Falalar Ciyarwa Shayarwa Da Tufatarwa

0
24

An karɓo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan As (Radiyallahu Anhu) cewa: Wani mutum ya tanbayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: Wane musulunci ne mafi alkahairi?

Sai ya ce: “Ka ciyar da abinci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba” (Bukhari 12, Muslim39). 

An karɓo daga Abu Sa’id Alhkudiri (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Dukkan mutumin da ya ciyar da mumini mayunwanci, Allah zai ciyar da shi ‘ya’ yan itacen Aljanna, kuma duk mumini da ya shayar da mumini da yake cikin ƙishirwa Allah zai shayar da shi rufaffen ruwa garai-garai, kuma duk muminin da ya tufatar da mumini matsiraici, Allah zai tufatar da shi kayan ado ranar alƙiyama.” (Abu Dawud, Tirmizi, Hadisi ne mai rauni Da’iful jami’i: 2249).

NAFILOLIN AIKIN HAJJI 

Kamar yadda aka sani, aikin Hajji rukuni ne na musulunci ga wanda ya ke da iko. 

Malamai sun yi saɓani dangane da matsayin Umara shin farilla ce ko nafila? Malaman Mazahabar Hanafiya da Malikiyya suna ganin Umara ba wajibi ba ce , yayin, da Malaman Mazahabobin Shafi’ iyya da Hambaliyya da zahiriyya suna ganin Umar wajibi ce kamar aikin Hajji. 

Domin karanta bayani akan Falalar Kuka Ranar Ashura Danna nan 

Kowane ɓangare suna da hujjojinsu da suka dogara da su a ayoyin Ƙur’ani da hadisai, waɗanda suna nan cikin littattafan fiƙhu1. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ku jeranta hajji da Umara saboda jeranta su yana kore zunubai da talauci kamar yadda ƙira yake kawar da tsatsar ƙarfe.”(Tirmizi 738, Nasa’I 2585.) 

Wannan hadisin yana nuna cewa yin Umara bayan aikin hajji akai-akai yana maganin talauci, yana kankare zunubai. 

FALALAR YIN UMARA A WATAN RAMADAN 

An karɓo daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Yin umara a watan Ramadan dai-dai da ladan aikin hajji ne, ko kuma dai-dai da ladan aikin hajji tare da ni yake”.(Bukhari 1764, Muslim !69). 

FALALAR SHAN RUWAN ZAMZAM 

An karɓo daga jabir (Radiyallahu Anhu) ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:”Duk buƙatar da aka sha ruwan zamzam saboda ita, Allah zai biya wannan buƙatar (Sahihin hadisi ne duba sahihul Jami’i 5502). 

Duba babin aikin Hajji a littattafan “Al-Muhalla na Ibn Hazm, Bidayatul Mujahid na Ibn Rushd da sauransu. hadisi ne duba sahihul Jami’i 5502).

Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya kasance idan zai sha ruwan zamzam yana karanta wannan addu’ar: Allahuma inni as’aluka ilman nafi’an wa rizƙan wasi’an, wa shifa’an min kulli da’in”. Hakim ne ya ruwaito. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

FALALAR SALLA A MASALLACI HARAMIN MAKKA DA MADINA 

An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Salla a masallaci na ta fi salla a wani masallaci sau dubu ban da masallaci mai alfarma”(Bukhari 1190 Muslim 1394). 

An karɓo daga Abdullahi Ibn Zubair (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Salla a masallaci na ta fi salla dubu a sauran masallatai ban da masallacin harami, kuma salla a masallacin harami ta fi salla dubu ɗari a wannan masallacin” (Ahmad, Ibn Khuzaimaha, Suhihul Jami’I 3841). 

FALALAR ZAMA A MADINA 

An karɓo daga Sa’ad (Radiyallahu Anhu) Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: ” Zaman Madina ya fi alkhari a gare su inda sun sani, duk wanda ya bar Madina Saboda ƙyamar ta, sai Allah ya kawo mata wanda ya fi shi. Duk wanda ya jurewa tsananin Madina da laulayinta zan cece shi ko zan zama shaida a gare shi ranar ƙiyama.” (Muslim 1378.) 

FALALAR BIYAWA WANI HAJJI KO UMRA 

Haƙiƙa duk wanda ya kasancce sanadin aikata alhairi za a bashi lada dai-dai da ladan wanda ya aikata wannan aikin ba tare da an rage komai daga ladansa ba, akan haka, wanda ya biyawa wani kuɗin aikin hajji ko Umra, za a ba shi ladan da za a baiwa wanda ya aikata aikin hajji ko umra.

Saboda haka, magabata suka kasance suna ɗaukar nauyin waɗanda ba su taɓa yin aikin hajji ko umra. Misalin Waɗannan magabata akwai Muslim Ibn Yasar da Abdullahi Ibnul Mubarak, waɗanda suka kasance suna aikin hajji duk shekara, kuma suna tafiya da mutane da suke ɗaukar nauyinsu!. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

FALALAR KARATUN AL- ƘUR’ANI 

Karatun ƙur’ani ibada ce babba wacce babu sama da ita musamman in ta haɗu da ikhlasi da lura da ma’anoni da manufofin abinda ake karantawa (Tadabbur) da karantawa dai-dai da ƙa’idodin karatun (Tajwidi) da kuma abinda ya fi komai muhimmanci wato aiki da abinda ake karantawa. 

Hadisai da dama sun zo kan bayanin falalar karatun Al ƙur’ani a jumlace, da kuma falalar karanta waɗansu keɓaɓɓun surori da ayoyi. Ga kaɗan daga cikinsu: 

FALALAR KOYO DA KOYAR DA AL- ƘUR’ANI 

An karɓo daga Usman Ibn Affan (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “mafi alkhairinku shi ne wanda ya koyi Alƙur’ani kuma ya koyar da shi” (Bukhari: 4739). 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceFalalar Ba Da Sadaka Ga Ɗan Uwan Da Yake Gaba Da Kai
Labarin na GabaFalalar Karatun Al- Kur’ani