Tag: Azumi

  • Waɗanne Abubuwa Ne Ke Lalata Azumi A Ɓoye?

    Waɗanne Abubuwa Ne Ke Lalata Azumi A Ɓoye?

    Amsa: Abubuwan dake lalata azumi a ɓoye su ne:

    Akwai yi da wani da shaidar zur da gulma da ƙin yin sallah sai lokacinta ya wuce, babu wani dalili na shari’ah, ƙin yin sallah kwata-kwata.

    Hujja: “Wanda duk bai bar zancen zur ba, da aikata zur, da yiwa mutane mummunar fassara; Allah baya buƙatar yabar abincinsa da abin shansa”.

    Marawaici Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Rashin Yin Sallah A Cikin Jama’a Na Lalata Azumi? danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Dalilan Wajabcin Azumin Ramadana danna nan.

  • Falalar Watan Ramadana 1

    Falalar Watan Ramadana 1

    Falalar Watan Ramadana – Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa, “Wanda ya azumci watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa da suka shuɗe”.

    Haka nan, a wani hadisi, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Idan watan Ramadan ya shigo, ana buɗe ƙofofin rahama da ƙofofin Aljanna, kuma ana rufe ƙofofin Jahannama; kuma ana ɗaure shaiɗanu”. Haka kuma an rawaito daga Anas Ibn Malik Radiyallahu Anhu cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Lalle wannan wata na Ramadana, haƙiƙa ya halarto muku, a cikinsa akwai wani dare wanda ya fi watanni dubu alheri. Duk wanda aka haramta masa (samun alherin dake cikinsa); haƙiƙa an haramta masa alheri dukkansa. Kuma babu wanda ake haramta wa alherinsa sai wanda ba shi da rabo”. (Sunan Ibn Majah 1644).

    A dunƙule, za mu iya lissafo wasu cikin manyan falalolin watan Ramadan kamar haka:

    1. A cikinsa Allah ya saukar da Alkur’ani daga Lauhul Mahfuz, zuwa saman duniya.

    2. Wata ne da ake ɗaure shaiɗanu, ayyukan sharri suna ƙaranci a ban-ƙasa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam ya ce; “Idan watan Ramadan ya zo, sai a buɗe ƙofofin Aljanna, sannan a rufe ƙofofin wuta, kuma a kulle shaiɗanu”. (Bukhari 4/97, Muslim 2/757).

    Dukkan wannan yana kammaluwa daga lokacin da daren farko na wata mai albarka ya shigo, saboda faɗin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam)cewa; “Idan daren farko na Ramadana ya kasance, sai a kulle shaiɗanu da kangararrun aljanu, a rufe ƙofofin wuta, babu wadda za a bari daga cikinta, a buɗe ƙofofin Aljanna ba za a bar ko ɗaya a rufe ba. Sai wani mai kira hhya yi kira; “Ya mai neman alheri matso kusa, Ya mai neman sharri yi nesa!

    Kuma Allah yana da wasu ‘yantattu daga wuta, wannan kuwa yana faruwa a kowanne dare”. (Tirmizi 682, Ibnu Majah 1642).

    3. A cikinsa ne ake samun dare mafi daraja, wato Daren Lailatul Ƙadri. Anas Ibn Malik (Radiyallahu Anhu) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Lalle wannan wata na Ramadana, haƙiƙa ya halarto muku, a cikinsa akwai wani dare wanda ya fi watanni dubu alheri. Duk wanda aka haramta masa (samun alherin dake cikinsa), haƙiƙa an haramta masa alheri dukkansa. Kuma babu wanda ake haramta wa alherinsa, sai wanda ba shi da rabo”. (Sunan Ibn Majah 1644).

