Yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa.

0
731

Mafi yawancin shan ruwan Manzon (sallallahu alaihi wassallam) a zaune ne, kuma yana sha a tsaye saboda wani uzuri.

Kuma yana ambaton Allah a farkon shan nasa, ya kuma gode masa a ƙarshe.
Sannan kuma yana numfashi ne a wajen abin shansa sau uku, kuma idan Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gama shan abu, sai ya miƙawa wanda yake damansa.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tafiyar Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

Wannan bayani anciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceCin Abincin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)
Labarin na GabaSaki-reshe Kama-ganyen Da ‘Yan Siyasa Suke Yi.