Category: Waƙa

  • Maƙala Mai Taken: Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a Sikelin Manazartan Ƙarni Na 21

    Maƙala Mai Taken: Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a Sikelin Manazartan Ƙarni Na 21

    Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a Sikelin Manazartan Ƙarni Na 21

     Daga

     Dr. Adamu Rabi’u Bakura

    Department of Languages and Cultures

    Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria

    Email: arbakura62@gmail.com

    Phone: 08064893336

     

    Da

     

    Abu-Ubaida SANI

    Department of Languages and Cultures,

    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

    Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng

    official@amsoshi.com | ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334

    Citation: Bakura, A. R., & Sani, A.-U. (2024, May 3–6). Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a sikelin manazartan ƙarni na 21. Paper presented at the International Conference on the Life and Songs of Alhaji Sa’idu Faru, Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria.

    Tsakure

    Masana suna la’akari da waɗansu alƙaluma yayin ayyana makaɗan Hausa a ƙarƙashin wani rukuni na musamman daga cikin tarin rukunonin makaɗa da ake da su a farfajiyar adabi da al’adun Hausawa. Waƙoƙin fada na daga cikin shahararrun rukunonin waƙoƙin baka. Wani abin lura shi ne, akan samu makaɗan da ke ƙarƙashin wannan rukuni da suke sauya sheƙa ko su kasance jemagu sakamakon tasirin zamani ko waɗansu dalilai masu alaƙa da tattalin arziki ko waninsa.

    Binciken nan yana da manufar bitar rayuwa da waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru domin ganin ko ya sauya sheƙa ko kuma ya kasance makaɗin sarauta kaifi ɗaya na tsawon zamanin kiɗansa? An yi amfani da dabarun ƙalailaice waƙoƙin makaɗin da kuma yin hira da masana a wannan fanni a matsayin hanyoyin tattara bayanai.

    Sakamakon binciken ya tabbatar da cewa, Sa’idu Faru ya tabbata makaɗin sarauta na yankan shakku, domin kuwa dukkannin waƙoƙinsa ba su fita daga da’irar sarauta da masarauta ba. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da nuna dacewar tattarawa da kundace waƙoƙin wannan shahararren makaɗi domin gudun salwantar su.

    Fitilun Kalmomi: Kiɗa, Waƙa, Waƙoƙin Fada, Waƙoƙin Sarauta, Makaɗan Fada, Makaɗan Sarauta

    1.0 Gabatarwa

    Allah ya arzurta mawaƙan Hausa da ɗimbin hikima da basira tare da fasahar sarrafa harshen Hausa wajen ƙaga waƙoƙi. Wannan ne ya sa sukan rera waƙoƙin da suka danganci fannonin rayuwar ɗan’adam daban-daban.

    A sakamakon haka ne masana da manazarta adabin Hausa suka karkasa makaɗan zuwa azuzuwa ta la’akari da rukunonin al’ummar da makaɗan ke yi wa kiɗa da waƙa. Masana kamar Bello (1982) da Yahaya (1983/85) da Mashi (1986) da Gusau (1996) sun raba mawaƙan zuwa rukuni-rukuni gwargwadon fahimtarsu, ta la’akari da abubuwa kamar haka:

    • Muhallin waƙoƙinsu
    • Kayan kiɗansu
    • Jigogin waƙoƙinsu

    Hasali ma kowane rukunin da makaɗan ke yi wa kiɗa da waƙa akwai kayan kiɗan da suka keɓanta da su wajen sarrafawa a yayin da suke aiwatar da sana’arsu ta waƙa. Bello (1982) da Ibrahim (1985) da Gusau (1996) sun raba mawaƙan Hausa ta la’akari da muhallin waƙoƙinsu, kamar haka:

    • Mawaƙan sarauta/Fada
    • Mawaƙan jama’a
    • Mawaƙan Sana’a
    • Mawaƙan ban dariya
    • Mawaƙan sha’awa

    Wannan aiki ya karkata kan binciko gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a cikin makaɗan fada. Makaɗan fada sun shahara wajen luguden kalmomin Hausa ta fuskar salo, raha, ƙaƙale, yabo, zambo, habaici, shaguɓe, zuga da adana tarihi, da sauransu. Sukan sauya falsafar da suka gada kaka da kakanni sakamakon sauyawar zamani da ire-iren sauye-sauyen da ke wanzuwa a tsarin sarauta da raguwar ƙarfin ikon sarakunan ƙasar Hausa.

    Wannan ya sa wasu makaɗan suka zama bigi-sa-bigi-taiki domin neman tara abin duniya. Fahimtar haka ne ya sa wannan muƙalar ta yi azamar ɗora waƙoƙin Ɗan’umma Uban Kiɗi bisa sikelin bin diddigin gano ko makaɗin ya sauya sheƙa sakamakon sauyawar zamani, ko kuwa yana kamilin makaɗan sarauta har ya karɓa kiran Ubangijinsa?

    2.0 Bitar Muhimman Batutuwa

    2.1 Kiɗa

    Kiɗa Bahaushiyar kalma ce wadda Hausawa suke kiran ta kiɗaa. Kalmar tana cikin jerin kalmomi na suna jisin maza. Jam’in kalmar kuwa shi ne kaɗe-kaɗe. A wani karin harshen kuwa sukan ce kiɗe-kiɗe. Kalmar tana ƙunshe da ma’ana kamar haka:

    • Buga ganga ko kalangu da abin bugawa.
    • Bugun ƙwarya ko goge ko garaya da hannu ko da makiɗi ko da wani abu, kamar yadda Kano, (2006 p. 243) ya bayyana.

    Garba, (1990 p. 89) cewa ya yi kiɗa na nufin: “Yin amfani da abubuwa don ta da amo iri daban-daban.” A wata ma’anar kuwa cewa ya yi kiɗa na nufin, “Fasahar tsara amo na muryar mutum ko daga abubuwa ko duka a haɗe.” Yayin da aka dubi waɗannan ma’anonin za a iya cewa, kiɗa yana nufin buga wani abu a kan wani domin samar da wani amon sauti da ka iya jan hakalin mai saurare.

    2.2 Waƙa

    Kalmar waƙa tana cikin jerin kalmomin suna jinsi mace. Jam’inta kuwa waƙoƙi ko waƙe-waƙe. Kalmar tana ƙunshe da ma’anar: “Magana wadda akan rera da baki, aka tsara bisa wani zubi na musamman” kamar yadda Garba (1990 p. 152) ya nuna. Shi kuwa Kano, (2006 p. 466) ya bayyana ta da ma’anar, “Tsararriyar magana da ake rerawa a kan kari ko rauji.”

    Waƙa a bisa ma’anarta, tana nufin furta abin da ke cikin ƙwaƙwalwa. Sau da yawa akan ji Bahaushe na cewa:

    1. Na waƙa yi masa dukan fitar arziki.
    2. Na sha waƙa zuwa aikin Hajji.
    3. Na waƙa masa farashin kayan.
    4. To, Allah ya sa ba waƙa ba ce.

    A wata ma’anar kuwa, waƙa takan kasance wata murya ko zaƙin murya mai shiga zuciya da faranta rayuwa. Misali , Bahaushe kan ce:

    1. Ai na zaci waƙa ce.
    2. Ya matse sauti kamar mai waƙ
    3. Zaƙin murya sai ka ce zabiya.

    Ta wata fuskar kuwa, waƙa takan kasance wata magana wadda akan rera da baki, wadda kuma aka tsara bisa wani zubi na musamman.

    Dangane da ma’anar waƙa ta ɓangaren adabi kuwa, za a ga masana adabin baka da dama sun ba da ma’anarta a wurare mabambanta gwarwadon fahimtarsu. Daga cikin masanan, Gusau (1984 p. 3) cewa ya yi:

    Waƙar baka ita ce wani saƙo cikin zance na azanci da ake rerawa ba faɗa kurum ba, ta cikin hikima da fasaha da zaɓaɓɓun kalmomi, waɗanda suka dace da saƙon. Kuma tana zuwa gunduwa-gunduwa, dangane da sautin murya da kiɗa da amshi da gaɗa da taɓi ko zabiyanu mai saka zuciya jin daɗi.”

    Shi kuwa Umar (1987 p. 7) ya bayyana ma’anar da cewa:

    Waƙa ita ce nau’in sarrafaffen harshe da ake gabatarwa da sigar gunduwoyin zantuttukan da ake kira baitoci ko ɗiyoyi, waɗanda ake ginawa a kan kari ƙayyadadde, kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman.

    Yayin da aka nazarci waɗannan ma’anoni da masana suka bayyana, za a ga cewa, suna ƙoƙarin nuna cewa, waƙa na nufin tsararriyar magana da ke ƙunshe da fasaha da hikimar sarrafa harshe da ake rerawa gunduwa-gunduwa, cikin wani amo na musamman.

    2.3 Waƙoƙi Fada

    Su ne wasu manazarta kan kira da waƙoƙin sarauta. Waƙoƙi ne da ake yi wa duk wani da ya jiɓinci jinin sarauta ko aka ba shi wani matsayi na musamman a majalisar sarki, inda ake taro domin gudanar da mulkin al’umma cikin tsari irin na gargajiya. Masu aiwatar da waɗannan waƙoƙin su ake yi wa laƙabi da makaɗan sarauta ko mawaƙan sarauta.

    Ta fuskar ma’ana kuwa, Gusau (1988 p. 165) cewa ya yi:

    Waƙoƙin baka na fada su ne waɗanda makaɗa na musamman ke gudanarwa ga sarakunan gargajiya da iyayen ƙasa da hakimai da dagatai da masu unguwanni da ‘ya’yan sarakuna da fadawa da masu riƙe da da muƙaman sarauta da sauran ƙungiyoyin da suka jiɓinci sarauta.

    Waƙar fada na zuwa ne a rere cikin sautin murya da daidaita shi, wanda ya sa take zuwa gutsure-gutsure (gunduwa-gunduwa) tare da maimaita gindinta a tsakaninsu. Kowane gutsure kammalalle ne ga kansa, amma wani zubin ma’anarsa takan cika ta tumbatsa har ta tsallaka ga gutsuren da ke bi masa. Gutsuren nan ne ake kira ɗan waƙa, jam’insa kuwa, ɗiyan waƙa.

    Ana iya cewa, waƙar fada shiryayyen zance ne mai zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa da ake yi wa wanda ya shafi sarauta domin a yabe shi, ko zuga shi ko kambama shi tare da fito da shi fili kowa ya san shi. Takan ƙunshi nakasa (aibanta) abokan hamayyar wanda ake yi wa waƙar ta hanyar yi musu zambo da habaici da shaguɓe da nuna hushi da tsoratarwa da firgitarwa da sauransu.

    2.3.1 Wanzuwar Waƙar Fada

    Ana kyautata zaton an soma waƙa ne a farfajiyar doron duniya a daidai lokacin aka ƙirƙiro farauta da samuwar addinin gargajiya. Gusau (1988 p. 167) ya nuna cewa, waƙa ta ƙara bunƙasa da haɓaka sanadiyyar yaƙe-yaƙe da bayyanar sana’o’i da wasannin motsa jiki da wasu lamurran da suka jiɓimci al’adun gargajiya. Masanin ya nuna cewa, a farfajiyar ƙasar Hausa farauta ta kasance daɗaɗɗiyar sana’a da aka fara aiwatarwa. Hasalima an sami waƙoƙin da suka dangance ta.

    Ana cikin irin wannan yanayi ne, sai sarautun gargajiya suka bayyana sakamakon taruwar al’ummar Hausa tsangaya-tsangaya. Wannan ya faru ne tun daga lokacin da suka kafa mazaunai don samar da wurin zama na dindindin, domin samun damar gudanar da sana’ar noma da kiwo da wasu abubuwan inganta rayuwa tare da kare kai daga farmakin namun daji.

    Ana kyautata zaton daga lokacin ne aka soma yi wa sarki waƙoƙi gajeru. Bayan bunƙasar waɗannan tsangayoyin mazaunin farko zuwa ƙauyuka da garuruwa da birane, sai yaƙe-yaƙe suka haddasu a tsakaninsu, domin ƙoƙarin tabbatar da mulkin danniya. Ana cikin irin wannan yanayi ne yaƙe-yaƙen ƙabilanci suka wakana a tsakanin ƙabilu da Hausawa domin son mulki da iko da kuma shugabanci na sarakuna da ke mulkin su, ko kuma don neman faɗaɗa ƙasa ta mulki domin ta zama babbar daula.

    Sakamakon irin waɗannan yaƙe-yaƙe da suka auku ne ya wanzar da samuwar wasu masu rauni da ke da kishin al’ummarsu; waɗanda ba su da ƙarfin karawa da dakarun yaƙi. Su ne suka dinga amfani da hikimarsu da basirarsu da zalaƙarsu wajen gudanar da kirari na yabon sarakunansu tare da zuga jarumansu domin ƙara musu ƙwarin guiwar fatattakar abokan adawa.

    A wani ƙaulin kuma, Gusau (1988 p. 167) ya nuna cewa, makaɗan da suka rinƙa yi wa sarakunansu guntayen waƙoƙi tun kafin a fara yaƙe-yaƙe ne suka cigaba da koɗa sarakunansu a fagen daga tun kafin a fita yaƙi ko bayan an dawo.

    A wani ƙaulin kuwa an bayyana cewa, a lokacin da ake kaɗa wasu kayan kiɗan yaƙi kamar: Tambari da kurya, sai Ɗanma’abba ya rinƙa aiwatar da kirari tare da zuga sarkinsu. Daga irin haka ne ‘Yanma’abban suka samu sukunin ɗinka ganguna da ƙudurin in an tafi yaƙi ko bayan an dawo su dinga cicciɓa sarki da jama’arsa.

    Hasali ma tare da su ake zuwa yaƙin. Ko an samu ɓacin rana, ba za a kashe su ba, sai dai su bi sarkin da ya samu nasara su dinga yi masa waƙoƙi suna zuga shi kan bajintarsa (Gusau, 1988 p. 168). A sakamakon haka ne wasu ƙasashe suka samu damar mallakar tamburran abokan hamayyarsu. Misali, kamar yadda ake hasashen cewa irin haka ne ya haifar da Gumawa suka mallaki tamburran Zamfarawan Anka.

    A tsakanin shekarar 1910 zuwa 1915 a daidai lokacin mulkin Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare aka daina kiɗan yaƙi, kamar yadda Gusau (1988 p. 170) ya nuna. Daga nan sai makaɗan suka koma ga aiwatar da waƙoƙin ga sarakuna suna yabon su ta hanyar bayyana musu irin bajintar da kakanninsu suka nuna a fagen fama.

    Wannan salon kiɗan shi ne ake yi wa laƙabi da kiɗan fada ko kuma a ce kiɗan sarauta ko na iko ko mulki. Hasali ma shi ne ya maye gurbin kiɗan yaƙi. Daga lokacin ne sarki kan gayyato mawaƙi ya yi masa waƙa a inda zai yabe shi, ya kuma zuga shi, kana kuma ya kushe abokin gabarsa. Yayin da mawaƙi ya gama rera waƙoƙinsa, sai sarkin ya yi masa gagarumar kyauta ta ƙasaita.

    A sakamakon wannan, mawakin yakan ji yana ƙaunar sarkin. Soyayyarsa takan sa ba wanda yake yi wa waƙa sai sarkin. Sakamakon haka ne sarakuna suka samu damar mallakar makaɗa da mawaƙa a fadojinsu, har suka zama makaɗan fada, kamar yadda Gusau (1988 p. 170) ya bayyana.

    2.3.2 Musabbabin Yin Waƙoƙin Fada

    Akwai abubuwa da dama da suka sabbaba ƙaga kiɗan fada. Ire-iren waɗannan abubuwan sun ƙunshi, nuna buwaya (gagara) da rinjaye (fifiko) da dawwama cikin samun nasara da galaba a kan maƙiya da soyayya da kyauta da sauransu.

    Sakamakon irin waɗannan abubuwa da mazaje suka keɓanta da su ne, ke sa a shirya musu waƙoƙi domin ƙara zuga su tare da fito da martabarsu da kwarjininsu a idon jama’a. Misali, ga abin da Malamin Kiɗa Sa’idu Faru ke bayyana wa Sarkin Kiyawa na Ƙaura Alhaji Abubakar, a inda yake cewa:

    Ni kiɗin yaƙi nay yi ma Abu na Isau,

    Ba ni son kana zaunawa banza,

    Ka ɗauki takobi da bindigogi da bakukuwa.

    Ba mu sansani sai bakin Tsabre,

    Kano da Katsina hak Kwantagora,

    Duk riƙon Namoda na, shi na ac can,

    Garba ka amshe riƙon duk da Umaru,

    Umaru yab bam ma.

    (Sa’idu Faru: Gwabron giwa na Shamaki, Baba Ubangandu)

    2.3.3 Makaɗan Fada/Sarauta

    Su ne makaɗan da ke yi wa sarakuna waƙa kawai. Ba kasafai suke yi wa sauran jama’a waƙa ba. Sun fi mayar da hankalinsu a kan uwayen gidansu. Sarakuna su ne iyayen gijinsu. A sakamakon haka, ba sa yi wa kowa waƙa sai da izinin sarkinsu. Wannan na faruwa musamman kasancewar sarakunan ne suke ɗaukar ɗawainiyarsu, kuma sun fi kowa ganin ɗaukaka da darajar sarakunansu. Makaɗa da dama da ke cikin rukunin farko na makaɗan sarauta suna da wannan falsafar a cikin zukatansu. Misali, Mu’azu Na’alalo cewa ya yi:

    Darajar kaza gashinta,

    Darajar makaɗi sarkinai,

    (Gital, 1984) a cikin Abba da Zulyadaini (2002)

    Haka shi ma Jankiɗi ya ce:

    Jumirin kwaram a kwana ana tafiya sai goga,

    Jaki bai kai nan ba,

    ‘Yan yara masu kurin waƙa ku bar wargi,

    Ma’ana ba ta zama ɗai ba.

    Ni ba ni kiɗin iska sai ga sarkina.

    Idan aka dubi waɗannan ɗiyan waƙa, mawaƙan fada suna nuni da cewa, yi wa sarakuna waƙa ya fi kome martaba, don haka suna kallon yi wa talaka waƙa kamar aikin banza ne. A ɓangaren sarakunan da ake yi wa waƙar kuwa, sukan ɗauki ɗawainiyarsu da ta iyalansu tun daga muhallinsu, har abin da za su ci da kuma suturarsu. Sa’idu Faru ma ya nuna yadda ubangidansa ke ɗauke da lalurarsa a cikin ɗiyan waƙoƙinsa. Misali, ga abin da yake cewa:

    Sarki zamaninka na ruhwa,

    Na ta da kaina,

    Kowag gane ni da Daudu,

    Ya san sarki garan gawurtacce.

    (Sa’idu Faru: Waƙar Abubakar Sarkin Kiyawan Ƙaura)

    A nan za a fahimci cewa, makaɗin na ishara ne da cewa shi makaɗin sarauta ne, don haka ne sarkinsa ke ɗauke da buƙatunsa.

    Haka kuma ya fito fili ya na bayyana wa al’umma cewa, shi ne kawai makaɗin sarauta da ya rage a wannan zamanin. Sauran makaɗa sun koma makaɗan jama’a sakamakon juyin zamani. Ga abin da yake cewa kamar haka:

    Sa’idu Faru ka waƙar iko,

    Komai kaj jiya ƙarya a kai,

    Sa’idu Faru ka waƙam mulki,

    Komai kaj jiya ƙarya a kai.

    (Sa’idu Faru: Turakin Kano Amadu)

    2.3.4 Rabe-Raben Makaɗan Sarauta

    A wannan rukuni na makaɗan sarauta (makaɗan fada) za a tarar cewa Gusau (1996) ya kasa su zuwa ɓangarori biyu. Kashi na ɗaya (1) da na biyu (2). Jerin makaɗan da suka faɗo ƙarƙashin kaso na farko su ne:

    1. Abdu Kurna
    2. Abubakar Akwara
    3. Alhaji Muhammadu Sarkin Taushin Katsina
    4. Aliyu Ɗandawo
    5. Buda Ɗantanoma
    6. Ibrahim Gurso
    7. Ibrahim Narambaɗa
    8. Idi Ɗangiwa Zuru
    9. Jibo Maituru
    10. Muhammadu Dodo Maitabshi
    11. Muhammadu Inyaga
    12. Salihu Jankiɗi

    Kashi na biyu kuwa ya ƙunshi makaɗan da suka haɗa da:

    1. Alhaji Ɗankurma Maru.
    2. Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun.
    3. Alhaji Sa’idu Faru
    4. Alhaji Sa’idu Maidaji Sabon-Birni
    5. Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo
    6. Muhammadu Ango Maitabshi
    7. Muhammadu Maidamma Sarkin Taushi
    8. Sarkin Taushi Muhammadu Ɗanbunguɗu
    9. Umaru Maisa’a Tubali

    2.3.5 Alaƙar Makaɗan Fada Da Sarauta

    Makaɗan fada na ɗaya daga cikin rukunin al’umma da sarakuna ke ɗauke da lalurorinsu na yau da kullun. Sarki yakan zama ubangidan makaɗi, shi yakan ɗauki lalurar cinsa da shansa, ya yi masa gida ya ba shi gona, ya kuma rinƙa yi msa sutura tare da iyalansa. Haka kuma yakan ba shi kuɗaɗen ɓatarwa.

    Sarki yakan amince wa makaɗinsa fiye da sauran fadawansa. Yakan zauna tare da shi su yi hira cikin sakin fuska sosai da zaman amana da taimakon juna. Shi kuma makaɗin zai dinga girmama sarkin da mutunta shi tare da yi masa ladabi da biyayya tamkar yadda al’ummar fada ke yi masa.

    A al’ada, makaɗin fada bai fita waje ya yi wa wani sarki ko jinin sarauta waƙa, sai da izinin ubangidansa. Yayin da ya je waƙa gun wani, zai nuna wa sarkinsa duk nau’in abin alherin da aka yi masa. Wani lokaci, yana iya bayyana masa a cikin sigar waƙa.

    3.1 Siffofin Makaɗan Sarauta Da Matsayin Sa’idu Faru

    Makaɗan sarauta suna da waɗansu siffofi da suka fi alaƙantuwa da su. Sun haɗa da:

    1. Makaɗin sarauta shi ne wanda kan samu wani basarake ya zauna a wajensa ya kasance ubangidansa da zai rinƙa yi masa yammaci (kiɗa daren Juma’a) ko daren salla. Sukan bi sarki a duk lokacin da zai fita rangadi (kewayar gundumar da ke ƙarƙashin mulkinsa).
    2. Sukan nemi izinin ubangidansu kafin su tafi yawon kiɗa gidan wani sarki ko alƙali ko bafade ko wani mai arziki da ke ɗasawa da ubangidansu.
    3. Akasarinsu sun gadi kiɗa da waƙa irin na sarauta idan aka cire Aliyu Ɗandawo Shuni, wanda ya kasance ɗan wani shahararren malami da aka yi a can Shuni ɗin da ake kira da suna Modibbo Aliyu, Kamar yadda Gusau (1984) ya nuna.
    4. Sun fi kowane Bahaushe sanya tufafin gargajiya, wato sanya manyan riguna da wandunan buje da taguwoyi masu manyan hannaye. Sukan kuma naɗa rawani. Suna riƙe wannan al’ada ce saboda irin wannan suturar sarakuna kan ba su. Abin la’akari shi ne, sarakuna ba sa rabuwa da sanya manyan suturu komi gumi ko zafi. Hasali ma sarki ba zai fito gidansa ba rawani a kansa ba. shi ya sa makaɗan sarauta suka riƙe wannan ɗabi’a domin kare martaba da alfarmar sarauta. Shi ya bambanta su da sauran makaɗa da mawaƙan ƙasar Hausa.

    Duban ire-iren waɗannan siffofi da aka ambata a sama da la’akari da irin sigar yanayin shigar Alhaji Sa’idu Faru za ka tabbatar shi cikakken makaɗin sarauta ne. A lokacin rayuwarsa ba ka raba shi da shiga irin ta iyayen gidansa.

    3.2 Kayan Kiɗan Makaɗan Fada Da Gurbin Sa’idu Faru

    Ta sigar kayan kiɗa kuwa, makaɗan sarauta sun sha bamban da sauran makaɗa da mawaƙan baka na ƙasar Hausa. Haka kuma sun kasu kashi-kashi dangane da kayan kiɗan da suke amfani da su, da nau’o’in waƙoƙin da kuma uwa-uba irin garuruwan da suke zaune da kuma inda suka ƙaurato. Ta fannin kayan kiɗa, za a iya kasa su zuwa kashi uku kamar haka:

    1. Masu kaɗe-kaɗe
    2. Masu bushe-bushe
    3. Bambaɗawa (masu kirari) (Ibrahim, 1983 p. 2).

    Ta wannan haujin kuwa, Alhaji Saidu Faru yana cikin sahun makaɗan fada da ke amfani da kayan kiɗa dangin na sarauta. Su ma kayan kiɗan sarauta sun karkasu kamar haka:

    (i) Tafshi

    (ii) Kotso[1]

    (iii) Jauje

    (iv) Tambari

    (v) Banga

    Waɗannan kayan kiɗa akan yi amfani da su wajen tsima sarki ta hanyar kambama shi da magabatansa.

    Kashi na biyu kuwa sun ƙunshi abubuwan busawa ne da suka danganci:

    (i) Algaita

    (ii) Kakaki

    (iii) Ƙaho

    (iv) Farai

    Waɗannan kayan busa suna ba wa talakawa labari ne cewa, sarauta tana nan daram ta kafu. Suna kuma jawo hankulan masoya sarki da cewa su zo su ji abin da za a faɗa game da masoyinsu.

    3.3 Sauya Sheƙar Makaɗan Sarauta Zuwa Na Jama’a

    Sauye-sauyen ubangida ga makaɗan fada yakan faru ne a zamanin da sarakuna ke da ƙarfin ikon gudanar da al’amuran tafiyar da ragamar mulkin al’ummominsu, kafin mulkin Jamhuriya ta farko. A waɗansu lokuta makaɗa na sauya ubangidansu, musamman saboda dalilai kamar haka:

    1. Yayin da ubangida (sarki) ya karɓa kiran Mahaliccinsa.
    2. Yayin da aka fitar da shi daga sarautarsa.
    3. Yayin da ya daina yi wa makaɗinsa alheri.

    4.1 Nau’o’in Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Sa’idu Faru ya yi wa sarakuna da jinin sarauta waƙoƙi da dama waɗanda shi ma kansa bai san adadinsu ba saboda yawansu. Hasali ma, dukkan waƙoƙin shi ne ya ƙaga su da kansa. Shi ba kamar sauran makaɗan sarauta ba ne da ke maimaita waƙoƙin da mahaifansu suka aiwatar ba. A ƙasa an kawo waɗansu sarakuna da hakimai da uwayen ƙasa da ya yi wa waƙa:

    1. Sarkin Yamman Faru Ibrahim
    2. Sarkin Yaƙin Banga Sule
    3. Sarkin Kiyawan Ƙaura Abubakar Garba
    4. Sarkin Gabas Na Mafara Muhammadu
    5. Sarkin Musulmi Abubakar III
    6. Sarkin Yawuri Alhaji Muhammadu Tukur
    7. Sarkin Sudan Na Wurno Alhaji Shehu Malami
    8. Sarkin Kano Ado Bayero
    9. Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
    10. Sarkin Gabas Shehu Uban Ƙasar Talata Mafara
    11. Turakin Kano Amadu
    12. Muhammadu Muhammadu Maidabo Tudun Falale
    13. Alhaji Muhammadu Mode, Ɗan Alin Birnin Magaji
    14. Sarkin Zamfaran Zurmi, Suleiman Muhammadu Sambo
    15. Sarkin Zazzau Alhaji Dr. Shehu Idris, da sauransu

    Ta fuskar waƙoƙin da ya yi wa ubangidansa kuwa, ya yi wa Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo waƙoƙi da dama. Abin da hannaye suka samu nasarar dafawa su ne:

    1. Farin cikin Musulmi duk kai muka taƙama yau,

    Muhammadun Muhammadu ɗan Abdu mai darajja.

     

    1. Sai na zo in yi mai kiɗi in ƙaro ilmi,

    Mamman Bajinin Magaji mai takakkay yaƙi.

     

    1. Farin cikin Musulmin Duniya, mai martaba na Abubakar,

    Ci fansa Alhaji Macciɗo.

     

    1. Kana shire Baban Yan Ruwa,

    Na Bello Jikan Ɗanfodiyo.

     

    1. Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari,

    Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.

     

    1. Shugaban sahun gabas riƙa ƙwarai,

    Muhammadun Amadu Uban Zagi.

     

    1. Hattara Bajinin gidan Bello Jikan Hassan maganin wargi.

     

    1. Ya yi Sarki daidai wada mai yanzu yar riƙa,

    Alhaji Macciɗo jikan Mamman mai dubun bara.

    1. Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.

     

    1. Hattara mai martaba Bello ɗan Bubakar,

    Sarkin Kudun Hausa.[2]

    Yayin da aka kwatanta Alhaji Musa Ɗankwairo a matsayinsa na mawaƙin sarauta kuma Sarkin kiɗan ‘Yandoton Tsahe Alhaji Aliyu, da Alhaji Sa’idu Faru, za a iya cewa, Ɗanƙwairo ya canza sheƙa sakamakon juyin zamani.

    Hasali ma ana hasashen cewa, tun waƙar Shirya Kayan Faɗa ba wata waƙa da ya sake yi wa ubangidansa. A madadin haka, sai ya karkata ga yin waƙoƙin jama’a da suka ƙunshi ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da malamai da tajirai. Wannan ne ya sa mafi yawan waƙoƙinsa suka zama na gama-gari. Misalan waƙoƙin sun haɗa da ta:

    1. Alhaji Shehu Kangiwa
    2. Kanal Umaru Muhammad
    3. Alhaji Ahmadu Aruwa
    4. Alhaji Kabiru Mado
    5. Alhaji Ali na Malan Bawa
    6. Alhaji Garba A.D. Kano
    7. Alhaji Garba Nadama
    8. Alhaji Ahmad Muhammad
    9. Alhaji Bala Maiyafe
    10. Malan Lawal Ƙalarawi
    11. Alhaji Bala Salisu
    12. Alhaji Sikofiyo
    13. Alhaji Bature Dogon Tela
    14. Alhaji Ibrahim Maganinta
    15. Waƙoƙin Faɗakarwa
    16. Waƙoƙin Jam’iyyun Siyasa

    Ta la’akari da jerin waɗannan waƙoƙin, za su iya kawar da Ɗanƙwairo daga cikin sahun mawaƙan sarauta. Ta fuskar Sa’idu Faru kuwa, babu waƙar da ya aiwatar da za ta iya fitar da shi daga cikin sahun makaɗan sarauta.

    4.2 Turakun Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Kasancewar Sa’idu makaɗin sarauta ne na asali, bai sake juyin zamani da kwaɗayin tara abin duniya ya ruɗe shi ba. Shi ya sa ya tsaya wajen gina waƙoƙinsa a kan turakun da iyaye da kakanni suka assasa tushensu tun farkon fara kaɗe-kaɗen fada (sarauta).

    Binciken masana kamar Gusau (1996 p. 121) ya tabbatar da cewa, Makaɗa Sa’idu faru ba ya yi wa kowa waƙa sai sarki da wanda ya kasance jinin sarauta. Waƙar farko da ya fara aiwatarwa ita ce ta Sarkin Yamman Faru Ibrahim. Gindin waƙar shi ne:

    Bi da maza ɗan Joɗi na Iro,

    Iro magajin Shehu da Bello.

    Hasken hitila ba ɗai da wata ba,

    Tauraro haskenka subahin,

    Dawaya kora ɗimau na wakili,

    Uban sarkin zagi Bello na yari.

    Ruwa da kada ɗibgau na Magaji,

    Sai tsohon wawa ka shigar su.

    (Gusau, 1996 p. 119).

    Tun daga wannan waƙar sai ya ci gaba da yi wa sarakuna da ‘ya’yan sarakuna waƙoƙi. Yana cikin irin wannan yanayi ne, Allah cikin ikonsa da baiwarsa ya sada shi da Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar na III, wanda ya sarauci ƙasar Talata Mafara daga 1953 zuwa 1956, kamar yadda Talata Mafara (2007 p. 17) ya nuna. Ya fara yi wa Sarkin Kudu Macciɗo waƙoƙi a daidai lokacin da yake riƙe da muƙamin Ubanƙasar Talata Mafara. Ga gindin waƙar da ya fara yi masa, a inda yake cewa:

    Kana shirye baban ‘Yanruwa,

    Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

     

    Gardaye zo ka yi man iso,

    Faɗa mashi murna niz zaka,

    Ɗan Sardauna jikan Hassan.

     

    Babban ɗa ga Baura Sarkin Kudu,

    Na Alƙali baban zagi,

    Mai ja ma ya bari ɗan Adamu.

     

    Na Sarkin Gobir Amadu,

    Ci fansa ga wan Sarkin Ƙaya.

     

    Waƙag ga da nim maka Muhammadu,

    Na ji daɗin ta Mamman Sarkin Kudu,

    Tun dak Kabi hak Kano ham Masar,

    Hab birnin Legas hab Bici,

    Kowa ya ji waƙar Sarkin Kudu.

    (Gusau, 1996 p. 120).

    Sa’idu Faru fasihin mawaƙin sarauta ne da ya naƙalci harshen Hausa ga baiwar da Allah ya yi masa ta fasahar ƙulla waƙa yadda za ta yi daɗi ta kuma yi armashi da ma’ana. Sakamakon haka ne ya kira kansa da Malamin waƙa, a inda yake cewa:

    Sa’idu Malamin waƙa,

    Mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba×2

    Ban wuce gonata da irina ba,

    Inda Sarkin Kudu nat tsaya.

    Gindin Waƙa: Farin cikin Musulmin duniya.

    (Faru: Waƙar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo)

    Sa’idu Faru bai taɓa yi wa talakka waƙa ba, komai tarin dukiyarsa. Hasali ma shi da kansa ya yi nuni da haka, a inda yake cewa:

    Ban zo gidan Ɗanbita niy yi roƙo ba,

    Ko ya raba lafiya ba ruwana.

    A wannan ɗiyan waƙar ya fito ƙarara ya tabbatar wa al’umma cewa shi bai taɓa yi wa talaka waƙa ba. Ya jaddada cewa ba zai yi haka ba ko da mutumin yana samar da kowane irin jin daɗi da ingancin jiki da kawar da ciwo daga jikin ɗan’adam. Shi bai damu da duk wannan ba, ballantana ya yi masa kiɗa da waƙa.

    Kalmar ɗanbita a nan tana nufin leburan da ke aikin gyaran hanyar mota. A daidai wancan lokacin, sarakuna ne ke bayar da waɗanda za su yi aikin hanya. Sukan zaɓo waɗanda suka dace da aikin hanyar daga cikin talakawansu. A daidai wancan lokacin akan ji tsofaffi na maganar aikin diga da ke nuni da aikin hanya. A sakamakon irin wannan aikin talakawa da dama sun tara abin duniya.

    Malamin waƙa ɗin ya bayyana dalilan da suka sa ba ya yi wa talaka waƙa da kiɗa kamar yadda Gusau (1996 p. 121) ya ruwaito su cewar:

    1. Ba wata hanya da zai bi ya ɓata wa talaka rai. A lokacin da talaka ya wulaƙanta makaɗi, to sai dai makaɗin ya yi na mai bara (haƙuri).
    2. Yayin da Sarki ko jinin sarauta ya yi wa makaɗi abin da ya ɓata masa rai, sai ya rama a cikin waƙa ta hanyar yi masa zambo ko habaici. Ba wani sarki ko jinin sarautar da yake son makaɗi ya yi masa su.

    Za a iya samun wasu rukunin al’umma su ce, idan haka ne wane dalili ne ya sa Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Alhaji Shehu Kangiwa waƙa? Amsa a nan ita ce, an yi waƙar ne a shekarar 1976 bayan an naɗa shi Turakin Kangiwa. Sarauta ce da Masarautar Argungu ta ba shi, a ƙarƙashin Shugabancin Maimartaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Muhammadu Mera.

    Ya zama ɗaya daga cikin jigajigan masarautar. Don haka, an yi masa waƙar ne a matsayinsa na ɗaya daga cikin masu riƙe da sarautun gargajiya a Msarautar Argungu. Idan aka yi la’akari da ma’anar makaɗan sarauta da lokacin da aka aiwatar da waƙar, za a iya tabbatar da cewa Makaɗa Sa’idu Faru bai taɓa yi wa talaka waƙa ba. Shi makaɗin sarauta ne tsantsa.

