Yadda ake fita daga cikin cutar damuwa.

0
288

Fama da matsanancin yanayi na damuwa abu ne wanda yake hana walwala da jin daɗi na rayuwar yau da kullum. Idan kana fama da tunani na baƙin ciki, kaɗaici, ko kana yiwa kanka kallon wanda bashi da amfani ko kallon banza, sannan kana ganin cewa kamar al’amuran ka bazasu daidaita ba, to ƙila fa kana fama da cutar damuwa ne.
Idan kanaso kasan yadda ake fita daga cikin cutar damuwa sannan ka koyi yadda zaka koma jin daɗin rayuwarka, ka bi waɗannan hanyoyin:

1. Hanya ta farko;
Fahimtar cutar damuwarka.

i. Kaje wajen likita ya duba ka.
Sai idan mutum yaje yaga likita ko masani akan fannin ciwuwwukan halayyen dan Adam ne tukunna za’a gane yadda cutar take da kuma asalinta.
Dayawa daga cikin magunguna suna iya bada gudun mawa izuwa ga cutar damuwa. Saboda haka, likitan ka shi zai baka gwaje-gwajen da ya kamata kayi, shi zai duddubaka ta yadda zai gano ta inda ƙarƙashin lamuran alamomin cutar suke.

ii. Ka gane cewa kana fama da cutar damuwa.
In kanaso ka fita daga cutar damuwar da kake ciki, sai ka fara tantancewa idan abubuwan da kake ji a jikin ka alamomin cutar damuwa ne. Duk da cewa alamomin cutar damuwa sun banbanta a gurin kowane mutum, ga wasu kaɗan daga cikin manyan alamomin cutar damuwa. Kana fama da cutar damuwa, idan:

 • kana jin kamar rayuwarka bata da amfani, ko kai kanka, kana cikin yanayi na rauni, ko kana jin kamar kana ganin kanka a matsayin mai laifi kana tsarguwa da kanka ba tare da sanin dalili ba.
 • kana jin rayuwar ka a raunane take sannan kana ganin ba abinda zai iya inganta maka rayuwarka.
 • kana yawan jin gajiya da kasala a jikin ka a ko mai kayi.
 • kana fama da rashin nutsuwa da rashin kwanciyar hankali da daddare, kuma kana fama da rashin barci da daddare da/ko tashi da safe.
 • ka daina jin daɗin abuwan da suke maka daɗi kuma suke sa maka farin ciki a da, kamar zama da abokai, yin abubuwan da suke saka ka nishaɗi, ko kuma jima’i.
 • akwai babban sauyin yanayi a yadda kake barcin ka ba kamar yadda ka saba ba, kamar rashin barci, tashi da sassafe, ko kuma nauyin barci.
 • bakajin kana son cin abinci ko kuma cin ka ya ƙaru sosai, amma kuma ka kasa dainawa.
 • yafi maka sauƙi ka zauna cikin kaɗaici akan kayi mu’amala da mutane.
 • abu kaɗan ne yake ɓata maka rai kuma ba tare da ƙwaƙwƙwaren dalili ba.
 • kaji ranka yana ɓaci ba tare da dalili ba.
 • ka taɓa yin tunanin kashe kanka. Idan kana tunanin kashe kanka to ka gaggauta neman taimako nan take.

iii. Ka fahimci abubuwan da suke da alaƙa da saka ƴiwuwar ciwon damuwa.
Duk da dai likotoci da masana fannin cutar basu bada dalili ɗaya kacal da yasa mutane suke fama fa cutar ba, suna ganin cutar tana tattare da mutane ne masu ƙwayoyin halitta iri ɗaya ta yadda zasuyi gadon ta, da kuma yanayi.
Ko wani ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya zama shine silar faɗawar ka cikin cutar damuwa:

