Category: Waƙa

  • Waƙa Mai Taken Haƙƙin Dabbobi

    Waƙa Mai Taken Haƙƙin Dabbobi

    1. Muna godiya ga jalla sarki Rahimuna,
    Da ya horace mana halittunsa bai ɗaya.
    2. Ya fifita ɗan Adam bisa dukka talikai,
    Na kogi tudu da masu tashi samaniya.

    3. Salati gurin Muhamman da ya zamo,
    Mai jinƙai da tausayi ga kowa a duniya.
    4. Salamu Alaikumu zumaina ina kuke?
    Batu zan yi kan hali na zulmu ga khalƙiya.
    5. Dabbobi nake nufi da tsuntsaye wanda ke,
    Zaman rayuwa cikinmu yamma da safiya.
    6. Allah ya huwace su gare mu mu mallaka,
    Mu turke mu garkace nau’i ne na dukiya.
    7. Wasunsu kayanmu munka lafta bisa nasu,
    Mai nauyi su kai wuri mai nisa na nahiya.

    8. Wasunsu Allahu ya ce mu ci su ne,
    Mu yanka da sunansa a gyare mu sha miya.
    9. Wasunsu har gonaki mukan sa su ayyuka,
    Na noma da huɗa duk buƙatunmu sun biya.
    10. Wasunsu don sha’awa muke kiwatar su ne,
    Ganin su ke ba mu jin nishaɗi a zuciya.
    11. Wasunsu girman jikinsu ya zarce tambaya,
    Wane namu har wa yau sun fi mu ƙarfin tsiya.
    12. Misali ɗau Raƙumi da Sa har da sha bugu,
    Da doki ya ‘yan uwa mu zam yin tunaniya.

    13. Allah ya hore mana muna sarrafa su duk,
    Ta duk yadda munka so muna masu fariya.
    14. Amanar su Rabbi ya aje gun mu mun shina,
    Domin jin daɗi namu mu bauce shi shi ɗaya.
    15. Abin ban takaici shi ne yadda muke musu,
    Mugunta da cin zali da dukan bulaliya!
    16. Ina mai sakin dabba kiwon Allah ya isa?
    A ran lahira wallahi kai za a tambaya.
    17. Ina mai aje kare da kyanwa wuri nasa,
    Ya kasa ciyar da su sai dai sui ta shan wuya?

    18. Ina mai lafta wa jaki kaya niƙi-niƙi,
    Ya daure yana tafe amma ga dukan tsiya?!
    19. Ina mai barin yara su kamo tsuntsu da ma,
    Sarkin-ƙwai domin wasa da su ba shi tausaya?
    20. Ina masu ragaita da dabba don su sayar,
    Ba ci sai galabaita ga zafi na shamsiya?
    21. Ina masu taskace ta dabba su killace,
    Ba ci ba fita ta nemi nata a rariya?
    22. Ina mai zama ƙoto kare na zaman suɗi,
    Farko ya hana shi ga bugu babu zanbiya?

    23. Ashe ba mu yin tsai mu tuna duk halittuka,
    Na Allah ne mu da su don Allah mu tausaya.
    24. Mu bar zaluntar dabba da tsuntsu da ƙwaruka,
    Allah za ya tambaye mu ranar hisabiya.
    25. Dukkansu rai ne da su jin daɗi suke biɗa,
    Kamar mu da ‘yancin rayuwa har da wataya.
    26. Idan ka aje dabba ka cishe ta kowashe,
    Ruwa mai kyawu ba ta a kwano kwatarniya.
    27. Lallai kar ka cuce ta da duka ko razani,
    Ko kyara da zagi in ka yo su tana jiya.

    28. Idan kai mai kiwo ne yawansu ya kai zuwa,
    Nisabin zakka ka fid da ta banda noƙiya.
    29. Manzo ya hana wahal da dabba a lokacin,
    Yanka ta ka zam wasa wuƙa kar ta sha wuya.
    30. Bayanin na nan a “Arba’una” da mun biya,
    Hadisi na sha bakwai ku duba shi bai ɗaya.
    31. Amma fa ku san kashe kunama halal yake,
    Da ɓera ɓarawon nan Hankaka Macijiya.
    32. Kare mai hauka a kar shi Kura da ma Tsaka,
    A duk inda an gan su kashe su halaliya.

    33. Don Allah mu tausaya wa dabba a kowashe,
    Mu ma sai Allah ya tausaye mu ran tambaya.
    34. Kiwo sai an haƙuri don Allah mu tausasa,
    Ku san babu hankali ga dabba haiwaniya.
    35. Abin duk da ka ciyar da dabba ai sadaka,
    Ake ba ka ladanta mu zam yin rigeniya.
    36. A nan zan tsaya da wagga waƙa ya ‘yan uwa,
    Ya Allah ka yafe mu kurenmu gaba ɗaya.
    37. Sunana Muhammad Nasiru G. ɗan Ahmadu,
    Kano birnin Dabo masu mota da Saniya.
    38. Fa’ulun Mafa’ilun fa’ulun Mafa’ilun,
    Ma’aunin Ɗawilu ke da waƙar da na biya.

    Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.
    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Haƙƙin Maƙwabci

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Baƙar Sana’a

    Waƙa Mai Taken Baƙar Sana’a

    1. Muna godiya ga Rabbi sarki ubangiji,
    Da ya ba mu hankali yake ba mu lafiya.

    2. Salati da sallama su duma ga Musɗafa,
    Da ya ƙarfafe mu kan mu nemo halaliya.

    3. Batuna a yau baƙar sana’a ce zan faɗa,
    Da ke damun dukkanin musulmi na duniya.

    4. Sana’ar da ke zub da mutuncin mutum duka,
    Ya zam ba shi ƙima a idanu ko da ɗaya.

    5. Sana’ar da ke zubar da ƙimar Arewacin,
    Ƙasarmu Nijeriya anai mana dariya.

     

    6. Sana’ar da Manzonmu ya ce mu guje mata,

    Don kame mutuncinmu dare har da safiya.

    7. Sana’ar BARA gami da ROƘO nake nufi,

    Da yara suke yi har da manya a rariya.

    8. Akwai yara ƙolaye na ƙauye da ke zuwa,

    Birane suna bara a kowacce nahiya.

    9. Akwai masu naƙƙasa ga hannu ko ko ƙafa,

    Sun ɗauke ta lasisin bara sun ƙi moriya.

    10. Abin ban takaici wai bara har gidan giya,

    Jagora da dare ke zuwa da makauniya.

     

    11. Akwai masu yawo ma da katin asibiti,

    Suna ƙaryar ciwo za su sai wai dawa’iya.

    12. Akwai masu bin masallatai an yi haihuwa,

    Gare su suna biɗar abin yin aƙiƙiya.

    13. Akwai masu ƙaryar sun shigo Islamu wai,

    Dangi sun kore su ba abin ci da rataya.

    14. Akwai ‘yan gefen tasha suna wai kuɗinsu ne,

    Na mota bai cika ba zuwa Gombe Zariya.

    15. Akwai mata masu ɗiban yara raɓe-raɓe,

    Suna neman na abin kalaci a rariya.

     

    16. Ko ko wai kuɗin mota ne babu suke biɗa,

    Zuwa Rijiyar Zaki ta Lemo Birgediya.

    17. Kawai sai ka ga mutum ƙaƙƙarfa da lafiya,

    Bara wai yake domin macewa ta zuciya.

    18. Ran nan nai sayayya sai kawai ga wani mutum,

    Cikin duk kamala a shigarsa ba kushiya.

    19. Ya ce min “Ni ne Sharu Naira goma za ka ban,”

    Na ce ban yi niyyar sadaka sai ka zagaya.

    20. Da ƙarshe ake faɗan cewa ai halinsa ne,

    Yana ɓata sunansu sharifai ‘yan Sidiya.

     

    21. Abin tambaya ina dalili na yin bara,

    Da roƙon mutane kullu yaumin a rariya?

    22. Dalilai ba sa wuce biyu ni a nau gani,

    Macewar zuci da ƙin zakkar masu dukiya.

    23. Macewar zuci kan sanya ƙato ya langaɓe,

    Wai shi ya naƙasta ba shi neman halaliya.

    24. Macewar zuci kan sanya mata na ƙauyuka,

    A birni ba ƙodago sai yawon barar tsiya.

    25. Macewar zuci kan sa mutum yai zaman kawai,

    Ba nema sai raraka da maula duk safiya.

     

    26. Macewar zuci kan sa ɗan boko ba zai dako,

    Ko yai leburanci sai ya zauna ba moriya.

    27. Macewar zuci in tai ƙamari ke haihuwar,

    Aƙidar Allah ba ku mu samu abin miya.

    28. Rashin ba da zakkar dukiya yadda anka ce,

    A Qur’ani shi ka sa talauci annakiya.

    29. Zakka ba sai wanda an sani za a bai wa ba,

    Dukkan mai buƙata na da haƙƙi na bai ɗaya.

    30. Zakka in an fid da ta haƙƙin fuƙara’u ce,

    Lallai ne a ba su dunƙule babu wariya.

     

    31. Mece ce ɗari biyar? A ba shi dubu biyar,

    Ko goma ya ja jari ya kauce wa shan wuya.

    33. Zakka har gwala-gwalai na mata sai an fitar,

    In sun kai nisabi shekara in ta dawaya.

    33. Idan har ana bashe ta zakka a kan kari,

    Ga wanda sun cancanta roƙo za ya sanyaya.

    34. Ka ɗauki lauje ka yo ciyawa ka zam sayar,

    Shi yaf fi yawon roƙo a ba ka ko a ƙiya.

    35. Idan har ɓera sata an ce wai halinsa ce,

    Wari ne halinta daddawa babu tankiya.

     

    36. Ta yaya mutum ƙalau madokin kare da shi,

    Zai zo ma bara ka ba shi ba yin tunaniya.

    37. Roƙo bai halatta sai idan an matsu ƙwarai,

    A hanzarta bar shi in buƙata ta zam biya.

    38. Yaƙi da macewar zuci lallai a kanmu duk,

    Bara ba sana’a ce ba roƙo haramiya.

    39. A nan zan tsaya kishi Allahu ba mu shi,

    Mu zam masu dogaro da kai dukka safiya.

    40. Sunana Muhammad Nasiru G. ɗan Ahmadu,

    Baiti Arba’in na shirya wannan ƙasidiya.

