Saki-reshe Kama-ganyen Da ‘Yan Siyasa Suke Yi.

0
550

Babu shakka yana daga cikin manya-manyan kurakuran ‘yan siyasa saki-reshe kama-ganye da suke yi, da kuma dabarar rashin dabarar da suke yi inda za ka ga wanda yake aikin da yake ɗaukar albashi duk wata na tsawon wasu shekaru masu dama

kuma yake da damar ci gaba da aikinsa na tsawon wasu shekarun masu yawa; amma kwatsam rana tsaka sai ya ajiye aikin da yake shi ne tabbas, ya tafi neman muƙamin da ba shi da tabbacin samun sa, idan kuma har ya same shi, sai a tarar da damar da yake da ita a kan muƙamin ta ɗan wani taƙaitaccen lokaci ce, wanda a ƙarshe idan ya rasa tudun dafawa a sakamakon faɗuwa ko ƙarewar lokacin muƙamin da ya samu, sai ya riƙa hargowar siyasa(ɓaɓatu) da bibiyar masu muƙamai a hannu, domin yin maula a matsayin sana’ar neman kwabo da ɗari, da tara cin yau da na gobe.

Haƙiƙa wannan shi ake kira SAKI-NA-DAFE Domin kuwa turba ce da ta saɓa da koyarwar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam).
An karɓo hadisi daga Abu Huraira, Allah yarda da shi ya ce:” Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Na rantse da wanda raina yake hannunsa, tabbas ɗayanku ya ɗauki igiyarsa ya je ya yi wo itace ya ɗoro a bayansa shi ne alheri gare shi a kan ya je wajen wani mutum ya roƙe shi ya ba shi, ko ya hana shi.”
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Kuma an karɓo hadisi daga Hakim ɗan Hizam, Allah ya yarda da shi ya ce: Na roƙi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) sai ya ba ni (abin da na roƙa) sai na kuma roƙon sa ya ba ni sannan sai na kuma roƙon sa ya ba ni, sannan sai ya ce da ni: ” Kai Hakim, dukiyar nan da kake gani ɗan wani ɗadi ne mai gushewa, kuma duk wanda ya same ta da son wanda ya bayar ba da naci da roƙo ba, to za a sanya masa albarka a cikinta, duk kuma wanda ya same ta da roƙo da ƙwallafa rai, to ba za a sanya masa albarka a cikin ta ba, tamkar wanda yake ci ba ya ƙoshi, hannun bayarwa ya fi hannun karɓa alheri”. Sai Hakim ya ce: “Ya Manzon Allah! (sallallahu alaihi wasallam) Na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya, ba zan sake tambayar wani komai ba, bayan ka, har in bar duniya……”
Bukhari ne ya rawaito shi.
Akbar! Hakan kuwa aka yi, wannan sahabi har ya bar duniya bai sake tambayar wani abu a wajen wani ba.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yin Ƙarya Da Sunan Yarfen Siyasa danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Hattara Dai ‘Yan Siyasar Musulmai wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin Danna nan.

labarin da ya wuceYadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa.
Labarin na GabaYin Ƙarya Da Sunan Yarfen Siyasa.