Ina Cikin Sallah Sai Na Tuna Akwai Najasa A Zani Na, Yaya Zanyi?

0
1388

Tambaya

Aslam alaikum malam.lokacin sallah ne yayi naje nayi alwala na tada sallah to inacikin sallah sai na tuna Akwai Najasa a zani na, dan Allah yaya zanyi zan sake sallar ne KO yaya⁉

Amsa:

Wa’alaikumus Salam Warahmatullah, irin wannan tambayar anyiwa SHEIKH ABDLH IBN ABDIRRAHMAN AL-JIBRIN ga amasrda yabayar.

Wanda yayi salla da najasa kuma da saninsa sallarsa tabaci, in kuma bai saniba sai bayan yasallame to sallarsa tayi ba’a lazimta masa biyaba.

Amma in yana kan sallan sai yasan akwai najasa atufarsa- inzai yiwu yacireta dawuri yaci gaba da sallarsa to ya halatta, domin ya tabbata ANNABI SAW yana salla watarana da takalmi sai Mala’ika JIBRIL yasanar dashi akwai najasa a takalman.

Nan take yacire takalman yacigaba da sallarsa batareda cewa farkon sallarda yayida takalmin ya lalaceba, hakama in yatuna najasar yana jikin rawaninsa sai yacire rawanin yacigaba da sallar.

Amma idan cire abinda yake dauke da najasan yana bukatan dogon aiki kamar kwabe riga ko wando ko makamancin haka- to bayan ya kwabe yafara salla daga farko.

Don haka baiwar ALLAH kinga cire zani da sauya wata zanin adaura dogon aikine, sai kicanza kifara salla daga farko,
BARAKALLAHU FEEK.

Domin sanin nasabar manzon allah danna koren rubutun nan

BAR AMSA

Please enter your comment!
Please enter your name here