Azuzuwa Da Kashe-kashen Makaranta A Tsangaya

0
420

Za a iya karkasa makaranta tsarin tsangaya gwargwadon matsayin karatu ko shekaru tsakanin sa’o’i daga almajirai.

Kowane aji na da siffofi da ake gane waɗanda ke ƙarƙashinsa, kamar yadda al’amarin yake a tsarin ilmin zamani tun daga kan ɗan firamare, sakandare da ‘yan manyan makarantu. Amma a tsarin tsangaya an fi la’akari da matsayin karatu fiye da shekaru wajen sanya suna.

Ƙolo:

Shi ne mafi ƙanƙanta a tsarin tsangaya ta fuskar karatu da yawan shekaru. Ƙolawa su ne a mafi yawan lokatu ke yin bara da ƙoƙo ko kwano don neman abinci. Shekarun ƙolo sukan fara ne daga shekaru bakwai zuwa shekaru goma sha huɗu. Kodayake dai da yawa akan samu iyayen da ke kai ‘ya’yansu tsangayu a ƙasa da shekaru bakwai. Rayuwar ƙolo na kasancewa cikin yanayi mai ban tausayi, musamman ma idan akwai ƙolawa da yawa a wannan tsangaya. ƙarancin shekaru da rashin cikakken wayo na gwagwarmayar rayuwa, kan ƙarawa rayuwar ƙolo tsanani. Rashin wanka da wanki a kan lokaci da kirci da datti, su ne a mafi yawan lokaci siffar almajiai a wannan aji.

Kirarin Kolo shi ne:

Ƙolo ɗan matar malam,
A taɓa ka a taɓa malam,
A bar ka, ka lalace
Da da hali, da an kai ka mandanari mandar,
Garin su gardi Lahirar ƙolawa.

Titiɓiri:-

Shekarun tittibiri kan fara daga shekaru sha huɗu, zuwa shekaru ishirin ko ishirin da huɗu. Titiɓiri shi ne almajiri da ya fara mallakar hankalinsa, domin kuwa a wannan lokaci, ya san ya yi wanka da wanki a kan lokaci. Hausawa kan yi wa titiɓiri take:
Titiɓiri masomin gardi,
Kai ba gardi ba,
Amma ka fi gardi ƙeta,
A saka gaba ka yi ƙeƙere ka ƙi sauri,
A bar ka a baya, ka tsikari matar Malam,
Wannan na nuna cewa titiɓiri na matakin balaga, Ma’ana ya zama murahiki.

Matashiya

Makaranta a tsarin tsangaya na da hanyoyin ladabtar da almajiransu ta hanyar yin nasiha, bulala, da dai sauransu. Idan kuwa aka samu gagararren yaro, malamai kan yi amfani da mari don ladabtar da shi. Irin waɗannan hanyoyi na da irin nasu matsalolin, tare da cewa suna taimakawa matuƙa wajen gyara tarbiyyar almajirai.

Gardi:

Shi ne makarancin da ya wuce ashirin da biyu kuma karatunsa ya yi nisa. A wasu lokuta a kan samu gardawa ɗaruruwa cikin tsangaya guda. Wannan kan sanya rayuwa makaranta samun cikakken yanayin tsangayar karatu, ta fuskar kishin kai da kuma nishaɗin zamantakewa. Tsangaya kan bunƙasa ne da gardawa, fiye da duk wani aji na makaranta da ya gabata. Makaranta kan ce idan tsangaya ta kai ta kawo cike da gardawa za a iya samun tsoma.

Tsoma aljani ne da ke rikiɗa cikin siffar gardi ya sauka a wata tsangaya ya ɓace cikin gardawa yana gogayya da kowa a matsayin makaranci ba tare da an gane ba. A duk lokacin da aka gane cewa wannan asali ba mutum ba ne, to shi ke na za a neme shi a rasa a wannan tsangaya. Labarai daga ƙasashen duniya na gaskata cewa akwai yiwuwar samun jinsin aljannu cikin masu neman ilmi a jami’o’i da wuraren taruwar ɗaliban ilmi, kwatankwacin tsoma a yanayin tsangayun Alƙur’ani na ƙasar Hausa.

Alaramma:

Shi ne mahaddacin da ke da ingantacciyar hadda. Da yawa wasu na ganin matsayin alaramma matsayi ne na wanda ya haddace Alƙur’ani, har ma ya rubuta shi. Ma’ana dai ya laƙanci duk wasu ilmai da luggogin baƙaƙe da wasulan Alƙur’ani. A wasu lokuta ma yana da ilmin “harji”. Harji wasu dunƙulallun kalmomi ne na harufan hisabi da makaranta ke amfani da su don tantance adadin kalmomi ko baƙaƙen Alƙur’ani. Barebari a wani lokaci kan kira mai irin wannan matsayin na Alaramma da Sayna.

Gwani:

Gwani shi ne matakin ƙoli cikin azuzuwan makaranta a tsarin tsangaya. Makaranci kan zama gwani bayan ya kai matakin gardi har zuwa matakin alaramma. Bayan alaramma ya yi shekaru da yin fice a fagen Alƙur’ani, makaranta kan ayyana shi a matsayin gwani a cikin su.
Ayyana makaranci a matsayin Gwani ya sha bamban da ayyana shi a matsayin alaramma. Makaranci kan zama alaramma ne da zarar ya cimma samun cikakkiyar haddar Alƙur’ani ko kuma rubuta shi da ka. Naɗa Gwani ko ayyana shi kuwa ya keɓanci wasu gungun makaranta keɓantattu a Arewacin Najeriya.

Irin waɗannan gidaje za a same su a Maiduguri. Wannan ya sanya al’amarin ayyana gwani tamkar bayar da silsila ne ko ijazi a wajen malaman Hadisi; musamman ma a ƙasashen Larabawa. Don haka ne ma zai yi wuya ka ga wani makaranci wanda ba ahlin abin ba, ya yi gaban kansa; ko ya bugi ƙirji ya ayyana almajirinsa ko wani makaranci dabam a matsayin gwani. Wannan ya sanya za a iya samum dubunnan waɗanda suka isa a kira su gwanaye, amma ba a kiran su da shi; saboda rashin samun zartarwar irin waɗancan malamai.

Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Samuwar Goni danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Kiɗan Fiyano danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAsalin Yawon Bundi Ko Ƙaura Wurin Makaranta
Labarin na GabaƊabi’un Makaranta da Halayensu Cikin Zamantakewar Tsangaya