Waƙar Gulma .

0
916

A baitukan yau na tsaya, Na fara zancen shiriya, Na tsara baiti ku biya, Na sanya zancen anbiya,  Ku bi ni sala-sala.

 

  • Na gode Allah a gaba,
  • Salati sallam na zuba,
  • Gurin Nabiyyi mai haiba,
  • A gun Sa ba a giba,
  • Sai dai ka koyo sallah.
  • ———————-
  • Ka gode Allah ɗan’uwa,
  • Ya yo ka mai kyan ƙwalwa,
  • Ya ba ka ilmu da yawa,
  • Ya ba ka hikmar baiwa,
  • Waninka ko sai ƙ
  • ————————–
  • Ka daina kallon kowa,
  • Ni’im suna nan da yawa,
  • Fa Rabbi ne mai kai wa,
  • Gare ka dukkan bawa,
  • Ka gode wannan falala.
  • ————————-
  • A yau na gane jama’a,
  • Suna da kyawun ɗa’a,
  • Fahimta ce ke bara’a,
  • Ta kauce tsarin ɗa’a,
  • Hakan ko babbar illa.
  • ————————-
  • Ka gane komai ka faɗa,
  • Idan kana son hulɗa,
  • Ana ɗaga shi a yaɗa,
  • A ɓata zancen a haɗa,
  • Domin a kushe falala.
  • ———————-
  • Idan ka ce an ƙi ka,
  • Ka ƙara kallon kanka,
  • Ka seta ƙalbin naka,
  • Sannan ka kalli waninka,
  • Akwai dalilai ƙanana
  • ————————
  • Ga shawara zan ba ka,
  • Ka gyara harshen naka,
  • Ka bar batun an ƙi ka,
  • Da ni da kai mui harka,
  • Haza ɗabi’armu Allah.
  • —————————
  • Ku duba zancen nan dai,
  • Da kyau da kallon daidai,
  • Ina ganin nai daidai,
  • Ban kauce zancen sai dai,
  • Ɗanbarno zo kai lela.

 

domin samun karanta cikakkiyar waƙar danna koren rubutu

labarin da ya wuceYadda Za A Gabatar Da Aiki Mafi Muhimmanci
Labarin na GabaWaƙar Hamdala .