Tag: Azumi

  • Abubuwa Goma Da Mai Azumi Ya Kamata Ya Sani

    Abubuwa Goma Da Mai Azumi Ya Kamata Ya Sani

    ZAFAFA GOMA: ABUBUWA 10 DA MUSULMI YA KAMATA YA SANI SANNAN YA KIYAYE A LOKACIN AZUMIN WATAN RAMADANA.

    GABATARWA:
    Alhamdulillahi Rabbil ‘Alamin. Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, iyalansa da sahabbansa baki ɗaya. Muna yi wa Allah (SWT) godiya da Ya raya mu har muka sake gamuwa da watan Ramadan, watan rahama, gafara da tsira daga wutar Jahannama.

    Ibadar azumin ramadana ibada ce wacce ta samo asali da umarni daga Allah (SWT) kuma ibada ce wacce aka umarci al’ummomin baya da ita. Dalilin haka shi ne faɗin Allah (SWT) “ya ku waɗanda suka yi imani an farlanta muku azumi kamar yadda aka farlanta ma waɗanda suka gabace ku domin ku yi taƙawa”. Duba bakara: 2:183.

    Haka kuma Allah (SWT) yana cewa “watan ramadana shi ne wanda aka saukar da alkur’ani a cikinsa domin zama shiriya ga mutane……”Duba bakara: 2:185. Haka zalika, An ruwaito manzon Allah (SWT) yana cewa: “ haƙiƙa watan Ramadana ya zo muku. Wata ne mai albarka. Allah yana lulluɓeku (da rahamar sa) a lokacin sa.

    Yana saukar da jin ƙan sa, yana kankare zunubai kuma yana karɓar addu’o’i. Allah yana kallon tsere da kuke yi ta ɓangaren kyawawan ayyukan ku sannan ya sanar da mala’iku cikin girmama ku. Saboda haka ku nuwa Allah nagartar ku. Tabbas matsiyaci shi ne wanda ya kasa samun rahamar Allah a lokacin Ramadan ”Duba “ Majma’uz-zaw’id 3:142

    Haka kuma Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yace “duk wanda ya azumci Ramadana yana mai imani da kwaɗayin samun lada, za a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka
    gabata….”.Duba Bukhari 2014 da muslim 759-760. A wani hadisin ƙudusi Allah (SWT) yana cewa “ dukkanin aiki (mai kyau) na ɗan-adam da ya yi yana da lada goma kwatankwacinsa har zuwa ɗari bakwai amma banda azumi.

    Haƙiƙa azumi nawa ne kuma ni zany ni sakayyarsa. Shi mai azumi ya bar cinsa da shansa, da sha’awarsa saboda umarni na” manzon Allah ya cigaba da cewa “ mai azumi yana da farin ciki har guda biyu. Farin ciki lokacin da yake buɗa baki da kuma farin ciki lokacin da zai haɗu da ubangijinsa” ….Duba Bukhari 1904 da muslim 161-1151

    A cikin wannan taƙaitacciyar tunatarwa, na ambaci abubuwa goma da Musulmi ya kamata ya kiyaye domin azuminsa ya zama karɓaɓɓe mai cike da falala. Allah (SWT) ya ba mu ikon amfana da wannan tunatarwa da kuma ikon aiki da waɗanan abubuwa (ZAFAFA GOMA) domin rabauta da dacewa.

    NA FARKO: NIYYA

    Azumi ibada ce, kuma ibada ba ta inganta sai da niyya tun daga dare kafin a tashi
    da azumi. Wajibi ne mutum ya ƙulla niyyar azumi da zarar an ga wata tun kafin ya
    kwanta bacci ko kuma kafin fitowar alfijir.

    Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce:“Duk wanda bai yi niyyar azumi da dare ba, babu azumi a gare shi.” (Abu Dawud, Tirmizi)

    NA BIYU: ƊAUKAR AZUMI DA GANIN WATA

    Azumin Ramadana yana farawa ne da ganin wata ko kuma cikar wata (sha‟aban zuwa 30) kuma yana ƙarewa da ganin wata (na shawwal).

    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Ku yi azumi idan kun ga wata, ku buɗa azumi idan kun gan shi. ”(Bukhari da Muslim)

    NA UKU: TSAYAWA DA SALLOLIN FARILLA

    Ko da mutum yana azumi, idan ya raina sallah, ya jefa kansa cikin haɗari. Allah (SWT) yana cewa “ ku kiyaye sallolin ku musammam sallar (tsakiya) La‟asar….. Duba bakara 2:238

    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Abu na farko da za a tambayi bawa a ranar Alƙiyama shi ne sallah….” (Tirmizi)

    NA HUƊU: YAWAITA KARATUN AL-KUR’ANI

    Ramadan wata ne na Al-Kur‟ani, don haka ake ƙwaɗaitar da musulmi da ya dage
    wajen yawaita tilawa da sauraron alkurani ba dare ba rana. Karatun alkurani shi ne
    zikiri mafi girma kuma a watan ramadana aka saukar da shi.

    Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya kasance duk watan ramadana mala‟ika Jibril yana zuwa sau biyu wajen sa domin tilawar alkurani tare da shi kuma an ruwaito sahabbai da magabata sun kasance suna duƙufa ba dare ba rana wajen raya dukkan kwanaki da karatun alkurani. Ana so mutum ya shagaltu sosai da karatun alkurani kuma ya zama shine mafi yawan ibadar sa acikin ramadana.

    Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce:“Ku karanta Al-Kur‟ani, domin lallai shi zai zo ranar Alƙiyama yana yi wa masu shi ceto.” (Muslim)

    NA BIYAR: YAWAN ZIKIRI

    Zikiri yana rayar da zuciya kuma yana ɗaga darajar bawa.
    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Kalmomi biyu ne masu sauƙi a harshe, masu nauyi a sikeli, masu soyuwa ga Rahama…” (Bukhari da Muslim)

    NA SHIDA: YAWAITA SALATI GA ANNABI صلى الله عليه وسلم.