    4.3 Ƙananan Turakun Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    4.3.1 Yabo

    Makaɗa Sa’idu Faru a cikin waƙoƙinsa yakan yabi ubangidansa ta haujin ambaton asalinsa. Yakan kuma danganta shi da asalinsa ta hanyar bayyana cewa ya gaji gidansu. Ta haka ne ya yabi Sarkin Kudu Macciɗo da irin wannan sigar a inda yake cewa:

    Allah ya ba ka albarkar nan ta Alu Babba,

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun yi roƙon Allah,

    Allah shi ba ka albarkar nan ta Shehu, Amin.

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun yi roƙo Allah.

    Allah shi ba ka albarkar nan ta Bello, Amin.

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun yi roƙon Allah.

    Allah ya ba ka albarkar nan ta Bubakar na farko.

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun roƙon Allah.

    Allah shi ba ka albarkar Bubakar na biyu,

    Ka gama lafiya da imani mun yi roƙon Allah.

    Allah ya ba ka albarkar nan ta Aliyu Babba,

    Ka gama da kyau da imani mun yi roƙon Allah.

    Allah ya ba ka albarkar nan ta Alu ƙarami,

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun yi roƙon Allah.

    Allah shi ba ka albarkar Abdullahi,

    Ka gama da lafiya da imani mun yi roƙon Allah.

    Allah shi ba ka albarkar nan ta Hassan Dattijo.

    Ka kammale, ka ɗibo jama’arka.

    Duk ka shirya mu gaban Ma’aikin Allah,

    Mu yi farin ciki,

    Mu ji daɗin da yaf fi daɗi daɗi na Annabi.

    Mu ji ƙamshin da yaf fi ƙamshi, ƙamshi na Bubakar,

    Allah shi sa ka samun martabar kakanka.

    Yayin da aka dubi waɗannan ɗiyan waƙar, za a ga cewa, Sa’idu Faru na yi wa ubangidansa Sarkin Kudu Macciɗo fatan Allah ya ba shi albarkar waɗannan kakanni nasa ya kasance tamkarsu tare da samun martaba irin tasu.

    Ba nan kawai ya tsaya ba. Har ma ya yabi Sarkin Kudu Macciɗo ta haujin iya gudanar da mulki, a inda yake cewa:

    Shugaban duniya Alhaji Bello Sarkin Kudu,

    Jan damishi Shehu Sarkin Gabas,

    Baban su Alƙali.

    Gadangadan Shehu Sarkin duniya,

    Ba mai riƙo na ba.

    Ai! Ina ba magana ba ce yanzu gidan Bani,

    Ba mai kamar Macciɗon Hausa.

    Girmanka ya kai muƙaminka ya kai,

    Riƙon duniya wada Abubakar yak kai,

    (Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kudu Macciɗo).

    A nan mawaƙin ya bayyana cewa, Macciɗo zai iya gudanar da mulkin wannan duniya sakamakon ƙwarewarsa a fagen mulki.

    Ta fuskar addini ma, ya yabi ubangidansa a inda yake cewa:

    Gindin Waƙa: Bajinin gidan Bello Mamman na Yari,

    Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.

    Jagora: Tsari gaskiya Bello kai Shefu yac ce,

    ‘Yan Amshi: Bari masu son dus su maishe ka yaro,

    Duk kyauta da ilmi da neman dalili,

    Da gode ma Allah da istingafari,

    Da su Bello ɓello ɗan Shehu yat tcarma kowa,

    Ka kai kamab Bello,

    Ka gadi Moyi,

    Saura ka kai inda mai Hausa yak kai.

    Yayin da aka dubi ɗiyan da suka gabata, za a ga yadda wannan turken ya ƙara tabbatar mana da kasancewar mawaƙin a gurbin makaɗin sarauta. Makaɗan fada ne suka yi fice wurin yabon uwayen gidansu ta fuskar addini. Hakan na faruwa ne kasancewar sarakunan ƙasar Hausa su ne shugabannin addinin Musulunci tun kafin jahadin Shehu. Jagorancin nasu ya ƙara bunƙasa ne bayan tabbatuwar jahadi. Da irin wannan yabon ne sarakuna suke alfahari da makaɗansu.

    A nan ya bayyana wasu siffofin da suka keɓanta ga sarakunan ƙasar Hausa, wato, kasancewarsu masu alheri ga al’ummarsu, da zamansu malamai masana dangogin ilmomin zaman rayuwar duniya, domin su ne tushen samun kyakkyawar makoma gobe kiyama. Ya kuma ƙara kawo abu da ya kasance tamkar ruwa da gishiri a fagen sarrafa abinci da sauran lamurran rayuwar duniya.

    A nan ya yi masa hannunka mai sanda ne da ya lizimci nuna godiya a kan ni’imomin da Allah ya yi masa da dagewa ga yin tuba game da kuskuren da yake aikatawa, domin ta haka magabatansa suka tsere tsara. Idan ya nace a kan haka, zai kai ga samun matsayin da Sarkin Musulmi Abubakar Sadik yake a kansa.

    4.3.2 Zuga

    A wannan haujin kuwa, Sa’idu Faru yakan harzuƙa ko tunzura sarkin da yake yi wa waƙa, ta hanyar kambama darajarsa. Dubi yadda yake cewa a waƙarsa da ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo mai take:

    Gindin waƙa: Kana shire baban ‘yan ruwa.

    Jagora: Wani taro da an ka zo Ikko na bariyac can,

    Da Turawa da kuma ministoci had da kansiloli,

    Sarkin Musulmi da Amdu Bello sun zo wurin dus sun ziyar tai,

    Tafawa Ɓalewa ya sauka ga Lamiɗo Barno,

    Nan kudu Shehu Talba,

    Sarkin Bidda ya sauka ga Sarkin Ilori,

    Kulluhinsu sarakunan majalisa sun taru Ikko,

    Muhammadu Bello jikan Hassan kai sun ka zaɓa,

    Don ka hi su kyawon shirin kawo dalillai.

    Idan aka dubi kwayar turken wannan ɗan waƙar, za a ga ya fito ne ƙunshe da zuga Sarkin Kudu Macciɗo tare da fifita shi a kan waɗanda suka halarci taron. A ɗaya ɓangaren kuwa, ya taskace tarihin taron da aka aiwatar a Ikko tare da fito da maigidan nasa fili domin waɗanda ba su san shi ba su san shi. Irin wannan zugar ke ƙara tabbatar wa masu nazari gurbin da mawaƙin ya kasance.

    4.3.3 Habaici

    A cikin waƙoƙinsa akwai wuraren da yakan yi wa abokan adawar ubangidansa habaici ba tare da faɗa masa wata muguwar magana ba. Wannan kan iya kasancewa a cikin sigar jifa a kasuwa ko kuma ya san da wanda yake. Hasali ma makaɗan fada sun fi shahara ta fuskar amfani da habaici domin ƙasƙantar da abokin hamayyar sarkinsu ko muzanta shi a bainar jama’a a fakaice. Misali Sa’idu Faru yana cewa:

    Zaki mai zama ga hilin Allah ga shi ga hili,

    To wak ka san ya far mashi,

    Kafin maza su shirya Mamman na Ali ya shirya.

    Sun dai yi ɓaɓɓakar dutsi,

    Sun yi gyangyaɗar dutsi,

    ‘Yan hannuwansu sun gaza.

    Na Audu ko da ƙarfin Allah kana shiga gidan.

    Na ce mai kama da ƙot,

    Haka nij ji gun Badakkare.

    Dogon sarki yana da ban sha’awa,

    Ko da anka zo taro ya fi kyau da riguna,

    Duk wanda ag gajere a aje shi gun rabon dawo,

    Shi kai ma wanga dunƙule.

    Aw wurin da mata ciki,

    Har tuman gada yakai.

    (Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Tudun Falale).

    Da duban waɗannan ɗiyan waƙar za a fahimci Sa’idu Faru ya yi wa wasu ‘ya’yan sarki habaici ne a kaikaice, domin ya fahimci suna son su yi jayayya da ubangidansa.

    4.3.4 Zambo

    A nan ma akan samu inda yakan yi wa abokan hamayyar ubangidansa wata mugunyar magana. Misali a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo yana cewa:

    Gindin Waƙa: Gogarman gidan Moyi ci fansa niƙatau,

    Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.

    Jagora: Na ishe dale tai ƙawa ga jama’at ta ba ƙawa.

    ‘Yan Amshi: Ya murɗe su duy ya zuba dogon akwati,

    Rana ta kewayo ya naɗe ya kai Ilori,

    Dac can yas sawo man kishe,

    Ya sai tabarau.

    Yayin da aka nazarci wannan ɗiyar za a ga cewa, ya yi wa wani ɗan sarki zambo ne ta hanyar siffanta shi da wata tsuntsuwa da ake kira dale. Ita dale akan gan ta ne lokacin kaka. Ta kasance nau’i biyu. Akwai ja mai baƙi-baƙi ga kai, akwai kuma mai launin ɗorawa da baƙi-baƙi ga kai.

    Ita dalen ba a ganin ta sai lokacin da amfanin gona ya kai. Saboda halayyarta ne ya kamanta ɗan sarkin da ita, domin bai amfana wa kowa komai. Hasali ma idan wani abun alheri ya zo da ya kamata ya ba al’ummarsa, sai ya yi sama-da-faɗi da shi.

    4.3.5 Roƙo

    Akan sami wasu ɗiyan waƙoƙinsa da Sa’idu Faru yakan yi bara ko ya roƙi ubangidansa wani abu kai tsaye cikin hikima. Wannan wata azaliyya ce da ta keɓanta ga makaɗan sarauta, wato su bayyana abin da suke so daga ubangidansu kai tsaye ba tare da wani sakaye-sakaye ba. Shi ma Malamin Waƙa ya aiwatar da shigen wannan a inda yake cewa:

    Manyan ma’aikatan gwamnati,

    Manyan ma’aikatan N.A.,

    Almajirinku na aike,

    Don bisa gare ku Allah ya shiya mana asiri,

    Na roƙe ku in da hali,

    Ku zam shirya muna kujera mui Haji.

    Na yi mafarki nai sallah Makka nai ɗawafi,

    Kuma na rungumo hirami

    Da makaru a fuskoki,

    An ce mani Alhaji baitul fasali kake,

    Wanga mafarki ya Allah ya nufa a shirya shi,

    Ya zam haka.

    (Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kudu Macciɗo).

    A waɗannan ɗiyan waƙar, za a ga mawaƙin ya fito ƙarara ya nuna buƙatarsa tare da ayyana dalilinsa wanda ya kasance mafarkin da ya yi da yake son a taimaka masa ya zama gaskiya. Za a iya cewa, ma’aikatan gwamnati da ya roƙa ai suna cikin rukunin talakawa. Lamarin a wancan lokacin ba haka yake ba. A daidai lokacin ‘ya’yan ahalul falala ake damƙa wa aikin hukumar En-e da na gwamnati.

    4.3.6 Koɗa Kai

    Sa’idu Faru fasihin makaɗan fada ne, musamman idan aka yi la’akari da wuraren da yakan wasa kansa ta hanyar nuna ƙwarewarsa wajen tsara waƙa fiye da sauran makaɗan fada. Kuma yakan yi hakan ne a ciki ɗiyan waƙoƙin da ya ƙulla wa maigidansa Sarkin Kudu Macciɗo. Kasancewar sa makaɗin fada, ya shahara wajen amfani da wasu halaye da siffofi na ɗan’adam, ya ƙaga su ga wani abu wanda ba mutun ba, wato abin da ake kira mutuntarwa. A waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu macciɗo cewa ya yi:

    Nan na bi Gusau sai niw wuce,

    Kuma nab bi Kwatarkwashi niw wuce,

    Kuma nib bi ta Tcahe ina gudu,

    Can na kusa kai wa Zariya,

    Sannan Daudu ni kau sai nit tsaya.

    Sai Sarkin Zazzau nig ga nay,

    Ya ce man Muhamman Sarkin Kudu.

    Sai nis saki hanya nig gabas.

    Can na taɓa ‘yar tafiya kaɗan,

    Sai ni ishe suda na kiwo,

    Tana barka Sarkin Kudu,

    Allah rai ya daɗe Sarkin Kudu,

    Allah sabbinane na Ahmadu,

    Allah shi ƙara mai nasara.

    Na ce suda waƙa akai,

    Ta ce lalle waƙa ni kai,

    Waƙar Mamman Sarkin Kudu,

    Waƙar nan da Ɗan’umma ya yi mashi.

    Baicin uwar tsuntsaye nike,

    In da kamar mulkina nikai,

    Da nai mai wasiƙa ya yi min kiɗi,

    San nan ni kau sai niw wuce,

    Can na taɓa ‘yar tahiya kaɗan,

    Sai ni iske burtu na kiwo,

    Yana barka Sarkin Kudu,

    Rai ya daɗe Sarkin kudu,

    Allah sabbinane na Amadu,

    Allah shi ƙara mai nasara,

    Na ce burtu waƙa akai,

    Ya ce lalle waƙa nakai,

    Waƙar Mamman Sarkin Kudu,

    Waƙar nan da Ɗan’umma ya yi mashi.

    In na yi ta za ni wurin kiwo,

    In na so abinci sai na rufe.

    A cikin waɗannan ɗiyan waƙar, za a fahimci cewa mawaƙin ya yi amfani da adon harshe ne domin jaddada cewa ba ya yi wa kowa kiɗa da waƙa sai sarakuna da waɗanda ke da alaƙa da fada. Ga shi har da tsuntsaye sun san da haka. A ɗaya ɓangaren kuwa yana ɗaukaka waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu, wadda sakamakon yadda ta tsaru ta yi armashi, har tsuntsaye na maganar waƙar.

    Waƙar da ya yi wa Sarkin Sudan Na Wurno Alhaji Shehu Malami, ita ma wata hujja ce mai ƙarfi da ke tabbatar da kasancewarsa makaɗin sarauta ne na gani-da-faɗa wanda sauyin zamani bai juya shi ba. A wasu ɗiyan waƙar, yana cewa:

    Gindin Waƙa: Muzakkarin sarki ɗan Audu,

    Abin biya Shehu na Ali.

    Jagora: Ɗan talakka komai yac cika huska,

    Sa’idu ni ba ni kiɗa mai, .

    Jagora: Ɗan talakka komai ya aje ƙarhe,

    Sa’idu ni ba ni kiɗa mai.

    Da duban waɗannan ɗiyan waƙar za a ga ya fito fili yana jaddada cewa shi ba makaɗin talakawa ba ne, kuma komai bajintarsu da ƙwazo da kuma uwa-uba mallakar tamani (jikkunan kuɗaɗe) ba zai yi musu kiɗa da waƙa ba.

    4.4 Sarrafa Harshe a Cikin Waƙoƙin Saidu Faru

    4.4.1 Ƙarangiya ko Gagara-gwari

    Makaɗan fada, musamman waɗanda suka fito daga yankin da ke cikin farfajiyar tsohuwar Daular Zamfara, wato yakin da ke cikin Masarautar Bakura da Zurmi da abin da ya gangara Sabon Birnin Gobir har zuwa Dacaɗi da sauransu, sun fi takwarorinsu da ba ‘yan asalin yankin ba ne wajen mallakar harshen Hausa da iya sarrafa shi.

    Sa’idu Faru ya yi wa takwarorinsa da suka yi zamani ɗaya da shi fintinƙau ta fannin sarrafa sautukan Hausa masu bugun juna ta hanyar maimaita su a cikin ɗiyan waƙa domin nuna ƙwarewarsa a harshen da yake waƙa da shi (Hausa). Ana kyautata zaton cewa, sukan yi amfani da wannan hikimar ne domin kawar da wani lamarin da ke ci wa sarki tuwo a ƙwarya ta yadda zai koma ga hayyacinsa har ya yi ƙoƙarin fahimtar yadda aka yi luguden kalmomin da fahimtar ƙunshiyarsu. A duba misalin inda Sa’idu Faru ke cewa:

    Yaro in taƙamar salon magana kaka yi,

    Ce tsare tsara,

    Ta hi tsantsamin tsantsara,

    Ko tsattsame tsari,

    Tsaf ga tsamiya.

    Tunkuɗa tunku cikin tukar rukuɓu,

    Tukuɗin Tumba yai tuɓus,

    Tumba taho yau da ke da taɓo,

    Da taɓo da’yat tuɓus..

    (Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kiyawa na Ƙaura).

    Yayin da aka duba waɗannan ɗiyan waƙar za a tarar cewa Sa’idu Faru ya yi luguden sautukan Hausa kamar: tsa, tu, ɓa, ɓo, ɓu, ɗa, ɗi, da kuma ɗu, domin ya nuna ya naƙalci harshen Hausa da yake waƙa da shi. Mai nazari zai iya yin tambaya game da hujjar kawo wannan dalili?

    Hujja ita ce, tun lokacin da addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa, a fada ya soma zama da kafa harsashe. Wannan ne ya sa Sarakunan ƙasar Hausa suka kasance malamai musamman bayan jahadin Shehu. Hasali ma sun kakkafa makaratun ilimi (zaure) inda ake koyar da fannonin addini da luggar Larabci da ake fassarawa cikin harshen Hausa. Wannan ne ya sa har gobe tsofaffin kalmomi da hikimomin Hausa sun yanke cibiya a makarantun zaure, ta la’akari da irin hikimomin da ke ƙunshe cikin Muƙamatul Hariyri.

    4.4.2 Dangantakar Kalmomi

    Ta wannan haujin za a ga cewa makaɗan sarauta sun sha bamban da na jama’a ta fuskar zaɓen kalmomin da suka dace da ke da dangantaka da juna tare da tsara su wuri ɗaya cikin waƙarsu. Makaɗa Sa’idu Faru shi ne kan gaba a wannan fagen. Allah ya ba shi basira da hikimar zaɓen kalmomi masu dangantaka da juna. Yakan kuma tsara su a wuri ɗaya cikin waƙarsa. Misali, yana cewa:

    Ihihiya da kunkuru shawara guda sukai.

    Bushiya da beguwa shawara guda sukai.

    Kurciya da hasbiya shawara guda sukai.

    Bubukuwa da jinjimi shawara guda sukai.

    (Sa’idu Faru: Waƙar Muhammadun Muhammadu).

    Ta la’akarida waɗannan ɗiyan waƙar za a ga cewa ya kawo jerin halittu da suke da dangantaka da juna ta siffofin yanayin halittarsu.