 • sabo da shan giya, ko ƙwayoyi, ko duk wasu abubuwan kayan maye.
  Idan ka saba da shan giya ko ƙwayoyi ko duk wani abu da zai saka maye, to wannan zai iya zama silar da ta jefa ka cikin ciwon damuwar da kake fama dashi. Likita ko wani masani kan lamuran sabo da shaye-shaye zai iya taimaka maka ya ɗora ka akan ƙa’idojin da ya kamata kabi domin fita daga cikin sabo da shaye-shayen ka.
 • samuwa ta gado. Idan akwai masu fama da ciwon damuwa daga cikin ahalin ka, musamman ta ɓangaren iyaye da kakanni, to fa kaima zaka iya kamuwa dashi ta gado.
  Zaka iya tattaunawa da mutanen gidanku ka tambaya ko da kuwa akwai wanda yake da cutar a cikin ahalinku, ko da kuwa ba’a taɓa gano asalinta ba; zaka iya tambayar iyayen ka ko wasu daga cikin ƴan’uwan ka ko an taɓa samun masu cutar a ahalinku da kai baka sani ba.
 • rashin daidaiton ƙwayoyim sarrafa abubuwa a jikin ɗan Adam. Idan kana fama da rashin daidaiton wasu ƙwayoyi na cikin jikinka masu sarrafa abubuwa, ƙila shine yake saka maka ciwon damuwar ka.
 • wata cutar daban. Likita zai iya taimaka maka ya gani ko kana fama da wata cutar daban ce wadda zata iya saka maka cutar damuwa, kamar cutar juyayi ko cututtukan da suka shafi tunanin mutum.
 • sakamakon wani magani da kake sha.
  Idan kana shan wani magani na wata matsalar da kake fama da ita, likita zai iya faɗa maka idan cutar damuwa yana daga cikin sakamakon wannan maganin kuma zai iya baka wani maganin da yake da amfani iri ɗaya wanda baya saka wannan sakamakon.
 • sauyawar yanayi.
  Wasu mutanen sukanyi fama da cutar damuwa saboda sauyawar yanayi. Misali, alamomin cutar suna iya bayyana a cikin yanayi na sanyi ko zafi.

iv. Ka duba abubuwan da zasu iya saka ka a cikin cutar damuwa masu dalili.
Ka fara tunanin abubuwan da suke da tushe na ciwon damuwar ka wanda suke saka maka zafin ciwon a rayuwarka ta kullum. Akwai yiyuwar cewa wasu abubuwan da suke faruwa da kai, da yadda kake tafiyar dasu, sune suke bada gudunmawa izuwa ga cutar damuwar ka. Ga wasu daga cikin abubuwan da kan iya janyo silar jefa ka cikin cutar damuwa ko kuma ma suke ƙara dagula lamarin cutar damuwar ka:

 • mutuwar aboki ko masoyi.
  Shiga cikin yanayi na baƙin ciki da alhini na rashin mutum abu ne wanda aka saba kuma mara aibu, amma, bayan wani lokaci, yawanci daga cikin mutane sukan dawo daidai. Idan baka daina jin baƙin ciki ba bayan watanni, to fa kila kana fama da cutar damuwa ne.
 • lalatacciyar dangantaka, mara daɗi, ta soyayya ko zamantakewar ma’aurata.
  Idan kana fama da zafin rabuwa da kayi da masoyinka, ko kana cikin dangantakar da take baka rashin kwanciyar hankali, zai iya bada gudunmawa izuwa ga cutar damuwar ka.
 • sana’a mara amfanuwa a gareka.
  Idan bakajin daɗin sana’ar da kakeyi, ko kuma kana wa kanka kallon banza a sana’ar da kakeyi, to ƙila aikin ka yana bada gudunmawa izuwa ga cutar damuwar ka.
 • yanayin zama mara kyau.
  Idan kana zaune ne da maƙotan da suke takura maka, ko kuma bakajin daɗin gidan ka ko unguwar da kake ciki, toh yanayin ka ƙila yana bada gudunmawa izuwa ga cutar damuwar ka.
 • matsalar kuɗi.
  Yawan damuwa akan inda zaka sake samun kuɗi ka biya kuɗin haya, ko abinci, ko wani abu mai amfani kan iya zama gagarumin silar jefa ka cikin ciwon damuwa musamman idan matsalar kuɗin mai cigaba ce.
 • yanayin damuwa da baƙin ciki da mata suke shiga bayan haihuwa.
  Yawancin mata sukan shiga cikin hali na baƙin ciki da damuwa bayan sun haihu. Wannan na iya zama mai tsanani wanda ake kira da cutar damuwar bayan haihuwa. Sai ayiwa likita bayani idan alamomin ki yayi kama da na wannan.