    4. Amsar addu’a da kuma ‘yanta bayi daga wuta a kowanne dare cikin watan Ramadana.

    5. Gafarta zunubai, kamar yadda ya zo cikin hadisin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa, ya hau minbari sai ya ce, “Amin! Amin! Amin!”. Sai aka tambaye shi, sai ya ce, “Haƙiiƙa Jibrilu (Alaihis Salam) ya zo ya ce mini: “Duk wanda ya riski watan Ramadan bai yi abin da za a gafarta masa ba, har aka shigar da shi wuta, to Allah ya nisantar da shi daga rahamarsa,”. Ka ce “Amin”. Sai na ce, “Amin”….(Imam Ahmad 2/246).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Ramadana 2 danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Gaggauta Buɗa Baki danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah) wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Sharuɗan Wajabcin Azumin Watan Ramadan

    Sharuɗan Wajabcin Azumin Watan Ramadan

    Azumin watan Ramadan yana sauka a kan wasu, sakamakon waɗansu dalilai da Shari’a ta aminta da su; shi ya sa wajen ci gaba da ayar da ta gabata, malamai suka bayyana ire-iren waɗannan mutane, tare da dalilan. Ci gaba da bayani, sai Allah ya ce; “Waɗansu kwanaki ne ababan ƙidayawa.

    To wanda ya kasance mara lafiya a cikinku, ko a kan wata tafiya; to (idan ya sha ruwa) sai ya rama a waɗansu kwanakin na daban, har ma waɗanda za su iya yin azumin; su ba da fansa ta ciyar da abinci ga miskini guda ɗaya, to dukkan wanda ya ƙara (a kan abincin miskini), to wannan ya ƙara wa kansa alheri.

    Amma ku riƙa yin azumin shi ne ya fi alheri a gare ku, in har kun kasance kuna sani”. Watan Ramadan shi ne wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa, shiriya ce ga mutane, kuma ayoyi bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa tsakanin ƙarya da gaskiya. Don haka dukkan wanda ya halarci watan cikin ku, to ya azumce shi. Kuma wanda ya kasance marar lafiya, ko a kan tafiya, (to idan ya sha ruwa) sai ya rama a waɗansu kwanaki na daban.

    Allah yana nufin sauƙi a gare ku, kuma ba ya nufin tsanani a gare ku. Don haka ku cika adadin (kwanakin Ramadan); kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da ya yi, kuma ku zamo masu godiya gare shi. Kuma idan bayina suka tambaye ka game da ni, to ni kusa nake (da su); ina amsa kiran mai kira, da zarar ya kiraye ni. To su nemi amsawata, kuma su yi imani da ni, domin su shiryu.

    An halatta muku saduwa da matayenku a daren watan Azumi, su sutura ce gare ku, ku ma suturu ce a gare su. Allah ya san ku kun kasance kuna ha’intar kawunanku, sai ya dawo da ku, kuma ya yi muku afuwa. To a yanzu ɗin ku sadu da su (da daddare), kuma ku nemi abin da Allah ya rubuta muku; kuma ku ci, kuma ku sha har farin zare ya bayyana daga baƙin zare na alfijir; sannan ku cika azumi zuwa dare, kuma kar ku sadu da su alhali kuna i’itikafi a masallaci.

    Waɗannan iyakoki ne na Allah, kada ku kusance su! Kamar haka ne, Allah yake bayyana ayoyinsa ga mutane; don su zamo masu taƙawa” (Bakara: 184 – 187).

    Waɗannan ayoyi a dunƙule sun yi bayanin waɗanda shari’a ta dauƙe musu azumin watan Ramadan; sakamakon wasu dalilai da karɓaɓɓu ne a Shari’a da sharaɗin bayan waraka daga waɗannan al’amura; sawa’un rashin lafiyar da za ta hana yin azumin ne, ko mace mai shayarwa ko juna (kamar yadda wasu malamai irin su Ibn Taimiyya da almajiransa; Auza’i, Hasanul Basri da Ibrahimul Nakha’i suka tafi a kan su ma marasa lafiya ne), ko matafiya ne; to za su rama waɗannan azumi da suka sha bayan kwanakin azumin, ma’ana bayan Ramadan.

    Sannan a cikin su, akwai bayanin waɗanda za su ciyar da miskinai abinci, sakamakon rashin lafiya; ko tsufa da mai ciki ko shayarwa bisa fatawar Abdullahi Ibn Umar, Abdullahi Ibn Abbas da Ishaq Ibn Rahawaihi; kamar yadda Sheikh Nasiruddeen Albani ya fitar a cikin littafinsa Irwa’ Alghalil 4/18 – 24).

