Falalar Gaggauta Shan Ruwa

0
77

SALMANU FARISS ADAMU

Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla) ya koya mana amfanin gaggauta shan ruwa ga mai azumin farilla da nafila, saboda irin alheri da ke cikinsa, kamar yadda wannan hadisin ya nuna mana;

حدثنى يحي عن مالك عن أبى حازم بن دينار عن سهل بن سعد الساعدى, أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال” لا يزال الناس بخير ما عجلواالفطر”

An ruwaito daga Yahaya daga Malik daga Abi–Hazim bin Dinari daga Sahlu bin Sa’adu Assa’ida, haƙiƙa ba su gushe ba da cikin alheri ba matuƙar suna gaggauta buɗe baki (shan ruwa).

Ma’ana akwai dalili masu matuƙar amfani a cikin wannan hadisin, wanda yake koyarwa kamar haka; saɓawa yahudawa da Nasara, saboda sun kasance suna jinkirta shan ruwa idan sun yi azumi, haka ma gaggauta shan ruwa sunnar annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla) ce. Kamar yadda ya zo a cikin wannan hadisin;

حدثنى مالك عن عبدالرحمن بن حرملة ألأ سلمى عن سعيد بن مسيب, أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال ” لا يزال الناس بخير ما عجلواالفطر”

An ruwaito daga Malik daga Abdulrahman bin Hurmal Al-assalami daga Sa’idul bin Musayyib (shugaban maruwaita), haƙiƙa Monzan Allah (Sallallahu alaihi wasalla) yace: “mutane ba za su gushe ba da aikin aheri, matuƙar suna gaggauta buɗe baki (shan ruwa)”.

حدثنى مالك عن إبن شهاب عن حميد بن عبدالرحمن أن عمربن الخطاب و عثمان بن عفان كانا يصليان المغرب حين تنظر إلى اليل الأسود ,قيل أن يفطر ثم يفطر أن الصلاة وذلك في رمصان .

An ruwaito daga Malik daga ibin shihabi daga Humidu bin Abdullah (yace) haƙiƙa Umar bin khaɗɗab da Usman bin Affan (R.A) sun kansance suna yin sallar Magriba a lokacin da dare ya yi baƙi (duhu) kafin su sha ruwa, sannan sai su sha ruwa bayan sun yi sallah (Magariba) wannan kuma ya kasance a cikin watan Ramadan ne.

Amma magana mafi shahara wanda kuma babban malamin nan ya tafi a kai (Imam Malik bin Anas) shi ne gaggauta shan ruwa kafin a yi sallar Magariba, Saboda haka ne ya kamata a ce a cikin masallatan mu a dinga bari mintuna biyar (5) bayan an kira sallah, saboda mutane su samu falalar aikata sunnar annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla), ba wai kawai ana gama kiran sallah ba, sai a tayar da sallah, amma idan an yi hakan, sallah ta yi sai dai ba a aikata sunnar annabi ba ga me azumi da sauransu.

Domin karanta Dalilan Wajabcin Ramadan danna nan 

Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceSharaɗan Ingancin Azumi
Labarin na GabaFassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya daga Masallaci mai Alfarma 14th March 2025