    Salati hanya ce ta samun rahamar Allah. Don haka yawaita salati ga manzon Allah
    صلى الله عليه وسلم a kowane lokaci ibada ce mai albarka da ɗimbin lada musammam kuma a lokacin azumi.

    Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce:“Duk wanda ya yi mini salati sau ɗaya, Allah zai yi masa sau goma.” (Muslim)

    NA BAKWAI: YAWAITA ADDU’A, MUSAMMAN A SAHUR DA BUƊA BAKI

    Mai azumi yana da matsayi na musamman wajen Allah. Lokacin da bawa ke azumi
    lokaci ne na addu’a gaba ɗaya amma kuma akwai keɓaɓɓun gurare da aka ayyana cewa
    ana so a yawaita addua kamar lokacin buɗa baki da lokacin sahur da sauransu.
    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Mai azumi yana da addu‟a wadda ba a mayar masa da ita ba a lokacin buɗa bakinsa.” (Tirmizi)

    NA TAKWAS: SALLAR TARAWIHI DA TSAYUWAR DARE

    Wannan wata dama ce ta gafara da gyaran rayuwa.
    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: “idan mutum ya tsaya domin sallar dare (tarawih ko ƙiyamul laili) tare da liman har aka ƙare sallar, Allah zai rubuta masa lada kamar wanda ya raya daren gaba ɗaya da sallah.” (Abu dawud 1375)

    NA TARA: SADAKA DA CIYAR DA MAI AZUMI

    Ramadan wata ne na tausayi da taimakon juna.
    Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, zai samu irin ladan azuminsa.” (Tirmizi)

    NA GOMA: I’ITIKAFI, ZAKATUL FITR DA UMARA GA MAI HALI

    Goman ƙarshe lokaci ne na ƙara kusanci da Allah da dagewa sosai domin ƙara yawaita ibadu musammam a kwanakin da ake sa ran dacewa da lailatul kadari watau daren 21, 23, 25, 27 da kuma 29. I’itikafi ibada ce mai tarin lada da samun kusanci da Allah (SWT) kuma ana shiga I’itikafi ne a goman ƙarshe a Ramadan.

    Haka, zakkar fidda kai (zakatul fitr) ibace wacce aka shar’anta ta a kan dukkan musulmi namiji ko mace, babba ko yaro ko ɗan jariri kowa ana fitar masa da zakkar
    fidda kai.
    Hujja: An rawaito cewa Annabi صلى الله عليه وسلم yana yin I’itikafi a goman ƙarshe na Ramadan.(Bukhari). Haka kuma ya wajabta Zakatul Fitr (zakkar fidda kai) domin tsarkake azumi, kuma ya ce: “Umara a Ramadan tana da ladan Hajji.” (Bukhari da Muslim).

    ‘Ƴan uwa masu girma haƙiƙa duk wanda ya kiyaye waɗannan abubuwa goma, ya yi azuminsa da ikhlasi, to da yardar Allah zai samu cikakkiyar falalar Ramadan wanda Allah kaɗai ne ya barwa kansa sanin irin tanadin ladan da zai ba shi. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya sa mu dace da Lailatul Qadr.
    Ameen.

    Husain M. Inuwa.
    usainiskima@gmail.com
    09042152353

    Danna nan don karanta Shan Azumi Ga Matafiya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Matsayin Azumin Ashura A Wurin Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma)

    Matsayin Azumin Ashura A Wurin Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma)

    Daga hadisan da suka gabata, za mu fahimci cewa ranar Ashura sananniya ce tun kafin bayyanar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kuma azumin ranar shi ma an daɗe ana yin sa tun zamanin yahudu da nasara har zuwa lokacin larabawan jahiliyya.

    To amma akwai waɗansu masu da’awar Son Ahlul Bait (Radiyallahu Anhuma), da bin tafarkinsu su ba sa yin wannan azumin; suna ko ganin ƙirƙirarsa aka yi kawai wai don nuna farin ciki da goyon baya; kan kashe Sayyidina Husaini (Radiyallahu Anhu) da aka yi a ranar ashura shekara ta 61 hijiriyya.

    Wannan yana nufin tun ɗaruruwan shekaru kafin a haifi Husainin aka fara murnar za a kashe shi; ɗan uwa ka yi tunani, a hankalce haka za ta yiwu?

    To amma mu duba mu gani shin su Ahlul baiti (Radiyallahu Anhuma); ya ya suka ɗauki ranar ashura da kuma azumin ranar? Ga amsa daga bakinsu:

    Sayyidina Ali (Radiyallahu Anhu): An karɓo daga Al-As-wad IbnYazid ya ce; “Ban ganin wanda ya fi Sayyidina da Ali da Abu Musa yawan umartar mutane da yin azumin ashura ba.

    An karɓo daga Abu Abdullahi daga babansa (Alaihis Salam) ya ce haƙiƙa Ali (Alaihis Salam) ya ce; “Ku yi azumin ashura da tasu’a saboda yana kankare zunubin shekara guda 2.

    Daga Abul Hasan (Alaihis Salam) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi azumi ranar Ashura”3)
    JA’AFARU SADIK (Radiyallahu Anhu)

    An karɓo daga Assadik (Radiyallahu Anhu) ya ce wanda zai iya azumtar watan Muharram gaba ɗayansa ya yi; zai tsare mai yin sa daga dukkan saɓo”.

    Daga Abu Ja’afar (Alaihis Salam) ya ce: “Jirgin ruwan Annabi Nuhu (Alaihis Salam) ya tsaya a jikin dutsen jude ranar Ashura, sai ya umarci gaba ɗayan mutane da aljanu da suke taře da shi da su yi azumi a ranar.

    Wannan kaɗan ne daga maganganun Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma) kan falalar azumin ashura, saboda wani babban malamin shi’a mai suna Radiyuddin Abul Ƙasim Aliyu bin Musa Ibn Ja’afar Ibn Tawus ya ce: Hadisai da yawa sun zo kan bayanin zaburarwar kan azumin ranar Ashura”.