     

    Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.

    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Abokin Tafiya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Abokin Tafiya

    Waƙa Mai Taken Abokin Tafiya

    1. Rabbi ban hikima basira,

    Baituka zan so na tsara,

    Kyauta aiki kan mu lura,

    Don mu ɗau hanya ta tsira,

    Duniya har ran tsayawa.

    2. Zan rubutun baituka ne,

    Kan Hadisin Musɗafa ne,

    Don misali ya saɓa ne,

    kan gudanmu a duniya ne,

    In ajal gu nai ya zowa.

    3. Ga mutum ga ‘yan uwansa,

    Su Uku da suke a gunsa,

    Zai tafi gun khaliƙinsa,

    Yai biɗar ɗaukinsu gunsa,

    Don su ne ya ƙyale kowa.

     

    4. Sai ya dubi gudansu yac ce,

    “Wane loto ya yi fauce,

    Me gare ni za ka zam ce,

    Taimaka min don na dace,

    Ban da kai ban nemi kowa.”

     

    5. Sai ya ce “Zan jinyatar ka,

    Zan tsaya nai hiddimar ka,

    In ko rai ya kau gare ka,

    Za na yo sutura gare ka,

    Zan biye ka zuwa kushewa.

     

    6. “Har da ni za ai saka ka,

    Ƙabbari a zamo rufe ka,

    Addu’a zan yo gare ka,

    San da duk an ambace ka,

    Zan tuna ka ina yabawa.”

     

    7. Wanga shi ne dangi nasa,

    Duk iyali har ɗiyansa,

    Za su ɗauke shi su kai sa,

    Sai su dawo can su bar sa,

    Fin haka ba sa iyawa.

     

    8. Ɗan uwa na biyu gare shi,

    Za ya nemi garai kira shi,

    Sai ya ce mar “Wane ga shi,

    Lokacina ya tuƙe shi,

    Zan tafi ba dawayowa.

     

    9. “Kanka nai duk rayuwata,

    Don biɗar ka na yo mutunta,

    Don na samu abin bajinta,

    Me kake amfanuwa ta,

    Yau na samu abin riƙewa?”

     

    10. Sai ya ce “Ai ni gare ka,

    Lokacin ruhi gare ka,

    Garkuwa kuma irli naka,

    Duk  buƙatu zan biya ka,

    Har ka zam ka zarta kowa.

     

    11. “In ko rai ya kau gare ka,

    Mun rabon hanya da ni ka,

    Za ka tai gun khaliƙinka,

    Ni ko ‘yan gado gare ka,

    Za su ɗau ni su zam rabawa.

     

    12. Wanga shi ne dukiyarsa,

    Wadda ya ba rayuwarsa,

    Duk wahalta ya yi don sa,

    Sun rabu bai ba shi fansa,

    Ko gare shi ya taimakawa.

     

    13. Ɗan uwa na Uku ya nema,

    Yac cane mar “Wane kai ma,

    Kai sani yau babu dama,

    Dawwamar ruhi jiki ma,

    Za na amsa kiran da anwa.

     

    14. “Me kake amfanatarwa,

    Don na zamto ƙetarewa,

    Zanguna da suke tahowa,

    Kwai haɗar da rikirkicewa,

    Zan buƙaci ka agazawa?”

     

    15. Sai ya ce “Duk inda za ka,

    Dukka zango ban barin ka,

    Tun kushewa ƙabbarinka,

    Zan cire kewa gare ka,

    Ran zuwan ‘yan tambayawa.

     

    16. “Ran tsayo gun khaliƙinka,

    In ka tashi ina biyar ka,

    Zan yiwo rana gare ka,

    Can a mizanin awonka,

    Zan shiga yai nauyayawa.”

     

    17. Wanga shi ne nasa aiki,

    Wanda ya yo shi na kirki,

    Kyautatar bauta ga Sarki,

    Kyauta niyya babu surki,

    Shi yake yin dawwamewa.

     

    18. Ko fa aiki bai yi kyau ba,

    Ya ƙazanta bai fari ba,

    Zai lazimci mutum a turba,

    Ƙabbari ba zai bari ba,

    Dole shi za yai riƙewa.

     

    19. Babu amfaninsa zai ci,

    Zai zamo babban kumurci,

    Yai ta saran sa yana ci,

    Hakka zai wanzu a ƙunci,

    Har zuwa ranar tsayawa.

     

    20. Gun awo muni na aikin,

    Sai ya rinjayi na kirkin,

    Rabbi tserar mu tafarkin,

    Muna aiki wanda kaidin,

    Shaiɗana ke shiryatarwa.

     

    21. ‘Yan uwa lallai mu farka,

    Tanadin aiki mu ɗauka,

    Wanda zai bi mu ya haska,

    Ƙabbarinmu har mu farka,

    Don fita ranar tsayawa.

     

    22. Ran da tarin dukiyarmu,

    Kaddarori dangi namu,

    Ba su amfani gare mu,

    Sai fa mai kyau ayyukanmu,

    Ba riya ba goratawa.

     

    23. Kar mu ruɗu yawan mutane,

    In a kan hanyar ɓata ne,

    Gwamma mun ɗau mai mutane,

    ‘Yan kaɗan in shiryata ne,

    Don mu samu abin riƙawa.