v. Fahimtar zaɓin hanyoyin magance cutar damuwar ka.
Likita zai faɗa maka zaɓin hanyoyin magance cutar damuwar ka da ya dace da kai. Ya danganta da yadda tsananin cutar damuwar ka take, ƙila kana buƙatar a haɗa maka da magunguna da kuma samun zama da masani kan halayyar dan Adam. Duk da magunguna suna iya ƙoƙarinsu na kawar da cutar damuwa, amma yanada matuƙar amfani mai fama da cutar damuwa ya fahimci cutar sannan ya koyi dabaru masu lafiya wanda zai jure wa cutar. Yawanci, ƙananan cututtukan damuwa a kan warkar dasu da zama da ƙwararru da masana halayyar dan Adam, da kuma gyara salon yadda mutum ke tafiyar da rayuwarshi.

 • akwai magungunan da an tabbatar da suna magance cutar damuwa.
 • akwai samun zama da akeyi da ƙwararru da masana halayyar dan Adam wanda shima yana taka babbar rawa a wajen kawar da cutar damuwa.
 • akwai kuma wata hanya da ake yiwa masu fama da matsananciyar cutar damuwa magani, itace hanyar da ake tayar da ƙwaƙwalwar mutum da na’ura. Wannan hanyar ana bin ta ne idan mai fama da cutar damuwa magunguna basuyi mishi aiki ba, ko kuma zama da ƙwararru bai mishi aiki ba.

vi. Ka samu littafi ka fara rubutu akan abubuwan da suka shafi rayuwar ka.
Fara yin rubutu akan abubuwan da suka shafi rayuwar ka kan taimaka wajen gano inda cutar damuwar ka take, da tunane-tunanen ka, sannan kuma zai sa kayi duba izuwa ga yadda kake tunanin ka a kullum. Ka ƙudurce yin rubuta a littafin ka a ƙalla sau ɗaya a kullum, musamman da yamma ko dare, ta yadda zaka kammala dukkan abubuwan da wannan ranar ta kawo a gareka.
Rubutu yakan sa kaji kana da alaƙa da tunanin ka, ya kan sa kaji kamar ba kai kaɗai bane, sannan yana sa kasan abubuwan da suke saka ka farin ciki da abubuwan da suke saka ka baƙin ciki.

 • rubutu yana taimakawa wajen sa ka mai da hankali izuwa ga kanka, sannan yana rufe zuciyar ka ga tunanin abubuwan da ke janyo rashin jin daɗi a rayuwarka.

2.
Hanya ta biyu;
Inganta rayuwarka.

i. Ka cire duk wata lalatacciyar zamantakewar da bata da amfani a rayuwar ka.
Idan zamantakewar da kake ciki yana saka maka baƙin ciki, to lokaci yayi da ya kamata ka daina shiga cikin halin rashin jin daɗi saboda wannan.
Ka rabu da duk wani wanda yake haddasa maka baƙin ciki, idan wanda yake saka maka wannan baƙin cikin ɗan’uwan ka ne wanda bazaka iya rabuwa dashi ba, to ka zauna da wannan mutumin a mafi ƙarancin lokacin da zaka iya.

 • idan akwai abinda yake damun ka a cikin wata zamantakewa, ka zauna ku tattauna sosai da wanda kake cikin zamantakewar tare. Misali, idan kana fama da cutar damuwa ne saboda matar ka tana cin amanar ka, ko kuma aminin ka yana satar maka kuɗi, to mafi dacewa shine ka tunkare su da maganar ta yadda za’a nemi mafita.

ii. Kulawa da lafiyayyen dangantaka da zamantakewa.
Duk da dai zaka ji wani lokacin ka fi son zaman kaɗaici ba tare da mutane ba, yana da kyau ka sani cewa abu ne mai kyau ga yanayin ka zama cikin mutane. Ka dogara ga abokan ka da kuma ƴan’uwan ka, sannan ga masoyinka in kana da shi.
Ka zauna da mutanen da suke saka ka farin ciki da nishaɗi na mafi yawan lokacin da zaka iya. Abokai na ƙwarai ba iya taimaka maka sukeyi wajen kawar da cutar damuwarka ba, har da taimaka maka wajen yadda zaka ji daɗi da kuma sanin cewa ana sonka da goyon bayanka sukeyi.

