Falalar Watan Ramadana 1

0
328

Falalar Watan Ramadana – Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa, “Wanda ya azumci watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa da suka shuɗe”.

Haka nan, a wani hadisi, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Idan watan Ramadan ya shigo, ana buɗe ƙofofin rahama da ƙofofin Aljanna, kuma ana rufe ƙofofin Jahannama; kuma ana ɗaure shaiɗanu”. Haka kuma an rawaito daga Anas Ibn Malik Radiyallahu Anhu cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Lalle wannan wata na Ramadana, haƙiƙa ya halarto muku, a cikinsa akwai wani dare wanda ya fi watanni dubu alheri. Duk wanda aka haramta masa (samun alherin dake cikinsa); haƙiƙa an haramta masa alheri dukkansa. Kuma babu wanda ake haramta wa alherinsa sai wanda ba shi da rabo”. (Sunan Ibn Majah 1644).

A dunƙule, za mu iya lissafo wasu cikin manyan falalolin watan Ramadan kamar haka:

1. A cikinsa Allah ya saukar da Alkur’ani daga Lauhul Mahfuz, zuwa saman duniya.

2. Wata ne da ake ɗaure shaiɗanu, ayyukan sharri suna ƙaranci a ban-ƙasa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam ya ce; “Idan watan Ramadan ya zo, sai a buɗe ƙofofin Aljanna, sannan a rufe ƙofofin wuta, kuma a kulle shaiɗanu”. (Bukhari 4/97, Muslim 2/757).

Dukkan wannan yana kammaluwa daga lokacin da daren farko na wata mai albarka ya shigo, saboda faɗin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam)cewa; “Idan daren farko na Ramadana ya kasance, sai a kulle shaiɗanu da kangararrun aljanu, a rufe ƙofofin wuta, babu wadda za a bari daga cikinta, a buɗe ƙofofin Aljanna ba za a bar ko ɗaya a rufe ba. Sai wani mai kira hhya yi kira; “Ya mai neman alheri matso kusa, Ya mai neman sharri yi nesa!

Kuma Allah yana da wasu ‘yantattu daga wuta, wannan kuwa yana faruwa a kowanne dare”. (Tirmizi 682, Ibnu Majah 1642).

3. A cikinsa ne ake samun dare mafi daraja, wato Daren Lailatul Ƙadri. Anas Ibn Malik (Radiyallahu Anhu) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Lalle wannan wata na Ramadana, haƙiƙa ya halarto muku, a cikinsa akwai wani dare wanda ya fi watanni dubu alheri. Duk wanda aka haramta masa (samun alherin dake cikinsa), haƙiƙa an haramta masa alheri dukkansa. Kuma babu wanda ake haramta wa alherinsa, sai wanda ba shi da rabo”. (Sunan Ibn Majah 1644).

4. Amsar addu’a da kuma ‘yanta bayi daga wuta a kowanne dare cikin watan Ramadana.

5. Gafarta zunubai, kamar yadda ya zo cikin hadisin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa, ya hau minbari sai ya ce, “Amin! Amin! Amin!”. Sai aka tambaye shi, sai ya ce, “Haƙiiƙa Jibrilu (Alaihis Salam) ya zo ya ce mini: “Duk wanda ya riski watan Ramadan bai yi abin da za a gafarta masa ba, har aka shigar da shi wuta, to Allah ya nisantar da shi daga rahamarsa,”. Ka ce “Amin”. Sai na ce, “Amin”….(Imam Ahmad 2/246).

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Ramadana 2 danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Gaggauta Buɗa Baki danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah) wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceSharuɗan Wajabcin Azumin Watan Ramadan
Labarin na GabaDalilan Wajabcin Azumin Ramadana