Tsayuwar Watan Ramadan

0
563

Tsayuwar Watan Ramadan – Azumin Ramadana yana tsayuwa ne da ganin jinjirin watan Ramadana; wato ba a amfani da ƙirgen kalanda ko lissafin taurari ba; a’a, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya alaƙanta yin azumin ne da ganin watan na Ramadana.

Hadisi ya tabbata daga Abu Hurairata Radiyallahu Anhu cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Ku yi azumi domin ganin sa (wato Ramadan), kuma ku sha ruwa domin ganin sa (wato Shawwal). Idan watan ya faku a gare ku (ba ku gan shi ba), to ku cika Sha’aban kwana talatin”. (Sahihul Bukhari (1909), Sahihuul Muslim (1081).

Wani abu muhimmi shi ne, ba sai kowa ya ga watan Ramadan ba sannan ya ɗauki azumi; ana iya ɗaukar azumi ko da mutum ɗaya ne ya ga watan. Domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Umar (Radiyallahu Anhu) cewa; “Mutane sun yi ƙoƙarin ganin jinjirin wata; sai na gaya wa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewar, “Ni na ga wata”. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ɗauki azumi, kuma Ya umarci al’umma da su ɗauka”. (Sunan Abu Dawud, 2342. Hakim, 423, da Ibn Hibban 3438).

Faɗakarwa:

Son zuciya da jahilci kan hana wasu tashi da azumi da hujjar cewa shugabanni ba adalai ba ne; alhali Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ba da dama a bi su hatta sallah, ballantana azumi. Bisa haka, idan adali ya shaida ya ga wata; kuma shugaba ya aminta da ganinsa, to wajibi ne a tashi da azumi.

Dangane da sauƙe azumin kuwa, sai mutane biyu sun shaida cewar sun ga watan Shawwal; sannan a ajiye kamar yadda aka rawaito daga Abdulrahman Ibn Zaid Ibn Khaɗɗab; yayin da ya yi wa mutane huɗuba a ranar shakku (wato ranar da ake kokwanton ko Ramadan ne ko, ba Ramadan ba ne) .

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Watan Ramadana 1 danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ciyar Da Mai Azumi danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceSallar Asham Da Raka’o’inta
Labarin na GabaSharuɗan Wajabcin Azumin Watan Ramadan