Menene Yake Jawo Fitar Farin Ruwa Daga Gaban Mace,Wannene Na Cuta Wannene Na Lafiya

0
99

Farin ruwa(white discharge) wanda ke fitowa daga farji ko azzakari,a lokacin sha’awa ko da lokacin jima’i ko bayan jima’i,akwai farin ruwan da yake fita daga farji domin taimakawa mace wajen jima’i.

Misali akwai wani nauyin farin ruwa da ake kira da (cervical mucus)shi idan ya fita yana wanke farji tare da ƙara masa santsi,ya zama kamar an shafa masa wani mai me yauki

sannan akwai wani ruwa wanda ake kira da (Penile fluid) wanda ke fita ta cikin bututu ɗaya da fitsari yana fita hanya daya da fitsari.

Wadannan ruwaye idan aka ga sun fita ba komai bane lafiya ce,a wasu lokuta,fitar ruwan yana nuni da cewa mutum ya kamu da cutar infection ne

Domin bayani akan Gyambon Ƙoda [Pyelonephritis] Danna nan

Fitar Farin Ruwa Lokacin Da Mace Taji Sha’awa

Sha’awar jima’i shine sanadin farin ruwa da farjin mace mafi yawanci lokaci,kuma wannan ruwa yana fita fari mai haske,wannan ruwan yana tsaftace da bata kariya ga farji.

Lokacin da mace daji sha’awar jima’i,wannan ruwan yana karuwa tare da fitowa daga gaban mace,kuma indai mace ba zafi take ji wajen jima’i ba wannan ruwan fitar sa ba komai bane face lafiya 

Fitar Farin Ruwa Lokacin Da Al’ada (haila) Tazo (Menstrual Cycle}

Ba matsala bane mace taga farin ruwa a lokacin da al’ada  tazo ko kuma a karshen al’adar tata,a lokacin ovulation lokacin da ƙwan haihuwar mace ke fita,farin ruwa na fita daga gaban mace kalar sa kuma kamar farin dake cikin danyen ƙwai sannan idan akai jima’i a wannan lokacin na ovulation za’a iya ganin wannan farin ruwan hatta akan azzakari.

Ganin Farin Ruwa Bayan An Gama Jima’i

Idan mace tana ganin farin ruwa bayan an gama jima’i da ita,to wannan lallai ba ta da infection a tare da ita,a takaice wadan nan suna wasu daga cikin lokotan da mace zata iya ganin farin ruwa yana fita daga gaban ta,ina fatan kuma yan uwa sun karu da wannan dan takaitaccen bayani nawa

Domin karanta Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki Danna nan

labarin da ya wuceDalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki
Labarin na GabaHalayen Dake Haddasa Lalacewar Ƙoda [Kinney Dx]