    5.1 Sakamakon Bincike

    Daga abin da ya gabata dangane da wannan nazari, ya fayyace mana tabbatuwar Makaɗa Sa’idu Faru a matsayin sahihantaccen makaɗin sarauta na gwadi da ya tsayu wajen kiɗan sarauta da sarakuna a manyan gidaje sarauta har ma da ƙananansu da ke farfajiyar ƙasar Hausa. Sauye-sauye zamani da ɓullowar siyasar dimokuraɗiyya da kwaɗayin neman tara abin duniya bai sa ya bar turbar iyaye da kakanni ba.

    Irin wannan dogiya tasa, da ra’ayin mazan jiya sun bambanta shi da takwarorinsa da suka yi zamani tare har ya zamanto bai taɓa yi wa wani mutun waƙa ba idan ba jinin sarauta ba ne. Hasali ma ko jinin sarauta sai wanda ke riƙe da wani muƙamin sarautar gargajiya. Ya bambanta da mawaƙa irin su Alhaji Musa Ɗanƙwairo da suka kasance cikin zango guda da shi, wanda ya koma yana karɓar gayyatar jama’a domin rera musu waƙoƙi.

    Haka kuma, an fahimci sarakuna na rungume da makaɗansu ne sakamakon yadda suke tsara musu waƙoƙi, wanda ke zama sanadin daɗa ɗaukakuwarsu a idon duniya. Wannan kan auku ne, ta hanyar yadda makaɗan ke ambaton su da kyawawan halaye da ɗabi’u, waɗanda kan fito da sunayensu fili fiye da kima. Da haka ne sukan sami ƙwarin guiwar gudanar da harkokinsu na mulki ba tare da kasala ko tsoro ba, sakamakon zuga da kirarin da mawaƙansu ke yi musu, tare da tunatar da su tarihin iyaye da kakanninsu, musamman dangane da kyawawan halayensu kamar kyauta, haƙuri, ƙwazo da juriya.

    5.2 Kammalawa

    Waƙoƙin fada sun kasance wata maƙerar sarrafa harshe da luguden kalmomin fasaha. Haka kuma, suna mazaunin wata makaranta da ke koyarwa ko cusa waɗansu halayen ƙwarai da kuma ƙarfafa guiwa ga waɗanda ake yi wa waƙoƙin, da ma sauran masu sauraro. A ɓangare guda kuwa, suna da matsayin rumbun adana al’ada da tarihi. Makaɗa Sa’idu Faru ya shahara a waɗannan lamura a matsayinsa na makaɗin fada na yankan shakku. Hasali ma, shi ne babban misali lamba ta ɗaya idan ana batun kiɗan sarauta.

    Manazarta

    Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corpora-Tion LTD.

    Abubakar, A.T. (2015). Ƙamusun Harshen Hausa. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Limited.

    Ammani, M.C. (2019). Nazarin Awon Baka Da Aiwatarwa Da Harshen A waƙoƙin Nafi’u Yakubu

    Baba Katsina. Juzu’i Na Biyu. (Ratayen Matanonin Waƙoƙin Da Aka Yi Nazari A Kansu). Kundin Bincike Da Aka Gabatar Domin Cikasa wata Ƙa’ida Ta Neman Digiri Na Adabin Hausa, A Sashen Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero Kano.

    Bango, A. & King, A.B. (1986). “An Introduction to Life and Works of Abubakar Akwara (C. –1876-1962)”. Seminer Paper. Zaria: Ahmadu Bello University.

    Bello, G. (1976). “Yabo, Zuga da Zambo a WaƘoƙin Sarauta”. Harsunan Nijeriya, Vol. VI: 21-34.

    Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre LTD.

    Bunza, A.M. (2014). In Ba ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo. Cairo: Elkods Printing House.

    Ɗangambo, A. (1984 ). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Trimph.

    Funtuwa, A.I. da Gusau, S. M. (edt) (2011). Waƙoƙin Baka Na Hausa. Kano: Century Research And Publishing Limited.

    Gital, G. M. (1984). “Adabin Baka”. Maƙalar da aka gabatar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha, Bauchi.

    Gusau, S. M. (1988). “Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu Da Yanayinsu, Musamman A Ƙasar Sakkwato. Juzi’i Na Ɗaya Da Sharhi. Kundin Binciken Da Aka Gabatar Domin Samun Shaidar Digiri na Ɗaya.

    Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kaduna: Fisbas Media Services.

    Gusau, S. M. (1996). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa Na 1. Kaduna: Ɗab’in Fisbas Media Services.

    Gusau, S. M. (2002). Salihu JankiɗI Sarkin Taushi. Kaduna: Baraka Publishes Limited.

    Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na WaƙoƘin Baka na Hausa.Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M (2011). Adabin Hausa A Sauƙaƙe. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2014). Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i Na Biyu. Kano: Century Research and

    Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Song). Kano: Published for Bay-Ero University.

    Gusau, S. M. (2015). Audu Karen Gusau. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2016). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa. Littafi Na Biyu. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2018). Diwanin Waƙoƙin Baka: Matanonin Wasu Waƙoƙin Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2019). Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i Na Huɗu: Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa

    Ɗankwairo Maradun (1909-1991) Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun Jahar Zamfara. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2020). Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i Na Biyar: Matanonin Wasu Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Makaɗan Baka. Kano: K.d.G.

    Ibrahim, M.S. (1983). Kowa Ya Sha Kiɗa. Ibadan: Longman Nigeria.

    Sa’id, B (edt) (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Yahaya, A. B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: FISBAS MEDIA SERVICE.

    Yahaya, A. B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: FISBAS MEDIA SERVICE.

     

    [1] Kotso abin kiɗa ne na makaɗan sarauta. Ya so ya yi kama da kalangu, amma shi fuska ɗaya kawai ake rufewa, a kuma kaɗa shi da hannu. Sa’idu Faru yana daga cikin sahun makaɗan da suka fi gwanancewa wajen kiɗan kotso. Ƙwararru kuwa sun haɗa da Ibrahim Narambaɗa da  Musa Ɗankwairo.

    [2] [Keɓantacciyar tattaunawa I. Muhammad, 14 ga watan Yuli, 2024] (A lokacin yana matsayin Ɗanmadamin Birnin Magaji)

    Danna nan don karanta Maƙala Mai Taken: Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashin Tashinar Zamfara

    Edita@rumasau-kallamu

  • Maƙala Mai Taken Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun Waƙoƙin Baka na Hausa

    Maƙala Mai Taken Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun Waƙoƙin Baka na Hausa

    Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun
    Waƙoƙin Baka na Hausa

    Adamu Rabi’u BAKURA1, Abu-Ubaida SANI
    Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria

    Tsakure: Rubuce-rubucen nazari da aka yi game da waƙoƙin Hausa sun fi shurin masaƙi. Duk da haka, mafi yawan rubuce-rubucen sun karkata ne kan zaƙulo fasahohi da ke cikin waƙoƙin tare da nuna yadda suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Wannan takarda na da fahimtar cewa an bar wani babban giɓi wanda shi ne nazarin fanɗare wa dokokin addini cikin waƙoƙin Hausa.

    Maƙalar nan na da manufar binciko muhallan da ɗiyan waƙoƙin baka na Hausa suka keta
    dokokin da Allah ya shimfiɗa wa bayinsa. An tattara bayanai ta hanyar sauraron waƙoƙin da tsamo misalan ɗiyan waƙoƙin da abin ya shafa, tare da ciro hukunce-hukuncen da suka yi bayani kansu daga Alƙur’ani da hadisan manzon Allah.

    Binciken ya fahimci cewa, akwai tarin misalan fanɗare wa addini a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Daga ƙarshe an ba da shawarwarin da suka haɗa da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da ire-iren waƙoƙin ba su yi tasiri wajen gurɓata tarbiya nagartacciya ba.

    Fitilun Kalmomi: Waƙoƙi, Addini, Musulunci, Fanɗarewa

    GABATARWA

    Musulmi ba a bar shi kara zube ba. An kafa masa sharuɗɗan tafiyar da rayuwa dukkanta. Ire-iren waɗannan sharuɗɗan suna ƙunshe cikin littafin Allah (Alƙur’ani) da Hadisan Annabi S.A.W. Daga cikin dokokin akwai na tilas, wato abin da Musulmi mai hankali ba zai iya rabuwa da shi ba, komai tsanani.

    Akwai kuma abubuwan ƙi, wato waɗanda ba a so Musulmin ya aiwatar da su ba. Haka akwai haramun, waɗanda aka hana mutun ya aikata su. Idan dukkannin rayuwar mutum ta kasance cikin ɗa’a, kuma ya nisanci saɓo, babu shakka ya kiyaye dokokin Allah Maɗaukakin Sarki.

    A gefe guda kuwa, kamar yadda Chiromawa, (n.d. p. 5-10) ya bayyana, ko da addinin Musulunci ya iso ƙasar Hausa ya tarar da al’ummomi da dama suna aiwatar da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe nau’i-nau’i da suka haɗa da:
    i. Kiɗan sana’a
    ii. Kiɗan jawo hankali
    iii. Kiɗan lallashi (rarrashi)
    iv. Kiɗan faɗakarwa

    v. Kiɗan zaburarwa
    vi. Kiɗan ƙarfafa zuciya
    vii. Kiɗan jaruntaka
    viii. Kiɗan farin ciki
    ix. Kiɗan ibada

    Duk ire-iren waɗannan kaɗe-kaɗe akan haɗa su ne da waƙe-waƙe. Kasancewar addinin Musulunci, addini ne mai sauƙi da sauƙaƙa wa mabiyansa, bai haramta waɗansu daga cikin nau’ukan kaɗe-kaɗe ba. Ya dai kawo gyare-gyare domin kare mutunci da martabar
    mabiyansa. Ya haramta shi ne yayin da aka aiwatar da abin da Allah ya haramta a cikinsa.

    Hasali ma akwai wuraren da Musulunci ya sunnanta kiɗa da waƙa, kamar a lokuttan ɗaura aure, tamkar yadda Imamu Buhari ya bayyana a “Babin Kaɗa Ganha” a ranar aure da walima. Bayan haka, akwai ranar kai amarya ɗakin mijinta, da ranar idi da ranar suna, da ranar zuwan wani shugaba da ranar komawarsa, da ranar kaciya (kugunu/kuidu).

    Akwai hadisai waɗanda Buhari da Muslim da Tirmizi da Hakimu da Nisa’i suka rawaito da ke nuni ga halaccin kiɗa da waƙa a babin aure da sallar idi. Halaccin kan tabbata ne matuƙar bai haɗa da alfasha ko motsawa zuwa ga saɓon Allah ba. A bisa wannan ne, maƙalar ta ƙuduri aniyar yin ƙwarya-ƙwaryar bincike a muhallan da makaɗan baka na
    Hausa suka keta ƙa’idojin da Allah ya shata ta hanyar kauce musu.

    Duk wasu ɗiyan waƙa da makaɗi ya yi za a yi ƙoƙarin kawo shi tare da auna shi da ma’aunin shari’a da aka ciro daga nassin Alƙur’ani da Hadisan Annabi S.A.W. domin tabbatar da hasashen. Ana iya samun ɗiyan waƙoƙin da ke ƙunshe da gurbin fanɗara a waƙoƙin makaɗan sarauta, da na jama’a da na maza da sauransu, kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya.

    Dabarun Gudanar Da Bincike

    Kadadar wannan bincike ta taƙaita ne ga waƙoƙin baka na Hausa a farfajiyar koyarwar addinin Musulunci. A ɓangaren waƙoƙin an ɗauko ɗiyan waƙoƙi da aka tattauna kansu kai tsaye ta hanyar sauraron odiyoodiyo da kallon bidiyoyinsu.

    A ɓangaren hukunce-hukuncen addinin Musulunci kuwa, an ɗauko su kai tsaye daga cikin Alƙur’ani mai tsarki da hadisan Manzon Allah (S.A.W.) ingantattu. An kuma nazarci rubuce-rubucen masana da manazarta a wannan fannin inda suka haska hanya ga binciken.

    Fanɗare wa Koyarwar Musulunci ta Hanyar Zambo

    Makaɗan saurauta sun shahara wajen yin zambo, domin ƙawata waƙoƙinsu. Masana da dama sun bayyana ma’anar zambo gwargwadon fahimtarsu. Gusau, (1984 p. 37) ya tafi kan cewa “Akan yi zambo don adanta waƙa da muzanta wanda ke hamayya da wanda ake yi wa waƙa.” Abba da Zulyadaini, (2000 p.63) sun bayyana zambo da cewa: “… nau’i ne na muzanta mutum ta hanyar ƙasƙantar da shi, ko wulaƙanta shi, domin a baƙanta masa tare da dusashe masa kwarjini a idon jama’a.

    Mawaƙan sun fi shahara da zambo don su aibanta duk wani ɗan sarki da ke ja da ubangidansu. Muhammad, (2005) kuwa na da ra’ayin cewa zambo zagi ne kai tsaye,
    … saboda akan ba da hoton wanda ake yi wa tare da bayyana cikakkiyar sifarsa ta hanyar ambaton duk wani abu da ya dace da shi. A lokacin da aka yi ma wani zambo akan fito da hotonsa ne zahiri, ta yadda duk wanda ya san shi zai gane cewa da shi ake. Muhammad, (2005 p. 28)

    A taƙaice kenan, zambo yana ƙunshe da ma’anar ƙaga wa mutun magana wadda za ta muzanta shi ta ɓata masa suna ba tare da bayyana wanda ake yi wa ba. A dubi misalin zambon da Alhaji Musa Ɗankwairo ya yi wa wani ɗan sarautar Tsafe:

    Kun san zamanin ga ya canza,
    Ga wani ɗan sarki da kandaye,
    Ya shaho hoda kamar Delu.
    (Ɗankwairo: Waƙar Sarkin Tsahe).

    Wannan zambon da Ɗankwairo ya yi wa ɗan sarki ya kai matuƙa wajen aibanta ɗan sarkin ta hanyar kamanta shi da ɗan daudu. Hakan ba ƙaramin muzantawa da dushe masa kima ya yi a idon al’umma ba. Tabbas kuwa hakan ya saɓa wa dokokin addinin Musulunci. An umurci Musulmi da ya tsare (kame) harshensa da yin furucin abin da bai halatta ba, kamar keta mutuncin ɗan uwansa Musulmi ba tare da wani abu mai wajabtawa ba na shari’a. Allah na cewa:

    Lalle Allah na yin umurni da adalci da kyautatawa, da ba wa ma’abocin zumunta kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana yi muku gargaɗi ko da kuna tunawa. (Surar Nahli: 16:90).

    Idan aka dubi wannan ayar za a tarar ta yi hani ga yi wa wani mugun baki (mugun fata), sannan ta yi hani ga alfasha. Ya kuma yi umurni da tausayawa tare da yin abu bisa gaskiya. Daga ƙarshe ta yi hani a kan ha’intar wani ta kowane ɓangare. Wannan na iya
    kasancewa ta hanyar lafazi ko a aikace. Ta la’akari da wannan ɗiyar waƙar, za a tarar mawaƙin ya kauce wa dokar da Allah ya ɗora masa.

    Annabi S.A.W. Ya Ce: Haƙiƙa, mafi sharrin mutane a matsayi wurin Allah a ranar alƙiyama shi ne wanda mutane suka ƙyale shi don ƙiyayyar alfasharsa. (Muslim ya ruwaito). Wanda duk wani mawaƙi ya yi wa zambo, to zai guje shi tare da yin kaffa-kaffa da al’amarinsa.

    Sau da yawa akan ba su kyauta ne bisa tilas don gudun zambonsu. A irin wannan yanayin idan aka nazarci hadisin, za a ga a nan ma sun kauce wa koyarwar Annabi
    S.A.W. A wani Hadisin kuwa Annabi (SAW) cewa ya yi: “Mumini bai kasancewa mai yawan suka ba ko yawan la’anta ko yawan alfasha, ko mai sakin harshe” (Tirmizi
    ne ya ruwaito shi).

    Wannan hadisin ya fito ƙarara ya bayyana mana cewa, duk mawaƙin da ya ba da gaskiya
    ga Allah da ranar lahira da manzancin Annabi S.A.W., zai kasance mai bin dokokin Musulunci kamar yadda suke. Hakan kuwa zai sanya ya guji yi wa Musulmi zambo.
    Akwai misalan wuraren da makaɗan jama’a suka yi wa abokan hamayyarsu zambo ta hanyar zagi kai tsaye.

    A irin wannan lamari ne mawaƙin jama’a kan fito da halayen mutun a fili, sannan ya zage shi. Misali, a waƙar “Gagara Badau,” Alhaji Mamman Shata cewa ya
    yi:
    Shata: Allah ya tsine ma tsohon mazinaci,
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Allah ya tsine ma da kai da iyalinka.
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Yanzu babban ɗan bai gani,
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Babban jikanshi kuma yana kama agwaginmu,
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Gida ya lalace.
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

    Dubi yadda Shata yake zagin wani basarake tare da nuna ɗansa ya makance, ya kuma kira jikansa ɓarawon agwagi. Wannan ba ƙaramar fanɗarewa ba ce, domin a shara’ar Musulunci an umurci Musulmi da ya kiyaye da yin zance da bai halatta ba, kamar ƙarya, da zage-zage da keta mutunci Musulmi. Allah na cewa: “…Kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana muku gargaɗi ko da kuna tunatuwa.” (Alƙur’ani,
    Suratul Nahl, 16:90).

    Fanɗare Wa Koyarwar Musulunci Ta Hanyar Habaici

    Habaici ko gugar zana salo ne ko azancin yi da wani a kaikaice ta yadda sai wanda ya san shi kuma ya san abin da ake magana game da shi ne kaɗai zai iya ganewa. Habaici wata hanya ce da makaɗan baka suke amfani da shi a cikin waƙoƙinsu domin ƙara musu
    armashi, ta hanyar ƙasƙantar da wani mutun ko kuma muzanta shi ko su zage shi ko kuma su soka masa wata magana a kaikaice. Misali, a cikin waƙar Mai Dubun
    Nasara Sardauna, Alhaji Musa Ɗankwairo yana cewa:

    Ga kare ga kura kowane ya hangi wani,
    Ga aura ya koma,
    Wagga nan hanya ba mu ga wurin wali ba.
    (Alhaji Musa Ɗankwairo, Waƙar Mai Dubun Nasara, ta Sardauna).

    Yayin da aka dubi ɗiyar wannan waƙar za a ga yadda Ɗankwairo ya siffanta Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da kura. Ya yi hakan ne domin bayyana irin ƙarfinsa kamar yadda kura ke da shi. Wannan kuwa ya shafi yadda take iya tauna ƙashi da kuma kwarjini da waibuwarta na sanya rashin kuzari ga halittar da ta tunkare ta.

