Tambayoyin Ramadan (117) Tare Da Amshoshin Su

0
299

1. Da me zan dogara wajen ɗaukar azumin Ramadan, shin sai na ga watan Ramadan da idanuna ƙuru-ƙuru?

Amsa: Mutum zai dogara ne da abin da shari’ar Musulunci ta umarce shi ya yi, shi ne ya ɗauki azumi da zarar hukuma ta sanar da ɗaukar azumin, ko kuma ajiye shi.

Hujja: “Ku ɗauki azumin Ramadan da zarar kun ga jaririn wata, ku ajiye azumi da zarar kun ga jaririn watan Shawwal” Marawaiji Ibn Umar, littafin Bukhari & Muslim.

2. Wane ne azumin Ramadan ya wajaba a kansa?

Amsa: Wanda azumin Ramadan ya wajaba a kansa, shi ne wanda gashin mara ya fito masa, mace ko namiji.

Hujja: “Shari’ar Musulunci ba ta aiki a kan mutum uku, su ne: Ƙaramin yaro har sai ya balaga” Marawaicin Aliyu ibn Abi Ɗaalib, Ummuna A’isha, littafi Musnadu Ahamada.

3. Mutum nawa ne ake buƙatar su ga wata kafin a ɗauki azumi?

Amsa: Mutum ɗaya idan ya ga watan azumi, ya wadartar ga mutanen wannan ƙasar, da mutum ɗayan nan ke ciki kowa ya ɗauki azumi.

Hujja: “Wani Balaraben ƙauye ya ce, “Ya ga jaririn watan Ramadan”, sai Manzo ya ce, “Ka shaida babu abin bauta da cancanta sai Allah, ka shaida Allah ne ya aiko ni?” Sai Balaraben ya ce, “Na shaida”. Sai aka umarci Bilal ya faɗa wa mutane, su tashi da azumi gobe”. Marawaici Ibn Abbas, littafi Ahamad, Turmuzi, Nassa’i Ibnu Maajah, Abu Dawud.

4. Akwai wata alama dake tattare da jaririn watan Ramadan?

Amsa: Babu wata alama da mutum zai gani, sai dai kawai zai ga jaririn watan Ramadan ne kamar yadda ake ganin sabon kowane wata idan ya kama.

Hujja: “Mutane sun ga jaririn wata, sai na ba wa Shugaban halitta labarin cewa, ni ma na gan shi” Marawaici ibn Umar, littafi alAbu Dawud, Haakim, Ibn Hibban.

5. Shin idan na ga watan Ramadan, zan yi shiru ne na ɗauki azumin ni kaɗai, ko yaya zan yi?

Amsa: Idan mutum ya ga watan azumin Ramadan, zai sanar da hukumar dake da alhakin sanar da al’umma, domin ɗaukar azumin.

Hujja: “Bilal faɗa wa mutane su tashi da azumi gobe…….. ” Marawaici Ibn Abbas. littafi Ibnu Kuzaima, Ibnu Hibban, Nassa’i.

6. Mene ne sahur?

Amsa: Sahur shi ne abincin da wanda zai tashi da azumi yake ci, kafin fitowar alfijir.

Hujja: “Ku yi sahur, domin a cikin sahur akwai albarka” Marawaici Anas Ibn Malik, littafi Bukhari Sahihul Muslim.

7. Shin dole ne sai mutum ya ci abinci sosai sannan za a ce ya yi sahur?

Amsa: Ko da ruwa mutum ya kurɓa, ko ya ci dabino, shi ake kira sahur, ba sai lalle ya ci abinci ba.

Hujja: Ko da ruwa ne mutum ya kurɓa, ya yi sahur, mala’iku na addu’a ga masu yin sahur”. Marawaici, Abu Sa’idul Ƙuduri, littafi Musnadu Ahamad, Sahihu Ibnu Hibban, Haisami, Attargib Wattarhib.

8. Idan na farka a makare lokacin sahur, ina fara cin abincin sahur, sai alfijir ya fito, yaya zan yi?.

Amsa: Mutum zai cinye abin da ya saka a bakinsa lokacin sahur, ko da alfijir ya fito, haka kuma, idan ruwa ne zai shanye wanda yake cikin kofin, ko da alfijir ya fito.

Hujja: “Idan ɗayanku yana cin abinci, sai ya ji kiran sallah, ya ƙarasa cin abincinsa”. Marawaici: Abu Huraira, littafi Musnadu Ahamad sunan, Abu Dawud, Ibn Hazmin, Ibnul Kayyim.

9. Ta yaya zan gane lokacin da zan dakatar da sahur, idan zan ɗauki azumi?

Amsa: Mutum zai dakatar da yin sahur, ta hanyar kiyaye lokutan fitowar alfijir da ake rubutawa na kowacce rana a kalanda, ko kafofin sadarwa kamar gidajen radiyo da talabijin da wayoyin hannu.

Hujja: “Ku ci, ku sha lokacin sahur, har sai hasken alfijir ya fito muku a fili”. Suratul Baƙara aya 187.

10. Zan iya amfani da kiran assalatu wajen dakatar da sahur?

Amsa: Mutum zai iya yin hakan, amma abin da ya fi shi ne, ya yi amfani da lokaci, maimaikon kiran assalatu, saboda wasu na saka assalatu a farkon kira, wasu kuma a ƙarshen kira, shi ma ladanin da lokacin yake amfani.

Hujja: “Bilal ne zai fara kiran sallar farko, ku ci, ku sha, har sai Ibnu Ummul Maktum ya yi kiran sallah ta biyu”. Makaho ne ba ya kira, har sai an ce masa alfijir ya fito. . marawaici: Ibn Umar, littafi Sahihul Bukhari da Sahihu muslim.

11. Shin idan na kwanta barci, sai na wayi gari janaba ta same ni, ta hanyar mafarki ko kwanciyar aure, zan iya ɗaukar azumi, ko sai na yi wanka?

Amsa: Mutum zai ɗauki azumi da janaba a jikinsa, wannan ba ya taɓa azuminsa.

Hujja: “Shugaban halitta yana wayar gari da janaba, sannan ya yi wanka” marawaici Ummuna A’isha da Ummus Salama, littafi: Sahihul Bukhari, Sunan Nassa’i, Tamhid ibn Abdulbarri.

12. Daga wane lokaci zuwa lokaci ne zan kasance da azumi a bakina?

Amsa: Mutum zai ɗauki azumi tun kafin hudowar alfijir, har ya zuwa faɗuwar rana.

