Falalar Kuka Ranar Ashura

0
27

A nan ma maƙaryata ba su yi ƙasa a guiwa ba, saboda sun ƙirƙiri cewa wai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: 

“Wanda ya yi kuka ranar da aka kashe Husaini za a tashe shi tare da manyan manzanni”. 

Kuka ranar Ashura, haske ne cikakke ranar ƙiyama. 

Waɗannan hadisai biyu hadisan ƙarya ne, suna cikin ɗimbin hadisai da wani shaiɗani mai suna Rutan Alhindi ya ƙirƙiro. Shi Rutan ɗan Mahuk, ya mutu a shekara ta ɗari shida da talatin da biyu daga hijira (632H) amma saboda ƙarya ya ce, “Shi sahabi ne”. Ya yi ta shirya ƙarya, wai hadisai ne! Tuni dai malamai irin su. 

-Imam Zahabi da Ibn Hajar da Suyudi suka fallasa dhi, Suka bayyana ƙagaggun hadisai, duba littafin Zailul La’alil Masnu’at Nalmam Suyuti shafi na 216 zuwa 226.

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

FAƊAKARWA 

1- Waɗansu malamai suna ganin cewa hadisin ciki wato hadisin da yake cewa: “Wanda ya hadisin cika-cika yalwatawa iyalansa ranar Ashura Allah zai yalwata masa wannan shekarar, suna ganin bai kai a kira shi hadisin ƙarya ba, sai dai a ce rarrauna ne ƙwarai waɗansu ma suna ganin zai iya zama hadisi Hasani n (kyakkyawa) ne. 

Amma maganna ta gaskiya hadisi ne rarrauna ƙwarai ko ma na ƙarya, a duba: – Almaudu’at na Ibnul Jauzi 2203. 

– Al Fawa’idul Najmu’a na Shaukani tare da bayanin Abdurrahman Ibn Yahya Almu’allimisha, Abdurrahman Ibn Yahya Almu’allimisha, shafi na99-100 

Domin ganin irin waɗannan hadisai na ƙarya kan Ashura duba: 

1- Al-Maudu’at na Ibnul Jauzi J. 2 sh. 199 204. 

2- Zailul La’alil Masnu’a na Imam Suyuti, J. 2.sh. 92-96. 

3- Alla Alil Masnu’a na Suyuti sh. 129. 

4- Alfawa’idul Maimu’a na Shaukani sh. 96 – 100. 

5- Tambihul Ghafilina – Samar Kandi 244 246. 

2 Ya ɗan uwa mai karatu, ka da zuwan waɗannan hadisai a ciki wasu mashahuran littatafai ya ruɗe ka, kamar littafin -Nuzhatul Majalis, da Tambihul Gafilina, da Arraudul Fa’ik da Algunya da sauransu, saboda waɗannan littatafai sun kawo hadisan da ba su inganta ba dama, shi yasa malamai suka faɗakar a kan a yi taka tsantsan da hadisan cikin waɗannan littatafai. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Duba littafin “Kutubun Hazzara Minhal Ulama na Abu Ubaida Mashhur Ibn Hassan AI-Salam J. 2 sh. 198 200 Magana a kan Tambihul Gafilina J.2 Sh. 19-20, 200=Magana a kan Arradul Fa’ik. 

3 Ya ɗan uwa duk lokacin da ka ga ko ka ji wani hadisi, kafin ka yi komai, ka bincika ko ka tambayi masanan ilmin hadisi kan matsayin hadisin. Saboda Manzon Allah (S.A.W) ya ce, za a yi masa ƙarya kuma an yi masa, sai dai Allah ya toni asirin maƙaryata tun da farar safiya, malamai sun fallasa su ta hanyar rubuta litattafai a kan hakan.

BAYANIN MATSAYIN MANYAN MALAMAN SUNNA A KAN SAYYIDINA HUSAINI (R.A) DA RANAR ASHURA

Haƙiƙa Sayyidina Husaini (R.A) yana da maɗaukakiyar daraja da alfarma a zukatan dukkan musulmi na ƙwarai, musamman a dalilin haka ya sa bakinsu ya zo ɗaya wurin bayyana ma malamai. Darajojinsu da falalarsa da nuna alhini da takaicin ƙarshen rayuwarsa ta kasance. 

Wannan yana tabbatar da ƙaryar masu cewa wai Ahlus sunna suna Cin ahlulbaiti ko kuma wai suna murna ga abin da ya faru ga Husaini da sauransu na. zaluntarsu da aka yi Wannan sharri ne ƙage ne. 

Amma a lokaci guda Ahlussunnah ba sa goyon bayan bidi’o’i da fitintinu da ake yi duk shekara idan ranar Ashura ta zo har zuwa kwana arba’in, da sunan nuna juyayi da ta’aziyyar Husaini tawagarsa,saboda babu wani daga cikin shugabannin Ahlulbaitin ko malamai na ƙwarai da suka aikata hakan. Su kuwa sun fi kowa son Ahlul baiti da goyon (R.A) da yan bayansu da damuwa da halin da suke ciki. 