 • idan kana da aboki ko ɗan’uwa wanda yake fama da cutar damuwa, ka musu magana, sannan kaga wani irin shawarwari zasu baka. Magana da wanda yake fama da irin cutar da kake fama da ita kan sa kaji bakai kaɗai bane.
 • idan kana cikin zamantakewar auratayya ne, ka samu ka samar da lokacin soyayya da kai da wanda kuke cikin zamantakewar tare. Ku samu lokacin da zaku zauna ku kadai kuna jin daɗin ku.
  Kaji daɗin zamantakewar ka da samar da lokacin zama da abokin zamantakewar ka a mafi yawan lokacin da zaka iya.
 • ka ƙarawa iyalanka lokacin ka. Iyalanka ya kamata su zasu saka ka kaji ana ƙaunar ka da goyon bayan ka, saboda haka, kayi ƙoƙarin zama a cikin iyalan ka a mafi yawan lokacin da zaka iya. Idan kana da nesa da iyalanka, musamman idan ba’a ƙasa ɗaya kuke ba, to ka dinga samar da lokacin da zaka dinga kiransu ta wayar salula.

iii. Ka tsara jadawalinka na kanka ta yadda zaka ciki shi da abubuwan da kakeso kuma kake ƙauna.

Idan ka tsara jadawalinka ta yadda zaka kasance kullum kanada abinda zakayi, to wannan zai sa dole zaka zama kana cikin aiki, zaka kasance kana jin karsashi, zaka zama kana mayar da hankali, sannan zaka dinga tunanin abu na gaba da zakayi.
Zaka iya tsara jadawalinka na kowace rana daga farkon mako, ko kuma ka tsara na kowace rana a kullum, a kowani dare kafin wannan ranar. Duk hanyar dai da ka ɗauka, ka tabbatar ka ƙudurce manufar riƙe wannan hanyar.
Ga wasu daga cikin abubuwan da ya kamata ka basu lokaci na kansu:

 • abota da mutanen kirki, nagari, masu goyon bayanka.
 • motsa jiki
 • ayyukan hutu da abubuwan da kakeso wanda suke baka nishaɗi.
 • lokacin da za ka zauna ka nutsu, kayi rubutu a littafin ka, ko kayi tunani.
 • lokacin da zakayi abubuwa na wauta wanda suke saka nishaɗi da dariya, tunda murmushi da dariya sukan saka mutum cikin farin ciki.
 • wasanni wanda akeyi a waje. Kada ka ɓata duka lokacinka a cikin gida. Maimakon hakan, ka fita waje cikin rana, ko kayi wasu ayyukan da ka saba yi a cikin gida a waje, kaman a gidan cin abinci mai kyau ta yadda baza kaji kana cikin kaɗaici sosai ba.

Idan ka kai bugun zuciyar ka sama na tsawon minti 27 ta hanyar yin wani abu na motsa jiki, ya kan iya ɗaga sinadarin da yake sawa ƙwaƙwalwarka nutsuwa. Saboda haka, zuwa yin gudu ko iyo a ruwa kan taimaka sosai.

iv. Ka nemo wani abu sabo wanda kake so.
Ba lallai kanason aikin da kakeyi a yanzu ba, kuma ƙila baka cikin matsayin da zaka sauyawa kanka aiki a yanzu. Neman abinda kakeso kan taimaka maka wajen jin cewar kanada manufa a rayuwarka kuma wannan shi zai baka dalilin tashi da safe kullum da zumma. Abinda kakeso kan iya zama duk abinda kake ganin kana muradin yin shi, ko da kuwa baka ƙware sosai a yin wannan abin ba.
Ga wasu daga cikin hanyoyin da zasu taimaka maka wajen neman abu/abubuwan da kakeso:

