SALMANU FARISS ADAMU
Babu laifi ga me azumi ya sumbaci matarsa matuƙar ya tabbatar zai iya kuɓuta daga faɗa mata, amma nisantar sumbatar mace ga me azumi shi ne ya fi alheri, amma annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla) ya kasance yana sumbatar iyalansa kamar yadda waɗannan Hadisai suka nuna haka:
حدثنى مالك عن هشام بن عروة عن أبيه عن عا ئشة أم المومنين رضي الله عنها قالت ” أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يصب بعض أزواجه وهوصائم ثم ضحهكت “
An ruwaito daga Malik daga Hashim bin Urwata (shima) daga mahaifinsa daga Nana Aisha Uwar Muminai (R.A) itace tace “Tabbas Manzan Allah (S.A.W ya kasance yana sumbatar sashin matayansa sai ya yi murmushi”
Saboda haka idan annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla) yana ɗakin ɗaya daga cikin matayensa guda tara ko goma sha ɗaya ko kuma goma uku ko goma sha biyar, yana sumbatar matarsa kuma a cikin watan Ramadan.
Haka ma a cikin wani Hadisin ko a cikin littafan Risala na sheikh Muhammad Al-akhdhari wani yace “Annabi yana sumbatar matarsa, sannan sai ya tafi masallaci, To a nan ka ga babu laifi ga wanda ya yi alwala ya sumbaci matarsa, sai dai nisantar aikata hakan shi ne ya fi alheri a gare shi, saboda komai zai iya faruwa.
Akwai dalilai masu tarin yawa, wanda yasa addinin musuluncin ya nuna mana mahimmacin sumbatar mace, haka kuma hadisai da yawa haɗi da litittafai masu yawa sun kawo annabi ya kasance yana sumbatar matayensa, ita sumbatar mace, tana ƙara so da shaƙuwa a tsakanin ma’aurata ta yadda ba ka tunani haɗi da samun nutsuwa mai ɗorewa a cikin zukatansu.
حدثنى مالك عن يحي بن سعيد: أن عاتكة إبنة زيد بن عمر بن نفيل إمرأة عمر بن الخطاب,كانت تقبل رأس عمر بن الخطاب وهو صائم, فلاينهاها.
An ruwaito daga Malik daga Yahaya bin Sa’idu (yace), haƙiƙa Atika ‘yar Zaidu bin Umar bin khaɗɗab ta kasance tana sumbatar kan (Sayyadina) Umar bin Khaɗɗab shi kuma (a lokacin) yana azumi bai hana ta ba.
حدثنى مالك عن أبى نضر مولى عمر بن عبيد الله, أن عائشة بنت طلهة أخبرته : أنها كانت عند عائشة زوج النبي صلى الله عليه وسلم فدخل عليها زوجهاهنالك وهو عبدالله بن عبدالرحمن بن أبى بكر الصديق وهوصائم,قالت له عائشة :ما يمنعك أن تدنوا من أهلك فتقبلها وتلاعبها:أقبلها وأنا صائم قالت :نعم.
An ruwaito daga Malik daga Abi-Nahir ya yi wa Umar bin Ubaidullah hidima (yace), haƙiƙa Aisha yar Ɗalhatu ta ba shi labarin ita ta kasance a gurin Nana Aisha matar annabi (Sallallahu alaihi wasallam) sai mijnta ya shiga gurinta (Nana Aisha) shi ne Abdullah bin Abudulrahman bin Abubakar Sadik a lokacin yana azumi, sai Aisha tace da shi, mai ya hana ku kusantar iyalanku, sannan ku sumbace su da wasa da su? (sai mijin na ta) yace, na sumbace ta kuma ina azumi? (sai Nana Aisha) tace eh.
Ka ga a nan ma babu wani laifi ga me azumi ya sumbaci matarsa ,kamar yadda sayyada Aisha ta yi wa wannan bawan Allah bayani, shi kuma sai maganar ta ba shi mamaki, saboda ya ga yana azumi daga ƙarshe tace ba komai , zai iya sumbatar matarsa haɗi da wasa da ita, amma idan ya san zai kubuta daga afka mata, Saboda kaffara azumi haɗi da ramuwa za su iya shiga ciki, matuƙar ya sadu da ita kamar yadda mu ka yi bayani a baya.
حدثنى مالك عن زيد بن أسلم: أن أبا هريرة و سعد بن أبى وقاص كانا يرخصان فى القبلة للصائم.
An ruwaito daga Malik daga Zaidu bin Assalama (yace), Lalle Abu-huraira da Sa’adu bin Abu-waƙas, sun kasance suna sauƙaƙawa game da sumbatar mai azumi.
Saboda haka suna sauƙaƙawa ga mai azumi zai iya sumbatar matarsa, idan zai iya kuɓuta daga ganawa da ita, amma nisantar daga hakan shi ne yafi alheri kamar yadda wannan hadisin na annabi (Sallallahu alaihi wasalla) ya nuna mana hakan.
حدثنى يحي عن مالك أنه بلغ عليه, أن عائشة زوج النبي صلى الله عليه وسلم كانت إذا ذكرت أن رسول لله صلى الله عليه وسلم يقبل وهو صائم نقول:أيكم أملك لنفسه من رسول لله صلى الله عليه وسلم.
An ruwaito daga Yahaya daga Malik, haƙiƙa labari ya same shi, tabbas Nana Aisha matar annabi (Sallallahu alaihi wasalla) ta kasance tana ambata mana haka, haƙiƙa manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) yana sumbatar iyalansa, idan yana azumi, sannan kuma tana cewa; Na hane ku (da aikata haka, saboda shi annabi) ya mallaki zuciyar sa (Sallallahu alaihi wasalla), daga afkawa matayensa a wannan lokaci.
Amma Urwata bin Zubair yana cewa shi bai ga komai ba a kan yin sumbatar mace, sai alheri.
حدثنى مالك عن زيد بن أسلم عن ألطاء بن ياسرأن عبدالله بن عباس سئل عن القبلة للصائم,فارخص للشيخ وكرها للشاب.
An ruwaito daga Malik daga Zaidu bin Asalama daga Aɗɗa’u bin Yasir: Tabbas Abdullah bin Abbas an tambaye shi game da sumbata game azumi (sai yace) an sauƙaƙa a cikin sa ga tsoho, sannan kuma an hana aikata haka ga saurayi.
Saboda a tunanin shi tsoho, zai iya kame sha’awarsa a wannan lokaci , sannan kuma sha’awarsa ta fara ƙasa, amma shi saurayi, yanzu ne sha’awarsa (take hau hawa da wuya ya iya kubuta da ka aikatawa haka, saboda haka ne ma za ka ga samari ba sa yin aure a cikin watan Ramadan).
حدثنى مالك عن نافع أن عبيدالله بن عمر كان ينهى عن القبلة والمبا شرة للصائم
An ruwaito daga Malik daga Nafi’u haƙiƙa Ubaidullah bin Umar ya kasance yana hana yin sumbata da runguma ga me azumi.
Saboda yin sumbata (Kiss) haɗi da runguma, yana iya kawo fitar maniyyi, sannan kuma komai zai iya faruwa a tsakanin su, musamman ga saurayi da sauransu.
Don karanta Sallar Idi danna nan
Edita@rumasau-kallamu