Hujja: “Har sai hasken alfijir ya fito, ya bayyana, sannan ku kame daga ci da sha da mu’amalar auratayya, har ya zuwa faɗuwar rana”. Suratul Baqara, aya 187.

13. Waɗanne abubuwa ne na fili dake karya azumi?

Amsa: Abubuwan fili da suke karya azumi su ne: cin abinci ta hanyar tauna ko haɗiya, shan ruwa ko wani abin sha mai kama da ruwa, kwanciyar aure ga masu aure, fitar da maniyi ga wanda ba shi da aure ta hanyar kallace-kallace a fili ko mujalla ko wayoyin hannu ko talabijin, sauraran labaran batsa, ko na motsa sha’awa kai tsaye daga wani ko ta hanyoyin sadarwa da gangan.

Hujja: “Wanda ya ci, ko ya sha, ko ya kusanci iyalinsa, ya karya azuminsa”. Marawaici: Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim, sunan Abu Dawud, Sunan Turmuzi, Sunan Nassa’i Sunan Ibn Maajah.

14. Waɗanne abubuwa ne ke lalata azumi a ɓoye?

Amsa: Abubuwan dake lalata azumi a ɓoye su ne: Akwai yi da wani da shaidar zur da gulma da ƙin yin sallah sai lokacinta ya wuce, babu wani dalili na shari’ah, ƙin yin sallah kwata-kwata.

Hujja: “Wanda duk bai bar zancen zur ba, da aikata zur, da yi wa mutane mummunar fassara, Allah ba ya buƙatar ya bar abincinsa da abin shansa”. Marawaici Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim.

15. Shin rashin yin sallah a cikin jama’a na lalata azumi?

Amsa: rashin yin sallar jam’i ba ya lalata azumi, matsawar mutum yana yin sallar a kan lokaci, kawai dai yana tabka asarar lada mai yawa.

Hujja: “Sallar mutum a cikin jama’a, ta fi sallarsa shi ɗaya a kasuwa ko gida da lada ashirin da biyar ko lada ashirin da bakwai”. Marawaici Abu Huraira, Ibn Umar, littafi Sahihul Bukhari.

16. Idan ina alwala, sai na zo kurkure baki, sai na haɗiye ruwa garin kurkure baki, yaya lafiyar azumina?.

Amsa: Mutum ba zai rama azumi ba, idan ya haɗiye ruwa lokacin kurkurar baki, ba da ganganci ba, a cikin alwala ko ba a cikin alwala ba.

Hujja: “Allah ya yafe wa al’ummata abubuwa guda uku, kuskure da mantuwa da kuma abin da aka tilasta su a kai”. Marawaici Ibn Abbas, Sunan Ibn Maajah, Sahihu Ibnu Hibban, Mu’ujamu Ɗabara’ni.”Ba ku da laifin abin da kuka yi bisa kuskure, sai abin da zuciyarku ta yi da gangan”. Suratul Ahzab aya 5.

17. Idan ina magana da safe bayan na ɗauki azumi, sai na haɗiye sauro ko kuma na haɗiyi ƙuda da rana yaya azumina yake?

Amsa: Idan mutum ya haɗiyi sauro, ko ƙuda ko wani kwaro, ko wani abu kamar zare, ko gashi, azuminsa na nan daram, babu komai.

Hujja: Mardaawi cikin littafin Ijma’a, Ibn Muflih cikin littafin Furu’u, Jasas cikin tafsirin da Zaila’i cikin littafin Haka’iki).”

18. Idan na ɗanɗana miya domin na ji fitowar gishiri, amma na tofar ban haɗiye ba , yaya batun azumina?.

Amsa: Idan mutum ya ɗanɗana miya, gishiri,suga,zuma,zobo, juicy, azuminsa na nan matsawar bai haɗiye ba.

Hujja: “Wanda ya ci ko ya sha, bisa mantuwa, azuminsa yana nan”. Marawaici Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari Sahihu Muslim.

19. Idan na shaƙi Mantaleta ko Rob ko na saka a leɓe, shin yaya makomar azumina?.

Amsa: Idan mutum ya shaƙi Mantaleta ko Rob, ko kuma ya shafa a lebe, babu komai; azuminsa na nan daram.

Hujja: (Littafin fatawa lamba 55455, littafin fatawa lamba 107799),

20. Idan na shaƙi hayaƙin turaren wuta ko turaren ƙamshi na ruwa, ko na sakawa a ɗaki, yaya azumina?

Amsa: Idan mutum ya shaƙi hayaƙin turaren wuta, ko turaren ƙamshi na ruwa, babu komai, azuminsa na nan daram.

Hujja: (littafin Fatawa 55455, littafin Farawa 107799).

21. Shin zan iya shaƙar maganin shaƙa na masu asma idan na ɗauki azumi sakamakon ciwon asma?

Amsa: Idan mutum yana fama da ciwon asma, ya hallata ya shaƙi maganin na masu asma, a lokacin da yake azumi.

Hujja: Fatawa Shaikh Usaimin.

22. Idan na yi haɓo da azumi a bakina kafin a sha ruwa, yaya azumina zai kasance?

Amsa: Duk wanda haɓo ya same shi, kuma da azumi a bakinsa, babu komai, azuminsa na nan daram.

Hujja: ( Daarul Ifata’i Almisiriya). (alajnatu da’ima lilbuhusul ilmiya wal ifta’i 10/264).

23. Idan na saka kwalli a idona, kuma sai na yi kaki, sai na ga wannan kwallin da na saka a idona a cikin wannan kakin, yaya azumina?

Amsa: Idan mutum ya yi kaki, sai ya ga kwallin idon da ya saka a cikin kakin da ya yi, babu komai, azuminsa na nan daram.

Hujja: (sahifatu ittihaadul kahira) “Sayyidina Anas Ibn Malik yana saka kwalli idan yana azumi” Marawaici Abu Dawud, littafi Sunan Abu Dawud, malaman dake ganin halaccin saka kwalli, Ibrahimun Nak’i,aamash.

24. Idan na yi amai da azumi a bakina, shin yaya azumina?

Amsa: Idan mutum ya yi amai, amma bai haɗiye wani ɓangare na aman da ya yi ba, babu komai, azuminsa na nan daram.

Hujja: “Wanda duk ya yi amai, babu komai na ramuwa avkan shi” Marawaici Abu Huraira, littafi Sahihu Ibnu Hibban, Darulkuduni, Haakim, Daarami.