 • ka bincika bangarenka na fasahar da kake dashi. Ka shiga koyon zane na rubutu, zane da launuka, ko ajin koyon yin abubuwa da yumɓu.
 • ka bayyana kanka ta hanyar yin rubutu. Ka gwada rubuta ɗan taƙaittacen labari, ko zube.
 • ka samo sabuwar soyayyar son koyon yaren da ba naka ba.
 • ka samo sabon wasa mai tawagar mutane, kamar wasan ƙwallo ko wasan ƙwallon kwando. Zaka samu abinda kakeso a yanayin da kakeyin sababbin abokai.
 • ka samo soyayyar ka da karatu ta hanyar shiga wata ƙungiya ta masu son karatu.
 • kayi ƙoƙari kasan manufarka a rayuwa. Menene abunda ya kamaceka kuma kakeso kayi a duniyar nan? Samo/ nemo waɗannan amsoshin kan iya taimaka maka wajen nema wa kanka mafita a kowane irin yanayi.

v. Ka ƙara akan yadda kake taimako, ka zama mai taimako da taimakawa.
Ka juyar da rayuwarka daga cikin cutar damuwa ta hanyar zama mai taimako izuwa ga mutanen da kakeso da kuma mutanen unguwarku. Idan kana taimako, hakan nasa mutum yaji rayuwarshi tanada amfani, kuma zaisa ka gina alaƙa mai ƙarfi tsakaninka da mutanen da kake tare dasu.

 • kayiwa abokan ka makusanta alfarma. Ba lallai sai alfarmar ta zama babba ba- idan babban abokin ka yana fama da aiki sosai, zaka iya zuwa ka daukeshi ko kuma ka mishi wanki da guga. Zakaji daɗi idan ka taimaka.
 • ka sa kanka cikin aikin taimako a masallacin unguwarku, ko gidan karatun unguwarku, ko makarantun unguwarku.
 • ka sa kanka cikin aikin taimako a gidan marayu, gajiyayyu, marasa muhalli, yan gudun hijira, sannan kaga irin gudunmawar da kaima zaka iya bayarwa.
 • ka sa kanka cikin aikin taimakawa wajen gyaran muhallinku a unguawarku, ko gonaki, ko lambu.
  Iya zama a cikin lambu mai shukoki da halittun Allah na tsawon wani lokaci kan taimaka wajen inganta yanayin ka.

3.
Hanya ta uku;
Sabarwa da kanka lafiyayyun halaye da al’adu na yau da kullum.

i. Ka inganta halayyar baccin ka.
Gyaran halayyar baccinka kan iya zama babban cigaba ga lafiyar ƙwaƙwalwarka. Ka duba kaga lokacin bacci da tashi wanda yafi dacewa dakai. Ga wasu daga cikin abubuwan da zakayi:

 • ka fara kwanciya da tashi a lokaci guda a kowani dare da safiya. Wannan zai sa kaji kafi samun hutu, kuma zai sauƙaƙa maka wajen yin bacci da tashi a koda yaushe.
 • ka fara sauka daga kan gadon ka da ƙafar dama. Ka tashi nan take daga kan gadon sannan kasha kofi daya na ruwa maimakon kayita juyi kafin ka taso daga kan gado.
 • ka gyara ɗabi’unka wanda kakeyi kafin ka kwanta bacci. Idan lokacin baccinka ya kusan zuwa, ka kashe talabijin, ka ajiye wayar ka ta salula a gefe, ka guji hayaniya da kuma karatu akan gado.
 • ka rage/daina shan sinadaren da suke hana mutum bacci, musamman wanda suke cikin shayi, goro, musamman da yamma ko dare. Basa sa mutum yayi bacci.
 • ka guji yin ƙananan baccin da suke wuce rabin sa’a, sai dai in kana buƙatar su- su na sa ka dinga jin kasala sannan su gajiyar da kai.

ii. Motsa jiki.
Motsa jiki na minti 30 kacal a rana yana yin tasiri sosai akan inganta lafiyar jikin ka da lafiyar ƙwaƙwalwarka. Motsa jiki yana ƙara maka ƙarfi sannan yana sa maka ƙwarin gwiwar yin abubuwa a kowace ranar da kayi shi.
Ka nemo tsarin motsa jiki wanda yafi dacewa da kai sannan ka riƙeshi ka dinga yi.