    Mai karatu ka ga yadda maganganun Ahlul Baiti (Alaihis Salam) suka dace da maganganun kakansu (Sallallahu Alaihi Wasallam) da na sauran musulmi kan azumin Ashura da falalarsa da tarihinsa tun zamanin Annabi Nuhu (Alaihis Salam).

    Sai dai kuma su Kulaini da Ɗusi da ire-irensu sun yi fatali da waɗannan maganganu na gaskiya da hadisai ta yadda suka Rago waɗansu maganganun suka jingina su ga Ahlul Baiti saɓanin waɗanda suka gabata.

    A irin waɗanan maganganu sai suka ce wai Abu Ja’afar da Abu Abdullahi sun hana yin azumin ashura; kuma yin sa bidi’a ne, kuma wai iyalan Ziyadu ne da banu Umayya suka ƙirƙiro domin murnar kashe Husaini; kuma duk wanda ya yi to zunubinsu ɗaya da waɗanda suka kashe Husaini, da sauran maganganu.

    To abin tambaya a nan shi ne, shin su ma Imaman da ma Annabi Nuhu da Ahlul Kitabi har ma da shugaban halitta (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) banu Umayya ne? Kuma wannan wacce irin tufka ce da warwara daga Imamai? Anya suna baki biyu? Ko kuwa dai akwai wata a ƙasa?

    Kuma su Ɗusi da Sadik da Hurrul Amili, da Nuri Attabrasj da Ibn Tawus da suka rawaito falalar azumin; suna yaɗa sunnar banu Umayya ke nan? Ɗan uwa ka yi tunani.

    Daga ƙarshe ya kamata a sani cewa ruwayoyin da suke tabbatar da falalar ranar ashura da yin azumi a ranar ingantattu ne a wurin malaman Shi’a; amma waɗanda suke hani da sukar azumin raunana ne! Kamar yadda shaihunsu Alhaj Assayyid Muhammad Rida Alhusaini Alha’iri ya faɗa a littafinsa mai suna; “Najatul Umma fi lkamatil aza’i ala! Husaini wal a’ imma shafuka na 145, da 147, bugun binin Ƙum na Iran shekara 1413.

    Gaskiyar Magana

    Daga abubuwan da suka gabata za mu fahimci cewa gaskiyar magana game da ranar ashura da azuminta ita ce; Ranar Ashura rana ce mai daraja da ake yin azumi a cikinta tun kafin bayyanar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam).

    Dukkanin musulmai tun daga annabawa har Ahlul Baiti sun yarda da haka. Duk abinda ya saɓawa abin da ya gabata ƙarya ne.

    Ya Allah ka ganar da mu gaskiya ka ba mu ikon bin ta.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ba Su Inganta Ba Game Da Ashura danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A Kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Azumin Watan Ramadan 2

    Azumin Watan Ramadan 2

    Idan kuma mutum ya kusa haɗiye abinci ko abin shan, sannan kuma sai ya ji ana kiran sallah, idan lokaci ne, ma`ana shi ne wanda ya fara kiran sallah a lokacin ko kuma mutumin yana da saurin yin kiran sallah, saboda shi mutumin ya tashi da wuri ya yi sahur ɗinsa, to mutum zai iya yin sauri ya haɗiye wancan lomar ko abincin ko abin shan.

    Saboda haka yana da matuƙar mahimmanci ko amfani ga mai azumi haɗi da mai kiran sallah su san lokacin da alfijir yake fitowa ko alamar fitowar alfijir a kowace rana, saboda wasu ladanan suna kiran sallar asubah ko kiran sallah na biyu kafin alfijir ya fito, wasu kuma ladanan suna kiran sallah ne bayan alfijir ya fito da jimawa, wasu kuma masu yin azumi da su suke yin la`akari.

    Haka kuma ya kamata ladanai da masu yin azumi mu san hukunce-hukuncen na yin azumi haɗi da yadda alfijir yake fitowa da yadda rana take faɗuwa, saboda a nan ma ana samun wasu matsaloli da yawa ga wasu ladanan, saboda suna kiran sallah magariba kafin rana ta gama faɗuwa ko lokacin kiran sallah magariba ya yi, su kuma wasu mutane da su ke la`akari da zarar sun ji kiran sallah sai su ɗauki abin shan su ko abin cin su, sai su kama ci ko sha ba tare da yin la`akari da duba lokacin shan ruwa ba.

    Saboda haka yana da matuƙar mahimmanci ga mai yin azumi, idan zai sha ruwa ya tabbatar lokacin shan ruwan ya yi, saboda da mutum ya yi gagggawar shan ruwa, kuma bai tabbatar lokacin shan ruwan ya yi ba, to gara ya jinkirta shan ruwa bayan an yi sallah, sai mutum ya sha ruwan, saboda idan ya sha ruwa kafin lokacinn shan ruwan ya yi, to ba shi da azumin wannan ranar, haka kuma idan mutum da gangan ko alfahari ko taƙama ya sha ruwan, to ya karya azuminsa, sannan kuma akwai kaffaran azimi a kansa guda sittin a jere haɗi da guda ɗayan can da ya karya.

    Saboda waɗannan misalan ya kamata ‘yan uwana musulmai mu tashi tsaye wajen ilimi addini da na zamani, saboda malam mai ” ahlari ” yace “bai kamata ba ga wani mutum ya aikata wani abu a cikin addinin musulunci, har sai ya san hukuncinsa ko abin da Allah (da manzom Allah) yace a kan abin da zai aikata a cikinsa”.

    Haka kuma wannan ƙa`idar take a cikin addinin musukunci, babu wani abu da wani mutum ya isa ya aikata har sai ya san hukuncinsa a addinin musulunci, saboda haka yana da matuƙar mahimmanci ga ladanai su koyi yadda ya kamata su dinga kiran sallah, saboda kaucewa wasu kura-kurai na kiran sallah.

    Bugu da ƙari kuma, idan mutum ya yi mafarki suna ganawa da rana da wani mutum (mace ko namiji), sannan kuma a cikin watan azumin Ramadan, yaya azuminsa yake ?, amsa, azuminsa yana nan matuƙar a wannan yanayin hakan ta faru.