25. Idan na tara yawu a bakina, sai na haɗiye, yaya azumina?

Amsa: Idan mutum ya haɗiye yawu, ko wani kaki, azuminsa na nan daram.

Hujja: (Allamatul dasuqi alma’liky,ibnu habib, littafi Hashiyatu Dasuqi 525/1.

26. Idan gumina ya shiga bakina, na haɗiye yaya azumina?

Amsa: idan mutum ya haɗiyi guminsa da azumi a bakinsa, babu komai, azuminsa yana nan daram.

Hujja: (Almazid fil fatawa 164965).

27. Idan na ɗauki yaro jariri, sai ya yi min tumbuɗi a cikin hanci, yaya azumina?

Amsa: Idan mutum ya ɗauki jariri, sai ya yi masa tumbuɗi a cikin hancinsa, azumin shi yana nan daram.

Hujja: (Almazid fil Fatawa 123962).

28. Idan navyi amai, kuma bai gama fita ba; akwai ragowa a maƙogwarona, sai na haɗiye, ba tare da ya fito kan harshena ba, shin yaya matsayin azumina?

Amsa: Duk mutumin da ya yi amai, sai ya mayar da ragowar dake maƙogwaronsa kafin ya fito kan harshensa, ya ci gaba da azuminsa, babu komai.

Hujja: (Faawar Ibn Abbas da Ibn Mas’ud) littafi Yusuful Qardawi.

29. Idan na saka jan baki a leɓena, sai harshena ya taɓa, har na haɗiye, tare da yawun bakina, shin yaya azumi na?

Amsa: Duk matar da ta haɗiye jan baki, sakamakon taɓawa da harshenta yake yi, har ta haɗiyi yawu da shi, azuminta yana nan, babu komai.

Hujja: (Ibnu Najim) littafi Albaharu Ra’iqu, Fatawa 181305. Mazhab Hanafiya.

30. Idan mutum yana wanka, sai ruwan sabulu ya shiga hancinsa, azuminsa yana nan?

Amsa: Idan ruwan sabulun wanka ya shiga hancin mai azumi, babu komai, azuminsa yana nan.

Hujja: (Alfatawa 261682).

31. Idan mutum ya saka maganin ciwon Ido, sai ya ji maganin har maƙogwaro, yaya azuminsa.

Amsa: Duk mutumin da ya saka maganin ciwon Ido, kuma ya ji shi har maƙogwaro, babu komai, azuminsa na nan.

Hujja: (Mazhabu Hanafiya, Ibnu Taimayyah).

32. Idan haƙorina yana min ciwo, zan iya barbaɗa magani ko ɗigawa a kan haƙorin, alhali kuma na ɗauki azumi?

Amsa: Babu laifi idan mai azumi yana fama da ciwon haƙori wanda bai hana shi ɗaukar azumi ba, ya ɗiga magani, ko ya barbaɗa magani a kan haƙorin.

Hujja: (Alfatawa 6338).

33. Mutum ne yake da larurar haƙori, wanda jini yake fita daga haƙorinsa, wani lokacin idan ya tofar da yawu, yana ganin jini, kuma ga shi yana azumi, shin idan ya haɗiyi yawu da wannan jinin, azuminsa ya karye?

Amsa: Babu abin da ya karya masa azumi a nan, kawai dai ya dinga ƙoƙarin zubar da yawun, saboda kar ya haɗiyi ƙwayoyin cuta, ya kuma nemi magani.

Hujja: (Fatawa Almisiriya).

34. Idan ƙuraje suka fito min a kan harshena, idan na goga tumaturi suna warkewa, shin zan iya hakan ko da ina azumi?

Amsa: Mai azumin da ƙuraje suka fito masa Akan harshe, ya hallata ya goga tumaturi, amma kar ya haɗiye yawun bakinsa na lokacin, sai dai ya tofar.

Hujja: (Alfatawa 6338)

35. Wani lokacin idan na tofar daga baya kuma na kan ji ɗanɗanonsa idan na haɗiyi yawu, shin ya azumina?

Amsa: Duk abin da mai azumi ya ɗanɗana shi a kan harshe, ya tofar daga baya, kuma ya haɗiyi yawu, sai ya ji ɗanɗanon abin, a dalilin rashin kurkure baki, azuminsa yana nan daram.

Hujja: (6338).

36. Shin ya hallata na wanke baki da man wanke baki idan ina azumi?

Amsa: Ya halatta mai azumi ya wanke bakinsa da kowane irin sinadarin wanke baki, babu komai.

Hujja: ( Daarul Ifata’i).

37. Shin zan iya zuwa a yi min allura da azumi a bakina?

Amsa: Yin allura ga mai azumi ya halatta, sai idan likita ne ya ce, ya ajiye azumin, to, wajibi ne ya ajiye, amma ita allurar ba ta karya azumi, ko da mutm ya ji wani abu mai kama da ɗanɗanonta a maƙogwaronsa.

Hujja: (Alfatawa 143225).

38. Idan mutum yana da cutar (ulcer), zai iya yin gwajin bututun zurawa a ciki, wanda ake zura shi ta baki?

Amsa: Matsawar likita ya ce ya yi, ba tare da ya ajiye azumi ba, to, ya halatta, saboda shi yin gwajin, ba ya karya azumi.

Hujja: (Mazhabu Hanafiya, Almu’utamarul Islami fi Dauratih Al’ashirah).

39. Shin zan iya azumin tazarce?

Amsa: A’a. Bai hallata mutum ya yi azumin da babu buɗa-baki ba, wato azumin tazarce kenan.

Hujja: “Mun ga kana yin azumin tazarce,to, wane a cikinku irina? Ni Allah yana ciyar da ni, ya shayar da ni” Marawaici: Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim.

40. Shin zan iya bada gudunwamar jini kuma da azumi a bakina?

Amsa: Bayar da gudunwamar jini ba ya karya azumi, sai idan likita ne ya ce, mai bada gudunwamar ya ajiye azumin nasa.

Hujja: (Lajnatul Fatawa bi Majmu’il Buhusul Islamiya).

41. Shin mai azumi zai iya ajiye azuminsa saboda (minor surgery) ƙaramar tiyata wadda ake wa mutum idonsa biyu?

Amsa: ya hallata idan likita sahihi ya ce da shi, sai ya ajiye azuminsa.

Hujja: (Daarul Ifata’i Almisiriya).

