Falalar Sallatut Tasbihi

0
817

Duk wanda ya yi wannan salla, Allah zai gafarta masa dukkan zunubansa na farko da na ƙarshe, tsoho da sabo, na kuskure da na ganganci, babba da ƙarami,na fili da na ɓoye.

Kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ƙarfafa a yi wannan sallah kullum in da hali ko sati ko duk wata ko duk shekara kai ko da sau ɗaya ne a rayuwar mutum. Wannan bayani ya zo a hadisin da Abu Dawud (1279, Ibn Mjah 1387, Hakim 1/318, 319, Ɗabarani 161/11, da Abu Nu’aim 1/25- 26 suka ruwaito ta hanyoyi daban-daban daga Ibn Abbas.

Matsayin Wannan Hadisi

An daɗe ana saɓani kan inganci ko raunin wannan hadisin.
Daga ciki masu raunana shi akwai (1) Imam Ahmad (2) Tirmizi (3)Ibnul arabi (4) Ibnul Jauzi (5) Ibn Taimiyya da sauransu.
Masu ƙarfafa hadisin kuwa sun haɗa da Muslim, Abu Dawud, Hakim, Baihaƙi, Iban Hajar, Ahmad Muhammad Shakir da Albani. Allah ya yi rahama a gare su.
Amma malamai irin su ibn Huzaimah da Zahabi sun yi gum da bakinsu, ba su faɗi komai ba kan matsayin hadisin.
Saboda wannan saɓani ne, a kan sami saɓani kan hukuncin yin ita sallar, waɗansu suka ce ana so a yi, su ne wanɗanda suka inganta hadisin, waɗanda suka ce ba laifi in an yi, amma waɗanda suka raunana hadisin suna ganin sam bai halatta a yi ba. To wannan al’amari dai mai sauƙi ne, wanda zai yi ya yi, wanda ba zai yi ba ya bari. Allah ya ganar da mu amin.

Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Tahiyyatul Masjid danna nan .

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Yin Salatut Tasbihi
Labarin na GabaSallar Tahiyyatul Masjid