Ma’anar wannan shi ne jera ayyuka cikin rayuwa ko burikanmu daki-daki. Ɗaya bayan ɗaya, gwargwadon muhimmancin kowannensu. Ta yadda aikin nafila ba zai jawo kuɓucewar farilla ba.
misali, wannan shi ne mutumin da ya yi sallolin ƙiyamul laili a cikin dare, amman bai iya yin sallar asubahi a lokacinta ba, ko barcin ya kwashe shi, har jam’i ya wuce shi.Kasancewar lokaci a rayuwarmu, wata ƙaddara ce mai daraja kuma yana gudu cikin gaggawa.
Saurinsa na awoyi 24hrs a rana, ko awoyi 168hrs a sati. Ko awoyi 1720hrs a wata, za ka ga akwai bukatar, mu san yadda za mu kasafta su, kamar yadda mahauci ke feɗe dabba ya kasafta ya ware kayan ciki da tsoka.
ya fitar da fata da kai da ƙafa. Dole kuma mu ririta lokacinmu na rayuwa, kamar yadda matafiyi ke taka-tsantsan wajen taɓa guzurinsa, ta yadda ba zai shantake a zango yana kwasar dabge da taba-ka-lashe ba, alhali akwai dogon tagi a gabansa, ga kuma guzirin kaɗan.
Za mu iya auna ayyukan da muke yi da muhimmancinsa a bisa waɗannan ma’aunai:
Aiki mai matuƙar muhimmanci, kuma mai buƙatar a gaggauta shi: Irin Wannan nau’i, ba a jinkirta shi, kuma ba a gabatar da wani aiki a kansa. Misali ayyukan ibada ko salloli biyar ko ɗaukar ɗanka da ya yanke, kuma jini ya ƙi tsayawa zuwa asibiti, ko shan magani a lokacinsa. Rashin bin wannan ƙa’idar zai iya jawo mummunan sakamako.
Aiki na larura mai buƙatar gaggawa, ƙarƙashin wannan nau’i akwai dukkan ayyukan da ba su kai darajar nau’in farko ba.
Misalin wannan shi ne, kai yara makaranta, saurararen baƙo ko karɓarsa idan ya zo.
Aikin da ba larura ba ne, amma yana buƙatar gaggawa: Ƙarƙashin wannan nau’i, akwai dukkan wani aiki da za a iya jinkirta shi, ba tare da an cutu ba. misali tsaftace haƙora da safe, shirya tafiya yawon buɗe ido, halartar wata lacca da dai sauransu.
Aikin da ba larura ba ne, amma yana buƙatar gaggawa. Dukkan aikin dake jawo asarar lokaci, kuma ba shi da alaƙa da cimma manyan burikanmu da manufofinmu a rayuwa a matsayinmu na musulmi.
Misali a nan shi ne, ka shirya za ka je duba mara lafiya asibiti, sai kallon wani fim a talabijin ya ɗauke hankalinka, har lokacin ya ƙure ka fasa.
Ko tsawaita hira ta talfon(waya) ko ma a kan taɗin kwallo, ko kakaci a kan siyasa ko sinima har ka kai tsakar dare. Abin mamaki irin waɗannan ayyuka kan cinye wani kaso mai yawa a rayuwarmu ba mu sani ba. Aikin da ba larura ba, kuma ba ya buƙatar gaggawa:
Misalan wannan nau’in su ne mafi muni, misali cinye awoyi a gaban talabijin don kallon fina-finai, karta ko ludo, karatun mujalla da jaridu na tsawon sa’o’i.
ɗaukar lokaci ana yawo a yanar-gizo (internet browsing) yawan barci, zama a kulob, zaman bencina a bakin titi, ko cikin lokuna ana hira.
Mai karatu shin ka taɓa tsara ayyukanka gwargwadon mahimmancin wanensu? Sau nawa ka taɓa gabatar da aikin da ba larura ba, bisa aiki mai matukar mahimmanci kuma na lalura?