Harsashin Gina Al’umma (Iyaye)

0
386

Samuwar mutum daga iyaye masu addini shi ne babban harsashin da za a gina kyawawan halaye da ayyuka na gari a kai. Kasanccwar mutum ya riga da ya gado wannan ɗabi’a ta addini daga mahaifa, hakan zai sanya shi bin dokokin addini ba tare da jin takura mai tsanani ba.

Saboda haka mutumin da ya siffantu da halin addini zai yi wa maƙiyansa waɗanda aka faɗa a baya wuyar ɓatarwa. Kuma saboda haka ne addinin Musulunci ya zaɓa wa mutum mace ma’abociyar addini wadda aka tabbatar da cewa ta fi mace mai dukiyar ko mai kyawu ko ‘yar dangi, matuƙar ba su da addini. Kuma saboda haka Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam ) ya umarci waliyyan (ma’aura) mata da cewa; da zarar wanda kuka yarda da addininsa (ya zo muku ) to ku aura masa. Babu shakka yin auratayya tsakanin mace da miji ita ce hanya mafi sauƙi wajen samar da mutum mai biyayya ga Allah ba tare da gumin goshi ba.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tarbiyyar Addini danna nan

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ɗan Adam Kamar Yadda Allah YaKe Son Sa. wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafi danna nan.

labarin da ya wuceKaratun Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)
Labarin na GabaKoyi Da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam)
Dr. Aminu Isma'il Sagagi
An haifi Dr. Sagagi a Unguwar Sagagi cikin birnin Kano a 1968 Ya yi PhD a IUA Khartoum 2012 Ya yi aikin koyarwa a Makarantar Munazzama Kura. Ya yi koyarwa a Makarantar koyon Sharia ta Malam Aminu Kano. Ya taba rike Mukamin Mai ba wa Gwamna Shawara a kan Ilimi 2009-2011 A yanzu Malami ne a Sashin Nazarin Addinin Musulinci a Jami'ar Bayero.