    Amma kuma idan mutum tunanin wani abu ne ko kuma ya kalli wasu abubuwa ne, sai ya fitar da wani abu daga gabansa mai kauri-kauri, sannan kuma fari-fari kamar ruwan kwakwamba ko ƙurji, to hukuncinsa shi ne, hukuncin wanda ya karya azumi da gangan, zai rama azumi guda sittin a jere na kaffara, sai kuma guda ɗaya wanda ya karya.

    Danna nan don karanta Guzirin Ramada Daga Rayuwar Sahabbai Da Magabata Na Gari

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Tambayoyin Azumi Da Amsoshi

    Tambayoyin Azumi Da Amsoshi

    Tambaya :- Idan mutum ya fara yin azumin kaffara zai iya hutawa ?

    Amsa :- Idan mutum  ya fara yin azumin kaffara ba zai iya tsayawa hutawa ba, sai idan yana da wata cuta, misali mace mai jinin haila ko wani mutum mai cutar gyambon ciki (ulcer) ko wata cuta ko hatsari ya samu mutum, wanda kuma  ba zai iya yin azumin ba, to wannan ya halatta a wannan yanayin mutum ya ajiye azumi har izuwa lokacin da mutum ya samu lafiya.

    Misali idan mace tana yin azumin kaffara, sai kuma hailarta ta zo mata, sai ta ajiye azuminta, bayan ta ɗauke mata, sai ta ci gaba da azuminta daga inda ta tsaya, haka ma mutum mai ciwon gyambon ciki zai aikata ko wanda wata cuta  rashin lafiya ta same shi zai aikata.

    Amma idan mutum lafiyarsa ƙalau, sannan  kuma babu wani dalili da shari`ar musulunci ta amince da shi na jingine ko ajiye azimi, har sai ya gama azuminsa a jere, idan kuma ya ajiye azuminsa a wannan halin, to dukkanin azumin da ya yi a baya sun rushe, sai ya sake tun daga farko.

    Misali idan mutum ya yi azumi guda hamsin da tara, sai yace bari ya huta,  idan Allah ya kai mu jibi ya ƙarasa cikon azumin guda ɗaya, to azumin da ya yi a baya sun ruguje, dole ne sai ya sake lissafi tun daga farko. Saboda haka yana da matuƙar mahimmanci a kanmu mu yi la`akari sosai a kan irin waɗannan matsaloli da sauran su.

    Tambaya: Idan mutum yana saduwa da matarsa a cikin watan azumin Ramadan sai alfijir ya fito, to yaya hukuncin azuminsa yake ?

    Amsa : Idan wani mutm yana cikin ganawa da matarsa sai kuma alfijir ya fito, azuminsa ya karyer matuƙar ya yi Inzali, sannan kuma akwai kaffaran azumi a kan su guda sittin (60).

    Tambaya: Mutum ne yake kwance bayan alfijir ya fito  ko bayan an yi sallar Asubah, sai matarsa ta zakke masa ,to yaya matsayin azumin su yake ?

    Amsa: Azuminsu ya ruguje ko ya rushe, sannan kuma akwai kaffaran azumin guda sittin a kansu. Bugu da ƙari kuma malamai sun ce ” mace ba za ta iya zakkewa ɗa namiji ba kai tsaye kuma ta yi Inzali ba tare da shi namijin yana so ba, Allahu a`alamu.

    Tambaya : mace ce take yin azumi, to kuma ya rage saura kamar mintuna biyu a sha ruwa, sai hailarta ta zo mata, ko lokacin haihuwarta ya yi, to yaya matsayin azuminta yake?

    Amsa:  Duk wacce haka ta faru da ita, to azuminta na wannan ranar ya rushe, sai ta sake wani azimin bayan an sha ruwa, amma kuma babu kaffara a kan ta.

    Tambaya: Menene hukuncin mutumin da ya aikata wani abu wanda yake karya azumi, amma kuma shi a lokacin da yake aikata wannan abun, shi bai san hukuncin aikata haka ba?

    Amsa:- Duk wanda ya aikata wani abu, saannan kuma a lokacin da yake aikata abin shi kansa bai san hukunci aikata haka ba, babu laifi a kansa, saboda Allah (S.W.A) ba zai kama mu ba da abin da muka aikata bisa ga rashin sanin hukuncinsa ba. Sai ya roƙi Allah gafara a kan abin da ya aikata, sannan kuma yana da matuƙar mahimmanci a kan musulmi duk abin da zai aikata a rayuwarsa ya san hukuncinsa, Allah yasa mu dace.

    Domin karanta Azumin Watan Ramadan danna nan

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Azumin Watan Ramadan

    Azumin Watan Ramadan

    Azumin watan Ramadan, wajibi ne a kan kowane musulmi, kuma wanda yake baligi, sannan kuma mai hankali, saboda mara hankali zai iya aikata duk abin da ya ga dama kuma a lokacin da ya so, ba tare da yin la`akari da halaccin ko haramcin abin da yake aikatawa ba, saboda babu hankali a tare da shi a lokacin da yake aikata haka.

    Haka kuma azumi yana zama ko tabbata ne, saboda cikar watan sha`aban (kwanaki ashirin da tara ko talatin) ko kuma saboda ganin jinjirin watan Ramadan da yamma, kafin ko bayan sallar magariba ta hanyar gani da ido ko samun labarin ganinsa (wata) a  wata jihar ko  garin ko unguwa, ta hanyar wasu mutane amintattu kuma masu halaye masu kyau haɗi da mu`amala mai kyau a tsakaninsu da mutane.

    Saboda haka da zarar mutane sun ga wata ko sun samu labarin ganin wata daga wajen irin waɗancan mutane, to azumi ya zama wajibi a kan mutum sai ya yi ko ya ɗauka, haka kuma za a aikata ko lura a lokacin ajiye azumi, ta hanyar ganin sabon tsayuwar watan shauwal ko ta hanyar cikar watan Ramadan kwana lokacin talatin(30).