42. Shin idan mutum yana da buƙatar ƙarin jini, kuma yana azumi, hakan zai taɓa azuminsa?

Amsa: Idan likita ya ce ana iya ƙara masa, ba tare da ajiye azumi ba, to, ya halatta, saboda shi ƙarin jinin ba ya karya azumi, sai idan likita ne ya ce ya ajiye azuminsa.

Hujja: (Lajnatul Fatawa bi Majmu’il Buhusul Islamiyya).

43. Idan mutum yana fama da rashin lafiya, yaya zai yi da azumi?

Amsa: Ya hallata mutum ya ajiye azumi saboda rashin lafiya da yake fama da ita, amma kuma rashin lafiya ta kasu gida 3, akwai ta ɗan lokaci, akwai dogowar jinya da take da magani, akwai dogowar jinya wacce ba a kai da gano maganinta ba, ko kuma babu maganin wannan jiyyar a ƙasar da majinyacin yake zaune, saboda dalilai masu yawa, misali ƙarancin ci gaban wannan ƙasa.

Hujja: “Waɗanda suke fama da rashin lafiya ko suke kan hanyar tafiya, su rama bayan sallah”. Suratul Baqara aya 184.

44. Idan jinya ce ta ɗan lokaci fa, zan ajiye azumin?

Amsa: Za ka ci ba shi, sannan kanrama idan ka warke bayan sallah.

Hujja: “Waɗanda suke fama da rashin lafiya ko suke kan hanyar tafiya, ya rama bayan sallah”. Suratul Baqara aya 184.

45. Idan jinya ce doguwa fa, zan ajiye azumi ne sai na rama?

Amsa: Idan dogowar jinya ce, wacce take ɗaukar shekaru ba ta warke ba, ciyarwa zai yi.

Hujja: “Ga waɗanda za su iya azumin, amma da ƙyar, sai su ciyar da abinci ga miskinai”. Suratul Baqara aya 184.

46. Idan jinya ce wacce ba ta da magani, ko kuma ba a gano maganinta ba, shin zan iya ciyarwa?.

Hujja: “Ga waɗanda za su iya azumin amma da kyar, sai su ciyar da abinci ga miskinai”. Suratul Baqara aya 184.

47. Duk jinyar da ba ta da magani ko ta dindindin ko babu maganinta a inda yake, kuma ba shi da ikon zuwa wata ƙasar neman magani, shi ma ciyarwa zai yi.

Hujja: “Ga waɗanda ba za su iya azumi ba, sai su ciyar da miskinai”. Suratul Baqara aya 184.

48. Idan mutum yana fama da ciwon saukar suga ko gyanbon ciki mai zafi, zai iya ɗaukar azumi?

Amsa: likita ne kaɗai zai iya ba shi amsar wannan tambayar, ta halaccin yin azumi ga wanda ke cikin irin wannan jinyar, ko haramcin hakan, kuma wajibi ne ya bi umarnin likita.

Hujja: Ga waɗanda ba za su iya azumi ba, sai su ciyar da miskinai”. Suratul Baqara aya 184.

49. Shin ya hallata mai ciki ta ɗauki azumi?

Amsa: Shari’ah ta ce, “Mai ciki ta haƙura da azumi, saboda ƙoshin lafiyar jaririnta”.

Hujja: “Duk wanda yake cikin halin rashin lafiya, ya rama bayan sallah”. Suratul Baqara 184.

50. Shin mai cikin da ta ajiye azumi ciyarwa za ta yi, ko bari za ta yi ta rama bayan ta haihu?

Amsa: Mai ciki da mai shayarwa, malaman da suka ɗauke su a matsayin marasa lafiya na ɗan lokaci sun ce, “Za ta rama bayan sallah”. Kamar Al-imamu Maalik, malaman da suka ɗauke su a matsayin marasa lafiya, sun ce, “Su ciyar kuma su rama bayan sallah”. Kamar Al-imamu Shafi’i, malaman da suka ɗauke su a matsayin waɗanda ba za su iya azumi ba, bisa uzuri na rauni kamar uzurin tsofaffi sun ce, “Ba za su rama ba, ciyarwa kawai za su yi cikin azumi” Kamar Ibnu Abass, Ibnu Umar.

Hujja: (Fatawar Ibnu Abbas da Ibnu Imar) littafi Bidaayatul Mujtahid wa Nihaayatul Muqtasid, Ibnu Rushdin.

51. Idan alfijir ya fito, kuma da janaba a jikina cikin Ramadan, yaya azumina?

Amsa: babu abin da ya haɗa azuminka da janaba, azuminka yana nan daram.

Hujja: (fatawar Al-imamun Nawawi, Majmu’ul Fatawa war Rasa’ili Mujalladi na 17).

52. Idan al ‘ada ta ɗauke, kuma ban yi wanka ba, har alfijir ya fito, shin yaya azumina zai yiwu?

Amsa: Macen da ta gama al’ada, da wacce ta haihu, jinin ya ɗauke, duk hukuncin su ɗaya da mai janaba, babu komai idan alfijir ya fito ba su yi wanka ba, kuma azuminsu bai ɓaci ba.

Hujja: (Fatawar A-‘imamun Nawawi, Ajmu’ul Fatawa war Rasa’ili Mujalladi na 17).

53. Idan Ramadan ya zo, kuma ana bi na bashin azumin Ramadan 5 ko 7 ko 10 na wanda ya wuce, yaya zan yi?

Amsa: Ba za ka rama ba, har sai Ramadan ɗin da ya zo, ya kare, amma kuma za ka ciyar gwargwadon yawan kwanakin da ake bin ka bashi, a cikin watan Ramadan ɗin da ya zo ya tarar da kai da bashi.

Hujja: (Mazhabu Malikiyya, Mazhabu Shafi’iyya, Mazhabu Hambaliyya, littafi Nailul Audar na Shaukani).

54. Ya yawan abin da zan ciyar yake?

Amsa: Za ka ciyar da abincin da yawan sa ya kai cikin tafin hannunka guda biyu har sau huɗu, shi ne ( Mudun Nabiyi) amma tafukan hannun mutum matsakaici, ba babba can ba, kuma ba ɗan ƙarami ba.

Hujja: ( haka Anas Ibn Malik ya yi lokacin da ya ciyar saboda tsufa, littafi Nailul Audar na Shaukani).

55. Su wane ne waɗanda suka cancanta a ciyar?

Amsa: Za ka ciyar da duk wani mabuƙaci, yaro ko babba mace ko namiji.

Hujja: “Ka ciyar da miskini ɗaya a rana” marawaici Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari.