Maganganun malamai suna da yawa dangane da falalar Husaini (R.A) da kuma matsayinsu a kan kashe shi da aka yi a ranar Ashura a shekara ta 61 daga hijra, saboda haka zan kawo kaɗan daga cikin su domin su wakilci sauran 

Domin Karanta Bayani akan Matakan Zaman Lafiyar Kishiyoyi, Haƙuri Da Junansu A Kan Kurakurai Danna nan

IBN ABDULBARRI ABU AMR YUSUF (A.H.S368 Y.M.S 495H) 

Ibn Ibn Abdulbarri haɗaɗɗen malami ne mai tsoron Allah da faɗin gaskiya, masanin hadisi, a cikin littafinsa na tarihin sahabbai mai suna “Al-lsti’ ab yana cewa: 

“Husaini ya kasance mutum ne mai daraja, da tsananin riƙo da addini, da yawan azumi da salla da aikin hajji. Ya yi aikin hajji sau ashirin da biyar a ƙasa, an kashe shi ranar Juma’a goma ga watan Muharram shekara ta 61 daga hijira”1

2-IBNUL ARABI AL-MALIKI (A.H.S. 468 Y.M.S543) Sahihin malami aIƙali, Abubakar Ibnul Arabi Almaliki bayan ya yi bayanin abin da ya faru a taƙaice na shahadar Husaini (R.A) sai ya ce: 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

“Ina ma dai a ce mai girma ɗan mai girma, sharifi ɗan sharifiya Alhusaini ya yi zamansa a gidansa, cikin iyalansa, ya ƙi sauraran duk wanda ya zo da maganar, ya nemi halifanci, koda kuwa irin su lbn Abbas ne da Ibn Umar, ina ma dai a ce ya tuna abin da kakansa ya faɗa a kan yayansa Hassan (ɗan nan nawa shugaba ne, Allah zai sasanta rundunoni biyu manya masu yaƙar juna saboda shi).

Da ya tuna ɗan uwansa ya rasa halifanci nan ahali yana da goyon bayan dukkanin rundononi kuma duk wasu manya a lokacin suna tare da shi, sai ya ga to shi yaya za a yi ya samu wannan halifanci ta hanyar goyon bayan tarkacen mutanen Kufa. Ga kuma manyan sahabbai sun hana shi, Suna janye jikinsu daga neman halifancin da yake? 

Kai ni dai na rasa ta cewa sai dai kawai na miƙa wuya ga hukuncin Allah, da kuma alhinin rasuwar jikan Manzon Allah (S.A.W) ba don manyan sahabbai sun san cewa, Allah bai ƙaddara halifanci ga iyalan Manzon Allah (S.A.W) ba, kuma bai kamata a shiga cikin fitina ba, ai da ba za su taɓa ƙyale shi ba. 

2- SHAIHUL ISLAM IBN TAIMIYYA (A.H.S 660 Y.M.S 728) 

A iya ɗan ƙaramin sani na, a cikin dukkan malamai da suka yi magana a kan abin da ya faru ga Hussaini (R.A) da kuma matsayinsu game da Yazidu da mahaifinsa Mu’awiyya, da kuma Shi’anci, babu wanda ya fi shan zagi da tsinuwa da tsana har ma da kafirtawa a wurin yan Shi’a kamar Ahmad Ibn Abdulhalim Ibn Abdussalam Ibn Taimiyya. 

Ibn Taimiyya ya wallafa wani babban littafi mai mujalladi tara “Nabawiyya fi Nakdhi Kalamis Shi’a Wal Kadariyya” kan bayanin aƙidun Shi’a, a ciki ya yi bayanai kan wannan mas’ala. Da kuma matsayin da ya ɗauka, mai suna “Minhajus Sunnatin” ba wani abu da ya keɓanta da shi ba, a’a akwai malamai da suka gabace shi da kuma waɗanda suka zo bayansa da suke a kan wannan matsayi, amma shi suka fi jin haushi, har ma da yi masa ƙazafin kin Ahlul baiti da ma Manzon Allah (S.A.W), saboda kawai tsananin ƙiyayya, da kwarewa a cikin ƙarya da ƙage. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

Wani babban malami wanda ya yi fice kan tattara littatafai da fatawowin Ibn Taimiyya, musamman waɗanda suke a rubutun hannu da buga su, mai suna Muhammad Ibn Kasim Rahimahullah, ya maganganun da lbn Taimiyya ya yi a kan Ahlul baiti, da sahabbai da matsayin Ahlusunna da ƴan Shi’a a kansu, kasancewar masu zargin Ibn Taimiyya da ƙin Annabi da tattara iyalansa, su ma yawancin maganganunsu daga wannan littafi ne. 

Amma fa a gaskiyar magana, ba sa kula da amanar ilmi a wajen ciro maganganun nasa, saboda ilmi a wajen ciro maganganun nasa, saboda suna yanko iya wurin da ya dace da son ransu, sai kawai su gina hukunci a kai, su yanke duk wurin da suka san asirinsu zai tonu in sun kawo shi.

Domin bayanin gaskiyar lamari kan matsayin Ibn Taimiyya a kan wannan mas’ala da ma waɗansu mas’alolin zan kawo gaba ɗayan babin da malamin ya kawo a cikin littafin, sannan kuma in kawo bayanin almajiransa, domin in tabbatarwa da mai karatu cewa Ibn Taimiyya cikakken masoyin Manzon Allah ne (S.A.W) da iyalansa. 

Amma kafin wannan ga abin da yake faɗa a cikin fatawarsa da manyan baƙaƙe: “Tsinuwar Allah da ta Mala’iku da ta mutane gaba ɗaya ta tabbata a kan wanda ya kashe Hussaini, ko ya taimaka aka kashe shi. Kada Allah ya karɓi ibadunsa na farilla da na nafila”. 

Ƙaunar Ahlulbaiti, tilas ce wajibi ne a kanmu, shi ne yasa kullum muke yi musu salati a cikin sallolinmu. Tsinuwar Allah da ta mala’iku da mutane baki ɗaya ta tabbata a kan maƙiya Ahlulbaiti. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceHadisai Na Ƙarya Da Raunana A Kan Ashura
Labarin na GabaManufar Makokin Husaini Da Ƴan Shi’a Suke Yi