     

    24. Mun yi roƙo Jalla Sarki,

    Sa mu dace wajje ɗaki,

    Mui kulawar kyauta aiki,

    Don mu dawwama kan tafarki,

    Wanda ba zai karkacewa.

     

    25. Nasiru G. Ahmadu ne,

    Kowashe almajiri ne,

    Mai biɗar ƙarin sani ne,

    Shi ya saƙo baitukan ne,

    Ayyuka mui kyautatawa.

    Alhamdu lillahi.
    Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.
    Edita@rumasau-kallamu
  • Waƙa Mai Taken Ladubban Tsuguno

    Waƙa Mai Taken Ladubban Tsuguno

    1. Da sunan Rabbi mai baiwa gare mu,

                       Da nau’o’in ni’imta ba musawa.

    2. Salati da sallama ga Rasulu Ɗaha,

                       Da ya ceto mu bin hanyar ɓacewa.

    3. Cikin ni’imar da Rabbi ka yi gare mu,

                       Fitar najasa ga mu don tsarkakewa.

     

    4. In ban da haka jiki za tai zamanta,

    Guba ce wallah za tai illatarwa.

    5. A don haka gode Allah ya wajabta,

    Bisa ni’imar ga kullum mui ta yowa.

    6. Musulmi an buqƙaci ya yo ladubba,

    Ya bambanta da gayyar kafirawa.

    7. Idan ya buƙatu banɗaki ya zaga,

    Da Bismillah ake son yai shigewa.

    8. Ya sanya ƙafar hagu yayin shigarsa,

    Ya zam addu’ar tsari daga jinnatawa.

     

    9. Idan ba ka ambaci Allah shigarka,

    Al’aurarka sukan riƙa kallatawa.

    10. Hijabi naka Basmala du’a’i,

    Idan ka yi ba su duba ko tsayawa.

    11. Kada ka shiga da sunan Rabbi Allah,

    Jikin zobe waninsa an hanawa.

    12. Idan sarari ka je don tsuggunawa,

    Cikin dajin Ilahu ka zam kulawa.

    13. Ba a tsuguno a kan hanyar mutane,

    Da inwoyi na amfani ga kowa.

     

    14. Ƙasan bishiya da ‘ya’ya ta yi ban da,

    Da gefanni na gulbi mai wucewa.

    15. Da ramukka tana yiwuwa da jinnu,

    Da yin bawali ruwa mai dawwamewa.

    16. Ka nesaci duk idanu kar su gan ka,

    Ko sauti mai fita wari jiyowa.

    17. A nemi wuri da babu ruwa bisansa,

    Bai zam shi faƙo ƙasa mai taurarewa.

    18. A zancen Hausa ma an ce Mugunta,

    Fitsari kan faƙo zai fallatsowa.

     

    19. Ba a cire riguna ko janye wando,

                       Sai an yi kusan isa ƙasa za a yowa.

    20. Ba a fuskantuwar Qibla a yayin,

                       Da an tsuguna a fili mui kulawa.

    21. Hakan nan ba ta baya an hana shi,

                       In ba sutura ko banɗaki ginewa.

    22. A yayin ko fitar najasa ana so,

                       Qafar hagu za a ƙarfafa dogarewa.

    23. Ba a magana a yayin tsuggunawa,

                       Abin karhantuwa an tsawatarwa.

    24. Tsarkin bawali akan fara gabanin,

    Muhallin gayaɗi sai mui kulawa.

    25. Idan najasar ta ƙare fita a tashi,

    Kada a jima yawan nishi anaiwa.

    26. Ba a tsarki da hannun dama yayin,

    Wanke najasa hagun za ai sakawa.

    27. Ko da da Tishu ya zamto za a goge,

    A yo da hagu kafin da ruwa biyewa.

    28. Hakan ne ma bin so in ya samu,

    Gudun hannu taɓar najasa ya yowa.

     

    29. Ba a sanya ƙashi don goge najsa,

    Ko ko tutu na dabba an hanawa.

    30. Kaza da dukansa dangogin abinci,

    Da duk abu mai darajja ba a yowa.

    31. Shi ma bawali a yo Istinjimari,

    Kafin tsarkin ruwa ya zamo biyewa.

    32. A zam addu’a idan za ai fitowa,

    Da banɗaki a bayan tsuggunawa.

    33. Mu zam gode wa Allah don raba mu,

    Da duk najasa da mun zam kasayewa.

     

    34. Kaza najasar ruwa da mukai bawalta,

    Aminta don gare mu yai daɗowa.

    35. A nan zan dakata ya ‘yan uwana,

    Kurenmu Tabaraka yai garafawa.

    36. Ya Rabbi daɗo salati babu haddi,

    Ga Manzo naka jikan Hashimawa.

    37. Idan an tambayi mai tsara waƙar,

    Nasir Ahmad iri na Bukar ya yowa.

    38. Baitoci Arba’in Biyu babu waƙar,

    Dubu Biyu sha Tara Maris na yowa.

    Alhamdu lillahi

    Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.

    Karanta Tarihin Marubuci Nasiru Garba Ahmad

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Jakadan Allah

    Waƙa Mai Taken Jakadan Allah

     

    1. Allahu ba ni dubun basira mayyawa,

                                 In yi baitukan bege ga ɗan Adanani

    1. Ga munasaba ta watan Rabi’ul Lawwali,

                                 Wata na samun Sayyidul kaunaini.

    1. Kafin zuwansa duniyar ga baƙi ƙirin,

                                 Duk ta nutse a duhun ɓata tai muni.

    1. Tauhidi loton babu shi sai nadiran,

    Kaɗaita bautar Rabbu tai nuƙusani.

    1. Sai kame-kame ake cikin kogin ɓata,

    Bautar wanin Allah da bin shaiɗani.

    1. Sai zulmu ko a ina da danne haƙƙuna,

    An juya shar’un Rabbana Mannani.

    1. A wanga hali Ɗaha ya zo duniya,

    Don tsarkake ta ga dukkanin ɗuguyani.

    1. Ta tsatson ababen zaɓuwa gun Rabbana,

    Nasaba da halayen ƙwarai ihsani.

    1. Ya zo a tsarkake ba ƙazanta ko kaɗan,

    Ya girma kamamme ga duk buɗlani.

    1. Mai gaskiya aka san shi fai har baɗini,

    Da riƙon amana sun kira shi Amini.

    1. Allahu ya zaɓe shi don manzantaka,

    Ta isar da Tauhidi ga dukkan kauni.

    1. Ya ba da dukkan rayuwarsa wajen isar,

    Saƙo na Tauhidi a san gufrani.

    1. An tsangwame shi a Makka har dangi nasa,

    Da dukan Sahabbai masu bin Rahmani.

    1. Yai shekara har Sha Uku a cikin matsi,

    Laifinsa Tauhidi da ƙin ausani.

    1. Ya bar garinsa na haihuwa a bisa haka,

    Haka ma Sahabbai nasa sun hijrani.

    1. A Madinatu Yasrib ya zauna har zuwa,

    Ƙarshe na rayuwarsa bisa ga amani.

    1. Qur’ani an saukar garai don shiriya,

    Bautar Ilahu da kyauta dukkan shani.

    1. Rayuwarsa ta zam bauta Rabbil izzati,

    Koyar da Qur’ani gami da bayani.

    1. Mai tausayi ga dukan halitta ya zamo,

    Mai kyauta hulɗa ne ga duk insani.

    1. Mai yafiya ga dukan kure ne Musɗafa,

    Mai tarbiyantarwa bisa ihsani.

    1. Mai tsai da adalci ga kowa Annabi,

    Mai ƙyamatar haƙƙin wani a yi danni.

    1. Mai koya shar’a aikace don ai biya,

    Bai bar a keta umarnukan Rabbani.

    1. Mai ƙas da kai ne babu girman kai ga shi,

    Mai girmamar babba da ma sibyani.

    1. Mai yin hidimtawar iyali nasa ne,

    Haka ma sahabbansa bila firƙani.

    1. Mai son lumana ba shi son ce-ce-ku-ce,

    Bai yaƙi kowa sai bisa burhani.

    1. Mai murmushi ne shi ga kowa Sayyadi,

    Kowa gare shi yana zuwa ya yi zauni.

    1. Mai yin du’a’in shiryuwar umma yake,

    Don sauƙaƙar tsayuwa gaban Rahmani.

    1. Kyawun halinsa ya ba Sahabbai kwaikwayi,

    Suka ɗabbaqa su a ko’ina ba zanni.

    1. Sun tarbiyantu gare shi baban Ƙasimu,

    Suka yaɗa Tauhidi a ƙauye birni.

    1. Sun keta dazukka Hamada sun isar,

    Sun ƙetare Kogi da dukkan Tsauni.

    1. Haka Tabi’ai suka bi a wannan hidima,

    Ta yaɗa saƙonnin farin addini.

    32.Matsayinsa gun Allahu mai girma yake,

    Tamkar ya shi babu cikon Manzanni.

    1. Duk Manzani izuwa mutanensu kaɗai,

    Ya taƙaita saƙon Rabbi kan imani.

    1. Shi ko Rasulullahi dukkan duniya,

    Allah ya ce ya isar da Alqur’ani.

    1. Haiwanu dabbobin tudu da na Maliya,

    Bayan dukannin ‘yan Adam wal Jinni.

    1. Ceto a ranar tsayuwa shi za a ba,

    Farko gabanin dukkanin Manzanni.

    1. An ba shi tafkin Kausara mai waraka,

    Ga dukan ƙishi Manzo jinin Adanani.

    1. Saƙon da an masa ya isar mun tabbata,

    Kamar da Rabbi ya ba shi ba nuƙusani.

    1. Musulunci ya ratsa dukannin duniya,

    Lungu da saƙo sai tilar Qur’ani.

    1. Ya Sayyadi baban Ruqayya da Ɗayyibu,

    Mun shaida ka yi isar da duk saƙonni.

    1. Ya mai yawan zikiri da bautar Rabbana,

    Mun yarda Allah ɗai yake Wahadani.

    1. Ya mai yawan jinƙai ga dukkan talikai,

    Ka ceci al’umma ga bin ausani.

    1. Ya Sahibas Siddiƙi Umar naka ne,

    Suruki wajen Usmanu Zun-Nuraini.