56. Idan ƙasar da nake babu mabuƙata a kusa, zan iya turawa wata ƙasar a ciyar?

Amsa: Kwarai da gaske, za ka iya turawa da ciyarwa zuwa inda mabuƙata suke.

Hujja: “Babu wasu mutane dake da buƙatar wannan fiye da ni da iyalina” marawaici Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari.

57. Zan iya ƙimanta abincin da zan ciyar na bayar da kuɗin a cibiyoyin addini a ciyar min?

Amsa: Ya halatta ka ba wa cibiyoyin addini kuɗin bisa ƙiyasin abincin da za ka ciyar, sai su ciyar a madadin ka.

Hujja: (Fatawar Sufyanus Sauri, littafi Arruhu na Ibnu Qayyim.

58. Wannan ciyarwar mece ce matsayin ta tunda ko na ciyar zan rama bayan sallah?

Amsa: Matsayin wannan ciyarwar, kaffara ce na ƙin rama azumi da gangan, har wani Ramadan ɗin ya sake zuwa.

Hujja: (Mazhabu Malikiya, Mazhabu Shafi’iya, Mazhabu Hambaliyya, littafi Nailul Audar na Aliyu Shaukani).

59. Idan na manta na sha ruwa ko na ci abinci cikin watan Ramadan, yaya azumina?

Amsa: Wanda duk ya manta ya sha ruwa ko ya ci abinci, azuminsa yana nan daram.

Hujja: “Wanda ya ci ko ya sha bisa mantuwa cikin Ramadan, ya ƙarasa azuminsa, babu ramuwa a kan shi, Allah ne ya ciyar da shi ya shayar da shi” marawaici Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari.

60. Idan ana bi na bashin azumin Ramadan 5 ko 7, har wani Ramadan din ya sake zuwa, zan iya ciyar da mutum 5 ɗin ko 7 a rana ɗaya lokaci ɗaya?

Amsa: Ya halatta mutum ya ciyar da mutane lokaci guda, gwargwadon yawan kwanakin da ake bin shi bashin azumin Ramadan din da ya sha.

Hujja: “Tafi da wannan, ka ciyar da miskinai sittin” Marawaici Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari.

61. Idan mutum ya samu kanshi ko ya yi tafiya zuwa inda rana take kaiwa wata shida ko kasa da haka, ba tare da dare ya shigo ba, ko kuma dare yake yin wata shida ko ƙasa da haka, ba tare da rana ta hudo ba, yaya zai yi da azumi?

Amsa: Idan mutum ya samu kansa a irin waɗannan ƙasashe da ake dare ko rana na tsahon lokaci, zai yi amfani ne da (time zone) wato ƙasashen da lokutansu ya zo ɗaya, amma su suna samun shigowar rana da dare, sai ya ɗauki azumi lokacin da suke ɗauka, ya sha ruwa lokacin da suke sha, haka kuma zai iya amfani da ƙasar da take kusa da su, wacce ba ta da irin wannan yanayin, ya kalli awowin da suke yin azumin Ramadan na wannan shekarar, misali suna yin azumin awa 11 ko 12 a rana, to shi ma haka zai yi, kuma ta fuskar ganin watan Ramadan ma ko Shawwal, haka zai yi.

Hujja: (Daarul Ifata’i Almisiriya).

62. Idan mutum zai yi tafiya, ko da a jirgi ne, zai ajiye azumi?

Amsa: Ita tafiya komai sauƙinta, sunanta tafiya, idan mutum ya ajiye azumi, ya aikata sunna, idan kuma ya yi azuminsa, babu laifi, azuminsa ya yi, sai dai idan yin azumin, zai jefa shi cikin asara, ta rai ko lafiya ko hankali, to a nan, wajibi ne ya ajiye azumin, sai ya rama bayan sallah.

Hujja: “Shugaban halitta ya sa ankawo masa ruwa a kofi, ya ɗaga sama, yadda kowa zai gani, sannan ya sha a kan hanyarsu ta tafiya, aka ce masa, wasu ba su ajiye azumin ba, ya ce su ne suka zaɓar wa kansu shan wahala”. Marawaici Jabir Ibn Abdullah, littafi Sahihu Muslim.

63. Mutum zai iya rama wa iyayensa azumin Ramadan?

Amsa: Tabbas mutum zai iya rama wa iyayensa ko wani nasa azumin Ramadan da ya sha kafin rasuwar sa.

Hujja: “Wanda duk ya mutu akwai ramuwar azumi a kansa, manema haƙƙin jininsa suna iya rama masa”. Marawaici Ummuna A’isha, littafi Sahihul Bukhari.

64. Shin mutum zai iya ciyarwa a maimaikon ya rama musu azumin Ramadan ɗin?

Amsa: Ya halatta mutum ya ciyar da abinci a madadin rama wa iyayens ko wani nasa azumin Ramadan.

Hujja: (Fatawar Sufyanus Sauri da Hassan, littafi Acrruhu).

65. Idan mutum ya yi tafiya, sai ya ajiye azuminsa, a lokacin iyalinsa tana al’ada, sai bayan rana ta yi zawali, har azahar ta yi, sai al’adar ta ɗauke, ta yi wankan tsarki, shin ya halatta su yi mu’malar aure da rana?

Amsa: Ko shakka babu, ya halatta, saboda wannan azumin za su rama shi ne bayan sallah, bisa uzuri da shari’ah ta yi musu, akwai wasu daga cikin malaman dake ganin su haƙura, domin su girmama watan, amma ijtihaadi ne kawai yin hakan, ba wulakanta watan ba ne, hasali ma ibada suka yi, domin abin da suka yi sunansa sunna.

Hujja: Al ‘lajnatud Da’ima 10202, Majmu’ul Fatawa Ibn Baaz 15/307, Fatawa Siyam Ibn Usaimin 344.

66. Shin idan mutum yana azumin Ramadan sai ya manta ya kusanci matar shi da rana?

Amsa: Babu ramuwa, kuma babu kaffara, azuminsa yana nan daram.

Hujja: Mazhabu Hambaliyya Mazhabu Shafi’iyua, Ibnu Taimayyah, Shaukani, Sun’ani, littafi , Nailul Audar,Subulus Salam.

67. Shin idan mutum yana cikin kusantar iyalinsa alfijir ya fito, yaya azuminsa?

Amsa: Daga lokacin da alfijir ya fito, sai ya dakatar daga ci gaba da kusantar ta, babu komai, azumin shi yana nan daram.

Hujja: Nawawi, Mawurdi, littafi Almajmu’u, Attaju wal iklil li muktasar Khalil.

68. Idan mutum ya ji kiran sallah na fitowar alfijir ya ci gaba da kusantar iyalinsa da gangan fa?

Amsa: zai rama wannan azumin bayan sallah, sannan kuma zai yi kaffara.

Hujja: Nawawi, Mawurdi, littafi Almajmu’u.

69. Idan mai azumi ya ji kiran sallah, amma bai ci gaba ba, sannan kuma bai zare al’aurarsa daga na iyalinsa ba nan take, har sai bayan mintina biyu ko uku fa?

Amsa: Zai rama wannan azumin guda ɗaya, amma babu kaffara.

Hujja: Nawawi mawurdi,

70. Mece ce ƙiyamul laili?

Amsa: Ƙiyamul laili ita ce duk sallar da mutum ya yi ta bayan sallar isha’i, ita ce ƙiyamul laili.

Hujja: (Muhammad Abdus sami’i Aminul Fatawa bi Daaril Ifta’i Almisiriya).

71. Akwai bambanci tsakanin ƙiyamul laili ne da tarawihi ko asham?

Amsa: Babu wani bambanci, duk abu ɗaya ne, sunan ne kawai kowanne da abin da yake nufi, idan aka ce ƙiyamul laili, ana nufin tsayuwar sallah cikin dare, tarawihi kuma, sallar da idan mutum ya yi raka’a biyu ko raka’a hudu, yakan ɗan zauna ya huta, kafin ya ci gaba.

Hujja: Nailul Audar Daarul Ifata’i Almisiriya.

72. Akwai bambanci ne da tsakanin tarawihi da sallar tahajjud?

Amsa: A’a. Babu bambanci duk ita ce ƙiyamul laili, fassarar tahajjud tana nufin dagewa ko kokari wajen yin sallar dare, ta hanyar daɗewa a tsaye kana karatun Alƙur’ani.

Hujja: “Yana ninka yin ibada a goman ƙarshe irin ninkawar da ba ya yi a wasu ranakun”. Marawaici Ummuna A’isha, littafi Sahihu Muslim, Ibn Maajah.

73. Me yasa aka fi son mai azumi ya dage a goman ƙarshen Ramadan, fiye da goman farko da goman tsakiya?

Amsa: Ana son mai azumi ya ƙara dagewa ne a goman ƙarshen Ramadan, saboda ninka lada da Allah Azza wa Jalla yake wa bayinsa, ga kuma ‘yanta bayinsa daga shiga wuta da yake ninkawa fiye da goman farko da goman tsakiya. Hujja: Alfatawa 77920 .

74. Idan mutum ba ya azumi saboda uzuri na shari’ah, shin zai iya duk ibadar da mai azumi yake yi kamar sadaka, ƙiyamul laili, karatun Alƙur’ani, salati, istigifari, da sauran ayyukan lada?

Amsa: Ko shakka babu, ya halatta ya yi komai idan har yana da damar yi, misali idan mace ce, babu damar ta yi ƙiyamul laili, matsawar uzurinta na rashin tsarki ne.

Hujja: Alfatawa, Daarul Ifata’i Almisiriya.

75. Shin idan ana bi na azumin Ramadan da na sha bisa uzurin al’ada, zan iya bari har sai Sha’aban ya zo na rama?

Amsa: Ƙwarai kuwa, ya halatta macen da ta sha azumi bisa wannan uzurin na al’ada, ta bari har sai Sha’aban ta rama, babu laifi idan ta yi hakan.

Hujja: Alfatawa 42206, Albayan.

76. To, idan kuma mijinta ya tuna mata cikin Rajab, ta ce sai a Sha’aban, sai kuma ta ɗauki ciki, har wani Ramadan ɗin ya zo ba ta rama ba fa?

Amsa: Babu komai na, kaffarar jinkirin ramuwa a kanta.

Hujja: Alfatawa 42206.

77. Idan kuma tabari sai sha’aban ta rama sai kuma ta rasu fa?

Amsa: babu laifi sai arama mata ko aciyar.

Hujja: Daarul Ifata’i Almisiriya.

78. Da wane lokaci ne mutum zai yi buɗa baki a shari’ah?

Amsa: Mutum zai yi buɗa baki ne da zarar rana ta faɗi.

Hujja: “Idan rana ta ba da baya, ta yi yamma, dare kuma ya ɓullo ta nan, to mai azumi ya buɗe baki”. Marawaici Ibn Umar, littafi Sahihul Bukhari.

79. Da me aka fi son mai azumi ya yi buɗa baki kafin ya ci abinci sosai?

Amsa: An fi so mai azumi ya yi buɗa baki da ɗan itace kowanne ne ya samu, ba lalle sai dabino ba, idan babu kuma, ya samu ruwa, ya yi buɗa baki da shi.

Hujja: “Idan ɗayanku zai yi buɗa baki, ya yi buɗa baki da dabino ko ruwa, domin ruwa na tsarkakewa”. Marawaici Sulaiman Ibnu Aamir, Anas Ibn Malik , littafi Sunan Abu Dawud, Sunan Turmuzi.

80. Shin akwai addu’a da ake yi kafin mutum ya yi buɗa baki?

Amsa: Akwai addu’a da mai yin buɗa baki zai yi, amma sai bayan ya yi buɗa bakin ake yin addu’ar.

Hujja: “Zahabaz zama’u, wabtallatul uruqu, wasabbatal ajaru insha Allah”. Marawaici Ibn Umar, littafi Sunan Abu Dawud, Sunan Nassa’i, Haakim, Baihaqi.

81. Shin lokacin buɗa baki, lokaci ne na amsa addu’ar mai azumi a kan wata buƙatarsa?

Amsa: Ko shakka babu, idan mai azumi ya yi buɗa baki, ya yi amfani da wannan damar, ya roƙi Allah Azza wa Jalla buƙatunsa, domin lokaci ne na amsar addu’a.

Hujja: “Mutum uku addu’arsu ba a dawo musu da ita, Allah yana amsa musu. Mai azumi har sai ya yi buɗa baki”. Marawaici Abu Huraira, littafi Sharhu Mahzab lin Nawawi.

82. Mene ne ittikaafi?

Amsa: Shi ne shiga masallaci da niyyar zaman ibada na wasu kwanaki, ba tare da mutum ya fita ko’ina ba.

Hujja: (littafi Adduru Sinniya, Mausu’a Fiqihiya).

