Cin Abincin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)

0
530

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ba ya kushe wani abinci.
Idan ya yi sha’awar abinci, yana ci; idan kuma ba ya sha’awarsa, yana barin shi. Kuma yana ambaton Allah Maɗaukakin sarki  a farkon cin abincinsa yana mai cewa: “Bismillahi” domin kar Shaiɗan ya ci  masa abinci.

Kuma yana gode wa Allah a ƙarshen cin abincinsa sai ya ce: “Alhamdulillahi”. Sannan kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ya cin wani abu a kishingiɗe.
Kuma ya kasance yana amfani da hannun damansa don cin abinci, kuma yana cin gabansa ne, haka kuma idan lomarsa ta faɗi ƙasa, yana ɗauka ya ci bayan cire inda ƙasa ta taɓa. Sannan kuma yana ci ne da yatsu uku, yana kuma suɗe yatsunsa da kwanon cin abincinsa idan ya gama.

Domin karanta cikakken bayani a kan Shan Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (sallallahu Alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi, wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi, domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceKukan Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)
Labarin na GabaYadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa.