Sallar Asham Da Raka’o’inta

0
563

Sallar Asham ita ce nafilfili da ake yi a bayan sallar Isha’i a cikin watan Ramadan, wato da zarar labarin ganin wata ya bayyana, domin wannan dare na Ramadan ne. Sannan yin ta cikin jam’i, sunna ce.

Hadisi ya tabbata daga Nana A’isha (Radiyallahu Anha) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fita a wata rana da tsakar dare, sai ya yi sallah a Masallaci, sai wasu cikin sahabbai suka bi shi. Da gari ya waye sai mutane suka ba wa junansu labari, da dare ya yi sai yawan mutane ya ƙaru, sai ya yi sallah su ma suka bi Shi.

Da gari ya waye sai mutane suka ƙara bai wa junansu labari, sai Masallaci ya cika a dare na uku, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fito ya yi sallah. A dare na huɗu mutane suka taru har Masallaci ya gaza ɗaukarsu; sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ƙi fitowa har zuwa sallar Asubahi.

Yayin da ya idar da sallar Asubahin, sai ya juyo ya fuskanci mutane, Ya ce; “Lalle halinku bai ɓuya gare Ni ba; sai dai Ni na ji tsoron kada a wajabta muku ita ku zo ku gaza”. (Bukhari 3/220, Muslim 761).

Bayan wafatin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) shari’a ta gama cika, tsoron da ake ji ya kau; sai Sayyadina Umar Bin Khaɗɗab (Radiyallahu Anhu) ya raya wannan Sunnah; kamar yadda Abdulrahman Bn Al-ƙariy ya faɗa cewa; “Na fita tare da Umar Bn Khaɗɗab a wani dare cikin Ramadan zuwa masallaci, sai ga mutane a warwatse, wani yana sallah shi kaɗai; wani yana sallah da yan mutane kaɗan.

Sai Umar ya ce: “Ni ina ganin da a ce na haɗe mutane bayan karatu ɗaya da ya fi kamata”.

Sai ya yi ƙoƙarin haɗe su a bayan Ubayyu Ibn Ka’ab (Radiyallahu Anhu). Sannan muka fita tare da shi a wani daren, mutane suna sallah a bayan limaminsu, sai Umar ya ce; “Madalla da wannan sabon abu…”

Game da adadin raka’o’inta kuwa, ya zo cikin hadisin Nana A’isha (Radiyallahu Anha) cewa; “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam ba ya wuce raka’a goma sha ɗaya a Ramadan ko waninsa”. (Bukhari: 1147). Sannan ta bayyana yadda kyawun wannan sallah take; da kuma yadda yake jimawa a tsaye, wanda har ƙafafuwanSa ke kumbura saboda tsayuwa.

Hadisi daga Jabir Bn Abdullahi (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) yayin da ya raya daren Ramadan da mutane; ya yi sallah raka’a takwas sannan ya yi wutiri. (Ibn Hibban 920).

Domin karanta cikakken bayani akan Ma’anar Azumi A Musulunci danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Kaffarar Azumin Ramadan danna nan.

Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceZakkar Fid-Da-Kai
Labarin na GabaTsayuwar Watan Ramadan