    A gefe guda kuwa, sai ya kira wanda yake yi wa habaici da kare, saboda ba sa zama
    inuwa ɗaya da kura. Hasali ma kare ba ya hangen nesa sosai, kuma mai gidansa yakan yi amfani da shi ne wajen farauta. Kiran mutun kare ba ƙaramin ƙasƙantarwa ba ne
    a al’adance. Wannan ne ya sa makaɗan baka sukan siffanta waɗanda suke son wulaƙantawa da kare saboda nhalayyarsa da ɗabi’unsa.

    Musulunci ya hana keta mutuncin Musulmi ko wulaƙanta shi ko zagin sa ko laƙa masa munanan sunaye, ba tare da haƙƙin shara’a ba. Allah na cewa: “… kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye” (Alƙur’ani, 49:11). Idan muka dubi wannan ayar, za mu ga cewa ta hana a kira Musulmi da sunan da zai kasance tamkar zagi ne gare shi. Yin haka kuma fanɗare wa umurnin Ubangiji ne.

    Annabi S.A.W. ya ce: “Zagin Musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙar sa kafirci ne” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi). Idan aka dubi wannan hadisin cikinsa da
    wajensa, aka kuma nazarci ɗiyar waƙar da ta gabata, za a tarar cewa, makaɗin ya kauce wa faɗar Annabin S.A.W., ya yi gaban kansa. Yin haka fanɗarewa ne ga dokokin addinin Musulunci.

    Bin dokoki da ƙa’idojin Musulunci kuwa dole ne, inda har Allah ke cewa: “Kuma abin da Manzo ya zo muku da shi, to ku riƙe shi, kuma abin da ya hane ku, to ku hanu” (Surah Al-hashr, 59:9).

    Fito-Na-Fito Da Koyarwar Muslunci

    Akwai misalan inda mawaƙa ke amfani da wasu kalmomin da suka kauce wa ƙa’idojin addinin Musulunci. Akan samu irin wannan fito-na-fito a fannonin da suka shafi sahihan aƙidojin da suka danganci ranar lahira, da matsayin mala’ikun Allah da makamantansu. Ya kuma haɗa da dokoki da ƙa’idojin addinin Musulunci ta fuskar hani da horo. Wannan
    ɓangare na aikin zai mayar da hankali wajen zaƙule irei-ren waɗannan misalai:

    Izgilanci

    Izgilanci ga abubuwan da addini ya zo da su nanuni ga halin ko-oho ga lamarin addinin. Musulunci kansa ya tsawatar da riƙo da dokokin da ke ƙunshe cikinsa ba tare da wargi (wasa) ba. Duk da haka, akan samu wuraren da mawaƙa suka yi izgilanci ga lamarin
    addini. Alhaji Muhammadu Ɗan’anace a waƙar Shago yana cewa:

    Jagora: In da lahira ana kasa dambe…
    ‘Y/Amsohi: Da Walakiri ya ji ƙwal ga gaba nai.
    Jagora: Duk wanda bai yi kallon Shago ba,
    Aradu yana da sauran kallo,
    Ya zaka duniya kamar bai zo ba,
    Kamar zuwan kare ga aboki,
    Tamkar mutum ya mari budurwa,
    Ko ya mutu ba a gafarta mai.

    In aka dubi wannan ɗan waƙar, za a tarar cewa, wannan makaɗin ba ƙaramar kasada ya yi ba. Ya nuna rashin jin tsoron aukawar wani haɗari (hatsari) ko shiga cikin abin da bai san sakamakonsa ba. Allah na cewa: “Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi a kansa.” (Surar Isra’i, 17:36).

    Idan muka nazarci wannan ayar, za a ga yadda Mahaliccin sammai da ƙassai ya faɗakar da masu imani da su yi kaffa-kaffa ga dukkan lamarin da ba su san haƙiƙanin yadda yake ba. Ko bayan batu kan abin da mutum bai sani ba, batutuwan da ke ƙunshe cikin ɗiyar
    waƙar na tattare da izgilanci ga abin da ya shafi imani da mala’iku da ranar ƙiyama.

    Goyon Bayan Karuwanci

    Kalmar karuwa, suna ne na mace. Jam’i kuwa shi ne karuwai. Karuwa na nufin mace mai zaman kanta wadda mazan banza ke neman ta su ba ta kuɗi domin saduwa (zina) da ita. Zina kuwa tana nufin saduwa (jima’i) da matar da ba ta halatta ga mutum ba ta hanyar aure, wato wadda ba matarsa ba. Tun kafin bayyanar Musulunci a farfajiyar
    ƙasar Hausa, Bahaushe ya ƙyamanci zina.

    Don haka karuwanci bai samu bagiren zama ba, balle a yi zina. Duk da kasancewar akwai al’adar tsarance, a inda saurayi kan gayyaci budurwarsa ta je ɗakinsa har ma ta kwana. Sakamakon irin wannan al’adar ce, ya sanya su amfani da al’adun tsafi domin tabbatar da amarya ba ta taɓa sanin wani ɗa namiji ba (zina) kafin a yi mata aure. A irin
    wannan al’adar ce, idan yarinya ta san maza kafin a yi mata aure, za ta kunyata a cikin jama’a.

    Idan kuma ta ɓoye ba ta faɗa ba, ta mutu, kamar yadda Ibrahim, (1985 p. 5) ya nuna.
    Yayin da addinin Musulunci ya bayyana, sai ya haramta zina. Hasali ma ya sanya ta cikin manyan laifuka, bayan kafirci, wato haɗa Allah da wani da kashe ɗan Adam. Allah yana cewa: “Kuma kada ku kusanci zina, lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya” (Alƙur’ani; Suratul Isra’i, 17:32)

    Haka kuma Musulunci ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da za ta iya zama sanadin aikata zina ta hanyar wajabta wa mata sanya hijabi. Sanya hukuncin jefe mazinaci da mazinaciya har su mutu a bainar jama’a, idan sun yi aure, ko a yi musu bulala idan ba su taɓa yin aure ba, na nuni da girman zunubin. Duk da wannan umarni na Ubangijin talikai da kuma uƙubar da aka tanadar wa mazinata, sai aka sami wani mawaƙi da ake kira Habibu Sakarci ya yi wa wata karuwa waƙa.

    A cikin ɗiyan waƙar yana cewa:
    Jagora: Shehuwar mata Safiya Kano, Ta gidan ‘Yajja
    Safiya Kano.
    Jagora: ‘Yan birni roƙo suke, Allah ba mu jaka bakwai,
    Mu gano ɗakin Safiya Kano.
    Jagora: Direbobi ma roƙo suke, Allah ba mu jaka
    bakwai, Mu gano ɗakin Safiya Kano.
    Jagora: Mutan birni yanga suke, Domin darajar Safiya
    Kano.

    Yayin da aka nazarci ɗiyan waƙar, za a ga cewa Habibu Sakarci yana tallar wannan karuwa ta hanyar bayyana ta a matsayin ƙasaitacciyar karuwa. Har ma ya nuna ‘yan birni da dirobobi na burin Allah ya ba su kuɗi masu yawa, don su tafi ɗakinta. Hasali ma ya bayyana ta fi sauran karuwan birnin kyau. Wannan ba ƙaramar fanɗara ba ce da keta dokokin Allah.

    Ya zo cikin hadisi
    Annabi S.A.W. yana cewa: Lalle ana rubuta wa ɗan’adam rabonsa daga
    zina, kuma lalle mai risker sa wancananka ne babu makawa. Idanu zinarsu ita ce kallo, kunnuwa kuwa zinarsu ita ce sauraro, harshe kuwa zinarsa ita ce zance. Hannuwa kuma zinarsu ita ce damƙa, ƙafa kuma zinarta ita ce taku, zuciya kuwa saƙa soye-soyenta ne, kuma tana guranta su, farji yana gaskata wancananka ko ya ƙaryata (Buhari da Muslimu ne suka ruwaito hadisin).

    Duk da irin waɗannan nassoshin Alƙur’ani da hadisan Annabi S.A.W., sai ga ya makaɗa na fanɗare musu ta hanyar gayyatar al’umma zuwa ga aikata fasiƙanci. Shi ma Alhaji Mamman Shata ya yi makamanciyar wannan waƙar, a inda ya yi wa wata mata da ake kira Karo Oma:
    Jagora: Duk ɗan birnin da ya riƙa,
    Ni kar ya yi mini yanga,
    In yana so ya isa
    In gan shi gidan Kara Oma.
    (Alhaji Dakta Mamman Shata: Waƙar Kara Oma)

    A nan Shata ya fito ƙarara ya tura ‘yan birni su tafi gidan wannan karuwa idan har sun isa. A ɗaya ɓangaren kuwa cicciɓa ta ya yi da cewa, sai manyan mutane wayayyu ne kawai suka isa su yi hulɗa da ita. Wannan waƙar ba abin da ya raba ta da fanɗare wa
    dokokin Allah da ya shata wa Musulmi.

    A shara’ar Musulunci, an san Musulmi da kunya. Hasali ma kunya tana cikin halayensa, kuma tana daga cikin Imani. Imani kuwa shi ne aƙida da rayuwar Musulmi. Manzon Allah yana cewa: “Kunya da imani suna zozozo da juna. Idan babu ɗayansu, ɗayan ma ba za
    a same shi ba” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

    Goyon Bayan Shan Giya

    Giya, kalmar suna ce da ke cikin jerin sunaye jinsin mata. Ita kuma nau’i ce da ake yi da hatsi ko alkama ko inibi wadda ake sha a yi maye. Ana kuma kiranta barasa, kamar yadda ƙamusan CNHN (2006 p.168) ya nuna. Shan giya a tsakanin al’ummar Larabawa kafin bayyanar Musulunci abu ne sananne. Shi ne ƙashin bayan doron ginin tattalin arzikinsu, kuma giya na daga cikin kayan fataucinsu.

    Har matansu sun kasance shahararru wajen haɗa ta. Hasali ma kowane gida akan
    same ta. Wannan ya sa har suna yabon giya a cikin waƙoƙinsu. Su ma al’ummar Hausawa ba a bar su a baya ba, domin sun mayar da shan giya musamman a lokuttan
    bukukuwan aure da na haihuwa tamkar ƙawa. Yayin da suka samu rabauta na karɓar addinin Musulunci, sai suka guje ta a sakamakon hanin da addinin ya yi gare su.

    Kasancewar Musulunci addini ne mai sauƙi da ke ƙunshe da dabarun magance abubuwan da ke haifar da fitsara da ta’addanci a tsakanin al’umma, sai ya fara bayyana wa muminai rashin kyanta. Daga nan kuma ya hana kusantar wurin ibada yayin da aka sha ta Daga ƙarshe ne kuma ya sauƙar da hani kai tsaye game da shan giya inda aka ce:
    “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku sani cewa, giya da caca da gumaka da ƙyaurayen duba ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nisance su don ku rabauta
    (Alƙur’ani; 5:90).

    A wannan ayar an bayyana wa masu imani munanan ayyuka da ake buƙatar mumini ya nisance su. Kuma duk al’ummar da ta rungume su za ta faɗa cikin masifa da rashin kwanciyar hankali. Ayar ce kuma ta zo da haramcin shan giya kai tsaye. Akwai hadisai da dama da suka tabbatar da haramcin shan giya da kuma abin da ake kira da giya.
    Annabi S.A.W. yana cewa: “Duk abin da ke bugarwa giya ce, kuma kowace irin giya haramun ce” (Muslim ne ya ruwaito shi).

    A Wani Hadisin Kuwa Cewa Ya Yi: Allah ya tsine wa giya, masu shan ta, da waɗanda suka zuba ta, da waɗanda suka sai da ita, da waɗanda suka saye ta, da waɗanda suka tatso ta, da waɗanda suka ɗauki kayan da ake tatsarta, da waɗanda suke ɗauke ta, da waɗanda aka kai wa ita, da waɗanda suka samu kuɗi a gare ta” (Abu Dawuda, da Al-Hakem a isnadi ingantacce, suka kawo shi)

    Yayin da aka dubi waɗannan nassoshi, za a tarar cewa, ƙin bin su sau-da-ƙafa keta shara’ar Musulunci ne, wato fanɗarewa faɗar Allah da annabinsa ne. Duk da haka, an ci karo da waƙoƙin da suka yi kira da a sha gida. Alhaji Mamman Shata Katsina ya waƙe giya. Har ma cewa ya yi:

    Jagora: Ka ji karatun masu bugun ruwa, Waɗanda…
    ‘Y/Amshi: Ke zikiri a Kuloniya, A sha ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: A nan muke sallarmu ta Juma’a, Mu tattara kayanmu mu kai Neja, Ku sha ruwan nan…

    Y/Amshi: Ba laihi ba ne, A sha ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: Ruwa na kwalba ba laihi ba ne, Ai kun ga…
    ‘Y/Amshi: Alhaji Shata sha yake. A sha ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: Yara mu koma wasa Kuloniya, Mu tashi kana
    mu koma Neja,
    ‘Y/Amshi: Nan ne muke zikirinmu na Juma’a. A sha
    ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: Malam ka sha ai ba laihi ba ne, Ga taka ga tau…
    ‘Y/Amshi: Kowa ya aje. A sha ruwa ba laihi ba ne.

    Idan muka nazarci waɗannan ɗiyan waƙar za a ga yadda mawaƙin ya yi fito-na-fito da dokokin Allah da Manzonsa. Allah ya haramta, shi kuma ya halatta. Dubi yadda mawaƙin ya ce a sha giya ba laifi ba ne, bayan Annabi S.A.W. ya ce kada a sha, a inda yake cewa:
    “Kada ku haɗa fulawa da dabino gaba ɗaya, kuma kada ku haɗa busasshen tafarnuwa da dabino sam-sam, ku bar su idan an niƙa su.”

    Yayin da aka niƙa su, nan take suna bugar da wanda ya sha su. Don haka ne Annabi ya umarci masu imani da kada su sha a haɗe yayin da suke niƙe, kamar yadda Munhajul Muslimu Jadawali na uku: Abinci da Abinsha ya nuna. Hasali ma mawaƙin ya bayyana cewa shi ma yana shan giyar tare da yaransa. Akwai hadisai da dama da suka nuna haɗarin Musulmi ya mutu yana shan giya, ko da bai halatta ta ba.

    To ina ga wanda ya halatta shan ta? Daga cikin ire-iren waɗannan hadisai akwai wanda
    Ibni Abbas ya ce: Manzon Allah S.A.W. ya ce: Duk wanda ya mutu yana cikin ɗabi’ar shan giya bai tuba ba, zai tarar da Ubangiji Allah Maɗaukakin Sarki tamkar wanda ya bauta wa gumaka (Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin).
    A wata waƙar ta mawaƙin da ake kira Horo/Horu, an ga baitukan da suka nuna ba laifi ba ne shan giya da ma cin mushe. Mawaƙin na cewa:

    Jagora: Arnaaa ku sha giya ku ci mushe, Aljanna mai rabo zai sama.

    A wani wuri kuwa, har ya nuna ma kashi ne ga mutum ya sha giya ‘yar kaɗan kuma ta wahalshe shi. Yana cewa:

    Jagora: Kowa ya sha giya yai yi amai, Ba ɗan halas ba ne, shege ne!
    Jagora: Su wane ‘yan giyan ƙarya ne, Shegu, kwalba guda take ka da su.

    Don karanta Tarihin Garin Rimin Gado danna nan

    Goyon Bayan Sata

    Abubakar (2015, p. 431) ya bayyana cewa, sata “tana nufin ɗaukar abin wani ba da saninsa ko izinin ba. ”Sata na nufin ɗaukar wani abu da hukuncin shari’a ko hankalin tuwo bai mallaka wa wanda ya ɗauka ba, tare da amfani da shi ko musanyensa da wani abu mai daraja kwatankwacin na kuɗi ko kuma mai amfanarwa, ba tare da izinin wanda ko waɗanda ke da mallakin abun ba.

    Sata ta kasu zuwa nau’uka daban-daban. Sun fi danganta da salon yadda aka gudanar da satan. Fitattu daga cikinsu sun haɗa da:
    i. Cuta
    ii. Damfara
    iii. Fashi
    iv. Fizge/Wabce/Fauce
    v. Ƙwace
    vi. Sane

    Sata babbar abar ƙyama ce a farfajiyar Hausa da Hausawa, tun ma kafin bayyanar addinin Musulunci. Sauyawan al’amurra da cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu sun wanzar da taɓarɓarewar tarbiyya da ƙoƙarin neman tara abin duniya ido rufe. Ta kai ga
    fanɗararru marasa kishin kansu cikin al’umma sun tsunduma a fagen wannan ta’addanci.
    Yayin da addinin Musulunci ya bayyana a ƙasar Hausa, sai ya ƙara ƙarfafa wa Hausawa ƙyamar wannan muguwar sana’a.

    Musulunci ya zo da dokoki domin kawar da duk nau’o’in sata. Allah na cewa:
    Ɓarawo kuma da ɓarauniya sai ku yanke hannayensu ya zama sakamako ne na abin da suka aikata, (wannan horo ne) daga Allah. Allah kuwa mabuwayi ne Gwani. (Alƙur’ani, 5:38). A addinin Musulunci ta kowace fuska ana ƙoƙarin kare dukkanin al’umma ta yadda za a zauna cikin aminci game da dukiyoyi da rayukan al’umma.

    Ita kuwa sata, mugun hali ce da ke haifar da rashin kwanciyar hankali da salwantar rayuwa a tsakanin al’umma. Don haka ne shari’a ta tanadar da hukuncin yanke hannun
    ɓarawo wanda zai hana watsuwar irin wannan muguwar ta’asa a tsakanin al’umma [14]. Allah na cewa: “Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar cuta ”(Alƙur’ani, 2: 188).

    Ayar tana tabbatar wa masu imani cewa, cuta haram ce. Ba ya halatta ga Musulmi ya yi zalunci ta hanyar zaƙin baki ko dabara. Haka kuma, bai halatta ya yi jagora don a cuci wani ba. Duk da irin waɗannan dokokin da Allah Maɗaukakin Sarki ya shimfiɗa domin samar da kyakkyawan zamantakewa da aminci a doron ƙasa, an samu gungun mawaƙa da ke jayayya da dokokin cikin lafuzzan waƙoƙinsu.

    Bunza, (2014) ya kawo baituka da dama daga bakin Alhaji Muhammadu Gambo Fagada.
    Gambo ya bayyana ƙarara cewa:
    Jagora: Don Waɗanda ka sata nay yi ganga, Ba do wani sarki mai naɗi ba.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Tsoho Tudu)
    A cikin waƙarsa ta Nazaƙi kuwa, an ga yadda hirarsu ta gudana da Nazaƙi bayan ya tuba daga sata.

