Niyyar Ɗaukan Azumi

0
408

Ana ɗaukar niyyar azumi ne kafin fitowar alfijir; saboda hadisin da Nana Hafsat (R.A) ta rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa: “Wanda bai ɗauki niyyar azumi da dare ba (kafin fitowar alfijir) ba shi da azumi”.

(Sheikh Nasiruddeen Albani ya yi tahƙiƙinsa a cikin Sahih Jami’ al-Saghir, 6536).

Sannan a yayin niyya, ba a ƙulla ta da lafazin cewa, na yi niyyar yin azumi, a’a ana ƙulla ta ne a zuci, da zimmar gobe zan tashi da azumi idan Allah ya kai mu rai da lafiya.

Domin karanta cikakken bayani akan Mafifitan Ayyukan Mai Azumi danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Shin Rashin Yin Sallah A Cikin Jama’a Na Lalata Azumi? danna nan.

Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Watan Ramadan (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceZiyarar WikiHausa Zuwa Engausa
Labarin na GabaHalayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su