 • iya tafiya a ƙafa na minti 20 a kowace rana yana iya zama motsa jiki.
 • ka nemi wajen/gidan motsa jiki, ko ka nemi aboki wanda zaku dinga motsa jiki tare, hakan na taimakawa wajen kaji kana jin daɗin motsa jikin.
 • ka ƙudurce manufar motsa jiki na tsawon wani lokaci ko yin wani abu sabo, zaka iya ƙudurce niyyar motsa jiki na tsawon sa’o’i ko kayi wani sabon salon motsa jikin da baka saba yi ba.

iii. Ka inganta cimarka ta cin abinci.
Cin abinci mai kyau, lafiya, ingantacce, a daidaice kan taimaka wajen kawar da cutar damuwa. Ko da kuwa bakajin kanason cin abinci, ya kamata ka jajirce kaci abinci sau uku a rana. In kana fama da cutar damuwa, kar ka bari ka rame sosai saboda rashin cin abinci, cin abinci mai kyau da lafiya akai-akai zai taimaka wajen inganta lafiyar jikinka da kuma lafiyar ƙwaƙwalwarka.

 • kada ka dinga ƙetare cin abincinka- musamman karin kumallo. Cin abinci sau uku a rana zai baka ƙarfi da karsashin da kake buƙata ka fatiyar da lamuran rayuwarka, sannan yana sa maka nutsuwa da mai da hankali.
 • ka ƙara ƴaƴan itace da kayan lambu sosai a cikin cimarka. Ka koma cinsu a maimakon kayan zaƙi ko abincin da bai da amfani.
 • ka tabbatar da kana cin daidaitaccen ƴaƴan itace, kayan lambu, hatsi, kifi, da abinci mai gina jiki a kullum.
 • kar ka matsawa kanka, idan kanajin kwaɗayin cin wani abu wanda kake marmari, zaka iya ci daga lokaci zuwa lokaci. Zaka fi jin dadin bin ƙa’idar inganta cimarka idan kana cin abubuwan da kake ƙwadayi da marmari daga lokaci zuwa lokaci.

iv. Ka dinga tunani mai kyau.
Yin tunani mai kyau na taimaka maka ka dinga kallon rayuwarka da duniyarka ta yadda zaka dinga fatan yin wani abu mai kyau ba akasin haka ba. Idan kanaso ka dinga tunani mai kyau, sai ka fara koyon yadda zaka iya gane tunani mara kyau, kuma ka yaƙe su da ƙarfin tunani mai kyau a duk lokacin da zaka iya.
Ta yadda zaka iya fara tunani mai kyau, ka nemi a ƙalla abubuwa guda 5 wanda kake godewa Allah a kansu sannan suke saka jin daɗi a koda yaushe.

 • kayi ƙoƙarin ajiye littafi wanda yake cike da abubuwan da kakeso ko suke saka ka farin ciki. Kullum ka rubuta abubuwa wanda kakeso ko suke saka ka farin ciki guda uku, ko fiye da haka, sannan a kowani sati ka karanta abubuwan da kakeso. Wannan zai sa ka dinga hangen rayuwa ta fanni mai kyau sannan zai taimaka maka wajen mayar da hankalinka akan abubuwa masu kyau akan marasa kyau.
 • idan kana aiki mai kyau ko kana kallon rayuwa ta mahanga mai kyau, hakan zai sa ka dinga tunani mai kyau.
  Kayi tsari a rayuwarka ta yin magana akan abubuwa masu kyau na rayuwarka ko ka dinga tafiyar da lokacinka a gurin yin abubuwan da suke saka farin ciki da nutsuwa.
 • idan kafi tafiyar da lokacinka akan yabon abubuwan da suke saka murmushi da farin ciki akan abubuwan da basu da kyau, ko abubuwan da suke saka baƙin ciki, ko abubuwan da baka so, tunanin ka zai karkata izuwa tunani mai kyau. Ka faɗawa kanka iya “ranar yau zata zama babbar rana a gareni” ko kuma “hakan yamin daidai, yau ina cikin farin ciki, ranar yau tana yimin daɗi, bazan bari a ɓata min ranar nan ba!” zai sauya yanayin ka izuwa ga yanayi mai daɗi sosai da sauƙi a gareka, zaka kasance kanajin daɗin yanayin da kake ciki a iya faɗawa kanka irin waɗannan kalaman.
  Ka kasance kana murmushi a koda yaushe, hakan yana saka cikin farin ciki, ko da kuwa baka cikin farin ciki.

