Jan Hankali Game Da Sallar Asuba

0
572

Sallar Asuba itace mafi Alheri fiye da barci, mu rage barci don mu ribanta da goben mu.

Barci amsawar zuciya ne; ita kuwa sallah amsawar kiran Ubangiji ne.

Barci mutuwa ne; ita kuwa sallah rayuwa ce.

Shi barci hutu ne na gangar jiki; sallah kuwa hutu ne na ruhi.

Shi baci, da mumini da kafiri duk suna yinsa ita kuwa sallah mumini ne kaɗai yake yinta.

Masu tashi lokacin futowar Alfijir sun rabauta, fuskarsu kuma ta haskaka; goshinsu kuma yayi haske da ƙyalli, lokacin su kuma yayi Albarka. Idan kana cikinsu toh ka godewa ALLAH daya fifita ka, idan kuwa baka cikinsu toh ka roƙi ALLAH Ya saka ka cikin su.

Amma menene yafi Alfijir kyau?

Farillarsa (Sallar Asuba) zata saka ka acikin kulawar Ubangiji

Sunnarsa (Rak’ataanil fajr) ta fi Duniya da abinda ke cikinta (Hadeeth)

Ita Sallah Asuba da Mala’iku masu dutyn dare; da Mala’iku masu dutyn safe duka suna Halartar ta. Ya kai ɗan’uwa, ya ke yar’uwa, kisani fa kaima kasani duk wanda ya rayu akan wani toh akansa zai mutu, wanda ya mutu kan wani aiki kuma akansa za’a tashe shi.

Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Raka’atil Fajr danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Nafilolin Sallah danna nan.

labarin da ya wuceIslamiya Daɗi
Labarin na GabaAbinda Ya Kamata A Sani Game Da Kabeji (Cabbage)