    1. Ya surukin Haidar Aliyu mazan ƙwarai,

    Kakan tagwaye Alhasan da Husaini.

    1. Ya wanda zai karɓi Luwa’ul Hamdi ran,

    Tsayuwa ga Allah Sahibat Tijjaani.

    1. Ya wanda zai ceci Musulmi na ƙwarai,

    Ranar hisabi da awon mizani.

    1. Ya Sayyadi Allah muke roƙo ya sa,

    Mu mutu bisa ga biyar Kitab was Sunni.

    1. Ya Abba Fatima Albatulu Habibuna,

    Allah ya ba mu zama da kai a Jinani.

    1. Allah muna yin hamdala munka zamo,

    A cikin Musulmi khiiratul adyani.

    1. Allah ka tsai da mu siraɗul mustaƙim,

    Izuwa macewa kar mu zam khusrani.

    1. Allah ka dumata zuciyarmu bisa biyar,

    Manzo naka da ka bai wa Alqur’ani.

    1. Allah muna a cikinsa ƙarshen zamani,

    Mai haɗari da yawan biye shaiɗani.

    1. Allah tsare mu da makarul a’adaa’i,

    Na son mu raunata har mu bar imani.

    1. Allah ka dawwama son Rasulu a zuciya,

    Ya zamo abin koyinmu dukka shu’uni.

    1. Begen masoyi ya halatta ga taliki,

    Balle Rasulu da Rabbi ya yi umarni.

    1. Yabon gwani ko wajibi haka anka ce,

    Manzo gwani na gwanaye ne ba zanni.

    1. Aikin da ya yi wa duniya tamkar ya shi,

    Ba a yo ba har yau in akwai wane ni?

    1. Kullum salati gare shi kar mu sake da yi,

    Guzuri gare mu manauyayin mizani.

    1. Sallaa alaikallahu ya khairal bashar,

    Wa ’Alika wa Sahabi wal ikhwani.

    1. Mai tsara waƙar Nasiru G. Ahmadu,

    Mai son Rasulu hasanarsa da rauni.

    Alhamdu lillahi.

    Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.

    Karanta Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Take

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Ta 2 Ga Farfesa Mu’azu Sa’adu Muhammad Kudan

    Waƙa Ta 2 Ga Farfesa Mu’azu Sa’adu Muhammad Kudan

    Daga Salmanu Faris Kudan, Shugaban Ƙungiyar Marubutan Arewa ta Ƙasa Nijeriya

    1.

    A yau mun taru cikin alkunya,

    Domin girmama gwarzonmu mai dubayya,

    Haske ya sake yalwata cikin Hausaniya,

    Da samun Farfesa Mu’azu a mai kyan halayya.

    2.

    Ka jima kana hura wutar hikima,

    Kana tsarkake harshenmu ba taƙama,

    A makarantu sun ɗauki darusa ba gardama,

    Sun zame wa ɗalibai hasken tafarki mai tsunduma.

    3.

    Mu’azu Sa’adu, ginshiƙin Hausar mu ta dauri,

    Ka ɗaukaka harshen da kakanni suka bari.

    A yau an saka maka rawanin girma tuturi,

    Ka zama damina mai sanyaya shuka ba fari.

    4.

    Salmanu Faris Kudan na taya ka murna,

    Da wannan matsayi mai jan hankalina,

    A madadin marubutan Arewan zaurena,

    Muna yi maka fatan ƙarin nasarori da zayyana.

    5.

    Girmanka ya zama abin jingina ba wariya,

    Ƙwararrun marubuta suna sanya ka a zuciya.

    Ka zama tubalin da ya ƙara ɗaure ginin Hausaniya,

    Harshen da ke ɗaukaka Arewa da Nijeriya.

    6.

    Muna yi maka addu’ar fatan alheri,

    Rayuwa mai cike da ƙarin annuri.

    Allah Ya saka maka cikin mafi alheri,

    Ya ƙara nisan kwana bisa tsari.

    Karanta Waƙar Murnar Zama Farfesa Ga Mu’azu Sa’adu Muhammad

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙar Murnar Zama Farfesa Ga Mu’azu Sa’adu Muhammad

    Waƙar Murnar Zama Farfesa Ga Mu’azu Sa’adu Muhammad

    Daga Salmanu Faris Kudan, Shugaban Ƙungiyar Marubutan Arewa ta Ƙasa Nijeriya

    1. A yau Arewa ta wayi gari da annuri,

    An kunna fitilar da ta daɗe da alheri,

    Gwarzon ilimi Mu’azu Sa’adu mai annuri,

    Ya ɗaukaka harshe cikin nutsuwa bisa tsari.

     

    2. Ranar nan ta zamo alfahari ga dukkanmu,

    An ɗaga rawani a kan ƙashin kaifin basirarmu.

    Ka hau kujerar Farfesa cikin ladabinmu,

    A ɓangaren harshen Hausa mai cike da tarihinmu.

     

    3. Ka zama jagoran harsunan Nigerian Languages,

    A Jami’ar Sule Lamiɗo, Kafin Hausa mai darajas.

    Ka ɗauki nauyin harshe da ƙarfin halis,

    Kana koya wa duniya kima da martaban Hausas.

     

    4. Ka reni ɗalibai da armashi da hikima,

    Ka zuba ilimi kamar ruwan sama.

    Darussanka sun zama turakun hawa sama,

    Sun gina ƙarni masu zuwa tun kafin anjima.

     

    5. A fagen nazari ka zama tamkar tauraro,

    Kana haskakawa masana masu sauraro,

    Littattafanka sun zama ginshiƙai abin dogaro,

    Duk inda ake Hausa, za ku taho har ɗan goro .

     

    6. Ka zama madoga ga marubutan Arewa,

    Mai tsarkake harshen har da rera wa,

    Ka zama ginshiƙi da ba ya dusashewa,

    Wanda ya daidaita harshenmu cikin dubawa.

     

    7. Ni Salmanu Faris Kudan, mai buƙata,

    Na miƙa wannan waƙa a madadin marubuta,

    Mu na yi maka barka da wannan babban kyauta,

    Allah Ya ƙara maka lafiya ban da kunyata.

     

    8. Rayuwarka ta zama izina ga matasa,

    Ga waɗanda ke neman hasken don yai tasa,

    Ka nuna musu cewa aiki ne jawur ga matasa,

    Su ne hanyoyin da ake hawa don tasa.

     

    9. Duniyar Hausa ta yi murna da annushuwa,

    Ta ƙara jin ƙima da samun ɗaukakawa,

    Nasara irin taka ta zamo abin dubawa,

    Ga duk mai son zama abin koyi a rayuwa.

     

    10. Malam Mu’azu, Allah Ya yi maka albarka,

    Ya ƙara nisan kwana da nutsuwa a gare ka,

    Ya zuba hikima wacce ba ta yankewa gare ka,

    Ka ɗaukaka fiye da yadda kake yanzu da albarka.

    Danna nan don karanta Tsokaci A Kan Littafin Salmanu Da Salma

    Edita@rumasau-kallamu

  • Matsayar Ɗanbala

    Matsayar Ɗanbala

    Lokacin da muke da manya,
    Lau muke ba a kashe wa.

    Zamanin da muke da manya,
    Babu bandits kaf Arewa.

    Sa’ilin da muke da manya,
    Babu kinafas Arewa.

    Lokacin da akwai su Baba,
    Duk da tarbiyya Arewa.

    Zamanin Ulama’u na nan,
    Babu mai kafurta babba.

    Lokacin da muke da manya,
    Ba mu yin rigima Arewa.

    Lokacin da su Inna na nan,
    Kanmu ɗai yake ba rabe wa.

    Lokacin Malamai su na nan,
    Ƙanƙana na bin na gabba.

    Lokacin su Waziri na nan,
    Malamai ba su fanɗare ba.

    Lokacin da muke da manya,
    Ba mu san Boko Haram ba.

    Zamanin da akwai mazaje,
    Ilimi namu bai zube ba.

    Lokacin da su Kawu na nan,
    Tsintsiya muke ba kawai ba.

    Yanzu da yake babu manya,
    Ba mu san asalin gabas ba.

    Yanzu da yake mun rasa su,
    Sai kashe mu ake Arewa.

    Yanzu da yake babu babba,
    Ƙanƙana ke zage babba.

    Tun da mun yi rashin su Inna,
    Dole mui ta ganin mu baibai.

    Kuma da yake ba magaji,
    Shi ya sa mu muke ta ɓarba.

    Babu babba a yau Arewa,
    In akwai sunansa kama.

    Na faɗa maka babu babba,
    In akwai ka kira shi yanzu.

    Da a ce ko muna da manya,
    Da ba mui ta ganin hakan ba.

    Da a ce da akwai su Baba,
    Ƙanƙana ba su zagi babba.

    Da da wanda muke jin tsoro,
    Da ba mu raba al’umma ba.

    Shehu Khalidu babu babba,
    Yanzu kaf a cikin Arewa.

    Wanga ita ce fahimta ta,
    Ko a gobe ina faɗa ma.

    Da da babba a yau Arewa,
    Da ba zan yi musun hakan ba.

    Ɗanbala daga Borno ne ni,
    Mai yabon a wurin Masoyi.

    Ɗan Amina abin nufina,
    Na riƙe shi ba zan shika ba.

    Ahlihi nasa na riƙe su,
    Ba riƙon igiya na yo ba.

    Da Sahabu ina biyan su,
    Ban da masu kiran gumaka.

    ©
    Mohammed Bala Garba
    6:39pm
    30 November, 2025.

    Karanta Ta’aziyyar Hauwa Ƙamshi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ta’aziyyar Hauwa Ƙamshi