v. Ka inganta yanayin shigarka da tsaftarka.
Banzatar da inganta yanayin da yadda kake shigarka da tsaftarka yana daga cikin abubuwan da suke nuna sakamakon cutar damuwa.
Duk da dai bazaka fita daga cutar damuwa ta iya inganta yanayin shigarka da tsaftarka kacal ba, idan ka ɗauki lokacinka ka gyara yadda ake ganinka, idan ka ɗauki lokacinka kana kula da yanayin yadda kake shigarka da kuma tsaftarka a koda yaushe, kai kanka zaka fi jin daɗi a kanka.
Ka dinga wanka kullum kuma ka dinga wanke bakinka da gashinka.

 • kayi aiki wajen inganta yanayin yadda kake shigarka da tsaftarka a lokacin da kake zaune kai kaɗai da kuma lokacin da zaka fuskanci mutane, ko da kuwa baka jin kanason kayi hakan. Wannan zaisa ƙwarin gwiwarka na fuskantar mutane da kuma jin cewa kaima kanada amfani duk su ƙaru.
 • idan kana ganin cewa ƙibar da kake da itace, itace sanadiyyar jefaka cikin cutar damuwa, to ka samar da wani tsarin da zai inganta kuma ya kula da wannan al’amarin na rage ƙibar da kake dashi, wanda zai inganta kuma ya ɗaga yanayinka izuwa ga yanayi mai kyau da bayyanar ka.

Rubutun nan a taƙaice
Shawo kan cutar damuwa yakan zama abu mai wahala, amma zaka iya koyon yadda zaka koma jin daɗin rayuwarka kamar yadda ka saba ta hanyar inganta zamantakewarka, dangantakarka, da kuma yin zabi mai kyau da lafiya a rayuwarka.
Misali, kayi ƙoƙarin samun lokaci ka zauna da ƴan’uwanka da iyalanka. Sannan ya zamana cewa mutanen da zaka kewaye kanka dasu mutane ne na kirki, masu tunani mai kyau, masu goyon bayanka idan ka shiga cikin wani hali. Bacin samun lokacin zama da mutane, kaima ka warewa kanka lokacin kanka, ka tabbatar da cewa ka ware lokacin da zaka dinga yiwa kanka aiki. Misali, ka inganta yanayi da halayyar baccinka ta hanyar kwanciya da tashi a lokaci guda a kullum domin hakan ya taimaka maka wajen jin cewa ka huta sosai yadda ya kamata, sannan ya ƙara maka ƙarfi da karsashi a jikinka. Kayi amfani da wannan ƙarfin ka haɗa wani tsari da zaka dinga motsa jikinka a kullum tunda iya minti 30 na motsa jiki kullum yana inganta lafiyar jikinka da ƙwaƙwalwarka sosai.
Domin koyon yadda zaka kawarda abubuwa marasa kyau wanda zasu dinga janyo ka baya, kaci gaba da karatu!

labarin da ya wuceYaren Soyayya A Mahangar Addini da Nazarin Kimiyyar Halayyar Dan Adam
Labarin na GabaRuwaya (quotation)
Sufian Ibrahim marubuci ne, kuma therapist ne, musamman mental health therapy da addiction therapy, poet ne, spoken word artist ne, jakadan zaman lafiya ne, sannan kuma mai san yaga chanji mai kyau a yanayin rayuwar al’umma ne. Yana karatu ne a Jami’ar Bayero dake Birnin Kano (BUK), inda yake karantar haɗakar nazarin halittu a ɓangaren kimiyyar rayuwa.