    Sannu a hankali har Gambo ya sake zuga shi yadda har sai da ya dawo satan. Gambon da kansa ya bayyana cewa:
    Ɓarawo in ina kusa ba tuba yakai ba,
    Ko ya aje gemu, ko ya yi saje,
    Ko ya fidda farin gashi ga kaina,
    In Gambo na kusa ba tuba yakai ba,
    Ba ko batun shegantaka ba.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Nazaƙi)

    A wannan ɗiyan waƙa, sai da ya jaddada cewa, batunsa ba “batun shegantaka” ba ce kawai. Wato dai haƙiƙanin gaskiya yake faɗa cewa idan yana kusa ɓarawo ba ya tuba domin kuwa zai ziga shi ya hana shi tuban. Wasu makaɗan sukan yi waƙoƙin yabo ne ga
    ɓarayin. Misali Alhaji Mamman Shata ya yi wa wani ɓarawo mai suna Mamman Ɗan’yarbayye waƙa, a inda yake cewa:

    Jagora: Mai hannun taɓa ƙofa in an bacci,
    Masu samame baƙon Ɗanmani.
    Na faɗa maka Mamman.
    In dai ka ɗauko sa’a,
    Har ka buɗe ƙofa,
    Ka tarar an bacci,
    To zari akwati tsakiyar shi ya fi kaya.
    Na saman hoto ne,
    Na ƙasan maganin ƙwari ne.
    Tafi zari akwatin tsakiyar shi ya fi kaya.
    Na Abdu ƙyale dangi sai an bacci,
    Iyalin Mamman, waɗanda ba su so a yi haske,
    Su sun fi so a tabka duhu da ruwa yaf-yaf-yaf.
    Wani don ya taka kara bai mai ƙara ba,
    Sannan ganyen ganji duk ya bi ƙasa.
    (Alhaji Dakta Mamman Shata: Mamman
    Ɗan’yarbayye)

    A waɗannan ɗiyan waƙar, mawaƙin ya yabi ɓarawon tare da ba shi shawarar yadda zai gudanar da sana’arsa ta sata. Wannan ya haɗa da yi masa ishara ga irin lokuta da yanayi da dabarun da zai bi wajen yin satar, da kuma nau’in abin da zai sata da ya fi saura daraja.

    Hakan kuwa karan-tsaye ne ga dokokin addini. Hadisin Manzo (S.A.W.) ya bayyana cewa: “Ɓarawo ba ya sata a lokacin da yake da imani” (Buhari ne ya ruwaito
    hadisin). Allah Maɗaukakin Sarki ya kawo nau’in hukuncin da ya dace a zartar wa masu fashi da makami, a inda yake cewa:

    Ba wani abu ne sakamakon waɗanda suka yi wa (Musulmi masu bin) Allah da manzonsa fashi ba, kuma suke tafiya a bayan ƙasa da ɓarna ba, sai kawai a kashe su ko kuma a tsire su ko a yanke hannayensu da ƙafafuwansu a tarnaƙe, ko kuma a kore su daga ƙasa. (Yin) wancan ƙasƙanci ne a gare su a duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma. (Alƙur’ani, 5:33).

    Allah ya bayyana mana cewa masu yin fashi da makami suna ƙoƙarin ɓata tsarin Allah da Manzonsa ne, saboda aiwatar da fashi ya kauce wa hanyar gaskiya da adalci, waɗanda Musulunci ke ƙoƙarin tabbatar da su a doron ƙasa. 3.5 Goyon Bayan Kisan Kai Kisan kai na daga cikin manyan zunubai masu matuƙar muni a Musulunci. A cikin Suratul Nisa’i, Allah na cewa:

    Wanda kuma ya kashe mumini da gangan, to Jahannama ce sakamakonsa, yana madawwamini a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma tsine masa, kuma ya
    tanadi azaba mai girma a gare shi (Alƙur’ani, 4:93).

    An jiyo Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato yana ziga fitaccen ɗan damben nan Shago domin ya yi kisa. A cikin Bakandamiyar Shago, yana cewa:
    Bayarwa: Yanzu inai maka kuka,
    Ba kukan tuwo ba, Ba na hura ba…
    ‘Y/Amshi: Kukan Ɓaleri ya raga bayi, Suna kirarin banza.
    Bayarwa: Ɗan Abdu ko ga girbin
    ‘Y/Amshi: Gero, bara-bara ta na hana wake….
    A wani wuri yana cewa:
    Bayarwa: Ɗan Abdu kashe mutum a gafarta ma. Ɗan Abdu…
    ‘Y/Amshi: Kashe mutum a gafarta ma.
    (Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

    Ba za a ce maganar kisa a nan ta taƙaita ga buge mutum a dambe ba kawai. Ya haɗa da kashewa har lahira. Hakan zai ƙara tabbata yayin da aka yi la’akari da lafuzza da ya riƙa amfani da su cikin waƙar da suka haɗa da:
    i. Kusheyi
    ii. Lahira a kai miki gawa
    iii. Lahira tana yin baƙo
    iv. Uwar mutum ta haifi wani, da sauransu.

    Gambo ma ya yi makamanciyar zigar nan inda yake ziga inda yake cewa:
    Bayarwa: Duw wanda ya ishe mai kuɗi lahiya lau,
    Ya yi sata yab bar mai kuɗi da rai nai,
    In yaz zaka Allah ya isam min za ni ce mai,
    Don wagga ba sata ta ba Gambo.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Kashe Mace)

    A nan, ko bayan ziga zuwa ga yin sata, mawaƙin ya nuna cewa satar ba ta cika har sai an yi kisan kai. Wannan kuwa fanɗarewa ne daga koyarwar addinin Musulunci.

    Goyon Bayan Kisan Kai

    Kisan kai na daga cikin manyan zunubai masu matuƙar muni a Musulunci. A cikin Suratul Nisa’i, Allah na cewa: Wanda kuma ya kashe mumini da gangan, to Jahannama ce sakamakonsa, yana madawwamini a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma tsine masa, kuma ya tanadi azaba mai girma a gare shi (Alƙur’ani, 4:93).

    An jiyo Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato yana ziga fitaccen ɗan damben nan Shago domin ya yi kisa. A cikin Bakandamiyar Shago, yana cewa:
    Bayarwa: Yanzu inai maka kuka,
    Ba kukan tuwo ba, Ba na hura ba…
    ‘Y/Amshi: Kukan Ɓaleri ya raga bayi, Suna kirarin banza.
    Bayarwa: Ɗan Abdu ko ga girbin
    ‘Y/Amshi: Gero, bara-bara ta na hana wake….

    A wani wuri yana cewa:
    Bayarwa: Ɗan Abdu kashe mutum a gafarta ma. Ɗan
    Abdu…
    ‘Y/Amshi: Kashe mutum a gafarta ma.
    (Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

    Ba za a ce maganar kisa a nan ta taƙaita ga buge mutum a dambe ba kawai. Ya haɗa da kashewa har lahira. Hakan zai ƙara tabbata yayin da aka yi la’akari da lafuzza da ya riƙa amfani da su cikin waƙar da suka haɗa da:
    i. Kusheyi
    ii. Lahira a kai miki gawa
    iii. Lahira tana yin baƙo
    iv. Uwar mutum ta haifi wani, da sauransu.

    Gambo ma ya yi makamanciyar zigar nan inda yake ziga inda yake cewa:
    Bayarwa: Duw wanda ya ishe mai kuɗi lahiya lau,
    Ya yi sata yab bar mai kuɗi da rai nai,
    In yaz zaka Allah ya isam min za ni ce mai,
    Don wagga ba sata ta ba Gambo.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Kashe Mace)

    A nan, ko bayan ziga zuwa ga yin sata, mawaƙin ya nuna cewa satar ba ta cika har sai an yi kisan kai. Wannan kuwa fanɗarewa ne daga koyarwar addinin Musulunci.

    Hani Ga Bautar Ubangiji

    Ko bayan kira zuwa ga aikata ɓarna da fasadi, akwai misalan ɗiyan waƙoƙi kuma da ke kira ga barin bautar Ubangiji. Na biyu a cikin shika-shikan Musulunci ita ce salla. Tana da matuƙar muhimmancin da har ya kasance kadarko tsakanin mutum da kuma shirka da
    kafirci. Duk da haka, sai ga ɗiyan waƙa da ke hani ga yin salla:

    Bayarwa: Ɗan Abdu ban da sallas swahe,
    ‘Y/Amshi: Domin yawan sallan nan yana rage maka ƙarhi.
    (Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

    Sakamakon Bincike

    Ta la’akari da nassoshin Alƙur’ani da Hadisan Annabi S.A.W. da kuma ƙumshiyar wasu waƙoƙin baka na makaɗan Hausa, za a a iya cewa, mawaƙa na wuce gona da iri a waɗansu lokuta. Yawanci hakann na faruwa ne yayin da suka yi ƙoƙarin adanta waƙoƙin nasu domin burge wanda aka yi wa waƙar da kuma sauran masu nsauraro.

    A haka ake samu ɗiyan waƙoƙin sun yi wa dokokin Musulunci karan-tsaye. A wannan nazarin an fahimci cewa duk wani aikin da ɗan’adam ya aikata wanda Allah da manzonsa
    suka yi hani da shi, yin haka nau’i ne na fanɗare wa dokokin Allah. Ya zama tilas kowane Musulmi ya nemi ilimin duk wani lamarin da ya shafi rayuwarsa, (kamar yadda mai Ahalari ya bayyana) don gudun auka wa fushin Ubangiji.

    An kuma fahimci cewa, a Musulunci kowane irin al’amari an ɗora shi a kan mataki-mataki. Wannan ne ya wajabta wa kowane Musulmi ya yi umurni da aikata alheri da kuma hani ga mummunan aiki gwargwadon ƙarfin ikon mutun.

    Kammalawa

    Yin fice da waƙoƙi suka yi wurin ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa, ba shi ke nuna ba a samun fanɗarewa a cikinsu ba. Nau’ukan fanɗarewa da ake samu cikin waƙoƙin Hausa sun shafi ziga zuwa aikata abin da Ubangiji ya hana, ko izgilanci ga
    abubuwan da Musulunci ya zo da su, ko kuma hani ga abin da Ubangiji ya yi umarni da a aikata.

    Abu ne mai kyau manazarta su riƙa zaƙulo ire-iren fanɗarewa da ake samu a cikin waƙoƙi domin faɗakar da al’umma da su kansu mawaƙan. Malamai da ke jagorantar nazarcenazarcen waƙoƙi a makarantu kuwa, ya kamata su mayar da hankali wajen yin shiri na musamman na faɗakar da ɗalibai ta fuskokin da suka dace yayin da aka ci karo da ire-iren baitukan fanɗarewa a cikin waƙoƙin da suke nazarta.

    Gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa ma na da rawar takawa wajen samar da ƙa’idoji da tsaretsaren tace waƙoƙi kafin sakinsu. Haɗakar waɗannan za su tabbatar da al’umma ba ta rinjayu da kiraye-kirayen waƙoƙin fanɗara ba zuwa taɓewa.

    MANAZARTA

    • Abba, M., & da Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan
    waƙar baka ta Hausa. Gaskiya Corporation Limited.
    • Abubakar, A. (2015). Ƙamusun Harshen Hausa.
    Zaria: Northern Nigeria Publishing Company LTD.
    • Al-Munajjid, M. S. (2004). Muharramat: Forbidden
    matters same people take lightly. International
    Islamic Publishing House, Saudi Arebia.
    • Bunza, A. M. (2014). In ba ka san gari ba saurari
    daka: Muryar nazari cikin tafashen Gambo Elkods
    Printing Hausa.
    • Chiromawa, U. A. U. (n.d.). Dalilin kiɗa a cikin
    Alƙur’ani da hadisi.
    • Gusau, S. M. (1984). Nazarin zaɓaɓɓun waƙoƙin
    makaɗan baka na Hausa, littafe na ɗaya.
    • Ibrahim, M. S. (1983). Kowa ya sha kiɗa. Longman
    Nigeria Limited.
    • Magaji, A. (2016). Kassu Zurmi da waƙoƙinsa.
    Spectrum Books Limited.
    • Muhammad, Y. M. (2005). Adabin Hausa. Ahmadu
    Bello University Press Limited.
    • Sani, A. U., & Jaja, M. B. (2019). Zamani Riga:
    Akalar Magungunan Gargajiya a Hannu Addini da
    Zamani. In The Nasarawa Journal of Humanities, 7,
    (1-2), 257-268. ISSN: 1118-6887.
    • Shehu, M., & Sani, A. U. (2019). Intra-Religious
    Conflicts within the Hausa Hausa-folk. In EAS
    Journal of Humanities and Cultural Studies, 1(3),
    145-150. ISSN: 2663-0958 (Print) & ISSN: 2663-
    6743 (Online) Available at:
    https://www.easpublisher.com/get-articles/344.
    • Umar, M. B. (1987). Dangantakar adabin baka da
    al’adun gargajiya. Kamfanin “Triumph” Gidan
    Sa’adu Zungur

    Danna nan don karanta Nazarin Hanyoyin Adana Kayayyakin Hausawa Na Gargajiya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Gudumar Dukan Rashawa

    Waƙa Mai Taken Gudumar Dukan Rashawa

    1. Ya Allah sunanKa farko,

    Don aikina ya yi ƙarko,

    Har al’umma duk su farko,

    Mu kauce hanya mai duɗewa.

     

    2. Na yi salati gun sa Manzo,

    Wanda ya ce duk mu yi ƙwazo,

    Biɗar halal duk inda mun zo,

    Shi ne tafarki mai ɓulewa.

     

    3. Waƙa zan yi a kan halinmu,

    Wanda ya zam shi jiki gare mu,

    Tamkar umarnin khaliƙinmu,

    Mun ɗauke shi muna riƙewa.

     

    4. Yin rashawa ko toshe baki,

    Don kwaɗayin ai wani aiki,

    Wanda ya kauce wa tafarki,

    Albarkarmu yake ragewa.

     

    5. Guba ce wallah in ka karɓa,

    Ko ko ka bayar anka karɓa,

    Dokar Allah ce ka saɓa,

    Ƙin gaskiya hanyar ɓacewa.

     

    6. Mutunci farko zai zubewa,

    Aiki ya zam ba kyautatawa,

    Sai amaja da sukurkucewa,

    Al’amuranmu su dagulewa.

     

    7. Mai haƙƙi ne an hana shi,

    Wanda take mai kyau niyarshi,

    An ba mai bayar da toshi,

    Wanda niyarsa abar gujewa.

     

    8. Muddin an haka ba amana,

    Ba adalci sai hiyana,

    Sannan babu zaman lumana,

    Sai ɗar-ɗar sai firgicewa.

     

    9. Kwai rashawar daɗaɗa zance,

    Wata da aiki kan kasance,

    Wata jaka ce za a sunce,

    Ɗan hasafi a zamo yiwowa.

     

    10. Wata ko kyauta za a ba ka,

    Iyaye ko ko a ba wa ɗanka,

    Domin biɗar wani abu gun ka,

    Ka yarda ko ko ka zam ƙiyawa.

     

    11. Kowane nau’i ya haramta,

    Annabi ya tsine wa yin ta,

    Mai karɓa har wanda yai ta,

    Dai dai ne suke ba rabewa.

     

    12. Ga lamura yau sun ƙazanta,

    Harka duk an sassaka ta,

    An rufe duk munin sifarta,

    Sunanta an kyautatawa.

     

    13. Na yi tunanin me ya sa ne,

    Ba ƙyamar ta wurin mutane?

    Duk mai cin rashawa mu gane,

    Har mai ba shi abin gujewa.

     

    14. Rashin kishi ni a ganina,

    Shi ke sawa har a raina,

    Halali sai a ga wai kaɗan na,

    Sai an ɗora haram daɗawa.

     

    15. Duk mai kishi ga ƙasarsa,

    Mai kishin kuma al’umarsa,

    Ba ƙofar rashawa a gun sa,

    Siraɗi gobe yake wucewa.

     

    16. Son kai yai kanta a zuci,

    Tai tsatsa sassanta ya ci,

    Shi ke sa rashawa ake ci,

    Ba ƙyama sai ƙawatawa.

     

    17. Ƙyashin samu ga waninmu,

    Da ci da zuci ke hana mu,

    Yin haƙuri bisa matsayinmu,

    Wanda Ilahu ya zam rabawa.

     

    18. Sai haɗama sa har da wannan,

    Son a fiye wancan da wannan,

    Su ke sa rashawa ƙasar nan,

    In mun bar su tana gushewa.

     

    19. Yaƙin halayen ga dole,

    Kishin ƙasa mu riƙe shi lalle,

    Sai lamuranmu su sake lale,

    Albarka ta isa ga kowa.

     

    20. Irin haka ne manyan ƙasashe,

    Da ke amo kowane sashe,

    Na duniya suka yi koyaushe,

    Al’umarsu take ta shewa.

     

    21. Ba su barin azzalumina,

    Sun taushe maciya amana,

    Ba sa ƙyashin ikhiwana,

    Cima gabansu suke biɗowa.

     

    22. Dubi yawan jama’a ta Caina,

    Sun haɗa kai babu hiyana,

    Sun aiki a dare da rana,

    Yau kayansu muke shigowa.

     

    23. Turawa haka sunka dage,

    Duk aiki nasu babu coge,

    Cin rashawa duk sunka toge,

    Ba sa yin sa suna ƙiyawa.

     

    24. Don haka ne duk al’umarsu,

    Tai bunƙasa arziƙinsu,

    Yai albarka kowanensu,

    Na fahari da abin da kewa.

     

    25. Mu ma dole mu ɗaura niyya,

    Yin aiki ja mui gamayya,

    Kowa ya zo yara da manya,

    Mu ɗau rashawa izuwa kushewa.

     

    26. Niyya ƙwaƙƙwara mu ɗaura,

    Don yaƙar duk asharara,

    Masu zagon ƙasa masu ƙera,

    Turakun ci bayan da kewa.

     

    27. Ba wasu ne maciya amana,

    Ga dukiya ta ƙasa su danna,

    Wasoso sun ƙi su daina,

    Ha’intar mu suna ta yowa.

     

    28. Ƙaunar ƙasa ta zamo gabanmu,

    Don bunƙasar arziƙinmu,

    Da ci gaban duk jama’armu,

    Alheri ya isar wa kowa.

