Munafuntar Al’umma Da Rashin Fayyace Alƙibla

0
823

A wannan zamanin da muke ciki, ‘yan siyasa sun mayar da yaudara tamkar adon siyasa, don haka, mafi yawancin su ba su da alƙibla guda da suka tabbata a kanta.

Tun wajen tara wa kansu mabiya da guraren tarurruka za ka tarar da abin da suke gaya wa jama’a, ba shi ba ne abin da suke binne a rai, kuma ba za ka iya fahimtar hakan ba, har sai sun kai ga samun abin da suka hara.
A wasu lokutan kuma za ka gan su suna kai gwauro, suna kai mari a tsakanin masu mulki a hannu, da zarar sun sami keɓewa da su, sai ka ji suna yabon su, suna wasa su; har ka ji suna cewa, ko a da can ba a yi kamarsu ba; kuma ko nan gaba zai wuya a sami kamar su, amma kuma da sun bar gabansu zuwa wajen sauran abokan siyasa basu da waɗanda suke zagi da cin mutuncin su kamar shugabannin nan da suke kururutawa a gabansu.

To, ‘yan’uwa musulmai a nan don mu san matsayin irin waɗannan jama’ar a musulunce ga hadisi kamar haka:

1. An karɓo daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Mafi sharrin mutane mai fuska biyu, wanda yake zuwa wajen waɗannan da wata fuska, waɗancan kuma ya zo musu da wata fuskar daban.”
2. An karɓo daga Muhammad ɗan Zaid ya ce: “Haƙiƙa wasu mutane sun ce da kakansa Abdullahi ɗan Umar, Allah ya yarda da su: “Mu mukan shiga wajen masu mulkinmu sai mu faɗa musu saɓanin abin da muke faɗa; idan mun fita daga wajensu. Sai Abdullahi ɗan Umar ya ce: “Mu a lokacin Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) mun kasance muna ƙirga yin haka munafunci ne.”
Imamul Bukhari da Abu Dawudaɗ-Ɗayalisi ne suka rawaito shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Fifita Sila Da Sanadin Faruwar Abu Fiye Da Hukuncin Allah Da Ƙaddararsa danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Hattara Dai ‘Yan Siyasa Musulmai wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceGulma (Tsegumi) Don Gurɓata Tsakanin Jama’a
Labarin na GabaFifita Sila Da Sanadin Faruwar Abu Fiye Da Hukuncin Allah Da Ƙaddararsa