu depression,anxiety, da stress. Motsa jiki na ba ƙwalwa damar karban sinadarai kamar su serotonin, da norepinephrine, wadanda ke rage rage damuwa.
Bugu da kari motsa jiki na samar da endorphins,wadanda ke kara farinciki sannan suke rage pain.
Domin sanin menene Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo Danna nan