    Bugu da ƙari kuma, ana iya ɗaukar niyyar azumin watan Ramadan ne, bayan ko a lokacin da mutum ya samu labarin ganin wata ko ya gani da idonsa kafin fitowar alfijir, saboda tabbatar tsayuwar watan Ramadan.

    Sannan kuma idan mutum ya ɗauki abincisa zai ci, to kafin ya fara cin abincin, dole ne sai ya tabbatar ya wanke hannunsa ko cokalin da zai ci abinci da shi haɗi da bakinsa, sannan kuma sai ya ƙulla niyyar yin azumin watan Ramadan guda ashirin da tara ko takatin.

    Misali, idan mutum ya ɗauki abincinsa ya ajiye a gabansa, kafin ya fara cin abincin, sai ya yi Bismillah,  sannan yace “Allahumma Inni nawaitus siyamu Ramadan tis`a wa ashiruna au salasuna” ko kuma mutum yace “Nawaitus siyamu Ramadan tis`a wa ashiruna au salasuna” .

    Ma`ana ya Allah na yi niyyar yin azumin watan Ramadan guda ashirin da tara ko guda talatin.

    Saboda haka idan mutum ba zai iya faɗar wancan kalma ba da larabci, to zai iya faɗar kalmar da harshen Hausa ko Fulatanci, Barbanci, Yarabanci ko harshen da yake iya magana da shi, hakan ya halatta, Misali “Na yi niyyar yin azumin watan Ramadan guda ashirin da tara ko guda talatin”,. amma kuma an fi so mutum ya faɗa da larabci.

    Bugu ƙari kuma, idan mutum ya yi niyyar yin azumin watan Ramadan tun a daren da aka ga wata, ma`ana tun niyyar da ya yi na azumin sa na farko,to wannan ya isar masa a cikin dukkanin azuminsa na wannan watan, saboda babu wani sharaɗi a kan mai yin azumi na sake yin niyya a cikin kowane azumi ko rana, matuƙar azumin na sa a jere zai yi, amma kuma idan ba a jere zai yi su ba, saboda wata matsala, to dole ne a kansa  sai ya sake yin niyyar azumin a duk lokacin da zai yi(azumi).

    Sannan kuma  yana daga cikin sunnah yin azumi gaggauta shan ruwa da jinkirta yin sahur, ma`ana da zarar mutum ya ji an kira sallar magariba, sai ya yi saurin shan ruwa (da dabino ko “yayan itatuwa ko ruwa) kafin mutum ya yi sallar magariba, saboda haka ne ma yake da matuƙar kyau ko ake buƙatar a samu kamar mintuna  huɗu ko biyar a tsakanin kiran sallah da yin sallah.

    saboda mutane su samu damar aikata wancan sunnah ta azumi kafin suyi sallah, amma kuma ba dole ba ne sai mutum ya aikata haka, amma kuma aikata haka yana da matuƙar kyau sosai, soboda sunnah ce ta annabi Muhammmad (Sallallahu alaihi wasallam).

    Sai kuma jinkirta yin sahur, ma`ana kada mutum ya tashi cikin dare ya yi sahur, ma`ana kamar misalin ƙarfe biyu na dare ko kafin a kira sallah na farko, amma kuma idan mutum ya aikata haka azuminsa ya yi, sai dai bai aikata sunnah ba.

    Haka kuma mutum ya nisanci cin abinci ko abin sha a lokacin da alfijir yake fitowa ko a lokacin da ake kiran sallah na biyu, saboda ana buƙatar a samu kamar mintuna goma  ko mintuna goma sha biyar(15) a tsakanin kiran sallah da gama yin sahur, amma idan mutum ya sa abinci a cikin bakinsa, sai kuma ya ji ana kiran sallah na biyu ko asubah, to sai ya yi sauri ya fitar da abin da yake bakinsa, saannan kuma ya kuskure bakinsa sai ya ci gaba da yin azuminsa.

    Danna nan don karanta Yaƙe-yaƙen Annabi SAW A Watan Ramadan

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su

    Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su

    Akwai waɗansu muhimman halaye da ya kamata mai azumi ya siffanta da su, a gan su da gaske a tattare da shi. Cikin halayen akwai:

    i. Haƙuri, wato mai azumi ya siffantu da haƙuri wanda shi zai zama jagaba a cikin lamuransa, ya hana shi bin son zuciya da saɓa wa Allah. Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Idan ɗayan ku yana azumi, kada ya yi maganganun fasiƙanci. Idan wani ya zage shi, ya ce Ni mai azumi ne” (Sahihul Bukhari 1894, Sahih Muslim 1151).

    ii. Riƙon amana, yana da kyau mai ya zama mai riƙon amana, domin tana daga cikin abar da za ta taimaka masa wajen kiyaye azuminsa.

    iii. Rahama, ana son mai ya siffantu da rahama, da sakin hannu da karamci, da kuma yalwar zuciya. Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da kwatankwacin ladan wanda ya ciyar ba tare da an rage ladan wanda aka ciyar ɗin ba” (Sunan al-Tirmizi 647, Sunan Ibn Majah 17).

    iv. Nasiha, yana da kyau mai azumi ya kasance mai yin nasiha da kuma umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.

    v. Sulhu, mai azumi yana da kyau ya kasance mai yin sulhu da sasanta mutane, musamman la’akari da cewa ƙiyayya da gaba na kawo tsaiko wajen karɓar ibada da addu’a.

    vi. Kame harshe, ya kamata mai azumi ya kame harshensa daga maganganu na shirme da shashanci, sannan ya nesanci giba, zagin mutane da yi musu ƙage ko sharri da ƙarya ko musu marar dalili, musamman abin da ya shafi siyasa ko wasan ƙwallo ko wanin waɗannan.

    An karbo hadisi daga Abu Huraira (R.A) cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wanda duk bai bar faɗin magana ta zur da aiki da ita ba, to Allah ba shi da buƙatar ya bar cinsa da shansa”. (Bukhari 4/99).

