Falalar Azumin Watan Ramadana 2

0
329

Azumin watan Ramadana na da falala mai yawa, daga cikin falalar akwai:

1. Azumi garkuwa ne. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam); ya umarci wanda sha’awar aure ta yi tsanani gare shi da ya yi azumi, sai ya sanya azumin garkuwa ne ga sha’awar; domin cewa shi azumi yana kange gaɓoɓi daga sha’awa.

2. Azumi sababin shiga Aljanna ne, sannan kuma yana nesantar da bawa daga wuta; kamar yadda ya zo cikin hadisin Abu Umamata (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) shiryar da ni kan aikin da zai kai ni ga shiga Aljanna”. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam ya ce; “Na hore ka da yin azumi, ba shi da tamka”. (Imam Ahmad 5/255-258. Ibnu Hibban 929).

Haka zalika, ya zo cikin hadisin da Imam Bazzar ya fitar cikin littafinsa cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce da Huzaifah; “Ya Huzaifa, duk wanda ya cika da azumin yini ɗaya mai nufin yardar Allah, Allah zai shigar da shi Aljannah”.
Game da nesantar da bawa daga wuta kuwa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Babu wani bawa da zai yi azumi na kwana ɗaya domin neman yardar Allah, face Allah ya nesantar da fuskarsa daga wuta tsawon shekaru saba’in”. (Bukhari, 6/35. Muslim, 1153).

A hadisin da Tirmizi ya fitar, cewa ya yi, “Duk wanda ya yi azumin kwana ɗaya domin neman yardar Allah; Allah zai sanya tazara tsakaninsa da wuta kamar tazarar sama zuwa ƙasa”.

A wani hadisin kuma ya ce; “Azumi garkuwa ne da bawa zai kare kansa daga wuta”. (Imam Ahmad 3/241).

3. Ana sakanya wa mai azumi da lada ba tare da ƙididdiga ba.

4. Mai azumi yana da farin ciki biyu. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ambata cikin wani hadisi cewa; “……. Kuma mai azumi yana da farin ciki biyu: idan ya yi buɗa-baki yana da farin ciki; haka idan ya haɗu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa”. (Bukhari 1805, Muslim 163).

5. Warin bakin mai azumi ya fi turaren almiski ƙamshi a wajen Allah. Kamar yadda hadisi ya tabbata daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Dukkan aikin ɗan Adam a gare shi ne, ban da azumi, domin nawa ne, kuma ni zan sakanya masa, azumi garkuwa ne.

Idan ya kasance ranar azumin ɗayanku, to kada ya yi batsa, kada ya yi jahilci (shirme); idan wani ya zage shi ko ya neme shi da faɗa, to ya ce masa “Ni azumi nake yi”. Na rantse da wanda ran Muhammad ke hannunsa; warin bakin mai azumi ya fi turaren almiski ƙamshi a wajen Allah.

Kuma mai azumi yana da farin ciki biyu; idan ya yi buɗa-baki yana da farin ciki; haka idan ya haɗu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa”. (Bukhari 1805, Muslim 163).

6. Azumi da Alkur’ani suna ceton ma’abocinsu, kamar yadda ya zo cikin hadisi cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Azumi da Alkur’ani za su ceci bawa ranar ƙiyama, azumi zai ce; Ya Ubangiji, na hana shi abinci da sha’awarsa, ka ba ni cetonsa…………….”.

7. Azumi yana kankare zunubai, Bukhari da Muslim sun fitar da hadisi daga Huzaifata Bin Yaman (Radiyallahu Anhu) cewa; Umar Bin Khaɗɗab (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Wane ne wanda ya kiyaye hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) wanda ya yi magana a kan fitina? Sai Huzaifa ya ce; “Ni ne. Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) yana cewa; “Fitinar da mutum zai samu a cikin iyalansa, da dukiyarsa, da makwancinsa, sallah da azumi da sadaka suna kankare su”.

8. Ƙofar Rayyan ta masu azumi ce, kamar yadda ya zo a hadisin Sahal Ibn Sa’ad (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Tabbas a cikin Aljanna akwai wata ƙofa, ana ƙiranta Rayyan, masu azumi ne za su shige ta ranar ƙiyama; babu wanda zai shige ta sai su, kuma idan suka shige ta za a rufe ta, babu wanda zai ƙara shiga. Kuma duk wanda ya shiga zai sha ruwa; kuma duk wanda ya sha ruwan, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada”. (Bukhari 4/95, Muslim 1/52).

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Watan Ramadana 1 danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Muharram danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunna); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceDalilan Wajabcin Azumin Ramadana
Labarin na GabaWaɗanne Abubuwa Ne Na Fili Dake Karya Azumi?