83. A waɗanne ranaku ne ake yin ittikaafi?

Amsa: Ana yin ittikaafi ne a goman ƙarshen Ramadan.

Hujja: “Shugaban halitta yana zaman ibada a masallaci a goman ƙarshen Ramadan, har Allah ya karɓi rayuwarsa”. Marawaici Ummuna A’isha, littafi Sahihu Muslim, Sahihul Bukhari.

84. Wane lokaci ne ake shiga, sannan wane lokaci ake fita?

Amsa: Ana shiga ne bayan sallar asuba, wasu malaman kuma sun ce, kafin rana ta faɗi Shugaban halitta yake shiga, wajen zamansa ne, sai bayan sallar asuba yake zuwa, yana fita ne bayan magriba, a daren idi, kafin shigowar yinin idi.

Hujja: marawaici Abu Huraira littafi Sahihul Bukhari, Sahihu Muslim, Abu Hanifa, Maalik, Sha’fi’i, Ahamad.

85. Akwai bambanci ne tsakanin yinin idi da daren idi?

Amsa: Ƙwarai kuwa, domin kowace rana sai daren ya shigo kafin yininta ya shigo, in ban da ranar Arfa, ita kaɗai ce yininta ke riga darenta zuwa.

86. Shin sai mutum na azumi zai shiga ittikaafi?

Amsa: Ana shiga ittikaafi ne da azumi.

Hujja: (Mausu’a Fiqihiya).. “Yana zaman ittikaafi cikin Ramadan”. Marawaici Abu Huraira littafi Sahihul Bukhari, Sahihu Muslim.

87. A wane masallaci ake son a yi ittikaafi?

Amsa: Ana so a yi ittikaafi ne, a masallacin da mutum ba zai rasa sallar juma’a ba a jam’i.

Hujja: (Abu Dawud Assajistan).

88. Waɗanne abubuwa ne mai ittikaafi zai nisanta?

Amsa: Mai ittikaafi zai nisanci fita daga inda yake ittikaafi, sai idan fitar ta zamar masa dole.

Hujja: (Ibnul Munzir)

89. Shin mace ma za ta iya shiga ittikaafi?

Amsa: Za ta iya shiga ittikaafi idan ba ta da miji, idan kuma tana da miji, sai idan ya yi mata izini.

Hujja: “Matan Shugaban halitta sun yi ittikaafi bayansa”. Marawaici Ummuna A’isha. littafi Sahihul Bukhari Sahihu Muslim, Fathul Baari.

90. Shin akwai wata ibada ce da aka fi son mai ittikaafi ya dinga yi?

Amsa: Duk ibadar da tafi masa sauƙi a cikin ibadun da yake yi, kafin ya shiga ittikaafi.

Hujja: (Mausu’a Fiqihiya).

91. Idan mutum yana ittikaafi, sai janaba ta same shi ta hanyar mafarki, yaya zai yi?

Amsa: Idan ya farka sai ya je banɗakin masallacin ya yi wanka, idan kuma babu ruwa sai ya yi taimama.

Hujja: (Fuqhu Maslim Alajnatu Da’ima).

92. Ana iya kaiwa mai ittikaafi ziyara?

Amsa: Ana iya kai masa idan buƙatar hakan ta taso, ko a yi masa waya idan bai kashe wayar ba..

Hujja: Sahihul Bukhari, Fathul Baari.

93. Shin mai yin ittikaafi zai iya fita ta’aziyya, wacce ta zama masa dole ko dubiyar mara lafiya ko siyan abinci ko biyan buƙata a banɗaki?

Amsa: Zai iya duk waɗannan abubuwan, haka kawai ne ba a so ya fita.

Hujja: Sahihul Bukhari, Sahihu Muslim, Almugni li ibni Qudama, Altalqin ala Mazhabi Maalikiya.

94. Ina son ƙarin bayani a kan bashin (wari) bakin mai azumi da ya fi miski daɗi a wajen Allah Azza wa Jalla.

Amsa: abin da ake nufi shi ne, zai wayi gari ranar Ƙiyama bakinsa yana ƙamshin turaren da babu irin shi a duniya. Ko kuma zai zama abin da kowane mutum zai yi burin zama ranar Kiyama, saboda darajar da ya samu, saboda wannan bashi bakin nasa, ko kuma zai samu tarin lada ne a kan hakan, saboda babu wani abu mai ƙamshi ko wari a gurin Allah, kowane abu yana kan ɗabi’arsa da ya halicce shi a kai.

Hujja: (Nailul Audar, Alqaadi Iyaad, Ibnu Abdulbarri).

95. Me ake nufi da daren lailatul ƙadari?

Amsa: Daren lailatul ƙadari wani dare ne cikin watan Ramadan da ibada a cikinsa ta yi daidai da ibadar watanni dubu, wanda ya yi daidai da shekara tamanin da uku.

Hujja: “Lailatul ƙadari kairun min alfi shaharin”. Suratul Qadar aya ta 3.

96. A wace ranar ce zan nemi wannan dare?

Amsa: A mara ake neman daren lailatul ƙadari, kamar ranar da azumi ya yi ishirin da biyu (22) da ranar ishirin da huɗu (24) da ranar ishrin da shida (26) da kuma ranar ishrin da takwas (28).

Hujja: marawaici: Anas ibn Malik , Ibnu Umar, Sahihul Bukhari, Attamhid li ibni Abdulbarri.

97. Wace alama ce mutum zai gane wannan daren shi ne daren lailatul Ƙadari?.

Amsa: mutum zai gane wannan daren lailatul Ƙadari ne ta hanyar jin hakan a jikinsa da kuma amincin da zai ji a wannan daren, ya bambanta da na kowanne dare, sannan kuma idan gari ya waye, zai ga rana ta fito haskenta ya yi dishi-dishi.

Hujja: “Salmum hiya hatt maɗɗala’ill fajar”. Marawaici Ubaiyu Ibnu Kaabin, Sahihu Muslim.

98. Idan mutum ya dace da daren lailatul ƙadari kuma ya gane cewa wannan shi ne daren lailatul ƙadari,shin akwai wata addu’a ta musamman ne da zai yi?

Amsa: Zai yi addu’a ne a kan buƙatunsa na duniya da lahira. Ko ya yi addu’ar da Ummuna A’isha ta koya daga Shugaban halitta..

Hujja: “Allahumma innaka afuwu tuhibbul afuwa, fa afu anni”. Sunan marawaici Ummuna A’isha, Turmuzi, Sunan Nassa’i, Sunan ibn Maajah, Musnadu Ahamad, Ibnu Daqiqul Eidi.

