Tag: (Sallallahu alaihi wassallam)

  • Yadda Manzon Allah  (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa.

    Yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa.

    Mafi yawancin shan ruwan Manzon (sallallahu alaihi wassallam) a zaune ne, kuma yana sha a tsaye saboda wani uzuri.

    Kuma yana ambaton Allah a farkon shan nasa, ya kuma gode masa a ƙarshe.
    Sannan kuma yana numfashi ne a wajen abin shansa sau uku, kuma idan Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gama shan abu, sai ya miƙawa wanda yake damansa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tafiyar Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayani anciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Cin Abincin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)

    Cin Abincin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ba ya kushe wani abinci.
    Idan ya yi sha’awar abinci, yana ci; idan kuma ba ya sha’awarsa, yana barin shi. Kuma yana ambaton Allah Maɗaukakin sarki  a farkon cin abincinsa yana mai cewa: “Bismillahi” domin kar Shaiɗan ya ci  masa abinci.

    Kuma yana gode wa Allah a ƙarshen cin abincinsa sai ya ce: “Alhamdulillahi”. Sannan kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ya cin wani abu a kishingiɗe.
    Kuma ya kasance yana amfani da hannun damansa don cin abinci, kuma yana cin gabansa ne, haka kuma idan lomarsa ta faɗi ƙasa, yana ɗauka ya ci bayan cire inda ƙasa ta taɓa. Sannan kuma yana ci ne da yatsu uku, yana kuma suɗe yatsunsa da kwanon cin abincinsa idan ya gama.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Shan Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (sallallahu Alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi, wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi, domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Kukan Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)

    Kukan Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana kuka a cikin sallah don tsoron Allah, kuma yana kuka yayin sauraron karatun Alkur’ani daga waninsa, kamar Abdullahi dan Mas’ud, Allah ya yarda da shi.

    Kuma Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana kuka domin tausayin wani abu, kamar yadda ya yi kuka don tausayin rasa ɗansa Ibrahim da rasa jikarsa wacce ‘yarsa Zainab ta Haifa.

    haka zalika, kukan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne, idanuwansa su yi hawaye, su kuma zubar da hawayen, idan kuwa kukansa ya tsananta sai aji yana shassheƙa kamar yanayin tafasar tukunya, kuma Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ya kwarma ihu a dalilin kuka.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Dariyar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi, wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Dariyar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam).

    Dariyar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam).

    Mafi yawancin dariyar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi murmushi ce, kuma dariyarsa kaɗan ce, matukar dariyarsa ita ce fiƙoƙinsa (haƙora) su bayyana, samsam bai taɓa yin dariyar da za a ga cikin bakinsa ba, abin nufi ba ya ƙyalƙyala dariya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Cin Abincin Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi wanda Abubakar Abbas Ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Karatun Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam).

    Karatun Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam).

    Allah Maɗaukaki ya ce da Manzonsa (Sallallahualaihi wassallam): “Ƙa kyautata karatun Alkur’ani matukar kyautatawa”.

    Suratul Muzammil, aya ta 4.

    Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yayyanka karatunsa, aya-aya, yana cewa: (Alhamdulillahi rabbil alamin)
    Sannan ya tsaya, sannan yace: (Arrahamanurrahim)
    Sannan ya tsaya, kuma yana jan muryarsa da karatu ja sosai. Sannan kuma karatunsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, karatu ne da za a iya fassara shi harafi bayan harafi

    Suratul Fatiha, aya ta (1-2).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kukan Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.