Falalar Karatun Al- Kur’ani

0
28

An karɓo daga Abu Umamah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Ku karanta Alƙur’ani saboda haƙiƙa zai zo rana alƙiyama zai ceci ma’abotansa.” (Muslim: 804) 

An karɓo daga Abdullahi Ibn Amr As (Radiyallahu Anhu) yace: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya karanta harafi daga littafin Allah, Za a ba shi kyakkyawan (Lada) ga kowane harafi, za a kuma ninka kowane lada sau goma. Ba ina cewa Alif lam mim harafi ɗaya ke nan ba, a’a Alif harafi ɗaya, Lam harafi ɗaya, Mimun harafi ɗaya”.(Tirmizi: Sahihul Jami’i 6469).

FALALAR FATIHA 

An karɓo daga Abu Sa’id Ibnul Mu’alla (Radiyallahu Anhu) yace: Na kasance ina salla a masallaci sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kira ni. Sai ban amsa ba, sanna sai na je wajensa na ce salla nake yi. Sai ya ce: “Shin Allah bai ce: ” Ku amsawa Allah da Manzonsa ba idan suka kira ku? 

Domin karanta bayani akan Falalar Kuka Ranar Ashura Danna nan 

Sai ya ce: zan sanar da kai surar da ta fi kowace saura girma a cikin Alƙur’ani kafin ka fita daga masallaci”. “Sai ya riƙe hannuna, da muka kusa fita sai na ce: “Ka ce za ka sanar da ni saurar da ta fi kowace sura girma a cikin Alƙur’ani, sai ya ce:”Ita ce Alhamdu lillahhi rabbil alamin; Ita ce(Mai ayoyi) bakwai da maimaitawa kuma itace Alƙur’ani, mai girma da aka ba ni” (Bukahri: 4202). 

FALALAR SURATUL BAƘARA 

An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “kada ku mayar da gidajenku kamar maƙabarta, Haƙiƙa Shaiɗan yana gudu daga gidan da ake karanta Suratul Baƙara a cikinsa”. (Muslim 708). 

An karɓo daga Abu Umamah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa ya ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “ku riƙa karanta suratul Baƙara saboda riƙo da ita albarka ne, barinta nadama ne, kuma matsafa basa iyawa da ita”. 

(Muslim 804) Wato karanta suratul baƙara yana maganin sihiri da tsafi da kuma sharrin shaiɗanu. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

FALALAR KARANTA AYATUL KURSIYYU 

An karɓo daga Ubayyu ɗan ka’ab (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ya baban Munzir, Shin ka san wacce aya ce mafi girma a cikin Al-ƙur’ani? Sai na ce: Allahu laa ilaha illa huwaL hayyul ƙayyum” ya ce: Sai ya bugi ƙirji na ya ce:

Ina taya ka murnar ilimi, ya baban Munzir (Wato yana taya shi murnar sanin hakan). 

FALALAR KARANTA AMANAR RASULU 

An karɓo daga abu Mas’ud Albadri (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce “Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Baƙara a cikin dare sun isar masa” (Bukhari: 3786, muslim 807). 

Malamai sun bayyana ma’anar “sun isar masa” da cewa za su zama garkuwa a gareshi daga dukkan sharri, ko kuma za su tsaya a masa a matsayin ƙiyamul laili”. 

FALALAR AYOYI GOMA NA FARKON KO ƘARSHEN SURATUL KAHFI 

An karɓo daga Abu Darda’i (Radiyallahu Anhu)Haƙiƙa Annabin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya haddace ayoyi goma na farkon Suratul Kahafi, za a kare shi daga Dujal” (Muslim 809) A wata ruwayar ayoyi goma na Ƙarshen suratul kahfi. 

FALALAR TABARAKALLAZI BIYADIHIL MULKU 

An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: haƙiƙa wata sura a cikin Alƙur’ani mai ayoyi talatin ta ceci wani mutum har sai da aka gafarta masa, ita ce: “Tabarakallazi biyadihil mulku” (Abu Dawud, Tirmizi, Nisa’I Ibn Majah, Sahihul Jami’i 2091). 

FALALAR ƘULHUWALLAHU AHAD 

An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) yace: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: ” Ku taru zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, sai waɗanda suka haɗu suka haɗu, Sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fito sai ya karanta “ƙulhuwallahu Ahad”.

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Sannan ya shiga gida, sai muka ce da junanmu muna zaton wahayi ne ya zo masa daga sama, shi ya sa ya shiga gida, sai ya fito ya ce haƙiƙa na ce da ku zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, ku faɗaka haƙika ita (ƙulhuwallahu tana daidai da ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani”. (Muslim 812). 

FALALAR FALAƘI DA NASI 

An karɓo daga Uƙubatu ɗan Amir (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ba ka ga waɗansu ayoyin da aka saukar da su jiya da daddare ba, ba a taɓa ganin irinsu ba”. Sune ƙul’a’ uzu bi rabbiL falaƙi” da ƙul’a’uzu birabbinnasi” (Muslim 814). 

FAƊAKARWA 

Ina nasiha da ba da shawara ga ‘yan uwa musulmi da mu kula sosai da Alƙur’ani ta wajen haddace shi, da yawan karanta shi, da koƙarin fahimtar ma’anonisa da kuma yin aiki da shi domin samun tsira da arziki da wadata a duniya da lahira. 

Allah ka sa mu dace, Allah ka sanya mu zama ahalinka a halin Alƙur’ani. Amin.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceFalalar Ciyarwa Shayarwa Da Tufatarwa
Labarin na GabaFalalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana