Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su

0
291

Halayen mai Azumi – Akwai waɗansu muhimman halaye da ya kamata mai azumi ya siffanta da su; a gan su da gaske a tattare da shi. Cikin halayen akwai:

1. Haƙuri, wato mai azumi ya siffantu da haƙuri wanda shi zai zama jagaba a cikin lamuransa; ya hana shi bin son zuciya da saɓa wa Allah. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce “Idan ɗayan ku yana azumi, kada ya yi maganganun fasiƙanci. Idan wani ya zage shi, ya ce Ni mai azumi ne” (Sahihul Bukhari 1894, Sahih Muslim 1151).

2. Riƙon amana, yana da kyau mai azumi ya zama mai riƙon amana; domin tana daga cikin abar da za ta taimaka masa wajen kiyaye azuminsa.

3. Rahama, ana son mai azumi ya siffantu da rahama, da sakin hannu da karamci, da kuma yalwar zuciya. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da kwatankwacin ladan wanda ya ciyar ba tare da an rage ladan wanda aka ciyar ɗin ba” (Sunan al-Tirmizi 647, Sunan Ibn Majah 17).

4. Nasiha, yana da kyau mai azumi ya kasance mai yin nasiha da kuma umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.

5. Sulhu, mai azumi yana da kyau ya kasance mai yin sulhu da sasanta mutane; musamman la’akari da cewa ƙiyayya da gaba na kawo tsaiko wajen karɓar ibada da addu’a.

6. Kame harshe, ya kamata mai azumi ya kame harshensa daga maganganu na shirme da shashanci, sannan ya nesanci giba, zagin mutane da yi musu ƙage ko sharri da ƙarya ko musu marar dalili; musamman abin da ya shafi siyasa ko wasan ƙwallo ko wanin waɗannan.

An karbo hadisi daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Wanda duk bai bar faɗin magana ta zur da aiki da ita ba; to Allah ba shi da buƙatar ya bar cinsa da shansa”. (Bukhari 4/99).

Haka nan wani hadisin dai daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) dake cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ba azumi ba ne barin ci da sha, shi azumi shi ne na yasasshen zance da batsa; ko da wani ya zage ka, ko ya yi maka wauta, to ka ce; “Ni mai azumi ne”. (Ibn Khuzaima 1996). Ibnu Majah ya fitar da hadisi mai ɗauke da razani ga mai yin maganganun banza a yayin da yake azumi, ya ce; “Sau da yawa wani mai azumin ladansa shi ne yunwa da ƙishirwa”.

7. Rintse ido da kame farji, yana da kyau mai azumi ya rintse idanuwansa daga kallon haramun; ya kuma kare farjinsa daga dukkanin haramtattun abubuwa. A nan muna jan hankalin waɗanda ke ganin kallon fina-finai ko tashoshi na gusar musu da yunwa; haƙiƙa wannan kuskure ne babba da kuma munana zato ga Allah, da kuma keta iyakokin Sa. Su ma masu sanya fina-finai a tashoshi wajibi su ji tsoron Allah; su sani ribar rayuwa da albarkar abin da suke so shi ne ginawa bisa tafarkin Musulunci.

8. Iklasi, ya kamata mai azumi ya ƙudurce cewa lalle yana yin wannan azumin ne saboda Allah; kuma domin neman yardar Allah, ba domin mutane su yabe shi ba. A nan, ana jan hankalin yan’uwa masu yin sadaka ko ciyar da masu azumi da masu tafsirin Alkur’ani; da limamai masu rera tilawa, da masu zuwa Umarah, da sauran aiyuka nagari; wajibi su sanya iklasi kada shaiɗan ya lalata musu ayyukansu.

9. Bin sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam); wajibi ne mai azumi ya nesanci bidi’o’i, ya tsaya kan sunna ka’in da na’in; domin kyakkyawan aiki yana cikin koyi da Fiyayyen Halitta (Sallallahu Alaihi Wasalam).

10. Tarbiyya, wajibi ne mai azumi ya tsaya wajen ƙoƙarin tarbiyyantar da kansa da ‘ya’yansa; ko ‘yan’uwansa ko waɗanda yake da iko a kansu. Kuma iyaye su ɗauki wannan wata a matsayin lokacin roƙarwa ‘ya’yansu shiriya.

Domin karanta cikakken bayani akan Mafifitan Aiyukan Mai Azumi danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan

Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceNiyyar Ɗaukan Azumi
Labarin na GabaIslamiya Daɗi