    Haka nan wani hadisin dai daga Abu Huraira (R.A) dake cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ba azumi ba ne barin ci da sha, shi azumi shi ne na yasasshen zance da batsa, ko da wani ya zage ka, ko ya yi maka wauta, to ka ce: “Ni mai azumi ne”. (Ibn Khuzaima 1996). Ibnu Majah ya fitar da hadisi mai ɗauke da razani ga mai yin maganganun banza a yayin da yake azumi, ya ce: “Sau da yawa wani mai azumin ladansa shi ne yunwa da ƙishirwa”.

    vii. Rintse ido da kame farji, yana da kyau mai ya rintse idanuwansa daga kallon haramun, ya kuma kare farjinsa daga dukkanin haramtattun abubuwa. A nan muna jan hankalin waɗanda ke ganin kallon fina-finai ko tashoshi na gusar musu da yunwa, haƙiƙa wannan kuskure ne babba da kuma munana zato ga Allah, da kuma keta iyakokinSa.

    Su ma masu sanya fina-finai a tashoshi wajibi su ji tsoron Allah, sani ribar rayuwa da albarkar abin da suke so shi ne ginawa bisa tafarkin Musulunci.

    viii. Iklasi, ya kamata mai Azumi ya ƙudurce cewa lalle yana yin wannan azumin ne saboda Allah, kuma domin neman yardar Allah, ba domin mutane su yabe shi ba. A nan, ana jan hankalin yan’uwa masu yin sadaka ko ciyar da masu Azumi da masu tafsirin Alku’ani, da limamai masu rera tilawa, da masu zuwa Umarah, da sauran aiyuka nagari, wajibi su sanya iklasi kada shaiɗan ya lalata musu ayyukansu.

    ix. Bin sunnar Manzon Allah (S.A.W), wajibi ne mai azumi ya nesanci bidi’o’i, ya tsaya kan sunna ka’in da na’in, domin kyakkyawan aiki yana cikin koyi da Fiyayyen Halitta (S.A.W).

    x. Tarbiyya, wajibi ne mai azumi ya tsaya wajen ƙoƙarin tarbiyyantar da kansa da ‘ya’yansa ko ‘yan’uwansa ko waɗanda yake da iko a kansu. Kuma iyaye su ɗauki wannan wata a matsayin lokacin roƙarwa ‘ya’yansu shiriya.

    Domin Karanta Abubuwan da Suke bata Azumi danna nan

  • Azumi

    Azumi

    MENE NE AZUMI?
    Ana iya fahimtar ma’anar Azumi ta fuskoki biyu:

    i. AZUMI A LUGGA
    Shi ne kamewa
    ii. A SHARI’ANCE: Shi ne kamewa daga barin ci ko sha da saduwa da iyali tun daga ketowar alfijir har zuwa faɗuwar rana da niyyar yin ibada.

    RUKUNAN AZUMI:
    1. Yin niyya
    2. Kamewa daga ci ko sha da saduwa da iyali
    3. Zamani (lokacin yin azumi)

    SUNNONIN AZUMI:
    1. Gaggauta buɗa baki
    2. Jinkirta sahur
    3. Addu’a yayin buɗa baki
    4. Yin sahur da jinkirta shi.

    MAKARUHAN AZUMI:
    1. Kai wa matuƙa wajen kurkuran baki
    2. Sumba
    3. Dauwamar da kallo na sha’ awa
    4. Tunani akan al’amuran saduwa
    5. Shafa ko runguma
    6. Ɗanɗanan wani abu
    7. Sanya tozali
    8. Yin kaho

    ABUBUWAN DA SUKE ƁATA AZUMI:
    1. Saduwan wani abu zuwa maƙoshi (narkakke)
    2. Fitar da maniyyi ko maziyyi da gangan
    3. Saduwa ta hanyar tilastawa
    4. Ci ko sha da tunanin sauran dare
    5. Ci ko sha da gangan
    6. Saduwan wani abu wanda ba narkakke ba zuwa maƙoshi
    7. Ridda.

    ABUBUWAN DA SUKE HALAS:
    1. Yin asiwaki
    2. Sanyaya jiki da ruwa
    3. Tafiya ta halas
    4. Sanya magani wanda ya dace
    5. Tauna wani abu ga ƙaramin yaro
    6. Sanya turare

    ABUBUWAN DA AKA YI RANGWAME:
    1. Haɗiye yawu
    2. Rinjayen amai da magwas
    3. Rinjayen wani ƙwaro zuwa ga maƙoshi
    4. Ƙuran kan hanya
    5. Wayan gari da janaba
    6. Yin mafarki da rana

    Ya kai ɗan uwa mai albarka, ka taya mu yaɗa wannan karatu/sako za ka samu lada mai yawa, domin yaɗa ilimi yana da daga cikin abubuwan da suke kusanta bawa ga Mahalicci.

    Domin karanta bayani a kan shekarar da aka wajabta azumi danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Abubuwan Da Suke Ɓata Azumi

    Abubuwan Da Suke Ɓata Azumi

    Akwai abubuwan da suke ɓata azumi matuƙar mutum ya aikata su; to azuminsa ya lalace, cikin waɗannan abubuwa, akwai:

    1. Ci ko sha da gangan, idan mai azumi ya ci abinci ko ya sha wani abin sha da gangan, to ya sani azuminsa ya lalace.

    2. Jawo amai da gangan, wanda ya janyo amai da gangan shi ma azuminsa ya lalace. Domin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ambata cikin hadisi cewa, “………… amma wanda ya jawo amai da gangan, to ya yi ramuwa”. (Abu Dawud 2/310, Tirmizi 3/79).

    3. Haila ko nifasi, idan mace ta yi jinin haila ko nifasi cikin wani yanki na yini sawa’un farko ne ko ƙarshe, to azuminta ya warware kuma ramuwa na kanta, idan kuma ta ƙarasa, to bai halatta ba, kuma ba ta da lada. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam ya faɗa cikin hadisai da suka zo daga Ibn Umar da Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa, “Ashe ba idan mace ta yi haila ba ta sallah, ba ta azumi ba? Suka ce “Haka ne”. Sai ya ce, “Wannan shi ne naƙasu a cikin addininta”. A wata ruwayar ya ce, “Tana zaman kwanaki ba ta sallah, tana shan azumi a Ramadan, to wannan shi ne naƙasu a cikin addininta”. (Muslim 79 – 80).