99. Idan mutum ya karya azumi da gangan mene ne abin da shari’a ta ce ya yi?

Amsa: Idan mutum ya karya azumi da gangan, zai yi azumin wata biyu a jere ko ya ciyar da mutane sittin ko ya’yanta bawa, wannan ita ce kaffarar laifin da ya aikata na shan ruwa da gangan cikin Ramadan.

Hujja: marawaici Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari Sahihu Muslim.

100. Idan ya zaɓi yin azumi sittin yana cikin yi, sai rashin lafiya ta same shi, idan ya ajiye shin sai ya sake daga farko ne?

Amsa: Idan ya ɗauko yin kaffara nayin azumi sittin, sai ya kamu da rashin lafiya ko ranar sallah layya ta shigo ko al’adarta ta zo, idan mace ce, babu komai, azuminsu na baya bai rushe ba, ɗora lissafi kawai za su yi a kan abin da suka jero, kafin rashin lafiya ko jinin al’ada ko kuma karo da ranar da ba a yin azumi, wato ranar Sallah Babba da Ƙarama.

Hujja: (Almausu’ah Shaamilah, Fataawas Siyaam).

101. Shin mace za ta iya shan maganin da zai hana al’adarta zuwa domin ta yi azumin Ramadan gaba ɗaya ko kuma idan akwai kaffara ta azumi sittin, domin ta yi su gaba daya a jere?

Amsa: Idan har likita ƙwararre ya ce maganin ba zai cutar da ita ba, kamar ya haifar mata da wata illa nan gaba, ba laifi ba ne idan ta sha, amma ta bar tsarin halittarta ta asali da Allah ya yi ta a kai, na tabyi al’ada duk wata, shi ne abin da ya fi.

Hujja: (Daarul Ifata’i Almisiriya).

102. Mece ce zakkar fidda-kai?

Amsa: Zakkar fidda kai, abinci ne da musulmi ke fitarwa ya babwa marasa ƙarfi, domin ya hutar da su daga neman abin da za su ci ranar shagalin sallar buɗa-baki, ranar da kowa yake farin ciki, domin su ma su shiga wannan farin cikin maimaikon su ba zama neman abinbda za su ci.

103. Wane irin abinci ake bayarwa, kuma yaya yawan abin da za ka fitarwa kowane mutum yake?

Amsa: Irin abincin da ake ci a yankin da kake zaune, gamagarin abinci ko na musamman gwargwadon wadartarka, ana fitarwa duk mutum ɗaya ciki tafikan hannunka biyu, har sau huɗu, shi ne (Mudun Nabiyi).

104. Yaushe ake so a fara fitarwa?

Amsa: Ana fara fitarwa ne tun daga kwanaki biyu kafin sallah.

105. Su wa yafi cancanta a fitarwa?

Amsa: Ana fitarwa da duk wani musulmi namiji ko mace, bawa ko ɗan jariri ne ko baligi.

106. Shin akwai laifi ne idan mutum ya ƙi fitarwa, alhali yana da wadartar yin haka, kuma yaushe ne idan ya fitar ya makara?

Amsa: Akwai asara mai yawa ga wanda yake da ikon fitarwa, amma ya ƙi fitarwa, idan mutum ya fitar bayan dawowa daga idi, toh abnan ya makara,bko ya fitar ba zakka ya fitar ba, sadaka kawai ya yi.

107. Shin yin Ummara a watan Ramadan yana da falala ne ta musamman?

Amsa: Gaskiya ne akwai falala ta musamman fiye da kowace Ummara, sai wacce aka yi da Shugaban halitta.

108. A wace shekara aka wajabta azumin Ramadan?

Amsa: An wajabta yin azumin Ramadan ne cikin watan Sha’aban, bayan canza alqibla da kusan wata ɗaya, wasu malaman kuma suka ce bayan watan Sha’aban ya shiga da kwana biyu.

109. Shekara nawa kenan Shugaban halitta ya yi azumin Ramadan a rayuwarsa?

Amsa: Ya yi azumin Ramadan ne na tsahon shekara tara.

110. A cikin azumin Ramadan na shekaru tara da ya yi, sau nawa ya yi azumi talatin, sau nawa ya yi azumi ashirin da tara?

Amsa: Ya yi azumin Ramadan ashirin da tara sau bakwai, ya yi azumin Ramadan talatin sau biyu.

111. Waɗanne yaƙe-yaƙe ne Shugaban halitta ya yi, tare da sahabbai a watan Ramadan?

Amsa: Yaƙi biyu ne kawai ya yi cikin Ramadan, yaƙin Badar babba da fatahu Makka.

112. Shin Shugaban halitta yana karatun Alƙur’ani na musamman cikin watan Ramadan?

Amsa: Ƙwarai kuwa, yana tilawar Alƙur’ani cikin watan Ramadan tare da mala’ika Jibrilu.

113. Shin mene ne hukuncin saukar karatun Alƙur’ani cikin kwanaki uku?

Amsa: Mustahabbi ne saukar karatun Alƙur’ani cikin kwanaki uku.

114. Mene ne haramcin saukar karatun Alƙur’ani cikin yini guda?

Amsa: Ya halatta mutum ya sauke Alƙur’ani cikin yini guda.

115. Mece ce matsayin saukar karatun Alƙur’ani cikin sallar tarawihi, shin sahabbai sun yi hakan ne?

Amsa: Saukar Alƙur’ani cikin sallar tarawihi ya hallata, tare da cewa sahabbai ba su yi hakan ba.

116. Shin ya halatta limamin sallar tarawihi ya dinga sallar tare da Alƙur’ani a hannunsa domin dubawa?

Amsa: Ya halatta ya yi wa mutane sallar tarawihi da Ƙur’ani a hannunsa da yake dubawa, ba ma sallar nafila ba, har ma ta farilla.

117. Shin idan hakan ya halatta, mene ne sakamakon kallon takardar Alƙur’anin?

Amsa: Kallon takardar Alƙur’anin ibada ce, kamar yadda karanta Ƙur’ani yake ibada.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa danna nan

labarin da ya wuceJagoran Noman Shinkafa A Nijeriya
Labarin na GabaJagoran Noman Masara A Nijeriya
Lawan Bello
Abu muzaffar Malami ne masanin ilimin zamani da na addini bisa tsaren Ƙur'ani da tafarkin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, mai hangen nisa a addini da kuma alummma, shugaban Abu Muzaffar foundation.