Gyanbon Ciki Wato Ulcer Disease

0
18

Ciwon olsa  ta zama daya daga cikin manyan cutukka da suke damun al’umma a ƙasar mu ta Najeriya.

Peptic ulcer disease:

(gyanbon ciki) general name na ulcer ciki gabaki daya.

Ita Peptic ulcer (gyanbon ciki ko ciwon ulcer) 

Ya kasu kashi uku kamar haka:

 • Gastric Ulcer (Gyenbo wadda yake kama fatar cikin ciki)
 • Duedenal Ulcer (Gyenbo wanda yake kama hanji)
 • Esophagus Ulcer  (Gyenbon maqogwaro)
Ciwon Olsa Yana Zuwa Da Alamomi Dayawa Gasu Kamar Haka: 
 • Konawar zuciya
 • Ciwon Cikin
 • Rashin cin abinci
 • Tashin Zuciya 
 • Amai
 • Ciwo har a gadon baya
 • Kashi da jini  ko bakkin kashi
 • Kumburin ciki
 • Ciwon cikin
 • Daukewar numfashi.
Me Yake Kawo Ciwon Olsa?

Kwayar cutar bakteriya mai suna H- pylori shi yake kawo ciwon olsa,haka kuma yawan shan maganin dauke ciwo kamar su  aspirin,shan taba (sigari) da kuma shan giya suna taimaka sosai wajen kawo ciwon olsa.

Domin karanta matsala da maganin Saurin Inzali (Premature Ejaculation) Danna nan

Ta Wacce Hanya Ake Daukan Ƙwayar Cutar Olsa?
 • Mutum yakan iya daukan wannan ƙwayar cutar ta hanyar musyar yawu (saliva) ko lokocin kiss.
 • Mutum yakan iya daukan wannan ƙwayar bakteriyan  ta hanyar ruwan sha da kuma abinci .

Idan ruwan sha ko abinci ya gurbanta da bayan gida ko fitsarin mai ciwon,wanda hakan yana faruwa ne ta hanyoyi da yawa.

Mesa Ita Ciwon Olsa Ba’a Warkewa Da Wuri?

Ba ba’a warkewa bane,ana warkewa daga cutar olsa ko wacce iri amma abinda yake faruwa shine 

 • Rashin shan magani yadda ya kamata,yau anwayi gari shan magani barkatai yazama ruwa dare a najeriya,mafi yawa ƙwayoyin cutar ansaba musu da wannan maganin har yazama suna jurewa .
 • Za kaga mutum ana bashi maganin wata daya ko sati biyu a ranan da yafara shan maganin idan yaji sauki shikenan ya rabu da maganin dai lokocin da alamomin cutar yasake zuwa zaici gaba da shan magani.

Domin sanin menene Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo Danna nan

labarin da ya wuceCutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo
Labarin na GabaMenene Amfanin Motsa Jiki?