Hyperstimulated Nervous System

0
26

(Wato Yanayi Ne  Da Sashin Dake Sarrafa Ƙwaƙwalwa Da Laka Kanyi Aiki Ba Bisa Ƙa’ida Ba)

A yanayin mutum zai riƙa fuskantar fargaba,tsoro,faɗuwar gaba,sarƙewar numfashi,rashin bacci,bugawar zuciya far-far-far haka kurum,gami da kasa sukuni,kasa nutsuwa ya zauna guri guda, ruɗewar ciki,har jininsa ya ɗan hau,ga ciwon kai,tare da riƙa jin kamar abu ya tsaya masa a maƙoshi,riƙa jin kamar mutum shifa lallai wani abu ba lafiya tattare dashi..

Amma kuma dalilin wannan yanayin ƙila yaje har asibiti an dubashi,har anyi gwaje-gwaje amma likita yace baiga matsalar komi ba,ba abinda yake damunsa. 

Wannan shi ake kira ‘Hyperstimulated Nervous System’, wato yanayi ne da sashin dake sarrafa ƙwaƙwalwa da lakar gadon baya a karan kansa batare da buƙatar umarni ba wato autonomic function ke birkicewa yaita rubunbunto ayyukansa batare da tsari ba.

Karanta cikekken bayani akan HIV/AIDS 

Galibi mutum bai buƙatar maganin komi, kurum maganganun kwantar da hankali da koya masa kau da kai daga damuwa da irin wannan yanayin da yake samun kansa kurum za ai,a hankali abin zai barsa komi jimawa,amma in abin ya cigaba toh sai an dora mutum bisa magungunan magance fargaba ko damuwa.

Domin karanta bayani akan dalilan da yake kawo rashin zuwan jinin al’ada da ‘ya mace ko ƙarancin bacci {Sleep Deprivation} ko ciwon zuciya danna wannan koren rubutun

Domin karanta Yadda Zaku Magancewa Marasa Lafiyarku masu Cutar Malaria Danna nan

labarin da ya wuceYadda Zaku Magancewa Marasa Lafiyarku masu Cutar Malaria
Labarin na GabaDalilan Da Yake Kawo Rashin Zuwan Jinin Al’ada Ga ‘Ya Mace