    Ta’aziyyar Hauwa Ƙamshi

    1. Rabbana Sarki Ilahu,
    Rabbi mai tayar da ruhu,
    Rabbi ga baiwarka Hauwa.

    2. Babu mai tsarki ya naka,
    Babu mai rahama kamarka,
    Rabbi kai rahama ga Hauwa.

    3. Babu mai jin ƙai kamarka,
    Babu mai tausai irin ka,
    Don Rasulu ka dubi Hauwa.

    4. Duk Karamci na wurinka,
    Ragwame ita ce sifarka,
    Rabbi rangwantawa Hauwa.

    5. Yadda duk ka yi babu mita,
    Ba mu jayayya da yin ka,
    Rabbi kai rahama ga Hauwa.

    6. Hauwa Ƙamshi jaruma ce,
    Babu shakka malama ce,
    Mai rubuce-rubuce Hauwa.

    7. Rabbi duk an mata shaida,
    Kamila ce mai ibada,
    Sayyada laƙabi na Hauwa.

    8. Rabbi ta yabi mai Madina,
    Kuma ta yi riƙon amana,
    Sa Rasulu ya san da Hauwa.

    9. Rabbi kai rahama gare ta,
    Rabbi kai jin ƙai wurin ta,
    Rabbi don kakarmu Hauwa.

    10. Rabbi sanyaya kabarinta,
    Rabbi kyautata kwanciyarta,
    Faɗaɗa shi saboda Hauwa.

    11. Sa Rasulu ya zo gare ta,
    Sa ya yo murnar zuwanta,
    Har ya ce “sannunki Hauwa.”

    12. Hauwa sai mun zo gare ki,
    Wataran za mu biyo ki,
    Za mu sadu ki ji ni Hauwa.

    13. ‘Yan uwa nai ta’azziya,
    Marubuta ga marsiyya,
    Na ta’aziyya ta Hauwa.

    14. Rabbana ka daɗo salati,
    Gun Habibu da yai wafati,
    Shi masoyi ne ga Hauwa.

    15. Ɗanbala suna Mohammed,
    In ka so ka kirani Ahmed,
    Ke ta’azziya ta Hauwa.

    ©
    Mohammed Bala Garba
    12:03pm
    2 October, 2025.

    Karanta Gyara Kayanka

    Edita@rumasau-kallamu

  • Gyara Kayanka

    Gyara Kayanka

    Rabbana tuba nake yi,
    Nayi saɓo ba kaɗan ba.

    Na yi alƙawari gare ka,
    Zan yi bauta ba da ɗar ba.

    Dana zo shaiɗan ya ja ni,
    Ban yi bautar ko kaɗan ba.

    Ya raba ni da kai masoyi,
    Bai bari na zaunu lau ba.

    Ya hana ni saninka Allah,
    Bai bari nai ilimi ba.

    Shi yake ta zuga gare ni,
    Ko zumunta ban idar ba.

    Ka hana ya sa ni nayi,
    Ban tunanin zunubai ba.

    Ka umarta ya hana ni,
    Bai bari na aikata ba.

    Ya haɗa ni Walidaina,
    Ba su yo fahari da ni ba.

    Nai wulakanci ga bayi,
    Ban ragwantawa na jini ba.

    Kuma na yayyaɗa karya,
    Ban ko binciki gaskiya ba.

    Na yi sata na yi karce,
    Ban ji tausan ‘yan uwa ba.

    Na yi zunɗe na yi gulma,
    Nai harara ba kaɗan ba.

    Na yi zamba cikin amince,
    Duk da dai ba ka fallasa ba.

    Na yi shaidar zur a fili,
    Ban tunanin mutuwa ba.

    Kana na ha’inci bayi,
    Har maƙwabta ban bari ba.

    Rabbi nai wasa Sallah,
    Ban yi san da kace a yo ba.

    Ka haramta na halarta,
    Ban zaton haɗuwa da kai ba.

    Babu mai ikon hana ni,
    Ko ya ce nayi ba da ni ba.

    Duka na’u’o’in kaba’ir,
    Ɗanbala bai bar guda ba.

    Duniya ita ce ƙawata,
    Ko da ɗai ba ta kunyatan ba.

    Ban tunanin za na ƙaura,
    Gunka wai domin na tuba.

    Ba shiri mutuwa ta zo min,
    Ba ta yo sallama da ni ba.

    ‘Yan uwana nata kuka,
    Ba su so mutuwa a nan ba.

    Suka min suturar Musulmi,
    Ba su ce Allah tir da ni ba.

    Har waɗanda na yi wa cuta,
    Suka zo mini ba kaɗan ba.

    Suka min sallah da roƙon,
    Gafara ba su gajiya ba.

    Suka kai ni cikin kushewa,
    Addu’a ba su daina yi ba.

    Suka juya za su koma,
    Nai kiran ba su waiwayo ba.

    Daga nan na gano bala’i,
    Ban zaton haka a ciki ba.

    Ga duhu zafi macizai,
    Ko kaɗan ba su tausayan ba.

    Sai Mala’iku sukka zo,
    Ba su yo sallama da ni ba.

    Suka min wasu tambayoyi,
    Ban ko amsa guda ciki ba.

    Daga nan na shige masifa,
    Wanda ban yi zaton gani ba.

    ‘Yan uwana sai mu farga,
    Duniya ba gun zama ba.

    Za mu girbi abin da mukkai,
    Walla ba maganar wasa ba.

    Rabbana shirye mu Allah,
    Rabbi ba don nai batu ba.

    Har iyayye da ‘yan uwana,
    Da Musulmai ban baro ba.

    Rabbana ninko salati,
    Ga Rasulu ba ka ƙi ya ba.

    Ɗanbala daga Borno yai ta,
    Ɗan Bahaushe ba Ibo ba.

    ©
    Mohammed Bala Garba
    8:27pm
    13 August, 2024

    Karanta Duka A Murɗe

    Edita@rumasau-kallamu