    Game da umarnin ramuwa kuwa, ya zo cikin hadisin Mu’azat da take cewa; “Na tambayi Nana A’isha na ce mata: “Me ya sa mai haila take rama azumi amma ba ta rama sallah?” Sai ta ce; “Baharuriya ce ke?” Sai na ce “A’a, ni dai ina tambaya ne”. Sai ta ce: “Ya kasance hakan yana samun mu, sai a umarce mu da rama azumi, amma ba a umartar mu da rama sallah”. (Bukhari 4/429, Muslim 335).

    4. Allurar ƙoshi, shi ne shigar da wasu sinadarai masu ƙosar da mutum cikin uwar hanji da nufin ƙosar da maras lafiya, to wannan yana karya azumi, saboda yana shiga ciki ne. Haka zalika idan uwar jini take bi, to ita ma tana karya azumi muddin tana zuwa ne a madadin abinci ko abin sha.

    5. Jima’i, Imam Asshaukani ya ce: “Jima’i babu saɓani kan cewa yana lalata azumi idan ya faru bisa mantuwa, to wasu daga cikin malamai sun haɗa shi da wanda ya ci ko ya sha alhalin ya manta”. Ibnul Ƙayyim ya ce; “Alƙur’ani ya yi nuni cewa jima’i yana karya azumi, kamar ci da sha babu sabani kan hakan”.

    Hadisi ya tabbata daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa; wani mutim ya zo gun Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ya Manzon Allah na halaka! Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce masa; “Me ya halakar da kai?”

    Sai mutumin ya ce; “Na sadu da matata cikin Ramadan!” Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce masa; “Za ka iya azumin wata biyu a jere?” Sai ya ce: “A’a”. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce masa; “Za ka iya ciyar da miskinai sittin?”. Sai ya ce “A’a”. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce masa “Zauna”.

    Sannan ya zauna; zuwa wani lokaci sai aka zo wa da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) da dabino, sai ya ce; “To ga shi nan, ɗauki ka yi sadaka da shi”. Sai mutumin ya ce; “A tsakanin unguwannin Madina kaf, ba wanda ya kai mu buƙata”. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya yi murmushi har haƙoransa suka bayyana; sannan ya ce masa “Ɗauki ka ciyar da iyalanka”.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ba Sa Ɓata Azumi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Laccocin Ramadan Na Mumbarin Jawabi Daga Malamai danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su

    Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su

    Halayen mai Azumi – Akwai waɗansu muhimman halaye da ya kamata mai azumi ya siffanta da su; a gan su da gaske a tattare da shi. Cikin halayen akwai:

    1. Haƙuri, wato mai azumi ya siffantu da haƙuri wanda shi zai zama jagaba a cikin lamuransa; ya hana shi bin son zuciya da saɓa wa Allah. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce “Idan ɗayan ku yana azumi, kada ya yi maganganun fasiƙanci. Idan wani ya zage shi, ya ce Ni mai azumi ne” (Sahihul Bukhari 1894, Sahih Muslim 1151).

    2. Riƙon amana, yana da kyau mai azumi ya zama mai riƙon amana; domin tana daga cikin abar da za ta taimaka masa wajen kiyaye azuminsa.

    3. Rahama, ana son mai azumi ya siffantu da rahama, da sakin hannu da karamci, da kuma yalwar zuciya. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da kwatankwacin ladan wanda ya ciyar ba tare da an rage ladan wanda aka ciyar ɗin ba” (Sunan al-Tirmizi 647, Sunan Ibn Majah 17).

    4. Nasiha, yana da kyau mai azumi ya kasance mai yin nasiha da kuma umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.

    5. Sulhu, mai azumi yana da kyau ya kasance mai yin sulhu da sasanta mutane; musamman la’akari da cewa ƙiyayya da gaba na kawo tsaiko wajen karɓar ibada da addu’a.

    6. Kame harshe, ya kamata mai azumi ya kame harshensa daga maganganu na shirme da shashanci, sannan ya nesanci giba, zagin mutane da yi musu ƙage ko sharri da ƙarya ko musu marar dalili; musamman abin da ya shafi siyasa ko wasan ƙwallo ko wanin waɗannan.

    An karbo hadisi daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Wanda duk bai bar faɗin magana ta zur da aiki da ita ba; to Allah ba shi da buƙatar ya bar cinsa da shansa”. (Bukhari 4/99).

    Haka nan wani hadisin dai daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) dake cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ba azumi ba ne barin ci da sha, shi azumi shi ne na yasasshen zance da batsa; ko da wani ya zage ka, ko ya yi maka wauta, to ka ce; “Ni mai azumi ne”. (Ibn Khuzaima 1996). Ibnu Majah ya fitar da hadisi mai ɗauke da razani ga mai yin maganganun banza a yayin da yake azumi, ya ce; “Sau da yawa wani mai azumin ladansa shi ne yunwa da ƙishirwa”.

    7. Rintse ido da kame farji, yana da kyau mai azumi ya rintse idanuwansa daga kallon haramun; ya kuma kare farjinsa daga dukkanin haramtattun abubuwa. A nan muna jan hankalin waɗanda ke ganin kallon fina-finai ko tashoshi na gusar musu da yunwa; haƙiƙa wannan kuskure ne babba da kuma munana zato ga Allah, da kuma keta iyakokin Sa. Su ma masu sanya fina-finai a tashoshi wajibi su ji tsoron Allah; su sani ribar rayuwa da albarkar abin da suke so shi ne ginawa bisa tafarkin Musulunci.

    8. Iklasi, ya kamata mai azumi ya ƙudurce cewa lalle yana yin wannan azumin ne saboda Allah; kuma domin neman yardar Allah, ba domin mutane su yabe shi ba. A nan, ana jan hankalin yan’uwa masu yin sadaka ko ciyar da masu azumi da masu tafsirin Alkur’ani; da limamai masu rera tilawa, da masu zuwa Umarah, da sauran aiyuka nagari; wajibi su sanya iklasi kada shaiɗan ya lalata musu ayyukansu.