     

    29. Lallai mu so wa ɗan uwanmu,

    Abin da muke ƙauna ga kanmu,

    Ko ma mu fifita shi kanmu,

    Babu ganin ƙyashi da rowa.

     

    30. Doka mai tsanani a yo ta,

    Kan rashawa duk masu yin ta,

    A kame don sun yo mugunta,

    A kai wa Yari ya zam tsarewa.

     

    31. A nusarshe da dukan mutane,

    Munin aikin don su gane,

    Su ƙyamaci mai yi ko wane ne,

    Don ba son mu yake yiwowa.

     

    32. Azzalumai ku mu yo rahoto,

    Zuwa hukuma don a ƙwato,

    Haƙƙoƙi kowane loto,

    Ba tsoro ko razanewa.

     

    33. Mutum ne zai tono masifa,

    Ba shi ɗai ne za ta shafa,

    Har kowa dole mu dafa,

    Ɓarnatai mu zamo hanawa.

     

    34. Cin rashawa ke sa talauci,

    Aikin ɓarna ya yi kauci,

    Duk lamura saura su ɓaci,

    Dole mu yaƙar ba gazawa.

     

    35. Aikin kowa ne da kowa,

    Hukumomi ku mu tallafa wa,

    Domin ƙasarmu ta zamowa,

    Abar fahari ba ha’inawa.

     

    36. Hukumomin jin ƙorafinmu,

    Sun tsaye domin taimakon mu,

    Yaƙar kaskar da ka cin mu,

    Cima gabanmu suna hanawa.

     

    37. Mu roƙi Allah taimakonsa,

    Kan yaƙi bisa ‘yan ta’asa,

    Masu ciye rashawa su ƙosa,

    Da ha’inai ‘yan handamewa.

     

    38. Allah ba mu yawan ƙana’a,

    Ƙaunar juna da muru’a,

    Cin rashawa mu yi mai bara’a,

    Don Manzo ɗan Hashimawa.

     

    39. Nasiru G. Ahmad ya yi ta,

    Don harkar rashawa mu bar ta,

    Mu soyi juna mu rabauta,

    Halinmu ya zamo yabawa.

     

    40. Goma huɗu baitinta jumla,

    Ce Arba’in na gode Allah,

    Allah tsare mu biye ralala,

    Amin sarki mai iyawa.

     

    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Masha-Jini

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Masha-Jini

    Waƙa Mai Taken Masha-Jini

    1. Allah ba ni buɗi in yi tsari na baituka,
    A kan ƙwaro wanda bai da tausai a duniya.

    2. Ƙwaron da yakan cutar da manya da ƙanƙana,
    Mai shanye jini na ɗan Adam ba shi tausaya.

    3. Gwanin zilliya yake da ɓoyo jikin tufa,
    Ko gashi na kai ya zam shi birni ya wataya.

    4. Gudun kar ku ƙosa Kwarkata ce nake nufi,
    Bai ƙyale baƙar fata fara ko ko rawaya.

    5. Abin da kan samar ta ƙazanta ce Lamba Wan,
    Haɗewar zufar jiki da dauɗa annakiya.

    6. Da wannan haɗi Allah kan samar da kwarkwata,
    Ta rayu tufar mutum gashin kansa kulliya.

    7. Tana sanya ƙwai ta ƙyanƙyashe shi da hanzari,
    Su zamto yawaita ɓamɓare ta akwai wuya.

    8. Abinci nasu jinin mutum za su yi ta sha,
    Ya kasa sukuni a dare ko ko safiya.

    9. Hanyar yaɗuwa tata kusantar jikin mutum,
    Da ya zam yana ɗauke da ta ko da sau ɗaya.

    10. Ko ko sanya rigarsa hula ko ko fattala,
    Hakan nan kwana da mai ita gun ɗaki ɗaya..

    11. Idan har ta samu sai a wanke dukan jiki,
    Da ruwa na kogi “Ma’ul Khalli” a gauraya.

    12. Mutum kan yi kwarkwata ba don ba shi tsaftace,
    Jikinsa sai Ibtila cire ta akwai wuya.

    13. Misali mutum Biyu cikin wanda anka wa,
    Busharar shiga Aljanna tun nan a duniya.

    14. Abdurrahamani Auf Sahabi attajiri,
    Zubairu ɗan Awwamu Sahabi abin biya.

    15. Allah ya jarabce su da ƙwaron ga kwarkwata,
    Tufarsu da gashin kai dare har da safiya.

    16. Har Manzo ya sauƙaƙa gare su halal yake,
    Rigar Alharini sunka sanya ta duniya.

    17. Hakan nan a Hajji ya halatta su aske kai,
    Su bayar da fiddiya ga nassin Ƙur’aniya.

    18. Dalili na Ukku nan ga samo na kwarkwata,
    Azaba ga kafirai su komo ga shiriya.

    19. Misali Fir’auna lokacin da ya kangare,
    Da shi da mutanensa ɓarna sun yi dulmiya.

    20. Aazabobin gargaɗi da anka saukar musu,
    Ciki har da kwarkwata jikinsu tufafiya.

    21. Har sai da sukai roƙon a janye ta za su bi,
    Musa Annabi ya roƙi Allah ta zam tsaya.

    22. Akwai wanda kwarkwata ba sa yin ta ko kaɗan,
    Luɗufi na Allah ne gare shi a duniya.

    23. Shi ne mai kuturta wanda ta ci yatsu nasa,
    Da ba yatsan kama ta gare shi ko da ɗaya.

    24. Ba a cin ta kwarkwata ƙwaro ne masha jini,
    Jini ko haramun ne umarnin kitabiya.

    25. Hakan nan abinci in ta faɗa ciki nasa,
    Ita da Kuɗin cizo barin cin sa lafiya.

    26. Jininta jikin tufar mai salla an sahhale,
    Ba ya ɓata salla ta dare ko ta safiya.

    27. Haka ma kashe ta nan a salla abin bari,
    Sai dai binne ta ka so ko ƙyale ta bai ɗaya.

    28. Ba a son a kamo ta a jefar abin ƙiya,
    Domin kar jikin wani ta hau tai ta wataya.

    29. Muna roƙon Allahu ya ƙare mu lafiya,
    Ya ije dukkan cuta gare mu baki ɗaya.

    30. Alfarmar Alƙur’ani da Sidi Muhammadu,
    Da an ba wa cetonmu a rana ta tambaya.

    31. A nan zan taƙaita ɗan bayanin da na shira,
    A kan kwarkwata masha jini babu tausaya.

    32. Sunana Muhammad Nasiru Garba Ahmadu,
    Almajir da ke biɗar sani kar ya sulmiya.

    33. Baitoci Talatin ne da Ukku ran Litinin,
    Alfaini da Isshirin Agusta yai gomiya.

    Alhamdu lillahi

    Karanta  Waƙa Mai Taken Nagartaccen Jagora

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Nagartaccen Jagora

    Waƙa Mai Taken Nagartaccen Jagora

    1. Da sunan Rabbana Karimi sarki guda,
    Da ke bayar da ɗaukaka daji ko gida,
    Da ya aiko wa duniya Ɗaha Muhammada,
    Da ya ɗora mu kan tafarki mara gargada.

    2. Baitoci ne nake nufin yi don shugaba,
    Babban masani kama tai ba a yi shi ba,
    Bai yarda a bar talakka halin ni-‘yasu ba,
    Bai mallaki duniya da ya bar bayansa ba.

    3. Shi ne ya zamo mujahidi rai ya ba da shi,
    Shi yat tari duk aradu ta faɗa kai nashi,
    Shi yai tsayuwar talakka komai a yiwo da shi,
    Shi yaj ja rundunar adalci a tsayar da shi.

    4. Ya samu amintatar dukan ‘yan Nijeriya
    Ya zam sane duk ƙasa Kudunta da Shimaliya,
    Ya zam jigo ƙasa da shi ne aka fariya,
    Ya rungumi duk talakka bai yarda da wariya.

    5. Na san wasu sun zaƙu shin waye a faɗa mana,
    Nagartaccen mutum nufina ba tsokana,
    Najeriya shi yake da siffar da na bayyana,
    Nasara garai suna da shayi har razana.

    6. Aminu Kano nake nufi ya san shari’a,
    Aikin da ya yi kawar da zaluntar jama’a,
    A neman ‘yantuwar ƙasa ya yi mubaya’a,
    A mulkin mallakar da Turai suka ɗabba’a.

    7. Mulkin mulaka’u sunka yaƙa da akai mamu,
    Mulkin kai sunka tabbatar ya samu ga mu,
    Mulki ya zamo ga ‘yan ƙasa don hidima wa mu,
    Mulki na Nasara ya tafi sai murna ga mu.

    8. Malam burinsa adalanci ba taƙama,
    Mai son a kawar da ɓangaranci ba haɗɗama,
    Mai son talaka ya tsira cuta bisa haƙƙuna,
    Maza mata lallai mu waye ba riggima.

    9. Ba za a yiwo batun siyasa ba a sa shi ba,
    Batun ‘yancin talakka malam na kan gaba,
    Ba za a faɗi gwagwarmayar haƙƙu a bar shi ba,
    Bangon talaka na jingina ban ga kamar sa ba.

    10. Bisa haka NEPU sun kafa haƙƙi don a bi,
    Biɗar talaka ya walwala babu tararrabi,
    Bisa haka sun wahaltu ɗauri kuwa bi da bi,
    Bi hamdillahi sun nasartu bisa martabi.

    11. Jamhuriya fari sun tsayu an ja sunka ja,
    Jan aiki ne sukai na sai da rayi ba amaja,
    Jari nasu lafiya da kutsen dukkan luja,
    Jama’a sun samu horuwa daga duk a ja.

    12. Karo na biyun jamhuriya an san ɗaukaka,
    Kafon P.R.P. jam’iya an tsayuwar daka,
    Karantarwar Aminu ta ratsa dawa ɗaka,
    Kano da Kaduna sun shiga tutar talaka.

    13. Haraji anka soke karɓar sa a nan jiha,
    Hakan nan jangali ka soke shi ba raha,
    Haƙiƙa talakanmu ya ‘yantu ya farraha,
    Harkoki sun yi kyautuwa don an sarraha.

    14. Malam ya kutsa takara an yi arangama,
    Matakin shugaban ƙasa yab biɗi yaz zama,
    Mai ba da abin Ilahu bai so bisa hikkima,
    Masoya nasa ya kafa manya sun zama.

    15, Fa mulkin lokacin Gawan soja da an kafa,
    Fahimtar daraja ta Malam mai falsafa,
    Fa an zaɓar Minista aiki ya yi kaifafa,
    Farar aniyarsa ta fito ta shiga duk kafa.

    16. Sanin haƙƙin nisa’u mata ɗan “ب” ya sa,
    Sahun farko biɗa ga haƙƙinsu shi ka sa,
    Samun ‘yanci na walwalarsu Malam ya sa,
    Saka su a gwamnati da saurran aikin ƙasa.

    17. Gogaggen malamin siyasa bai zam rago,
    Goran ƙarfe fagen sani maliya bai shigo,
    Goni a kitabu har da sunna kan ɓuɓɓugo,
    Goman fanni dubunsa Malam ba ya tago.

    18. Sun ɗaukaka ɗaliban da ya zam koyar da su,
    Sukul fannin siyasa sun zamto ba ya su,
    Su ne hulafa’u nasa har gobe muna da su,
    Sunansu ba zan kira al’umma ta san da su.

    19. Aminu Kano mutum da bai ƙyamar jama’a,
    Abin hannunsa bai bari sai ya wazza’a,
    Abin koyi tawali’u ga shi da ƙanna’a,
    Allahu Gwani ka tausasa mar mun addu’a.

    20. Lamarin harkar siyasa yau an sa ƙin kula,
    Lallai shiriyar Aminu in mun bi a hankala,
    Lagon matsalar da ke ciki har duka mushkila,
    Labari zai zamo gaba sai yin hamdala.

    21. Allahu ka kyautata makwancin mai jama’a,
    Aminu Kano garai rahama taka wassa’a,
    Aljanna ka sa ta zam gare shi ran Waƙi’a,
    Albarkar  Musɗafa ka tashe shi da fara’a.

    22. Nasir Ahmad ya yi ba a san ni ba ko’ina,
    Na dai zam mai biɗar sani ilmu na shinshina,
    Na gaishe da dukka kowa nai jinjina,
    Nai roƙo ga Rabbana ba mu yawan shina.

    Alhamdu lillahi.

    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Kowa Ya Bar Gida…
    Edita@rumasau-kallamu

     

     

  • Waƙa Mai Taken Kowa Ya Bar Gida…

    Waƙa Mai Taken Kowa Ya Bar Gida…

    1. Suna na Allah farawa,

    Baiwarsa mun yo godewa,

    Yawan salati ƙarawa,

    Wajen Rasulu abin kewa,

    Gare mu ba ma fasawa.

    2. Batu nake son saƙawa,

    Kan duniyarmu ta Hausawa,

    Da ba shi kyautu mu mantawa,

    Tadarmu mai kyau da daɗewa,

    Da ayyukanmu na kyautawa.

    3. Sunanmu ya tafi nesawa,

    Da kyan halinmu na yabawa,

    Aikin fasaha da ƙwarewa,

    Abin amana mu tsarewa,

    Da gaskiya ba sauyawa.

    4. Tsarin shigarmu gwanin ƙawa,

    Da kwarjini ba kushewa,

    Kowa ya gan mu yana shawa,

    Duk duniya tai shaidawa,

    Kyawun ɗabi’un Hausawa.

     

    5. Tsarin sarautun mulkawa,

    Mun yi fice mun tserewa,

    Mun gaji wannan da daɗewa,

    Har yau muna ta kiyayewa,

    Don kar su zam salwancewa.

    6. Zumuntaka mai ɗorewa,

    Haƙƙin zumunci sadawa,

    Ƙauna ga juna aikawa,

    Kullum muna sabuntawa,

    Da ƙin zumunci yankewa.

     

    7. Mun yi fice gun kyauta wa,

    Dukkan maƙwabta ba rowa,

    ‘Ya’yanmu duk babu rabewa,

    Tare muke tarbiyyarwa,

    Sashensu ba fifitawa.

    8. Kowa yana da abin yowa,

    Yara ga tarbiyyantarwa,

    Ba ware Bora ko Mowa,

    Babu batun wannan nawa,

    Don me ka bi shi ka mar tsawa?

     

    9. Kowa sana’a ka riƙewa,

    Don al’uma amfanawa,

    Mu ke saƙa tufar sawa,

    Mu zam rina ta ta yi ƙawa,

    Kafin mu kai ta ga ɗinkawa.

    10. Mu jeme fata tsafcewa,

    Mu yo jaka takalmawa,

    Taiki Kube da Zabirawa,

    Har da su Banten ɗaurawa,

    Domin mu kare tsiraicewa.

     

    11. Abinci mu ke nomawa,

    Mu taskace mai saidawa,

    Kowa ya ƙoshi ba yunwa,

    Nama muna kiwantawa,

    Muna fita mu farautowa.

    12. Ba mai zama haka Hausawa,

    Kowa sana’a tai kewa,

    Zama na banza ba maiwa,

    Wanda ya ɗau sangarcewa,

    Ba zai yi matar aurawa.!

     

    13. Zaman iyalinmu da ƙawa,

    Kwai disfilin adaltawa,

    Yara ba a bambancewa,

    Ɗan kishiya ma ka riƙewa,

    Tamkar uwar da ta haifawa.

    14. Akwai haɗin kai da gamewa,

    Idan larura ta zo wa,

    Wani guda ba kasawa,

    Taro ake don a kawarwa,

    Cike da ƙauna tausawa.

     

    15. Yara biyayya sunke wa,

    Duk babbuna babu rabewa,

    Yi na yi bar shi su dainawa,

    Su kuwa manya tausawa,

    Ga yara sunka zamo yowa.

    16. Kaɗan na yo lissafawa,

    Na kyan zamewar Hausawa,

    Da munka gada da daɗewa,

    Da ya wajabtu mu danƙewa,

    Domin na baya su tararwa.

     

    17. Abin takaici da ƙiyawa,

    Halin ga ‘yan yau ka gujewa,

    Na martabarmu ta nunawa,

    Don taƙamar sun wayewa,

    Hanyar ba za tai ɓullewa.

    18. Dolenmu mui jajircewa,

    Ga raya tada mu riƙewa,

    Shi ne tafarkin burgewa,

    Kayan aro mu yi watsarwa,

    Don katara ba shi rufewa.

     

    21. Allah ka ba mu amincewa,

    A nan da ranar komawa,

    Duk laifukanmu ka yafewa,

    Don Musɗafa mai shiryarwa,

    Manzo da ka zam aikowa.

    22. Nasiru G. suna nawa,

    Ɗan Ahmad babu musawa,

    Birnin Kano na zamtowa,

    Nai shukura na yi daɗawa,

    Waƙar a nan ta yi tuƙewa.

    Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafin TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad Ya wallafa.