    Shahid dai, waɗannan ayoyi ƙunshe suke da cikakkun bayanai game da wajabcin azumin Ramadana; da kuma nuni a kan waɗanda azumin ya wajaba a kansu, misali dukkanin musulmi, baligi, mai hankali; kuma wanda yake da ikon yi, mazaunin gida. Sannan an bayyana matakan da aka bi wajen shar’anta shi, da kuma waɗanda azumin ya zama wajibi a kansu. Domin neman cikakken bayani, sai a tuntuɓi malamai a majalisunsu domin jin yadda abin yake.
    A gefe guda kuma, akwai waɗanda azumin Ramadana ya sauka a kan su, ma’ana, su azumin Ramadana bai wajaba a kan su ba.

    Cikin irin waɗannan akwai:

    i. Kafiri.

    ii. Yaro, amma za a iya umartar sa da yin azumin domin ya saba.

    iii. Mahaukaci, wannan kuwa koda balagagge ne, domin ba ya cikin hankalinsa. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam ya ce, “An ɗauke alƙalami a kan mutum uku: mai barci har sai ya farka, yaro har sai ya balaga, da mahaukaci har sai ya warke”. (Sahihul Jami’ al-Saghir (3513).

    iv. Tsoho, amma zai bayar da mudun-nabi guda biyu, ko ya ciyar da miskini dafaffen abinci a madadin kowacce rana.

    v. Marar lafiya, sai dai akwai ramuwa a kansa bayan ya warke, wannan kuwa ko da bayan shekara nawa ne. Amma cutar da ƙwararrun likitoci suka tabbatar ba za a warke ba, sai dai kawai a ciyar a madadin kowacce rana.

    vi. Matafiyi, zai yi ramako bayan Ramadana.

    vii. Mai jinin haila ko jinin biƙi, amma ita ma akwai ramuwa a kanta.

    viii. Mace mai ciki ko shayarwa, ita ma za ta iya ajiye azumi idan tana tsoron cutuwarta ko cutuwar abin dake cikinta, ko abin da take shayarwa idan ta ci gaba da azumin.

    An rawaito hadisi daga Anas Ibn Malik Al-Ka’abi (Radiyallahu Anhu) cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Haƙiƙa Allah ya ɗauke wa matafiyi rabin sallah, kuma ya ɗauke azumi ga matafiyi da mai ciki da mai shayarwa”. (Sunan Ibn Majah, (1667).

    A nan malamai suka yi bayanin cewa, idan matuƙar dai matafiyi da mara lafiya za su rama azumi, to babu abin da zai sa a ce mai ciki ba za ta rama ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tsayuwar Watan Ramadan danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Dake Cikin Yin Sahur danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Sa Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tsayuwar Watan Ramadan

    Tsayuwar Watan Ramadan

    Tsayuwar Watan Ramadan – Azumin Ramadana yana tsayuwa ne da ganin jinjirin watan Ramadana; wato ba a amfani da ƙirgen kalanda ko lissafin taurari ba; a’a, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya alaƙanta yin azumin ne da ganin watan na Ramadana.

    Hadisi ya tabbata daga Abu Hurairata Radiyallahu Anhu cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Ku yi azumi domin ganin sa (wato Ramadan), kuma ku sha ruwa domin ganin sa (wato Shawwal). Idan watan ya faku a gare ku (ba ku gan shi ba), to ku cika Sha’aban kwana talatin”. (Sahihul Bukhari (1909), Sahihuul Muslim (1081).

    Wani abu muhimmi shi ne, ba sai kowa ya ga watan Ramadan ba sannan ya ɗauki azumi; ana iya ɗaukar azumi ko da mutum ɗaya ne ya ga watan. Domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Umar (Radiyallahu Anhu) cewa; “Mutane sun yi ƙoƙarin ganin jinjirin wata; sai na gaya wa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewar, “Ni na ga wata”. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ɗauki azumi, kuma Ya umarci al’umma da su ɗauka”. (Sunan Abu Dawud, 2342. Hakim, 423, da Ibn Hibban 3438).

    Faɗakarwa:

    Son zuciya da jahilci kan hana wasu tashi da azumi da hujjar cewa shugabanni ba adalai ba ne; alhali Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ba da dama a bi su hatta sallah, ballantana azumi. Bisa haka, idan adali ya shaida ya ga wata; kuma shugaba ya aminta da ganinsa, to wajibi ne a tashi da azumi.

    Dangane da sauƙe azumin kuwa, sai mutane biyu sun shaida cewar sun ga watan Shawwal; sannan a ajiye kamar yadda aka rawaito daga Abdulrahman Ibn Zaid Ibn Khaɗɗab; yayin da ya yi wa mutane huɗuba a ranar shakku (wato ranar da ake kokwanton ko Ramadan ne ko, ba Ramadan ba ne) .

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Watan Ramadana 1 danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ciyar Da Mai Azumi danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Ma’anar Azumi A Musulunci

    Ma’anar Azumi A Musulunci

    Azumi a Shari’a shi ne: kamewa daga barin ci da sha da jima’i da abin da zai ɗauki hukuncinsu; tun daga fitowar Alfijir; har zuwa faɗuwar rana ga keɓantattun mutane da niyyar bauta wa Allah.

    Domin karanta cikakken bayani akan Dalilan Wajabcin Azumin Ramadana danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sallar Ƙiyamul Laili (TAHAJJUD) danna nan

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Watan Ramadan (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Azumin Litinin Da Alhamis

    Azumin Litinin Da Alhamis

    Kamar yadda ake son azumin ranakun Alhamis da Litinin.

    Falalarsa.

    An karɓo daga A’isha (Radiyallahu anha) ta ce: “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana yin azumin ranakun Litinin da Alhamis” (Tirmizi 7451 Nasa’i 2/86).

    Kuma Usama Ibn Zaid ya tambayi Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) kan azumin litinin da Alhamis da yake yi, sai ya ce: “Waɗannan ranaku ne biyu da ake bujirar da ayyuka ga Ubangijin Taliƙai a cikinsu, in an so a bujirar da aikina ina azumi”(Nisa’I 2357, Ahmad 5/201).

    Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam) da Falalarsa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal (Sitta Shawwal) danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Muharram danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam)

    Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam)

    Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam) shi ne, yau a yi, gobe a huta. Iya tsawon rayuwar mutum.

    Falalarsa.

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Sallar da Allah ya fi so,, ita ce sallar Annabi Dawud (Alaihis salam) Kuma azumin da Allah ya fi so, shi ne azumin Annabi Dawuud (Alaihis salam)”

    (Bukhari 1976. Muslim 1159).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Raya Daren Lailatul Ƙadari danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Raya Daren Lailatul Ƙadari danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Falalar Dasa Bishiya danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane

    Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane

    Afɗara indakum saa’imuuna wa akala ɗa’aamakum abraaru; wasallat alaikumul mala’ikatu“.

    {Allah ya sa masu azumi su yi buɗa baki a wajenku; kuma Allah ya sa nagartattun bayi su ci abincinku; kuma Allah ya sa Mala’iku su yi muku addu’a}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ciyar Da Mai Azumi danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Da Ga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki

    Addu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki

    Zahabaz zama’u wabtallatil uruƙu, wa sabatal ajru in sha’allaahu”.

    {Ƙishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah ya so}.

    Abdullah bin Amr bin Al- As ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: “Mai azumi yana da addu’a da ba a mayar da ita idan ya zo buɗe baki”. Abdullahi bin Amr ya kasance idan ya zo buɗa baki sai ya ce:

    Allaahumma innii as’aluka bi rahmatikal latii wasi’atu kulla shai’in an tagfiralii“.

    {Ya Allah! Ina roƙon ka saboda rahamarka da ta yalwaci komai, ka gafarta mini}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Gaggauta Buɗa Baki danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.