    9. Bin sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam); wajibi ne mai azumi ya nesanci bidi’o’i, ya tsaya kan sunna ka’in da na’in; domin kyakkyawan aiki yana cikin koyi da Fiyayyen Halitta (Sallallahu Alaihi Wasalam).

    10. Tarbiyya, wajibi ne mai azumi ya tsaya wajen ƙoƙarin tarbiyyantar da kansa da ‘ya’yansa; ko ‘yan’uwansa ko waɗanda yake da iko a kansu. Kuma iyaye su ɗauki wannan wata a matsayin lokacin roƙarwa ‘ya’yansu shiriya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mafifitan Aiyukan Mai Azumi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Mafifitan Ayyukan Mai Azumi

    Mafifitan Ayyukan Mai Azumi

    Ayyukan Mai Azumi – Akwai ayyuka mafifita da ya kamata mai azumi ya kusance su; daga ciki akwai:

    1. Karatun Alƙur’ani Mai Girma, wato mai azumi ya lazimci karatun Alƙur’ani da kuma fahimtar saƙon da yake cikinsa, amma idan ba za a iya karatun ba, to babu laifi a lazimci majalasin karatun, wato wajen da ake karantawa tare da fassara Alƙur’ani.

    Nana A’isha, Abu Huraira da Ibn Abbas (Radiyallahu Anhuma), sun faɗa cikin hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa, “Mala’ika Jibrilu ya kasance yana karanta wa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) Alƙur’ani a kowane dare na watan Ramadana, sau ɗaya a kowacce shekara, sai ya karanta masa sau biyu a shekarar da zai yi wafati”. (Sahihul Bukhari 4997 – 4998, Sahihu Muslim 2450).

    Wannan hadisi ya nuna cewa karatun Alƙur’ani shi ne mafificin aikin ibada ga mai yin azumi a watan Ramadana, don haka, sai a himmatu da karatunsa.

    2. Kyauta, ana son mai azumi ya yawaita kyauta ta hanyar ciyar da jama’a da kuma sakin hannu gare su, da taimakon gajiyayyu da makusanta. An karɓo hadisi daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fi kowa kyauta, kuma ya fi yawaita kyautarSa a cikin watan Ramadan, musamman a lokacin da yake ganawa da Mala’ika Jibrilu. (Bukhari 4997).

    Haka nan Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce, “Alherin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fi sakakkiyar iska”. (Bukhari 1902).

    3. Sallar Nafila, ana so mai azumi ya yawaita nafila, musamman Ƙiyamul Laili (wato sallar dare); saboda kwaɗaitarwar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya yi cikin hadisin Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa, “Duk wanda ya tsaya yin sallar Ƙiyamul Laili, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa da suka gabata”. (Bukhari 2009).

    Haka nan cikin hadisin Abu Dharrin Alghiffariy (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Wanda ya yi sallar asham tare da liman, har ya idar, za a rubuta masa ladan ƙiyamul laili”. (Sunan Tirmizi 646, Ibnu Majah 1327).

    4. Yawaita zikiri, ana son mai azumi ya yawaita yin zikiri da salatin Fiyayyen Halitta (Sallallahu Alaihi Wasalam); domin akwai gwaggwaɓan lada ga yin zikiri da salatin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam).

    5. Ciyar da mai azumi abin buɗa-baki, yana daga cikin mafificiyar ibada ciyar da masu azumi abin buɗa-baki. Hadisi ya tabbata daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa; “Duk wanda ya ciyar da mai azumi abin da zai yi buɗa-baki, yana da kwatankwacin ladan mai azumin, ba tare da an rage ladan wanda ya ciyar ba”. (Sunan Tirmizi 647, Ibnu Majah 1746).

    A nan, muna jan hankalin masu hali a kan su taimaka wa mabuƙata, musamman makusantansu. Domin za ka iske mutumin da yake da hali a unguwa; amma kaso mafi yawa suna rasa abin da za su yi buɗa-baki, a wani lokacin kuma, masu ƙoƙarin yin sadakar ma, za ka iske suna yi ne cikin rashin kyautatawa, face kaɗan. Yana da kyau masu hali da shugabanni su gane, taimakawa a irin wannan lokaci; cikin iklasi da neman yardar Allah, wallahi rabautuwarsu ce. Amma ina tausayi da rahama, kai ka ci mai kyau, amma maƙwabtanka suna fama da yunwa!

    Yana da kyau ku ciyar daga mafi kyawun dukiyarku; kuma cikin abu mai kyau; tare da sakin zuciya da jin dadi da walwala.

    6. Umarah, yin Umarah cikin watan Ramadana na daga cikin mafifitan ayyuka; don haka, mutumin da yake da iko sai ya ɗauki azama. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Yin Umarah a cikin watan Ramadan daidai yake da aikin Hajji”. A wata ruwayar kuma Ya ce, “Wanda ya yi Umarah a watan Ramadan; tamkar ya yi aikin Hajji ne tare da Ni”. (Sahihul Bukhari 863).

    A nan ma, muna ƙara jan hankali, musamman ga waɗanda sun yi Umara; amma suna ta ƙara maimaitawa, alhali maƙwabtansu na fama da yunwa, da baƙin talauci. Ku sani, duk da wannan falala ta Umara ta nafila; duk da wannan lada, ciyarwa ita ta fi sama da Umarar da za ka tafi, alhali ga maƙwabtanka; ko danginka na fama da yunwa, da wahala ta rashin abin da za su ci, idan za su yi sahur; ko za su ci, idan za su yi buɗa-baki.

    Kuskure ne alhazan ke yi, sun je, ba sau ɗaya ba; ba sau biyu ba, su ƙara niƙar gari su tafi, alhali ga mabuƙata nan a kewaye da su.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Suke Ɓata Azumi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Muharram danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.