    Karanta Waƙa Mai Taken Ɗan Achaɓa

     

  • Waƙa Mai Taken Ɗan Achaɓa

    Waƙa Mai Taken Ɗan Achaɓa

    1. Salamu Alaikumu barka da yanzu,
    Gaishe ku nake da fatan za ku karɓa.
    2. Batu zan yo da fatan za ku so shi,
    A kan goganku wato Ɗan Acaɓa.
    3. Mutum mai taimakon jama’a a kullum,
    Cikin sanyi da rana har da raɓa.
    4. Da yin asuba ka leƙo za ka gan shi,
    Da rana haka dare kwai Ɗan Acaɓa.
    5. Idan tafiya ta kama za ka yi ta,
    Cikin sauri ka nemo Ɗan Acaɓa.
    6. Wuri in ya zamo nisa da titi,
    Shigar sa mutum guda ne Ɗan Acaɓa.
    7. Idan hanya ta zam mai “go slow” ce,
    Idan sauri kake ɗau Ɗan Acaɓa.
    8. Shi ne zai kai ka kai gararin gabanka,
    Ya mai da ka idan haka nan ka zaɓa.
    9. Mutum ɗaya har biyu ɗauka yake yi,
    Ya kai ya zube ya juyo Ɗan Acaɓa.
    10. Tsananin sanyi ba ya hana ɗan acaɓa,
    Tsakar rana ruwan sama za ya caɓa.
    11. Akan jinga da shi a biya shi mako,
    Ko ko a wata in ya cika sai ya karɓa.
    12. Kamar yara ya kai su ga makaranta,
    Uba ko wuri na aiki ba shi saɓa.
    13. Wannan su ne wasu daga fa’idoji,
    Na wannan taliki mai yin acaɓa.
    14. Akwai kuma aibuka jingim gare shi,
    A muninsu da wari sun fi jaɓa.
    15. Masifar son kuɗi Jimina kira shi,
    Kai ya fi makauniya nema a caɓa.
    16. Bai ɗau rai nasa komai ba bare ma,
    Na fasinjansa goga Ɗan Acaɓa.
    17. Tafiyar hauka da ganganci gare shi,
    Dukan runtsi ya je sai ya laɓaɓa.
    18. Sanin doka ta hanya ba ruwansa,
    “Shiga a haka” yake yi Ɗan Acavɓa.
    19. Shigarsa kwana ƙafa tai za ya harba,
    Siginar ya ciccire domin a kwaɓa.
    20. Mota ƙarama da bas har gingimari,
     Ratsa su yake gaba-gaɗi mai acaɓa.
    21. Burinsa kawai ya kai fasinja nasa,
    Ya karɓi kuɗin ya ɗau wani mai acaɓa.
    22. Idan ya yi ma karo babur ya lotse,
    Taron dangi suke maka ‘yan acaɓa.
    23. “Ɗan uwa namu ka cuta ba mu yarda,
    Biya za kai asara ba mu karɓa!
    24. “Domin ba nasa ne ba wanga babur,
    “Waninsa ka mallaka shi ko acaɓa.”
    25. Ɗaruwwan famfamai kullum ka samu,
    Biyansa balas a nan ne za a saɓa.
    26. Tun kan ranar yake ta cika ya batse,
    Ganin ƙyashi yake yi Ɗan Acaɓa.
    27. “Mutum na zaune ni ko ga ni rana,
    Ina nema shi ko sai dai ya karɓa!
    28. “Tsananin sanyin Disamba duk a kaina,
    Ya ƙare ni ka yin aikin acaɓa.
    29. “Wannan ɗanyen hukunci ba ni yarda,
    Kura a buga kuɗin gardi ya karɓa!!”
    30. Da ya ɗan fara zowa sai ya noƙe,
    Ku ɗaura burum-burum ho Ɗan Acaɓa!
    31. Ya ɗauke wuta wata har sai ya shuɗe,
    Bai zo da balas ba goga mai Acaɓa!
    32. Idan ko an yi sa’a zai ta kai wa,
    Zuwa wasu ‘yan watanni ba shi saɓa.
    33. Daga nan babur yakan ce ya yi tsufa,
    A sayar a sayo wani don yai Acaɓa.
    34. Idan har ka ƙiya wani za ya nema,
    Ya aje ma naka sabo za ya karɓa.
    35. Ka nemi sayar da shi in an taya ma,
    Abin ba kyau gumi za kai ta sharɓa.
    36. Wannan halinsu kenan aksarinsu,
    Marasa kishi na zuci ‘yan a kwaɓa.
    37. Amma fa akwai nagartattu cikinsu,
    Da ke neman halal hanyar acaɓa.
    38. Tuƙin nutsuwa sanin doka ta hanya,
    Abin da ka ba shi duk shi za ya karɓa.
    39. Ba ya wasa da kai haƙƙi na babur,
    Wurin mai shi amintaccen acaɓa.
    40. Albarka Rabbana kan sa wa wannan,
    Cikin samun da zai hanyar Acaɓa.
    41. Idan ka tashi neman Ɗan acaɓa,
    Mutum mai hankali nutsuwa ka zaɓa.
    42. Guji mai karkacewa in ya zauna,
    Ya sa hana-salla ɗan gararin acaɓa.
    43. Idonai ya rufe da baƙin gilashi,
    Danja ko ta tsayar shi za ya raɓa.
    44. Takensu irin waɗannan “Sai ka kai shi!”
    “Ko ba rai!” za ya amsa Ɗan Acaɓa.
    45. Muna roƙon ka Allah taimake mu,
    Ka sa gyara cikin sana’ar Acaɓa.
    46. Gwamnati dole ta yo wani agaji kai,
    Domin samun rage haɗuran acaɓa.
    47. Haka su ma masu babur kar su ba da,
    Sai ga mai nutsuwa da zai aikin Acaɓa.
    48. A nan zan dakata sai an jimanku,
    Salamu Alaikumu har Ɗan Acaɓa.
    49. Muhammadu Nasiru G. Ahmadu ne,
    Ya yo waƙar bayanin Ɗan Acaɓa.
    50. Baiti Ashirin biyu daɗa goma kansu,
    Hamsin ke nan a kan sana’ar Acaɓa.
    Alhamdu Lillah.
    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Alƙawari Kaya
    Edita@rumasau-kallamu
  • Waƙa Mai Taken Alƙawari Kaya

    Waƙa Mai Taken Alƙawari Kaya

    1. Sunanka farko ya Allah,

    Tsira amincinka Allah,

    Ƙara su gun Manzon Allah,

    Shi munka burin mui kalla,

    Ko da cikinsa mafarkinmu.

     

    1. Yau damuwa ce ke raina,

    Bisa batu da muke raina,

    Cikin darenmu ko rana,

    Son rai gare mu abin ƙauna,

    Kan dukkanin harkokinmu.

    1. Cika shi alƙawari sunna,

    Ga dukka manya da ƙanana,

    Saɓa shi ko aikin ɓarna,

    Da Rabbi sarki ya yi hana,

    Ga duk maza har matanmu.

    1. Muna barin sa umarnin nan,

    Na Rabbana da ya yo ɗin nan,

    Ayar cikin Qur’anin nan,

    “Ku zam cika alƙawarin nan,

    Don za a tambayi shi” gun mu.

     

    1. “Ya muminai shin mis sa ne,

    Kuke batu” a tsaye zaune,

    “Da ba ku yin sa a aiki ne?”

    Faɗin Ta’ala sarki ne,

    Gare mu kan hali namu.

     

    1. Abin takaici mun ƙyale,

    Wannan umarni sai hole,

    Ran tambaya ba ma kalle,

    Halinmu ba kyawu walle,

    Don babu alƙawari gunmu.

     

    1. Alƙawari in mun ɗauka,

    Na lokaci kan duk harka,

    Ko yin wani aiki gun ka,

    Ni kam gaske nake ɗauka,

    Amma cikawa bai samu.

     

    1. Murna muke in mun saɓa,

    Muna ganin ai mun caɓa,

    Har jinjina muka zam karɓa,

    Kuka ya dace mui sharɓa,

    Don ya  ƙazanta aikinmu.

     

    1. Ga ‘yan siyasa ko ado ne,

    Suna ganin mai sauƙi ne,

    Hanyar zuwa ga muradi ne,

    Bayan guba mai halaka ne,

    Gare su har umma tamu.

     

    1. Babu dalilin saɓawa,

    Sai don mugunta aikawa,

    Nuna isa ko burgewa,

    Ko sakaci ga mutuntawa,

    Da munka yi bisa zatinmu.

     

    1. Ƙarfe goma ka ce zan zo,

    Ko ko ka ce wa wane ya zo,

    Ba kai shiri goman ta zo,

    Sai uzuri ba yin ƙwazo,

    Ba ka nadama ko damu.

     

    1. Ka ce wa yaro bar kuka,

    Abu kaza ne zan ba ka,

    Alƙawari ne ka ɗauka,

    Amma ka saɓa wa ɗanka,

    Ka muna tarbiyyar ɗanmu.

     

    1. Wannan fa mugun hali ne,

    Amma gare mu abin so ne,

    Da takamar mun burge ne,

    Bayan ko laifi babba ne,

    Za ai hisabin sa kanmu.

     

    1. Bai zam cikar addini ba,

    Bai zam shi halin kirki ba,

    Bai zam abin tunƙaho ba,

    Bai zam cika ga kamala ba,

    Saba wa alkawari namu.

     

    1. In ka tsananta ga cikawa,

    Ka ƙyamaci a yi saɓawa,

    Wai ka yi halin Turawa,

    Halinka na da tsanantawa,

    Don ka ƙi mugun halinmu.

     

    1. Faɗa a cika dattaku ne,

    Ko da ko mai yin yaro ne,

    Ko a ina mai ƙima ne,

    Abin a ba wa aminci ne,

    Mai martaba gun sarkinmu.

     

    1. Da mu ya dace ai koyi.

    Ya zam gare mu abin ya yi,

    A zahiri da cikin rayi,

    Mun bar Nasara kaɗai ke yi,

    Mun zaɓi ɗaukar son ranmu.

     

    1. Wannan abin jin kunya ne,

    Gare mu babban aibu ne,

    Abin ragewar ƙima ne,

    Da za mu taru mu gaggane,

    Da sun yi kyau harkokinmu.

     

    1. Tsari rashin sa ka damun mu,

    Na lokutan harkokinmu,

    Loto abin banza gunmu,

    Shi ne ko ai rayo tamu,

    In ya wuce bai komen mu.

     

    1. Faɗa a saɓa laifi ne,

    Loto a sauya aibu ne,

    Warware zance nakasa ne,

    Kin cika kawari sabo ne,

    Mu zam cire shi a halinmu.

     

    1. Shi alƙawar ai kaya ne,

    Bisa ga kai nannauya ne,

    Kula da shi imani ne,

    Cika shi aikin lada ne,

    Mai nauyaya mizaninmu.

     

    1. Allah ya ba mu dukan dace,

    Mu’amalarmu ta zam tsafce,

    Ta zam gudana dinance,

    Yara su koya su gwanance,

    Su zam du’a’i bayanmu.

     

    1. Nan zan tsaya na ciyo burki,

    Tabara ba mu yawan ɗauki,

    Mu tabbata a halin kirki,

    Kullum bisa dukka mataki,

    Na rayuwa har ƙarshenmu.

     

    1. Mai tsara waƙar Nasir ne

    Ahmad rarrauna ne,

    Gare mu mai yin addu’a ne,

    Bisa ga kyautata hali ne,

    A dukka alƙawarorinmu.

    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Haƙƙin Dabbobi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙar Neman Mafita Da Riba Babba

    Waƙar Neman Mafita Da Riba Babba

    1. Allah sarki ne mai yawaita

    Falala da tsari da kyauta

    Bismillah zan karanta

    Waƙar mafita da riba

    2. Zamanin nan ya ƙazanta

    Lamurra duk sun jirwanta

    Ayyuka da halin mugunta

    Ga cin amana bai tsaya ba.

    3.  Garkuwa don kuɗi da sata

    Ga yawan fyaɗe da ƙeta

    Ga rashin ladabin ‘yammata

    Duk ba zai mana mafita ba.

    4. Tur da sauyi maras nagarta

    Mai ɗorawa mutum kurumta

    Ayyukan sharri ko mugunta

    Mance Allah ba zai mana ƙa’ida ba

     

    5. Son kuɗi duk ya tsananta

    Burin kowa ya huta

    Da kuɗi mata da mota

    Babu cas, ko as dat ta’abba.

     

    6. Shi yasa ayyukan mugunta

    Munana, masu raba zumunta

    Ayyuka na rashin aminta

    Sun yawaita ba ma huta ba.

     

    7. Ga uwa ta saida ɗanta

    Ga uba ya haiƙewa ‘ƴar ta

    Ga ɗa yay fansa da wauta

    Ya subhanallahi ka tsare mu gaba

     

    8. Ran Hanan dai ya salwanta

    Malaminta ya ha’inta

    Ya aikata abin mugunta

    Aikin sa gareshi babu riba

     

    9. Aisha mai kasshe kanta

    Wani jami’i shi yai lahanta

    Cin zarafi mai muni na mata

    A zamanin nan ana yi ba da ƙa’ida ba

     

    10. Shugabanni da halin mugunta

    An sa talaka yana ragaita

    Daɗin haraji, tsada, duk an azabta

    Janye tallafin mai ba abu ne mai kyau ba

     

    11. Masu tsafi kun ƙazanta

    Masu caca kuna da wauta

    Luɗu da cin zali duk sun haramta

    Wanda duk bai bi Allah ba ba zai zauna lafiya ba

     

    12. Yau fasadi ya inganta

    Mai bin shaiɗan zai kafirta

    Ayyukan sa duk sun muzanta

    Annabin Allah ya hane mu da cin riba

     

    13. Masu shirka sun yawaita

    Masu kiran haram saboda wauta

    Ayyukan gaskiya ya ƙaranta

    Lalle masifa a duniya ba ta gushe ba

     

    14. A yau ƙarya ita ce mai tsafta

    Wasu ma sun ƙware a kanta

    Samun kuɗin su shi ne mafitta

    Ai kuwa hakan ba abu ne mai kyau ba

    15. Aikin ‘yan ta’adda ya ƙazanta

    Zubar jini a yankin mu ya yawaita

    Asalinsu akwai cin hanci da ƙeta

    Jami’ai masu cin amana ƙarshensu ba zai yi kyau ba

     

    16. ‘Ƴan siyasa ya kuke ta

    Yaudarar talaka da sata

    Kun hana arziƙi ya wadata

    Kawunan ku kuke so ba talaka mai wahala ba

     

    17. Ya kamata fa mu fahimta

    Arziƙi ko da ya tsananta

    Ko talauci in ya rabanta

    Ga bawa ƙaddara ce wadda ba a guje ba

     

    18. Tun gabannin yin halitta

    Rabbuna Allah ya hukunta

    Arziƙin ɗa, bawa ko jarrabta

    Duk abinda mutum zai yi ba zai keta ƙa’ida ba

     

    19. Yanzu menene mafitta?

    Ga zukata sun firgitta

    Rashin natsuwa ya yawaita

    Duk abinda mutum zai yi ba zai sake ba

     

    20. Fahimtata a rayuwa ta

    Sai mun sauya jigon nagarta

    Sai mun rage raɗaɗen masu jinta

    Sai muso juna da alheri banda gaba

     

    21. Jama’ar mu akwai nagarta

    A basu ilimi shi na fahimta

    Zai kawar da talauci mai kanta

    Duk mai aiki da hikima ba zai sha wuya ba

     

    22. Ilimi mai sa nagarta

    Mai gyara ayyuka da fahimta

    Jahilci kuwa idan ya yi kanta

    Dole ayyukan jama’a ba za su yi kyau ba

     

    23. Tarbiyya ko mafi inganta

    Turbar Islama binta

    Ba fasadi babu cuta

    Komai aka mayar ga Allah ba zai zama mai wuya ba

     

    24. Ladabi abu mai kyau ga mata

    Rufe tsiraicin su za su kuɓuta

    Bin iyaye da magabata

    Barin fariya, yin ɗagawa abu ne ba mai kyau ga lahira ba

     

    25. A koyar da yara jarumta

    Aiki tuƙuru shi ne za a huta

    Lalaci, sakaci ko sata

    Ayyuka ne haramtattu da ba za a yi su da ƙa’ida ba.

     

    26. Mu kalli Japan, Sin da Kolkata

    Matasa na fafutika, kai hatta

    Yara ƙananu da mata

    Kowa na son ceton ƙasarsa ba cutar da ita ba

     

    27. Neman halak abu ne mai tsafta

    Mai gyara ƙasa da zukata

    Idan zukata suka ladabta

    Ayyukan bayi da dama ba za su ƙetare ƙa’ida ba

     

    28. Wajibi zalinci ya huta

    Adalci shi ake buƙata

    Tsayar da haddi ga masu gata

    Matsawar kuɗi suka rinjayi adalci ba za mu zauna lafiya ba

     

    29. Ya Allah ka ba mu mafitta

    Ya Rahmanu sarkin Nagarta

    Ya man iza da aka fa ajibta

    Ya Laɗifu ka yaye mana  rashin aminci da gaba

     

    30. Ni Sadiq Gwarzo na yawaita

    Damuwa shi yasa na rubuta

    Waƙar ina kewa da buƙata

    Ina adduar samun tsira da rabo babba.

    ALHAMDULLAHI

    Karanta Tarihin Garin Rimin Gado

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Rabbi Kare Min Mijina

    Waƙa Mai Taken Rabbi Kare Min Mijina

    Rabbi kare min mijina

    Abin kirana farin ciki na

     

    1. Ni ina sonsa sahibina

    Shi nake so nake wa ƙauna

    Shi yake sanya murmushi na

    Shi yake yaayen fushi na

    Shi nake yi wa kwalliya ta

    Ina adon gyara fuskata

    Na sanya kwallin idaniyata

    Na fesa ƙamshi ga suttura ta….

    Rabbi kare min mijina!!!

    Rabbi amsa min kira na!!!

    Rabbi kare min mijina!!!

     

    2. Ni a guna sam bai da tamka

    Duk sirrikana shi za su riska

    Da nay fushi, in ya zo na sauka

    Hidimtakarsa ke sani kuka

    Ya abin so farin cikina

    Na mallaka maka dukka kaina

    Ina ƙaunar ka dare da Rana

    Ina yawan sonka sahibiyna…

    Abin kirana farin ciki naaaa!!!

    Rabbi kare min mijinaaa

    Abin kirana farin ciki naaa

     

    3. Yau da kullum na ayyukansa

    Hawa da sauka a lamurransa

    Yana cikin sauke haƙƙunan sa

    Yana yawan bani lokacin sa

    Shi ya sanya nake ta son sa

    Ina ta Rama don ambaton sa

    Ina shirin kare lafiyar sa

    Ina nufin na zama garkuwar sa…

    Haba masoyi ka ceci raina!!!

    Rabbi amsa min kira na!!!

    Rabbi kare min mijina!!!

     

    4. Son ka ya keta zuciya ta

    Yayi cafkar idaniya ta

    Yana ta yawo a jijiya ta

    Son ka shineee Rayuwa ta

    Zan biyayya a lamuranka

    Zan yi tamkar Sa ɗakar ka

    Zan duƙursawa zantukan ka

    Za ni girmama ‘ƴan uwan ka…

    Ni ina sonka ya miji na..

    Rabbi kare min mijina

    Abin kira na Farin cikina 

     

    5. Shi ne mijina farin ciki na

    Shi ne yake gyara laifuka na

    Shi ne yake saita lammura na

    Shi ne yake ɓoye kuskure na

    Bautar sa Bautar Ubangiji ne

    Fushin sa wannan abin gudu ne

    Ka ɓata rai ko na yo kure ne

    Haba masoyi, rashin sani ne..

    Ka ceci raina, ya kai mijina!!!

    Ni ina son masoyiyata

    Son ki ke mulka zuciya ta.

    haƙƙin mallaka @Sadiq Tukur Gwarzo

    Danna nan don karanta Tarihin Garin Rimin Gado

    Edita@rumasau-kallamu